Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Cancanta (Kashi na 21)

Cikin abin da bai wuce awa ɗaya ba muka ƙaraso Gwarzo kayana aka saukemin ganin jiran samun napep za ta zamarmin aiki machine na hau ba dan na saba ba, nafi sabawa da napep tafi sirri jakata na gaban machine ina baya duk sai na ji daban sa'ata guda ma hijabi nasa, unguwar da zaikaini na faɗa masa sabuwar unguwa ke nan har kofar gida aka saukeni na sauka na bashi kuɗi ya saukemin jakata ya wuce gidan su Abbah nake kallo babu laifi gidane mai kyau da ƙaton gate ɗinshi tunanin rayuwar da muka bari kuma muka dawo nake yi a lokacin da nake kallon gidan, muryar Rumaisa da na ji ta dawo dani daga tunanin da nake yi

"Yaya Sumayyah oyoyo"

Kallon Rumaisan na yi da murmushi fuskata

"Rumaisa daga Ina kike haka”

Kai ta ɗan sosa” naje gidan Aunty Jamila ne”

Na kalleta” kya sosa ƙeya da kyau ai da safe kin Kama hanya gidan mutane, ban san tun lokacin da kika tafi ba, Ni kamamin jakarnan mu je ciki”

Kamamin ta yi muka fara tafiya, Rumaisa ta ce” A'a fa Yaya ban daɗe da zuwa ba Mama ta aikeni ma”

Na jinjina Kai muka ƙarasa kofar gidan tura kofar gate ɗin mukayi muka shiga da sallamarmu Hajiya da take zaune brander din dake gefen ɗakunansu, kallonmu ma bata yi ba bare amsawa dauriya na yi na ce” Hajiya sannu da gida, ina yini”

Tsaki ta yi min"na yi tunanin ai ansamu guri ba za a dawo ba, anje ana cin gajiyar Wanda ya yi aiki tuƙuru ya tara ba malalacin ubanku ba, ai danasan Hashim zai dauke ki gidanshi da ban amince ba gwara a barku ko za ku mutu cikin talauci, laifin duk na ubanku ne malalaci mai sakaran zuciya shi lallai so ya ƙi rabuwa da uwarku ya samu ko ya samu madafa ma”

Kallon Hajiya kawai muke harta gama maganarta sai kace mu tsarartane, wannan zancen nata kan kawai taƙi jininmu saboda kaf cikin 'ya'yan ta Abbanmu ne bashida wadata shi ne kawai abin da ya janyo hakan, ko dake ba ma ita ba har Baba Abbansu Abbah haka yake yin maganganunshi shi acewarshi ya gama dawainiyar karatu da Abbah ya zauna sakarci dan aikin ma ko koyarwa baisamu ba

Muryar Rumaisa na jiyo cikin zafin zuciya da ban san tana dashi” ai Hajiya arziƙi ba nufinmu ba ne mu kanmu ba haka muka so ba rayuwar tamu"

Ina ƙoƙarin tsawatar mata na ji Hajiya na ce wa” to mara kunya, ai Allah ya ce bawa na tashi na taimakeka ku yi zuciyar neman nakai ku yi kuɗi ba zuciyar maida magana ba ma rasa kunya masu gadonta Kun gada wajen uwarku fitsararriya mai mugun hali”

Saurin jan Rumaisa na yi da Jakarta tawa, zuwa ɓangarenmu, ni ma na san jan magana tane matar da sallamarmu bata amsa da za ta samu lada ina ga amsa gaisuwa ta, bayan na san halin Hajiyar ma sai addu'a ita indai ba ka da shi to ba abokin yinta ba ne,

"Yaya aida kin barni da ita ya za ta riƙa faɗama na magana mune muka halicci kanmu, Kuma duk maganarta tafi ga Mama, ai gwara Abbah ɗan tane shafuwarsu ce” cewar Rumaisa, ni ban san haka ma Rumaisa ta iya tsara zance ba kamar wata babba ko ni na tsara wannan zancen abin mamaki ne, wajen wasu, duba da ƙanƙantar shekaru na, saidai Rumaisa ta zuciyane da alama dan ita din magana ma bata dameta ba, shiru kusan shi ne amsarta sai kallo, abunda zai harzuƙata babbane ko ni bata min bare Hajiya kuma wadda ta haifi Abbah, muna shiga ɓangaren mu da sallamarmu, jin sallamata duka sukayo waje daga ɗaki sunamin oyoyo falon muka rankaya muka shiga mamah ce zaune da fara'arta ta kalle ni

