Ticker

6/recent/ticker-posts

Makauniyar Shari'a [Kashi na 1]

Ya Allah ina godiya da bisa dukan ni'imominka a gareni. Yanda na fara Lafiya ka ba ni ikon gamawa Lafiya. Alkhairan da ke cikinsa ka ba ni ladansa, sharrin da ke ciki ka yafe min.

Allah ka dauka Alkalamin marubuta a duk in da suke

Gaisuwa ta musamman gareku na hannu dama ta.

 • Besty (Sarat Alkasum)
 • Maman Amatullah
 • Ummu shkura
 • Fadila Sani Bakori
 • Maman Sharifa
 • Mamashu
 • ABBA Yakubu
 • Dan Salma
 • Da Autan Jarumai.

Waɗanda ban samu damar kiran sunansu ba, duk ina mika sakon gaisuwata a gare ku.

Yayyena abun Alfaharina

 • Hadiza
 • Hussaina
 • Hassana
 • Maryam

Gaisuwa ta mussaman gareki

Anty Zulai, mutan Kano, surukar Auta na.

Jarumai Writers Association, marubuta masu aiki da Jarumta wajen Fadakar da Al'umma

MAKAUNIYAR SHARI'A

MAKAUNIYAR SHARI'A

IKILIMA ADAM (Kyauta daga Allah)

09069080725 ko +22953726162 (Whatsapp kaɗai ban da kira)

Marubuciyar da ta nishaɗantar da ku a littattafanta kamar haka:

 1. Kai ka ja wa kanka
 2. Kanwata
 3. RAI DAYA (Jan Za ki)
 4. RUDANI (mai tafiya daukan rai)

Da sauran su.

Yanzu ga ni ɗauke da sabon littafina mai suna MAKAUNIYAR SHARI'A

SHAFI NA ƊAYA

Ahankali take bin kusurwa na jejin tana tafiya cikin wahalilliyar azabar ciwon baya da ya sa take taku kamar wacce aka daura wa kaya a bayan ta, ba tare da ta ankare ba, tsohuwar kofin da ke hannun ya fadi kasa wargas, nan dan nan idanunta, suka cika da ruwan hawaye, cikin rawar murya ta ce, " Washh bayana ta ya zan durkushe daukar wannan kofin ". ta kai karshen zancen cikin rawar murya, lokaci daya idanun ta ya kada jajir kamar gauta, kwallan da take dannewa ne ya samu daman zirarowa yanabin kyakkyawar fuskarta, kallon hagun ta ta yi ta hango wasu yan Yara matasa da ba za su wuce shekaru sha-uku, sha-biyar ba, kallon su take yanda suke tafiya suna jifanta da kallo me nuni da tsantsan tsana da takaicin ganinta, Lura da hakan ya sa zuciyarta harbawa da karfin tsiya kamar ze bar gangar jikinta, kallon banzar da suke bin ta dashi, ban da mutum daya daga cikinsu da ya nuna kalan tausayi a gareta, ya sa ta yi kasa da kanta, ganin sun harare ta suna ƙoƙarin wuce ta ya sa cikin Karfin hali, murya raunace cike da fargaba tace,

" Dan Allah ku dauko min kofin nan ban iya durkushewa bayana ke masifar yi min ciwo ". Ta idasa zancen tana tunanin me ze biyo ba, domin tsayuwar da suka yi ta san akwai badakala.

Wani kallon Banza suke bin ta da shi, hade da kallon jikinsu, kana suka kai dubansu a kan suturar da ke jikin ta ayage kana iya hango saman na shanunta da suka fara tasawa daga kirjinta, daya daga cikinsu mai dan hankali ya yi karfin halin Fadin" Subuhannallah sannu !! ko"!. ƙoƙarin Dauko mata kofin yake, yaji yan uwansa, suna fadin " haba ya zaka dauko kofi ka bata, so kake ta shafa maka bakin fenti, wannan Yarinyar ina tabbacin mayu ne, yo inba maita ba, tun tana yar shekara biyu zuwa uku suke makale kar kashin bishiya itada tsohonta da rashin gaskiya ya sa kwatakwata yaki bari asan fuskarsa kullum sanye yake da rawani kamar Sarkin Aska, fuska kuma arufe kamar buzaye, su ma buzayen basa rufe fuskarsu, ya mai da kansa kamar mata masu yawo da nikaf, tsabar rashin gaskiya duk inda yarinyar nan ta zo to babu nasara a wajen ". ya yi magana yana kara nuna mata tsanarsa a fili, lumshe idanunta ta yi domin kalamansa ba karamin huda na gashin jikinta ya yi ba, ji take kamar yagama ci mata fuskar, bata san meya kalmar mayyah yake nufi dan wasu maganganu Papynta ke koya mata bata taɓa rabar cikin mutane ba.

Shi ko be kula da batun dan uwansa ba, hakan nan yaji yana bukatar taimakonta kamar yanda ya saba zuwa kai musu taimakon abinci da sauransu ba tare da yan uwansa sun sa ni ba, dauko ma ta kofin ya yi yana goge kasar da ya taba kofin da rigarsa, kana ya mika mata cike da girmamawa.

Duk da mawuyacin halin da take ciki hakan be hana ta murmusawa ba, cikin langwabar dakai ta ke ma sa godiya, kauda kanta ta yi da kallon takaici da sauran suke bin ta dashi, hanzarta barin wajen ta yi gudun kar su ma ta mugun abu, dan matuka sun ji haushin dan uwansu da ya taimaka ma ta, tafiya take, tana jin tashin hayaniyarsu da yan uwansa a kan sai sun fadawa iyayensu, ya taimaka mata, tana tafiya tanajin tausayinsa.

Kallon ta suke dukan su, yan uwansa, cikin takaici suka ce, "wannan Yarinyar mai tsufar Al'janu ka taimakawa, yarinyar sai shegen kyau kamar ita ta yi kanta, ga shegen bakin jini kamar mujiya, ni fa ban da kyaun halittar ta da zubin kirarta da wallahi inna ganta a hanya canza hanya zan yi. "

Cikin damuwa wanda ya taimaka ma ta ya ce, "be kamata ka yi wannan furucin ba saboda ita ma ba yin kan ta ba ne ta ke cikin tsinannen talauci ba, kuma maganar sai kun fada a gida dan Allah kubar shi. " Nan dai sukayi ta surutai akanta shikuma sai hakuri ya ke ba su karsu ballo masa ruwa ya san yanda iyayensa suka tsani yarinyar nan.

Ita kuwa tafiya ta ke tana bin rairayi na titin jirgin kasa, tana tafiya tana ciza yatsarta har ta isa bakin titi, kasantuwa duk ranar Juma'a ne ranar da ake rabon nonon shanu, a hankali take taku kamar kazar da kwai ya fashe mata aciki, har ta karaso wajen amsar sadakan, fararen idanunta masu haske kamar kyandir ta ke kallon jerarrun kofuna da suke a kasa, kasa durkushewa ta yi bare ta ajiye nata kofin ajerin na sauran yaran.

Tana kallo wani Alhaji, cikin farar shaddarsa sanye da babban riga, ya siyan nonon shanun wajen jerin mata san yara fulanawa masu sanye cikin kayansu na asali, be bata lokaci ba, ya zo ya daidaita sahun kofofuna da ke jere a kasa, cikin nutsuwa ya ke zubawa jerin kofufunan da suke akasa nonon yana gama zubawa ya dago daga durkushen da ya yi caraf idanunsu suka tsarke cikin na juna shi da Yarinyar, ahanzarce ya ɗauke ganinsa akanta, jin mummunar faduwar gaba, dan ba karamin kidimewa ya yi ba, ganin ya gama zuba sadakan Nonon, wanda ya jawo yaran fara kokawan wajen daukan kofinansu . Yarinyar kuwa kwalla masu zafi ne suka cika kwarmin idanunta, cikin kukan zuci ta ce, "  ba suke nan yau bazan samu sadakan ba, kuma sun ki koda kallo na bare nasa ran samun Nonon". Fara neman wajen zama take yi domin ba ta san yanda zata koma muhallinta babu Nono a hannunta ba, duk mata san yaran da aka yiwa rabon nonon kowannen su, daukar rabonsa yake yana ficewa tare da kwabe baki suna kallon ta. Na karshen ne da ze fice ya yi karfin halin Fadin " kin tsaya girman kai anyi rabo babu ke. " Tsunkuyar da kai ta yi dan a zatonta be cancanci amsa ba, wata zuciyar ta ce", kar ki damu da abin da yake fade duk da besan zuciyarki da niyarki ba". Da wannan tunanin ne ta yi banza da shi ya yi ta maganganun sa ta yi biris kamar bata san yana yi ba, yana gajiyawa ya kama hanya ya fice yana surutai. Ita kuwa cikin kunan zuciya take bin bayan sa da zararan idanunta masu haske da kallo. Cike da mamaki take kallon mata san yan matan fulanin masu siyar da nono a wajen ko wacce ta daukan kwarya ta, suna kallonta suna kwabe baki hade da jinjina taurin kai irin nata.

