Ticker

6/recent/ticker-posts

Makabarta (Maƙabarta)

1. Ran da duk kwana ya ƙare,
 Maƙabarta za a kai ka.

2. Bar gadarar kafi kowa,
  Watakil a ciki su fi ka.

3. In gadarar kyau kike yi,
 To ki shafa Bula da Toka.

4. In sarauta ce ta jaka,
 Ɗan uwa ja rawaninka.

5. In giyar mulki ka kurɓa,
 To ka dubi mazan gabanka.

6. Ba batun girman fuloti,
  A cikinta saka a ranka.

7. Yadda aka yi wa talaka,
 Haka za a yi wa gwaninka.

8. Ba a yin zaɓen aboki,
  Ko maƙoci ɗan uwanka.

9. Wanda duk Allah Ya kawo,
 Za a sa shi jikin gidanka.

10. Watakil mace kamila ce,
 Ko ko ɗan wiwi kamarka.

11. Har da gun yara cikinta,
 Ba ta bambance yarenka.

12. Ba ruwanta da ɗan sarauta,
 Ko ko wanda ya rayu bunka.

13. Za a gansu suna maƙota,
  A cikinta da so da kinka.

14. Ga na Mudi mai tumatur,
  Ga na sarkin zamaninka.

15. Ga gidan Idi mai gadi,
  Ga na mai mulkin ƙasarka.

16. Ga na fes ledi Samira,
 Ga na mai kosai a kaka.

17. Maƙabarta kin ci suna,
 Naki, mai saka wasu sarƙa.

18. Wasu sun mance ki tabbas,
 Shi ya sa nai miki waƙa.

19. Ran da duk zan je cikinta,
  Rabbi sa ni a ni'imarka.

20. Ɗanbala ya rubuta waƙar,
 Ya rufe da yabon GwaninKa.

Da fatan mun sha ruwa lafiya.
Mohammed Bala Garba
9:13pm
6 Ramadana, 1444AH
28 Maris, 2023.

Post a Comment

0 Comments