"A'a Sumayya ba tsammani, haka ayam"

Murmushi na yi mata na zauna ni ma gefenta a saman tabarmar da take kai duka suma zama sukayi kusa dani

"Mama ashe kun daɗe da dawowa nan ko a waya ba ku faɗa min ba”

Murmushi mama tayi” To ya za ayi Sumayya mu ɗaga miki hankali, Mai gidan ya ce indai ba mu bar gidan ba a washe gari ya dawo waje zai fiddo mana da kayan ya gaji da zaman namu ba kuɗin haya, shi ne dai Abbanku shi ma ya fusata ya kwaso kayanmu muka dawo gida, a nan ɗin Baba da Hajiya dakyar suka bar mu muka zauna”

Shiru na yi Kamar ba zan yi magana ba saboda takaici na ce "yanzu ma mun tadda faɗan Hajiyar, Rumaisa saida ta tankamata”

Mama ta kalli Rumaisa” Kin kyauta Rumaisa kina gani tun da muka dawo zama baya mana daɗi shi ne Kika biye mata, saboda ki sani a wata matsalar, dama shirin naki na munafinci ne rashin kunya ce cike da bakinki ko?, ina sakwan nawa”

Rumaisa da kamar tasa kuka tace” kiya haƙuri Mama, abunne munata jin ciwanshi Hajiya bata kyautawa, Aunty Jamilar ta ce za ta aiko Shureim bata ƙarasa murzawa ba”

Mama na kalla da murmushi” Yau Mama taliya 'yar murjj za a ma na ke nan, na ji daɗi jallop ce ko da miya?"

Mama ta kalle ni da hararata "to da Maggi za a ci ba kuɗin siyo barkono ma, sai dai ƙila Jamilar ta haɗo mana dashi”

Na yi saurin girgiza Kai” A'a Mama ga kuɗin da Abbansu Halima da na Batul suka bani, na hau mota to sai yaya Baffa ya bayar ma”

Mama ta yi murmushi” Masha Allah, Allah ya bar zumun ci, amma da baki anso ba dai, wannan lokaci kowa na ta kanshi”

Sadik da yake ta kallona na san da magana bakinshi na ko ji ya fara” Yaya Sumayya ina tsarabarmu take "

Na ce masa” yanzu za a siyo ba dai biscuit da alewa ba na manta a mota ban siyo ba”

Na juya ga Mama "Yawwa Mama ina Ahmad ya zo ya siyo, na ga banji motsinshi gidan ba”

Mama ta ce” Lallai Sumayya kin manta Ahmad da kwallo ke nan tun da yau weekend ina za ki ganshi kuwa ai ya shige unguwa, sai yunwa ta ciyoshi kyaga ya dawo Kamar yaci babu, ga Rumaisa ko Khadijah sai ta siyo, ko Sadiƙ, Khalil ma yasan wajen ina rubuta masa shike nan"

Na ce "Haka ne Mama amma dai Ahmad nashan zagi wajen Hajiya da Baba na san"

Mama ta yi 'yar dariya” kema kin san za su fasa ne, haka suke ce masa mai zuciyar ubanshi sai iya ball ya iya yawan tafiya, ni kuma dama 'yar matsiyata ban san daɗin arziƙi ba bare nasa Ahmad ya tashi ya nema”

Dariya ni ma na yi na ce” Haba ainasan za a rina, ina Aisha take ne mama”

"Tana ɗaki tana barci, kin san Asma'u ta zo tana Katsina ƙila yau za ta dawo ta wuce gidan nata, wannan karan a motarta ta zo ma, ta fara driving tana baro cikin gari da motar"

Murmushi na yi kawai jin zancen Mama” kuna cikin wani rigimar ke nan Aunty Asma'u ai 'yar hau ce Mama wallahi, nifa banasan ma a ce muna da wani relationship"