 Kusan mintuna talatin ta dauka tana a wannan yanayin, bata ankara ba sai ji ta yi muryar wata Mata daga sama, cikin karfin hali Matar tace, " yan Mata me kike yi a nan wajen? ina Gidan ku? ina iyayen ki? kike zaune nan wurin ke kaɗai da duk alamun ma bakida isassen lafiya ". ta yi magana cikin tausayawa.

Afirgice take kallonta jin maganganun ta daga sama ba zato ba tsammani, kallon ta take da idanunta, masu cike da damshin ruwan hawaye, numfashi me karfi ta fesar kana cikin rawan muryan, da kadawar harshe ta ce, " yanzu nan zan koma Gida tun da sadakan nonon ma dana zo karba ban samu ba, ga kishi mai tsanani yana damuna ko za ki taimaka min da Ruwa ". ta kai ayar zancen idanunta nakan matar da ke sanye cikin doguwar riga bleu sky mai zanen tsuntsaye, gajera ce me yar kiba da kauri, kana fuskarta tana da zanen Kanawa me uku-uku, baka ce mai dan fadin fuska.

Matar kuwa tsaf ta kura mata idanu cikin kankace Murya tace, " ya sunan ki Yar nan".? Kallon take babu kiftawar idanu, ganin kamar batada shirin bata amsa ya sa ta yi kwafa tare da sake narkan da murya cikinsalon jan hankali. Maganar da take shirin yi ne ta katse jin yarinyar na magana.

" Sunana Farida, amma Papy na, nakira na da " Amatullah. " Tana kai aya, ta fara yunkurin tashi domin ta tsani tambaya.

" Dan tsaya mana, ga me tsaida ruwa cen dan Allah tsaya ki amsa sannan na ga kina hucin zazzabi akwai magani a jakata, shin za ki karba?. "

Gyada mata kai ta yi ba tare da ta kalle ta ba, matar hanzarta karbo ruwan ta yi tare da bata tasha, ga mamakin ta sai gani ta yi ta shanye ledar pure water biyu nan take, kana ta fara mai da numfashi, ballo ma ta maganin ta yi ta mika mata hade da kara karbo ruwan, nan ma sai gani ta yi ta karba hannun ta na rawa ta hadiye ta shanye shi.

Murya cike da kuka Amatullah tace, " yanda kika farantamin kema Allah ya faranta miki, kinsan darajan dan adam ke ce ta biyu a nahiyar nan da kike iya ba ni abu babu shamaki ko tsoro ". tana kai aya, bata jira cewar Matar ba takama hanya cike da dan tsaurin ta, tana tafiya tana waige -waige sam bata son Matar taga hanyar da tabi bare tasa ran biyota, koda ta yi nisa ganin ta ba cewa Matar ne ya sa ta canza hanya izuwa ainihin hanyarta.

Ita kuwa da kallo ta bita har ta ba cewa ganinta. Ta dade daga tsayuwar da take tana nazarin fuskar yarinyar da kamanninta, domin yanda take magana akwai hikima aciki. " Barin wani tunanin ta yi, tare da kai dubanta a kan me siyar da ruwan da ke jiran ta biya shi kudinsa, cikin hanzarinta tattare da kuzarin ta, ta karasa gaban sa, Fesar da numfashi me zafi ta yi kana furta.

" Wannan Yarinyar dana karbarwa Ruwa a hannunka, dan Allah daga ina take fitowa?. " tana kai ayar zancen, wayarta ya fara ruri, hankalin ta da nutsuwarta, ta tattara gun amsa kiran daya shigo wayar ta, sosai ta mai da hankalinta a kan wayar da take, batare da ta ankare ba mai saida pure water gaba ya yi abun sa yana banbamin fada a kan bata ma sa lokaci da ta yi ga shi ze je islamiyya, itakuwa tana gama Wayar, Murmushi kwance a kan Fuskarta ta waigo da shirin yi masa magana, ragowar kalamanta ne suka samun damar makalewa nan da nan annurin ta ya ɗauke, ganin wayam babu shi babu dalilin sa kamar saukar aradu, zazzare idanunta, ta soma hade da kara ware su dan tabbatar ba gizo idanunta suke ma ta ba, ganin dagaske babu shi a wajen ta fara nazarin ta ina yabi bayan be karbi kudin sa ba, idanunta, ta mai da a kan kasar wajen, sahun kasar take kallo duk da yashi ne amma ga mamakin ta, bata ga sawayen sa ba, hankalin ta kara tashi ya yi cikin tsoro da fargaba ta fara tafiya cikinsauri-sauri, ƙoƙarinta, shi ne taga tabar wajen, gabanta wani rass rass yake badawa da masifar karfi.

Garin Abuja Asokoro

A hankali ya ke taku yana tafiya cikin isa da kasaita ya yin da mabiya bayansa suka kewaye shi kamar sun taho da Sarki ko shugaban kasa.

Baki daya all Gidan dukar da kansu su kayi, suna kwasar gaisuwa, fuskarsa babu yabo babu fallasa yake amsa musu, kana ya gyara tsayuwarsa yana mai binsu da kallo daya bayan daya.

Sautin muryansa ne ya sa ni kara matsowa domin tun da nake bantaba jin murya mai daɗin amo da dadin saurare irin nasa ba, kallo daya na masa na ga hadadden gaye tsaye sanye cikin riga da wando bleu sky mai suite, bakin takalmin kafarsa mai shening ba karamin daukar hankalin mai kallonsa ya ke ba, fari ne sol zubin larabawa, kwantaccen sumar kansa da ya yi yanayi daya da sajen fuskarsa wanda suka kara miki kyau da cikar haibarsa, hancinsa kamar biro ya yi daidai da karamin bakinsa mai jajayen labbai. Gefensa daya kuwa Aminisa ne Mansur wanda suka taso tun suna yan yara dasu, ra'ayinsu daya ba su taba canza ra'ayi ko tunaninsu ba, saidai afannin mata shi Ridwan ya tsani Mata, hatta Mahaifiyarsa sam baya sake mata, kannensa mata da dan sauki-sauki dan wataran su kan ga Annurinsa, dariyarsa ce za su iya rantsewa ba su taba gani ba, ban da Mahaifiyarsu kila ita ma tun yana Yaro ne. Mahaifiyarsa Hajiya Saratu Abubakar, da kannensa kannensa hudu mata uku namiji daya.

" Ina ga mun iso Gida kowannen ku yana iya komawa muhallin sa. " Cewar kyakyawar matashin.

 Hannun ya mikawa na kusa dashi da dukan alamu shi ne Abokinsa Mansur, na kut-kut, musabaha suka yi ya yin da abokin nasa yake fadin" Ridwan na samu labarin a Jahar Kano a Garin Daguzau babu Wutar nepa kimanin yau wata biyar  ba suke nan". Ya idasa zancen nasa yana kara fito da wata farar jaka transparent mai ɗauke da file bil adadi marasa iyaka, wata yar farar takarda ya mika masa hade da kara kusanto inda Ridwan yake.

Shi kuwa kamar anɗauke ɗauke Wutar Lantarkin jikinsa haka nan yaji jikinsa ya fara tsuma, a zahiri kana kallon sa zakayi tunanin fuskarsa babu fushi ko damuwa amma kasar zuciyar sa kamar ana dandatshi da dutsen Wuta, wani irin zufa da ya fara keto masa a dukan sassan jikinsa. Hannayensa na rawa ya karbi File din daga hannun Mansur abokinsa, kana ya fara ware zararan idanunsa masu ɗauke da eyelashes da medical glass, yana kallon file din cikin tafasar zuciya ba tare da ya iya furta wata kalma me tsawo ba ya ce, " Mansur Muje daga ciki. " daga haka be kara furta komai ba. Ya yin da ya yi gaba Mansur ya take masa baya, mabiyan sa kuwa, tsayawa suka yi suna kus-kus suna fadin wai ace Minister of power shima yana fuskantar kalubale ga aikin sa, kuma Gidansa sam ba'a yanke Wuta da. . . . . . Sauran kalamansa ne suka makale ya yin da yaga duhu ya mamaye da ilahirin Gidan ko ina. dafe da kirji suka ce, " subuhananallah yanke wuta agidan Minister of power na Nigeria, sossai suka tsaya suna mamakin lamarin, nan dai suka bar hiran tare da fara neman tochla domin haskawa kasantuwa ko ina na gidan ya dau duhun gaske. Wasu daga cikinsu tochla wayoyin su haska domin gudun afkawa inda cancanta ba.

C'en cikin Gida

Cikin gigita Mamy ke tafka salati hade da fara lalubar inda wayarta ya ke, razana ta yi jin kamar an shako wuyar ta daga baya, callara ihuu ta yi wanda yasa, ta fara ƙoƙarin faduwa a harzance, Ridwan da ya karaso falon rike da hasken Tochla din Wayar sa ya haskata akanta, kafun ta kai ga yin kasa tuni ya sa hannayensa masu taushi ya tallafe ta. Itakuwa zazzare idanu ta ke tana fadin" Ridwan shake ni akayi fa!. " Cikin zararre idanu me nuni da zallan tsoro da fargaba take bin haske tochla din Wayar sa, da ya dan haske daidai fuskarta kana yana kashe ma ta idanu da mugun hasken, hakan ya sa ta sa tafukan hannayenta, ta tarufe fuskarta, ahanzarce ya'yan ta da ke falon suka zagayeta kowannen su, cikin damuwa suna ta fadin" anya Mamy ba tsoro kikaji ba?, babu wanda ya shigo falon nan sai, Ya Ridwan. "

 Ganin sun ki aminta da zantukanta ya sa ita kanta ta fara tabbatar wa kanta eh Lallai ze iya zama tsorone ya firgita ba. samun wuri ta yi ta zauna da taimakon Ridwan, Wayarta suka lalubo ma ta tare da mika mata, sannu suka jero mata lokaci daya.

 Ridwan da sam be mance bacin ransa da yake ciki ba cikin hanzarin sa ya mike tare da kama hanyar da zata sadashi da dakinsa kamar daga sama yaji muryan Mamy tana fadin,

" banganeba me kake nufi ba? Ko kuma wani wurin ne akace maka ba su da wuta shi ne zaka yanke mana wutar gidan mu, haba Ridwan kai wani irin Yaro ne da sam baka kula fushin iyayen ka, me ya sa baka son farantamin rai a kan komi na rayuwa, harda wutar nepa? ".

Cak ya tsaya beyi gaba ba beyi baya ba, sossai gabansa ke bugawa gab gab da karfi, cikin rauninsa ya dan juyo tare da dawowa falon taku befi uku ba ya karaso gab da ita hade da kama hannayenta, Mamy cikin zallan mamaki take kallon yanda ya rike mata hannu dan zata iya rantsewa rabonta da ta ga hakan tun yana karaminsa, cikinsanyin murya wanda da ita kaɗai yake wa magana a hakan, cikin tausasa Lafazi yace,

" Mamy kiyi hakuri bari a kunna sola kawai, ba zan iya kunna Wutar nepa ba sai har na tabbatar da na gyara matsalar wasu yankin ". ya dire ayar zancen sa cikinsanyin murya, sam ba ya son jin wasu kalami daga bakinta, hakan ya sa ya mike kaman ana tsira masa allura fit,

Yana ƙoƙarin barin falon ne hasken sola ya mamaye Gidan gabakidaya, nan take ko ina ya dau setti fanka da esi da Tv duk suka kawo, Tv ya cigaba da aiki kamar yanda yake kafun yanke Wutar, isowar Mansur ne ya tabbatar masa da shi ne ya kunna solar dan sai yanzu ya karaso hadadden falo na Alfrma mai cike da kayan jin dadi na rayuwa, Mansur yana mai bin Ridwan da kallon mamaki, kana ya mai da kallon sa a kan Mamy da ke zaune cikin dan bacin rai alamu dai anyi mata laifi.

"Biyoni". Shi ne kalmar daya furta ba tare da ya kai dubansa a kan Mansur ba.

Shi kuwa Mansur Girgiza kai ya yi tare da karasowa gaban Mamy, durkushewa ya yi ya gaisheta cike da ladabi.

fuskarta babu yabo ba fallasa ta amsa masa kana ta tura dan yatsar ta daya abaki alamun tarin mamaki game da ɗauke wutan da Ridwan yake musu agida ko wani time, bayan ta san ko da wasa a Yan nepa basa yanke musu Wuta.

Mansur kuwa gaisawa da kannen Ridwan ya yi, inda suka amsa masa cike da da Fara'ar su.

 Hankalinsa yana kan dakin Ridwan hakan ya sa beyi watawata ba, kai tsaye ya yi hanyar dakin sa cikinsassarfa da zakuwa, a hankali yake murda handle kofar, murya a sanyaye ya doka sallama jin babu amsa ya tabbatar masa kila yana cikin banɗaki ne, ga zallan mamakinsa, yana shiga, hango sa ya yi cen bakin karshen Gado yana rusa kuka kamar karamin yaro harda sheshekarsa, nan da nan ya hanzarta karasawa dakin, cikin barin jiki hade zallan damuwa tattare dashi.

" Ridwan me ya saka kuka? Shin Ridwan kanada damuwar da ban cancanci in sani ba ne?, ko kuma ba ni da matsayin da zan san Personnel dinka ba ne?. " Ya kai ayar zancen yana mai ƙoƙarin dago kansa daga durkushewar da ya yi.

 Cike da nutsuwa Ridwan ya kai duban sa a garesa kana ya dan langwabar da kai, cikin za kin muryan sa mai sanyi da dadin sauraro yace,

" Babu tashin hankalin da ke daga min hankali irin in ga kauyuka ba suda wutar nepa, ina gudun bakin mutane akaina, ina tsoron tsinuwar Allah shin ya ka ke tunanin in iyayenka ne a kauyen ko yan uwanka, shin baka gane Alkibla ta ne?, Mamy sam bata gane inda na dosa, kuma bana fatan ta gane ko da a nan gaba ne domin. . . . ". Saurin katse shi Mansur ya yi cikin kar kada kai, ya mai da masa da amsa tareda fadin.

" A'a Ridwan banason ka ce komi dan Allah kayi shiru basai karasa ba ". ya kai ayar zancen yana mai kamo hannun sa a cikin nasa. suna face din juna, kallon kallo sukewa juna inda kowannen su da abin da. yake sakawa yana kwancewa a cikin zuciyarsa.

Kashe Gari

Garin Gabasawa Daguzau loct (Kano state)

Tunda sanyi safiya Amatullah ta tashi da dan karfin ta sakamakon jin sauki sossai tattare da ita, ahankali cikin kuzari ta fara ƙoƙarin dan gyara wajen da suka kwana, sai a sannan nakai dubana inda na hango katuwar tsohuwar bargo shinfide a kasa, a gefenta kuwa yan roba ce mai dan murfi guda sai kofofina da cokali, kana a gaban ta tsohuwar buta ce wacce duk cikinsa ya yi gansa kuka.

Muryan ta ne yadawo da dubana a kan ta, jin tana fadin " Papy dan tashi ka dan zauna in gyara maka shinfida nasan tun jiya rabon da muci wani abu, nonon ma da muke ajiyewa shima ba mu samu ba a jiya ". Ta idasa zancen cikin halin damuwa.

Dattijon da ya yi zurfi a tunani, firgit kalamanta suka dawo da shi hayyacinsa, cikin muryan sa da basa fita sosai yace, " Amatullah kar ki damu ai akwai sauran Dabino a tattare damu, ki tuna ayar da Allah yake fadi duk tsanani yana tare da sauki, shakka babu in dai muna raye wataran sauki na nan tafe ". Ya kai ayar zance yana mai ƙoƙarin tashi.

Itakuwa gyada masa kai ta yi ba tare da ta sake furta komi ba, cike da nutsuwa ta dan gyara wajen, ganyayyakin da ke zubo musu saida ta tattara su waje daya, sai a lokacin na kula cikin ciya yi suke kwana ga katuwar bishiyar mangwaro da ya yi musu rumfa.

Zabga uban tagumi ta yi bayan kammala gyaran wajen, a hankali ta ke jin hawaye masu zafi suna bin kuncinta ganin har rana ta yi haske ba su karya ba, agogon roban da ke hannun ta, ta kalla ganin karfe goma ya sa ta yin mika hade da tashi, kana a sanyaye ta dauko dabino ta ci me dan yawa wanda be zarce goma ba hade da bi da ruwan yar, cikin dan kuzarin ta, take ƙoƙarin fita dan nemo abunda za su karya da shi.

" Papy zanje ko Allah ze sa na samu na safiyar nan. " ta yi magana hade zura kodaddiyar takalmin ta a kafarta.

Da Allah yatsare ya bita dan shi kansa ya san yana jin yunwa.

ABUJA CITY

Bangaren Ridwan da Mansur sammako sukayi tun karfe bakwai na safiya domin Zuwa kauyen Daguzau sun kusa isowa Garin ne Wayar Ridwan ya fara ring, a hankali ya kai duban sa a kan Screen din Wayar sa, ganin mai Gadin gidansa ke kiran sa, ya san magana ce mai muhimmanci, a hanzarce ya kara Wayar a kunnensa bayan ya daga, yana ƙoƙarin yin magana yaga motarsa ta fara juyi dashi tana ƙoƙarin kade Wata Yarinya da ke tafiya ba tare da ta san inda take jefa kafafunta ba. ban da innalillah babu abin da suke maimaita sakamakon ganin har motar su ta. . . . . . . . . . . . .

Makauniyar Shari'a yanzu a aka fara kudai ku biyoni domin ganin yanda abubuwan za su kasance

SHAFI NA BIYU

Sakamakon ganin saura kiris su buge Yarinyar, wawan birki ya ja, hade karfafar ajiyar zuciya me nuni da tsantsar fargaba da tashin hankali.

Kusan a tare suka dafa saitin kansu, suna girgiza kai alamun bacin rai, fesar da numfashi Ridwan ya yi ta madubin glash din motarsa yake kallon, Yarinyar da ta daura hannayenta akai, kallon yanda ta ke durkushe waje daya, tsirin tsaki ya yi yana ƙoƙarin fita, Mansur ya dakatar dashi, so yake ya yi magana takaici ya hana shi, fahimtar hakan ya sa Mansur fadin " jirani ina zuwa". Be bashi amsa ba, binsa ya yi da idanunsa da suka canza launi zuwa bacin rai, yatsarsa daya abakinsa yake hango ta ta cikin glass din motarsa.