"Kin ga Sumayya ba ruwanki da Asma'u duniya makaranta ce, karta kamaki ta lallasa, dan tun da ta gan mu gidan kamar jiranmu take ko gaisawa da Hajiya naje yi su Khalil kuwa ba damar suyi wasa da Haidar, da farouk, sai faɗa tayo kaina Kamar ni ce Khalil ɗin shi dama nata Khalil din ta hanashi wasa dasu ya hanu shi kuma, ai Asma'u tana taƙama da arziƙin nan, Kamar ita ta farayinshi”

Ƙagara na yi Mama ta kammala zancen Mai cike da ɓacin rai

"Wai mama ina Abbah na matsu na ganshi ne”

"Ba zai jima ba zai dawo kije ki huta haka”

Na miƙe jin kalaman Mama ina dafa cikina” Wallahi kuwa Mama yunwa ma nake ji, Sadiƙ ya siyo mana biscuit din Rumaisa ta siyo kayan miya mama Dan Allah ta manja za ayi mana, miyar jajjage, Rumaisa sai ta jajjaga ai greater dinmu na nan ko"

Rumaisa ta kalle ni” Kai Yaya Sumayyah bana son greating kema kin sani hannuna ya dinga yaji”

Mama ta kalli Rumaisa ta yi tsaki” waye to zai miki shi, Ahmad ɗin bayanan da Kika raina na saki aiki ki ce shi zai yi ya ce zai yi”

Dariya na yi na ce” Mama ai kin san tsakanin Ahmad da Rumaisa da amana ai”

Daganan na fice na shiga dakin gadon Mama saman katifarmu da take jingine na tayar na kwanta, barcin gajiya da na zafin duka ya daukeni mai wahala dan har lokacin bai gama zafi ba dukan da nasha bana wasa ba ne, kai kace sata na yi, biscuit ma ban tsaya jira ba sai barci 2:30pm na tashi, shi ma kukan Aisha ya tasheni na dauketa na fita da ita na miƙewa Mama nayo alwala na tayar da sallah ina idarwa Abbah na shigowa kallonshi na yi kawai dan da ganinshi a galabaice yake da yunwa Allah sarki Abbah, ni dai na san idan bai ci ba ba mai bashi kuwa ko Hajiya Kai kace ba ita ta haifeshi ba duk tunaninsu auren Mama ya ƙara tsiyatar da shi kuma dama shi tun asali ba shi da shi, ko da bai auren ba ba zai yi ba 'yan uwanshi masu san zuciya ne, sunfisan kansu a kan 'yan uwansu kamar ball suke bugashi yana musu dawainiyar da basa gani ba wanda yake niyyar masa cuku cukun samun aiki, saboda san zuciyarsu, ganin karatun nashi ya fara nisa ba’a bun yi yaga gwara ya yi auren ya tara iyalai shi ma, suko su Hajiya ba su damu ya yi ba, kuma bata gaji da ƙinshi ba saboda ba shida komai fafutukar karatu ya gama na masters yana gamawa ya tattagi aure ya rufawa kanshi asiri kafin Allah ya kawo abinyi girman gidan su ya sa part din Baba ya zama nashi ya sa Mamanmu ciki mamar tamu ba wai arziƙin shi ta kallah ba dan kam bashida shi ita ma nata iyayen haka mamarmu ce hope dinsu a kan sanadinta za su rage wani kukan, saboda yadda samari masu kuɗi ba ma kuɗin iyayensu ba ke zuwa wajenta, amma ta tsaida Abbah, da kanta ta tunkari matsalar ba wani ya tunkarar mata ba, halaccin da Mama ta yiwa Abbah shi ya sa ya kasa rabuwa da ita duk da hakan 'yan uwanshi suke so, duk da yasan rabuwar canjin alkhairi za ta zamarwa Mama amma shi tashi rayuwar da makomarmu kaɗai yake kallo da tausayawa, zuwa yanzu da al'amuran suka sake rincaɓewa, maganar Abba ta katsemun tunani na

"Mutanan katsina, yau kike tafe ashe”

Kallon Abbah na yi da ko a yana yin maganar a galabaice yayi

"Eh Abbah sannu da zuwa”