Mansur hanzarta fitowa daga Motar ya yi ganin Yarinyar ta daura hannunta akai da ke nuni da tashin hankali da tsoro tattare da ita. Afusace cike da tsananin bacin rai ya ce, " amma fa ke Yarinyar nan kincika mara hankali dan rainin hankali so kike ki ja mana kalata muna zaman zamanmu, ban da shashanci da rashin hankali ke bakya kallon gabanki ne? Ko kuma titin Gidan ku ne?. " Cikin takaici ya ci gaba da zazzaga mata ruwan masifa.

Rintse idanunta ta yi domin gani ta ke tana dago kanta, dukanta ze hau yi. Ganin bata tanka mishi ba ya sa shi yin tsaki yana mai kare bin ta da kallo tun daga sama har kasa gashin kanta da suka cure waje daya saboda rashin taje kai da kuma rashin kitso yake bi da kallon takaici, takun tafiyar Ridwan ne ya sa shi dawo da kallonsa akansa.

Ridwan kuwa ahankali yake takunsa mai cike da burgewa ya karaso gab da Mansur, din ya yi daidai da dago kanta, caraf idanunsu suka tsarke cikin na juna, nan take yaji kansa ya sara notice din jikinsa da jijiyoyin jikinsa duk sun mimmike ji yake zirrrrrrrrr yammmmm gaba-daya tsantsan jikinsa zuwa gargasa. Ita kuwa tozali da kyakkyawan idanunsa ba karamin rikitata ya yi ba, nan take taji jikinta ya dau rawa kamar mazari, atsorace ta soma ja da baya baya tana domin ba zata iya jurar kallon kwayar idanunsa ba.

 Ridwan daga shi har Mansur kallon mamaki suke bin ta dashi, kana suka kalli junansu akaro na biyu, hannayensa ya saka a aljihun wandonsa yana taku daya bayan daya kamar ba son tafiyar yake ba, ganin Yarinyar tana shirin faduwa ta baya tsabar tsorata dashi. ya sa shi fadin" Kee!!!". Atsawace ya yi magana yana kara kusanto inda take, jin tana tashin wariwari daga jikin ta, ya sa shi ja da bayabaya, kana yakara dubanta cikin idanu ganin yanda cikin kwayar idanun hawaye suka taru, karfafan ajiyar zuciya yakara saukewa a karo na biyu, kana dakyar da ƙoƙari ya dan bude bakin sa tareda fadin " Ni babu abin da zan miki saidai ina mai baki shawara da kiji tsoron Allah, ki kuma kiyaye fushin Allah". Ya yi magana cikin silent voice, batare da ya kara bi ta kanta ba, ya kamo hannun Mansur suka shige motarsu. Ko da suka tayar da motar yana zaune mazaunin drever amma idanunsa na kanta, har yabar wajen.

Itakuwa cikin tsananin mamaki take juya kalaman sa, shin me yake nufi da taji tsoron Allah, me ta aikata me muni, wanda ya sa ya yi wannan furucin, kallon jikinta, tasoma ganin saman na shanunta a waje, kana rigarta duk sun yayyage, wani sashi na zuciyar yace kidaina damuwa da maganganun mutane inba haka ba za su kaiki su baro, da wannan tunanin ne, ta fara ƙoƙarin barin wajen, gudun kada su kara biyo hanyar su ganta.

 Bangaren Ridwan sun dade suna hiran ta shi da Mansur, cikin takaicin matsalar da ta so janyo musu. Mansur ƙoƙarin kwantar masa da hankali yake domin ya manta da ita.

 Babu bata lokaci suka karasa cikin Kauyen. Ridwan da Mansur sosai suke kallon yanayin garin da kuma mutane masu kai kawo, wasu yan mata ne tafe ahanya wasu mazane, duk wanda ze wuce ta wajen idanunsu na kan motarsu dasu kansu da suke son sanin waye su masu hadadden motar nan, abunka da kauyen nan da nan akayi ta shelanta yan birni sun zo garin kuma da dukan alamu sun zo rabon abincine.

Ya Allah ka kawowa Kasata Nigeria dauki ka cire mu acikin kangin wahala, wanda abinci ke wahala, ya Allah ka yassare musu da mu dasu din.

 Ji labarin isowar su ya sa nan da nan manya-manya masu fada aji a kauyen suka, taresu tare da musu barka da isowa. Babban Masaukin baki da ke office din KEDCO nan aka sauke, nan da nan wutar nepa ta dawo, ac din office din ya hau seti, nan aka shiga kawo musu abun tabawa, duk abin da aka jera musu acikinsu babu wanda kalla bare su sa ran dauka, fushin da Rudwan ya boye ne ya fara fitowa a fili, ganin duk wanda yake son gani sun halarta a wajen, cike da nutsuwa ya fara magana da dan fadafada yace, " babu wanda ya isa acikin ku yace bana iya bakin ƙoƙari na ganin kowace jaha da kauyuka sun samu wutar lantarki wadattaciya, shiyasa yanzu na kira Manager KEDCO na Jahar Kano nan, domin ya zo naji yanda abubuwa suke kasancewa har ake rasa wutar lantarki, kuma tsabar munafunci dan na shigo garin shi ne zaku saki wuta ku atunaninku kuna da wayau ko?. yana kai ayar zancen ya yi shiru kamar bashi ne ya yi magana a yanzu ba.

 Mansur kuwa ta window yake bin kofar wajen ma'aikatan da kallo, ganin yanda yan kauyen suka cika unguwar domin son ganin Ridwan, cikin su harda yan mata. girgiza kai ya yi yana mamaki ina suka samu labarin isowarsu haka, dan kwata kwata sun zo da niyar zuwan sirri ne.

Amatullah data sha yawonta har ta gaji bata samu komi ba, hango wata tsohuwa ta yi da kwanunta tana fadin " Bari mu yi sauri kada abincin ya kare ".

Nan da nan Amatullah ta juya kwayar idanunta zuwa ga cinkoson jama'ar da take hangowa daidai kofar office din yan nepa.

Cikin rudewa da junyar da ke kwakwalarta ta diba ahanzarce ta yi wurin taron.

 

Tana isowa wajen ganin sam sun hana ta ganin gabanta, bare har ta san ma me ake rabo ne.

Daga ciki, Ridwan sosai yake fada yana nuna musu hukunci daze dauka inhar ba su kiyaye ba, dakuma wa'yanda ze dauka domin su ringa kula da yanda suke sakin wuta a kauyen. Manyan da ke wajen sosai suka shiga bashi hakuri dan tunda suke dashi be taba takowa kauyen ba sai awannan karan, kuma ya zo su biyu ba tare da su Bodyguard dinsa ba. Mansur ne ya fara tashi hakan ya sa shima Ridwan tashi suka fara musabaha na bangirma da jama'ar da ke wajen, kana su kayi farfajiyar tsakar gidan.

Amatullah ganin haryanzu sam, sun hana ta taga me ake rabo ne, ya sa ta callara ihuu! tana fadin" wai dan Allah bazaku matsa ba ne in karbi sadakan ba, rabona da abinci tun shekaran jiya. " ta kai karshen zancen murya na rawa ga wasu hawaye masu zafi da suka cika mata kwarmin idanunta.

Cikin gigita Ridwan ke juya kalamanta, daidai kuma lokacin idanun jama'ar da ke wajen ya sauka akanta suna marmatsa mata domin bata hanya ta isa inda take son zuwa. Koda ta karaso cikin fargaba da tsoro take kallon Ridwan da Mansur da suka zuba mata shanyayyun idanun su masu kwarjini, jama'ar da ke wajen ko wannensu mamaki ya cikasu da karfin hali irin na yarinyar.

Da bayabaya ta fara neman hanyar guduwa nan da nan taji kafafunta sun gaza daukarta, jikinta yahau kyarma, hartayi reverse zata juya ta ji muryan Ridwan a khausashe yana fadin" ya ilahi yau wace irin bakar rana ce mara sa'a data riskeni, kuma ki rasa inda za ki tako sai gabana ni Ridwan Hummm ". hannu ya saka cikin aljihun wandonsa tare da zaro bandir din kuɗi sun kai akallah dubu dari, soma taku ya ke yi yana kusanto inda take, itakuwa tana ja da baya baya, jin motsin takun tafiyar sa ya sa ta hanzarta durkushewa a wurin, cikin tsananin tashin hankali da tsoro daya cika mata ruhi da gangar jikinta, robar hannunta yake kallo cikin tsananin takaici da kyankyami ya daura wannan bandir din kudin aciki. Gabakidaya wajen suka fara" yallabai yarinya karama zakaba wannan kudin, yarinyar nan fa duk wanda ya rabe su sai bala'i ya same shi har karshen rayuwarsa, dan haka tunda da wuri ka amshi kudin ka daga hannunta. " ya idasa zancen cike da hassada da ke cin sa.

Amatullah jin abin da mutumin ke fada ya sa ta diba aguje rungume da kudin, robar baran nata a nan ta barshi.

Ridwan da idanu yake bin ta har tabar wajen, kana ya sauke sanyayyen ajiyar zuciya, sam babu tsoro tattare da shi ya ce, " ai babu bala'in daya wuce wanda yan Npower suke ƙoƙarin jefani cikinsa ". ya kai ayar zancen tareda sake daukl bandir din dubu dari yace a rabawa yaran da suka taru a nan wajen.

Babu bata lokaci suka hanzarta barin wajen domin komawa garinsu.

Nan fa jama'ar wajen suka hau fara shawarar yanda za subi sahun Amatullah domin kwace kudin acewar su taya za'a ba su dari su raba ita kuwa ita kaɗai ta karbi dubu dari, daya daga cikin su yace, gaskiya abari sai dare aje a karbe kudin, da wannan shawarar suka watse. kowannensu ya dau alwashin koya musu hankali.

ABUJA CITY ASOKORO

Bayan sallah magrib système ne gaban Ridwan, babu abin da ka keji sai karar keyboard cikin annashuwa da fara'a yake aikinsa da dukan alamu ya yi zurfi cikin aikin nasa, karar bude kofar, ya sa shi dago kansa ya kalli me shigowar, kana yakara dawo da kallonsa a kan system dinsa.

Itakuwa Kanwar sa cikin hanzarinta ta karaso dakin hade da zama kusa dashi, kallon shi take ganin babu riga ajikin sa daga shi sai gajerar wando. fadaddan kirjin sa take bi da kallo ganin yanda gashi suka kwanta lublub gwanin ban sha'awa. Duk da sam baya sake mata koda wasa hakan be hana ta fadin" yaya kaide duk cikin mu kaida faisal duk kunfimu kyaun jiki, jikinka saikace a novel". ta idasa zancen cikin yauki. Dawo da kallonsa ya yi a kan ta yana nazartan kalamanta, cikin daurewar fuska ya ce, Anisa yaushe raini ya shiga tsakanina da ke? kuma waya baki izinin shigo min dakina kai tsaye ba tare da izinina ba, kuma bayan ban nemiki ba". ya kai karshen zancen tare da mai da kallonsa a kan system. Itakuwa duk da ba sabon yanayi ba ne, wannan halin nasa da yake nunawa a kan su ba, amma na yau sai take ganin kamar cin fuskar ya yi yawa. Cikin dauriya da kankance murya mai nuni da alamar tsoro tace, " yaya daman Mamy ce tace inzo in gayamaka kudin da kake ba mu na karshen wata ya kare kuma daman inason na siye ankon kawata zatayi Aure ". nan fa tashiga jero masa bukatunsu.

Duk abin da take fade besa ya dago kai ya kalleta ba, zaka iya karantse sam besan ma da zamanta, domin yanda ya ba banza ajiyar ta, yana ayyukansa yanayi yana kara kusanto system a gabansa. Anisa zazzare idanu take ganin yanda ya bude ruwan faro da ke kan center table da ke kusa dashi, ahankali ya kafa roban ruwa abakinsa yana sha, ji kake kol kol kol yanda kasan ya wuni be sha ba, yana ajiye ruwan ne ya rufe systems dinsa, mai da kallonsa ya yi a kan ta, kana cikin muryansa da takasance dabi'ar sa ya ce, " daga yanzu duk abunda ake bukata aringa min liste ana rubutawa a takkada batun bayar da kuɗi in ba Mamy ba na soke shi, kuma batun anko na kawarki za ta yi aure, babu inda za kije bare har ki saka anko dan haka kina iya fita na sallame ki. " Ya kai karshen zancen tare shiga banɗaki, ya barta a nan tsakiyar dakinsa, bayan sa tabi da kallo har ya ba ce mata da gani. Shiga duniyar tunani ta yi ta rasa meye damuwar ya'ya Ridwan me ya sa sam bashi da lokacinsu bare na Mahaifiyarsa, gudun kada ya fito ya isketa ya sa ta hanzarta barin dakin jikinta na tsuma. Kai tsaye iske Mamy ta yi ta sanar mata yanda sukayi da Ridwan din. Mamy yatsarta ta saka a baki tana fadin " Yaron nan badan a Gida na haifesa ba wallahi cewa zanyi canzamin akayi kuma baya ga haka yana tsantsar kamanni da Mahaifinku, gwamma faisal sau dubu a kan sa danshi kawai be aikin komai ne. Amma na tabbatar in shi ne yake samun da Ridwan ya ke yi wallahi sai mun huta, kuma ze ringa janku ajikinsa kamar yanda sauran yan uwa suke yi d. . a. . . . . . . . ". sauran kalamanta ne suka makale sakamakon ganin Ridwan na saukowa daga kan matakalan step din, sanye ya ke cikin jallabiyarsa fara da hula fara, sai kyalli haske da sheki ya ke yi kamar Balaraben Égypte.

 cike da girmamawa ya gaida Mamy, kana murya a tausashe yace, " sauri nake ana shirin tayar da sallah". be jira cewar su ba ya hanzarta barin falon.

Da kallo suka bishi dukan su, kana kowannensu ya tashi domin zuwa yin sallah, sun san babban matsala ne ya dawo daga masallaci yaga ba suyi sallah ba.

Kauyen Daguzau

Ko da yan kauyen suka idar da sallah, tsantsani wasu daga cikinsu, sukayi suna shawarar yanda za su yi su amso kudaden da ke hannun Amatullah, sannan su binne su da rai daga ita har papynta dan sun tabbatar tun zuwansu bala'i da masifa yake ta afka musu. Mata san yara yan samari wajen goma aka tara ana tsara musu yanda za su yi komi cikin tsari kuma su tabbatar da sun amshe kudaden kafun su binne su. Malam Idi wanda shi ne ya haddasa taron nan ya kara da fadin " yo inbanda iskanci da rainin wayau kudin da yallabai yaba yara kusan arba'in shi ne ya bata ita kaɗai". Matansu da ke wajen suna ta tofa albarkacin bakin su kowa beda burin ganin anbinne su anhuta dan sun dade suna rayuwa a nan wajen.

Ba karamin tashin hankali Salim ya shiga ba, ganin har suna daukan fatanya da duk abun bukata domin haka rami. ba tare da ya bari an gan shi ba ya tsuri tochla din mamarsu da ke ajiye tafiya yake yana tsula uban gudu yanayi, yana gudun yana faduwa, da ya gaji sai yadan huta, kana ya daura daga inda ya tsaya, cikin ikon Allah, har ya isa daidai inda su Amatullah suke. Yana karasowa soma sauke ajiyar zuciya ya yi sakamakon haska tochla da ya yi ya hango suna sharara barcin su. Cikin gigita yake tayar dasu, wanda ya sa suka zabure, bakin Amatullah na rawa tace, " Salim me kake nema wajen mu a wannan daren?. ".

Cikin rawar murya da tsoro da fargaba yace, Papy wasu daga cikin yan gari sunyi tsantsani domin binne ku da ranku dan haka, babu lokacin magana, Papy dan Allah tashi, kema maza dauko kayan ku da kudinku, kai ba sai kun dauki kayan ku ba, ku rike kudin naku dakyau ze muku amfani. " ya idasa zancen yana rike da hannun Papy.

Banda innalillah wa'inna ilairajun babu abin da Papy da Amatullah suke maimaitawa samun kansu, sukayi dabin Umarnin sa, nan da nan cikin gudu da tsoro suka fara bin dajin Allah mai cike da ciya yi da kayoyi. Har sun suka kawo bakin titi ne suka hango tsantsanin jama'ar da ke rike da wukake da duk alamun sune masu aikata musu ta'asa. nan da nan suka fara. . . . . . .

Comment and share pls

Domin son magana dani kai tsaye ta whasap 09069080725

Taku har kullum kyauta daga Allah

[10/23, 5:37 PM] Kyauta Daga Allah: Makauniyar Shari'a

 Sai a Lahira

 

NA

IKILIMA ADAM

 (kyauta daga Allah)

Littafin nan, na kuɗi ne da zaran free page ya kare za ki daina ganin sa. hanzarta ki biya naki kada a yi babu ke.

Dari biyar kacal

3115484026 Ikilima Adam firts bank

Tura shaidar biya a kan wannan lambar (09069080725) ko kuma kati kuna iya turawa ta wannan number.

Siyen Nagari mai da kuɗi Gida

Jarumai writ association marubuta masu aiki da jarumta wajen Fadakar da Al'umma. 📚📚

TALLA! TALLA!

Marubuciyar nan taku Sarat Alƙasum wacce kuka fi sani da (Maman Nusaiba) wadda ta baje basirarta ta nishaɗantar da ku a cikin littafanta kamar su : Amir da Amira, Aljanar Jarumai, Hafsat, Ƙaddara ce, Tani da Manu, Rayuwar ma'aurata, Sumaiya baiwar Allah, Aljanar Gidanmu, A maƙabarta ne, ABBA NE, Fa'ima.  Yau ma ga ta ɗauke da sabo zazzafa mai suna A HAKA NAKE SON SHI Littafin da ya ƙunshi abubuwa daban-daban zalunci, makirci, cin amana, zallar tsagwaron soyayya mai ratsa zuciyar mai karatu, da sauran su. Ka ku bari a baku labarin wannan kayataccan littafin.

Littafin A HAKA NAKE SON Na kuɗi ne nomal ~N~ 300 vip ~N~ 500 ne.

Za ki tura kuɗin ku kai tsaye ta wannan banki.

Account number 0003187186

Name account, khadija Salisu

Name Bank, Ja'iz Bank

Domin Ƙarin bayani ki tuntuɓi wannan number +966577675904

SHAFI NA HUƊU

Hajiya Rabi mai Iko shin mene ne? burinki a rayuwa. " dan jim ta yi alamar tunani kafin ta ce, " gaskiya ban da burin da ya wuce in san suwa suka kashe mijina margayyi, Justice Haruna Aliyu. " ta kai ƙarshen zancen, murya a raunace wanda ya yi silan karyewan zuciyan dan jarida da ke mata tambayoyi.

Nan da nan Papy ya mike zumbur tare da kashe Rediyon, ban da bugawar zuciya babu abin da kake ji, cikin tsananin tashin hankali Amatullah take kallon yanda yake huci kamar zakanya, wanda a tsahon rayuwar ta wannan shi ne na farko da ta taɓa ganinsa, cikin wannan yanayin. tunkarar shi ta yi cikin rawar jiki, murya na rawa ta ce, "Papy meye ya sa daga jin sunan Hajiya Rabi mai Iko ka rikice kasanta ne?. " Ta je fa masa tambaya yatsarta daya abaki tana mai kara kallon yanda gumi ke sassafo masa dukan ilahirin jikinsa, firgit yadawo hayyacinsa, yana mai ƙwayar idanunta, yanda suka sauya launi daga fari zuwa ja, cikin raunin muryan ya ce, " Amatullah sunan matar ne ya zo daya da sunan Mahaifiyata, kinga dole in tunata Uwa ba abun wasa ba ce ". ya kai karshen zancen kansa a kasa domin beson cigaba da kallon kwayar idanunta.

Amatullah sam bata gamsu da bayanansa ba, hakan ya sa ta zurfafa a tunani tana tunanin barkatai acikin zuciyarta, cikin dauriya da boye damuwarta ta ce, " Papy Allah yajikan kakata ashe daman sunanta Rabi kake ta fadamin A'isha. " sakin zancen ta yi tana kallonsa yanda jikinsa ke tsuma da haryanzu be dawo normal ba.

Cikin gigita yake juya kalamanta babu zato babu tsammani jin amsa daga bakinta, bakinsa na rawa ya ce, " Amatullah ai Rabi suna ne da yaran unguwa suka sanya mata, Kinga sunan ai yabita tunda gashi na kasa mancewa. " Murmushi mai kama da ciwo ya yi yana kama hannayenta cikin nasa.

" Please banason yawan tambaya, kinji my Friday. " ya yi furucin cikin son canza mata tunani.

Kakalo murmushin dole ta yi, batareda ta ba shi amsa ba. Amma tabbas ta dau Aniyar sanin wacece Rabi mai Iko meye alakarta da Papynta, barin wannan tunanin ta yi ganin yanda Papy mai karfi har yana shakewa.

 

Benin République (Cotonou). Kwatano

Kwatano babban gari ne, wanda ya yi kaurin suna a nahiyar Afirka, garuruka da dama sosai suke kulla alakar kasuwanci da jahar, duba ga yanda suke shigo da motoci daga kasar Waje, a saukake suke siyar da kayansu ba mota ba har duk wasu abun bukata, wannan dalilin ya sa kasashe kulla haɗakan kasuwanci dasu.

Alhaji Isah Sharifai, duk a na'iyar Africa yana sawun gaba amatakin arziki da rufin asiri. Mata biyu Allah ya mallaka masa.

A'isha da Basma, ya'yan sa goma 11 dukansu mata, sai namiji daya acikinsu.

Hajiya A'isha ita ce Uwargidansa ya'yanta bakwai, amma biyar ne a gabanta, namiji shi ne babbansu sauran ya'yan zallan mata ne. Ahaka ta yi rayuwa da ya'yanta biyar.

Basma kuwa ya'yanta hudu mata.

Cikin Gidan yana zaune da Mahaifiyarsa Hajiya Mariya, wacce take zaune a part dinta daban.

A'isha zaune a tsakiyar dakinta inda ya'yanta da ke Gidajen Aurensu ban da Autarsu suka zagayeta, cikin tsananin damuwa suke fadin" Mama kibar Gidan nan mana haba !! dubi dukiyar Abba amma ace kina ciwo mai tsanani amma yana nuna halin ko in kula a kan ki, wanda kowa ya san illan hawan jini amma sam yaki koda kai ki Asibiti ne. " Babbar cikinsu mai suna Fauziyya ke magana cikin tsananin damuwa, nan da nan yan uwanta suma suka karbi zancen da fadin " ai mun ga motar Abba yana Gida dakinsa za mu tafi domin gayamasa illan barinki Gida. " Cewar Fauziyya cikin dan bacin rai, tana ta shi kannenta suka take mata baya. Mamarsu ƙoƙarin dakatar dasu ta ke amma ina har sun fice daga dakin, wasu zazzafan hawaye ne suke bin kuncinta, ta san abin da ze biyo baya bayan isarsu dakin Abbansu.

Babban falo na Alfarma komai na bukata na jin dadi a rayuwa ansaka a falon, carpet da ke malale a tsakiyar falon, me walkiyya da laushi nake karewa kallo, red color. Zaune yake a kan carpet din ya yin da ya jingina da kujerar falonsa mai matsifar tsada dakyau. Takun tafiyar da yaji ne ya sa shi kai dubansa ga masu shigowa, firgit cike da zallan mamaki yaga su Fauziyya yaran da ze iya rantsewa sun kwashe shekaru basa shigowa sashinsa. Tashi ya yi daga kishingiden da ya yi da kujera yana mai gyara zamansa harda mike kafafunsa. Ta cikin tabarau da ke idanunsa yake kallonsu, cikin zallan mamaki da son jin me suke nema yake binsu da kallon me alamun mamaki.

Gaishe shi su kayi dukansu, ba suyi mamaki ba dan be amsa ba inda sabo ai sun saba. Cikin dan bacin rai Fauziyya ke fadin " Abba munzo ne dan mu fada maka Mama bata da lafiya in har baka sani ba, in kuma kasani to yakamata a cire hakkin Allah tunda dai har yanzu Mata ce acikin Gidanka". ta kai karshen zancen tana jin zafi da takaicinsa. shiru ya yi alamun nazari, cen sai yaji jikinsa ya yi sanyi, ƙoƙarin magana yake, wani dan siririn maciji baki wul wanda baka iya ganinsa, takan babbar yatsar kafar Alhaji yashige yaringa tafiya yana bin kafafunsa har ya zo tsakiyar kansa, nan da nan idanun Alhaji suka kada jajir kamar Gauta, kara yin kasa ya yi inda yabi ta hancinsa daga nan yaje kan harshensa ya samu masuguni ya zauna, sai a sannan Alhaji ya kai dubansa akansu Fauziyya da keta mamakin yanda ya yi banza dasu tsawon lokaci.

" Banson shashanci da diban Albarka, Mamarku bakomai ba ce face dabba yafita daraja a wajena, wallahi kuka kara danganta dani, duk abunda nayi muku saikun yi nadama a Rayuwar ku, ku din ma wa yake da tabbas din ku jinina ne, yan iska yara masu kama da jinin Fir'auna, duk shegiyar data kara shigo min dakina wallahi tallahi saina mata rashin mutunci daidai da ita ". Yana kai karshen maganar ya tashi a fusace ze hau kan matakalan step, ya yi daidai dajin takun tafiyar Hajiya Basma, wacce take sanye cikin tsadadden leshi me tsada doguwar riga ta ci awarwaro da sarkoki da yan kunnen zinari, sai ba za kamshi take, tana murmushi har fararen hakoranta masu ɗauke da hakorin Makkah suka bayyana. Cikin karyewar Murya ta ce, " Alhaji me ya haɗaka da yaran A'isha, naji sai fada ka ke yi?. " ta kai karshen maganar tana kallonsu suna ƙoƙarin barin falon.

" Ku dakata, ina magana da Alhaji kun fice batareda mun gais. . . . . ". kamo hannunta da Alhaji ya yi ne suka hau matakalan step ya sa bata karasa ragowar kalamanta ba, domin be son ta musu magana.

Fauziyya da kannenta a nan suka durkushe suna kuka mai tsuma, zuciya, dakyar da rarrashi Fauziyya ta tashi tabi sahun yan uwanta suka fita a falon.

Shi kuwa Alhaji suna shiga dakinsa na Alfarma rungume Basma ya yi kamar karamin yaro, nan yashiga zayyana mata abubuwan da yaran suka fada masa, sosai ta razana ta yi jin ya ce ai yaso ya tausaya musu da ya tuno ba suda mutunci daga su har Uwar tasu ya sa ya yi masu rashin mutunci. Cikin tsoro da fargaba ta ce, " Alhaji Please in Yaran nan suka zo wajen ka karinga barin, ina magana dasu kar wataran su saka kayi abin da ba daidai ba ".

Da " to. " Ya amsa mata kana suka samu zama kan lallausan Gadonsa me kamar na zinare.

Cen bangaren.

Mama cikin kuka ta ce, " nace kada kuje kuka tafi yanzu ma yakara kiranku da ya'yan shegu ko? ". Cikin kuka Fauziyya ta ce, A'a Mama be zagemu ba, kawai ce mana ya yi beda kudin kaiki asibiti, wannan dalilin ya sa muke kuka. Sallamar da akayi ne ya sa su kai dubansu a kan ya'yansu Faruk hannunsa ɗauke da ledar magunguna ya karasowa duk abin da suke fade yana jinsu a bakin kofa, cikin kayan kanikancinsa masu datti gareji ya karaso wajensu yana share kwallan da ya taru masu kwarmin idanunsa, cikinsassaita nutsuwa da mutuwar jiki ya ce, " Fauziyya ban so ku ka je wajen Alhaji Isah ba, ya ce mu ba ya'yansa ba ne, wai meye kuke takurawa sai kun dagantaka kanku dashi ala dole ". ya kai karshen zancen cikin takaici.

" Akul ". Shi ne furucin da Mama ta furta, kana ta dan soma gyara kwanciyarta, hakan ya sa cikin hanzari suka taimaka wajen zaunar da ita. Cikin nishi mai wuya da take fitarwa ta ce, " Umar kar ka kara kiran Mahaifinka da Isah, ko babu komai shi ne ya haifeku, baku da Uba bayansa". ahankali takarasa zancen nata cikin mawuyancin hali.

Faruk ya ce, " A'a Mama kidaina dangantashi damu ya ce, mu ba ya'yansa ba ne, Kinga  ba suke nan ya san Mahaifinmu". yakarashe zancen cikin kuka.

Mama kasa magana ta yi ban da hawaye babu abunda ke bin kyakkyawar fuskarta. Nan dai suka yi ƙoƙarin ganin sun bata magani tasha. Faruk kuwa hanzarta komawa wajen aikin nasa ya yi, su Fauziyya kasantuwa dare ya yi itada yan uwanta ban da Autarsu, tashi sukayi domin tafiya gida dasu da yan kananun yaransu, cike da kuka sukayi sallama da Mama acewar su gobe suna nan tafe, Autarsu Yasmin har waje ta rakasu, inda suka biya wajen kakarsu Hajiya Mariya domin suyi mata sallama, suna shiga sashinta, razana sukayi ganin yanda, tajika garin tuwo a kwano ta zuba masa ruwa tana ƙoƙarin shanyewa dan tsananin yunwar da take kwasarta. Agigice Yasmin ta karasa wajenta baki na rawa ta ce, Inna yaushe kayan abincin naki suka kare?. " Murmushi dole ta saki cikin danne damuwarta ta ce, au ashe su Fauziyya kuna cikin gidan nan, kawai dai na dai jika ne dan an ce yana maganin olsa. "

Zazzare idanu su kayi daga Fauziyya har yan uwanta, tabbas kukan kurciya jawabice mai hankali ke iya ganewa, cikin hikima ta ba su amsa ba tare da budaddan zance ba. Hawaye ne kebin fuskar Yasmin har yayyenta, share kwallan da ke shatata a fuskarsu suka yi, nan dai Fauziyya taba Yasmin kudin da za ta yi cefane ta yi wa kakarsu girki, kana suka kira Faruk suka sanar masa kayan abincin kaka ya kare. Dagacen ya amsa da in sha Allah yana nan tafe dasu.

ABUJA CITY

Bayan sati daya

Amatullah, cikin damuwa, take kallon Papy jin yana fadin kudin hannunsu dari biyar kacal ya rage musu, kuma duk kayan abinci ya kare, cikin tsananin damuwa ta dau buta domin zuwa ba haya, nan da nan taji cikinta ya murda, tashiga bahaya yafi a kirga, tana samun sassauci ne ta dawo ta zauna a wahalce kusa da Papy da ya zabga uban tagumi, cikin dauriya ta ce, "Papy zanje ko Allah zesa na samu sadaka duk da nan ba kamar kauye ba ne ". Ta yi furucin cikin tsananin damuwa. Be iya hana ta ba dan ya san shi ba iya fitan zeyi ba.

Cikin muryansa da baya fita ya ce, Amatullah Please dan Allah kar kiyi nisa, kuma in baki samu ba, kidawo Gida kuma kar ki yarda wani ko wata yace ki bishi gidansa ko rakashi. " Gyada masa kai ta yi alamun gamsuwa, kana ta zura takalmi da hijab dinta tabar bukkansu. Tafiya take tana waigewaige tana isowa bakin titi, babu abin da ya fado mata a rai sai Salim, tunani take Allah ya sa asirinsa be tonu ba, to inhar ya tonu ta san yashiga tashin hankali, sosai ta zurfafa a tunaninsa tare da mance abin da yafito da ita daga gidansu. Horn din mota da ake yi mai karfi ne ya dawo da ita cikin hayyacinta firgit!! cikin tsananin mamaki take kallon Matar nan da ta. . . . . . . . . . . . . . . . .

Makauniyar Shari'a kuke bibiya kar ku bari  

Domin son magana dani kuna iya tuntuɓata a kan 09069080725

Share and comment please.

SHAFI NA UKU

Nan da nan ya kama hannunsu, suka boye bayan wani kantin, wani bawan Allah da besan suna wajen ba, cikin tsananin tsoro suke kallon yanda suke tafiya irin na iska, daya daga cikinsai fadi yake, " ai sai mun mata fyade kana mu binne ta, shegu tarkacen Fir'auna ". ya kai karshen zancen ya yin da suke doshi hanyar jejin.

Ganin tafiyar su ne ya sa suka fito daga buyar ta su, cikin azzama da sauri suka karaso bakin titi, ban da bugawar zuciya babu abin da kake ji, Fat ! fat ! fat ! tafiya me dan nisa su kayi kafin suka samu motar daya debo fasinja, hannu suka fara yiwa motar alamun yatsa. Motar fakawa ya yi daga gefe daya, Drever da ke kallon su, ta cikin motar, cikin daga murya yace, " ina zakuje ne?. " ya yi magana me nuni ahanzarce yake. Cikin rawar murya Salim yace " malam motar ina ce?".

" Abuja za mu je ". Direba ya bashi amsa a dakile.

" su ma cen suka nufa. " ya yi magana yana me zaro dubu biyar daga Aljihun wandonsa, mikawa dreba ya yi tare da fada wa drever ba su da kaya. Babu bata lokaci suka shige motar, bakinsu na rawa suna shirin yi wa Salim godiya, drever yaja motar cikin hanzarinsa.

Salim kuwa durkushewa ya yi a wajen yana kuka mai tsuma zuciya, domin Allah kaɗai ya san irin kaunar da yake wa Amatullah yau yana ji yana gani ya rasata a kauyen. Ganin kukan ba mafita ba ne ya sa kama hanyar Gidansu, tafiya yake duk babu kuzari ajikinsa.

Amatullah cikin motar, sauran fasinjojin sai rufe hancin su, suke sakamakon cika su da wari da sukayi. Cikin fada wani yace, " bayin Allah, ya zaku shigo mota kuna doyi, haba ai wannan cutarwa ce. "

Amatullah da Papy kasa magana sukayi sai kif kif da idanu suke domin su kansu sun san suna wari, to amma ya za suyi da ƙaddararsu tun da akauyen ba kullum suke samun dibar ruwa ba.

Bangaren Mata san

Su na isa suka ga babu su, babu alamunsu, sai kayayyakin su da ke wurin, ganin hakan ya sa suka fara dube-duben ko sun dan fita ne su dawo, sun fi minti talatin suna jiran tsammani, daya da ga cikinsu ne ya yi karfin halin fadin, " anya ba'a samu munafukin da ya zo ya sanar mu su ba kuwa?. " ya yi magana cikin kaduwa.

Babu abin da ka ke ji a jejin sai tashin hayaniyar su, suna fadin " wallahi koma waye ya fada musu ze fuskanshi hukunci". cike da takaici suka baro jejin suna tafiya suna yarfa hannu, alamun tarin damuwa.

Aguje cikin azzama suka karasa Gida inda suka sanar da rashin nasarar su, mamaki ne yakamasu, jin wai ba'a gansu ba. Kannen Salim su kace, " Baba ina Salim yaje tun dazu da sai yanzu ya dawo, wallahi muna da yakinin shi ne ya fitar dasu ". Su kayi magana cikin confidence.

Nan da nan hantar cikinsalim ya kada idanunsa su ka juya daga fari zuwa ja, cikin tsoro da rawar murya da in'ina da ya zo masa lokaci daya yace, wan. . . . nan. . . . wa. . ni. . . . i. . ri. . . ma. . . . ga. . na. . ce, Au. . . wal. ". ya karashe maganar cikin kaduwar harshe.

Auwal yace, " wallahi kai ne ai rannan da kofinta ya fadi, kowa yaki daukar mata kaine ka dauka ka bata, kuma kana yawan zuwa kai musu abinci, daga magana fa nan da nan ka rude, kasan mara gaskiya ko a ruwa gumi yake ". ya karashe zancen yana tabe baki. Ran Iyayen nasu ya yi matukar ɓaci, cikin takaici Baban Salim ya hau dukansa duk inda ya samu ajikinsa, ganin be gamsu ba, yace wa'yannan mata san da su tara masa gajiya. Cikin kuka ceton rai, Salim yace, " ba ni ba ne bansan wanda yafitar dasu, Auwal karya yake min, don Allah ku fahimceni". ya karashe magana murya a rude. Baban Salim cikin takaici da haushinsa yace, " wallahi in baka fadi inda suke ba a jejin nan zakasha na jaki ". ya yi furucin iya gaskiyarsa. ban da hawaye babu abin da ke kwaranya daga idanun Salim, kin magana ya yi hakan ya sa Mahaifinsa ya bada umarnin a masa duka. Sosai suke bugunsa, muryarsa kasantuwa dare ne saida ya karade gidaje mafi kusa dasu. Saida mahaifiyarsa tasa baki ganin yanda hancin Salim ke fitar da jini, tsorata tayi, arude ta kama d'anta ta yi cikin gidan dashi tana tafka salati wanda ya sa gabakidaya kowa da ke wajen rikicewa harda masu bugun nasa.

ABUJA CITY

Ridwan sai karfe goma ya dawo Gida tun fitarsa, Sallah, ya na karasowa yaga dukan kannensa a falon ban da Mamyn a cikinsu. Gaisuwar da suke masa ya samu damar amsawa fuska asake, kana ya kai dubansa a kan Faisal da ke kallon tv, cikin zazzakar muryansa ya ce, " ina Mamy ta ke?. " ya yi furucin cikin kosawa da jiran amsa. Cikinsakin fuska da murmushi Faisal ya ce, "ai tun da ta je sallah isha'i bata dawo ba ". ya karashen zancen ya na mai ƙoƙarin bin hanyar dakin Mamy domin dubota. " Dakata. " ya ji muryan Ridwan ya doki dodon kunnensa. Cak ya tsaya tare da waigowa, fuska a sake yana kallon yanda yake juya labbansa.

" Ba sai ka je ba kyaleta, za mu hade da safe in sha Allah. " ya kai karshen zancen tare da hawa kan matakalan step cikin nutsuwa da haibarsa.

Anisa da Rukayya cikinsanyin murya suka ce, " yaya Faisal Please dawo ka ci gaba da kallonka, domin yaya Rid lamarinsa sai du'a i. " Samun kansa ya yi da bin maganganunsa, mamaki fal acikin ransa, cikin damuwa ya ce " bansan me ya sa ya'ya Rid kwata kwata babu walwala arayuwar sa ba. " Anisa kwabe baki ta yi tana kallonsa cikin gajiyawa da zancen yayansu ta ce, " ba mamaki shi haka Allah ya halicce shi kawai dai, shi bame son hayaniya ba ne ". Rukayya da ke jinsu cikin yar dariya ta ce, " ku kyale yayan mu ya huta haba kunsan yawancin yayye maza basa son kannensu su rainasu". ta kai karshen zancen tare da mai da hankalinta a kan kallon TV. Faisal da Rukayya sosai suka shiga juya kalamanta suna murmushi.

 

Bangaren Amatullah da Papy sai karfe shabiyun dare kusan karfe daya, motar ta faka a Garin Abuja direct tasha a ka saukesu. kasantuwa Dare ne ya sa ba duka suka samu damar tafiya gidaba. Amatullah bayan sun biya kudi, wajen Masallaci da ke cikin tashar suka samu wuri suka zauna itada Papy ga mamakinta, ganin Papy ta yi ya dauko rawani yana daure kansa, ya kuma zagaye fuskarsa dashi baka iya ganin komai sai kwayar idanunsa, ma'ana shigar buzaye ya yi. Amatullah ganin tsohon dare ne, hakan ya sa bata samu damar ce masa ya ajiye rawanin ya huta mana.

Kiran Sallah farko na Asuba a kan kunnensu, cikin rarraba idanu Amatullah ke fadin " Papy ban da suturar kirki a jikina ga shi muna cikin babban gari, kuma har gyalena na barshi acen kauyen ya zanyi. " ta karasa maganar cikin damuwa. Ganin ana ƙoƙarin ta da sallah ya sa be tsaya bata amsa ba, kai tsaye alwala ya dauro, cikin hanzarinsa ya yi cikin masallaci. Ana idar da sallah ya fito, cikin rashin kuzari da rashin sabo da inda su ka zo. Hango Amatullah ta zabga tagumi ya yi ba karamin shock ya shiga ba nan da nan idanunsa su ka cika da kwalla, murya a disashe ya ce, " Amatullah !! kina ba ni tausayi, Amatullah!! Bansan yan da zan miki bayani ba, Amatullah !! Amatullah. " ya karashe kalamansa cikin kuka mai gunji. Barci barawo ya yi awon gaba da ita, bare ta san halin da ya ke ciki. Be tashe ta ba illah kai tsaye wajen wani mai shago ya nufi ganin shi ne farkon wanda ya fara bude shagonsa da sanyin safiya, cikin muryansa da sam bayason a tantance ya shake murya cikin kasa kasa da murya ya ke tambayar inda ze samu doguwar riga da hijab, mutumin kwatance ya masa, tare da tabbatar masa sai karfe wajen tara na safiya suke bude kantinsu.

Kauyen Daguzau

Iyayen Salim cikin tsananin damuwa suka fara shawarar, kai Salim Asibitin Murtala da ke cikin jahar Kano, kasantuwa yanda ko kwakwarar motsi baya yi, Mahaifiyarsa cikin rudani ta ke fadin " gaskiya baku kyauta min ba, a kan zarginku na banza! da wofi kuna neman kashemin D'ana ".

Babu wanda ya tanka mata ganin yanda duk ta rude ta fita hayyacinta. Burinsu be wuce ganin ankaisa asibiti kai tsaye ba. Baban Salim cikin ban hakuri yake rarrashinta dan ya san sun tafka kuskure mai girma.

Kwanaki suna shudewa inda yau sati daya Amatullah da Papy suka yi a Garin Abuja a unguwar Ghetto, dan karamin bukka suka kama haya, tare da siyen duk abubuwan bukatunsu, ciki harda botiki da tsontson wanka da brush da makilin harda sabulun wanka, sabuwar butar da suka mallaka bakaramin sanya Amatullah jin dadi ya yi ba, haka ma yanzu da take ganin tana da sutura har kala biyu, haka ma hijab da takalmi, tukunyar tuwo dana miya da plate da cokula har da kofi da botiki wanka dana shan ruwa, ba karamin sanyata a nishadi ya yi dan wannan shi ne karo na farko a rayuwarta data ga sun mallaki sabbin abu na kansu. Cike da jin dadi ta dauki sabuwa katifar soso wanda ta shimfidawa zanin gadon gwanjo. daga katifar ta yi hade share dakin, ta gyara shi tass kana ta dawo ta zauna tana kallon yanda Papy ya zabga Uban tagumi kamar bashi ba. Har ta bude baki za ta yi magana sai taga ya lumshe idanunsa kamar me shirin yin barci, ƙoƙarin kai hannunta take domin kwantar dashi, cak ta ji muryansa cikinsanyi da nutsuwa yana fadin" Ba fa barci nake ba ". daga haka be sake furta komi ba, yaja bakinsa ya yi shiru.

Kallon kallo take masa tana son ta fahimci wani abu tattare dashi to amma mene ne? Wannan abun ta san babu wanda ze bata amsa sai shi da kansa. ƙoƙarin yin magana take, ya yi hanzarin fadin" Amatullah dauko min Rediyo dina in kunna domin debe kewa ". ya yi furucin cikin yanayin damuwa. Babu musu ta mika masa kana ta kasa kunne jin yana chanza tasha har ya zo kan tashar Dala FM na Kano kasa kunne ta yi domin ita kanta tana son sauraren rediyo musamman in ansanya shirin Farar Saka. Jin labaran Duniya ake yi ya sa ta danyi karamin tsaki. Papy kuwa sosai ya razana jin Muryan Hajiya Rabi mai Iko, nan da nan ya dimauce ya nemi nutsuwarsa ya rasa, Amatullah sosai take hankalce dashi, kasa kunne ta yi domin jin abin da ake fade a rediyo.

Ga abin da ake fade daga cikin rediyo kamar haka.  

Hajiya Rabi. . . . . . . . . . . . . . . . . . . . 

Littafin nan, na kuɗi ne. Da zaran free page ya kare za ki daina ganin sa. Hanzarta ki biya naki kada a yi babu ke.

Kibiya dari biyar kacal domin samun shiga group na musamman.

Domin Karin bayani a tuntuɓe ni ta wannan lambar 09069080725 ko + 22953726162.

Siyen nagari mai da kuɗi gida.

Post a Comment

0 Comments