Mama na jin muryar Abbah ta yi saurin leƙowa

"Abbahn Sumayya kazo ga abinci, tun fa safe ba kaci komai ba, sai ku yi maganar zuwa anjima”

Cikin falon ya shige ni ma bin bayani à Abbahn na yi muka zauna zaman cin abincin lokacin har Ahmad da banji shigowar shi ba, sai lokacin na ganshi, kallonshi na yi

"Lallai Ahmad ayawo ke nan, koma ka zo mu gaisa ka san ina cikin daƙi”

Kai ya gyaɗa "Barni Yaya yunwa nake ji wallahi, yanzu Mama ke faɗa min kindawo ƙila kin tada sallah, na ji yunwa, muci abinci ke dai kawai”

Dariya na yi kawai "Ana ta shan ball har 2 bance ma kayi sallah ba”

"Kai Yaya da wannan ranar wata inuwa muka samu muka kwanta ne, saida mukayi sallah, tukunnah, na taso na dawo gida”

Da haka na zuba abincin nafara ci kamar kar ta kare Saida na ƙara wata inason taliya ta murza d miyar jajjage ta manja sosai musamman ta sha Maggie star Ina tayiwa Mama Santi har muka gama, Abbah kuwa wani plat mama ta taƙe masa saida ya cinyeshi tas, hannu duka muka je muka wanko aka buɗe faifan fira, Abbah Mama ya kallah

"Hauwah taya aka samu kuɗin cefane?, harda wannan miyar haka mai daɗi gaskiya da da kuɗin gobe ma ita za mu yi”

Mama dariya tayi” Ka san dama wajen Asiya na samo fulawar to ɗiyarka Sumayyah na zuwa ta ba da kuɗin na motane da Abbah Ahmad, da Abbansu Halima suka bata sai shi Baffah ya biya kuɗin motar"

Abbah ya yi murmushi "Allah sarki na ji daɗi Sumayyah, Allah ya yi miki albarka, zanko kira su na musu godiya, ya Kika taho haka”

Hawayen da ke ƙoƙarin fitomin na maidasu ina girgiza kai, abunda ya faru duka na zayyana wa Abbah da Mama saidai ko zancen wata soyayya tsakanina da Yaya Samir duk ban ba su ba iya dukan da nasha wajen Abbah, na fadamusu, ina tunanin Zan sake dagula lissafin su Abbah da wannan zantukan, ina tunanin Zan samu daidai dani ne, ba wai Hamid ko Yaya Samir ba, sai yanzu nake jin Ina ma na karɓi Yaya Hakim amatsayin halaccin da zanwa Halimah, amma dakaina naƙi amincewa saboda wasu tunanuka nawa da ban tabbatar da har lokacin Firdausin na tare da Yaya Hakim ba amma dai na barshi da zaɓin shi na asali da addu'ar Allah ya daidaita su.

"Yaya Kika zauna Abbah Hashim ya doke ki haba dan Allah, a kan ƙaramar matsala, shi to wanda kika ce ya zo wajenki har haka tafaru me ya sa yaka sawa Abbah Hashim bayani dalla dalla cewa saƙo aka bashi ya baki to ina ruwanki da alaƙarsu da Fatimah kince ba ma ki jima ba, kawai mu dai ba’a ƙaunarmu ne kawai, mun zama bare ne, saboda ba muda shi, amma Allah bai manta mu ba, yana sane damu da halin da muke ciki ubangiji ke azurtawa samu da rashi na shi ne, ba ma tunanin akwai mutumin da zai tsiyatamu ko azurtamu face da izinin ubangiji”

Kukan da yake cin zuciyata na fashe dashi, da jin maganganun Ahmad yana magana Kamar wani matured saboda yadda rayuwar ta zo mana muka samu experience na rayuwar da muke ciki, ƙaryar da na yi ke nan, na barwa Fatima Hamid zancensu ma bana so na ji na sake tsanar tun karar rayuwar su Abbah Hashim ko da a cikin mafarki bare ido buɗe, na sake tunawar yanzu da idona da kunnena duk na fahimci tsanar tsantsa da akemana a dangin Abbah da sune ginshiƙinmu wani kukan na sake fashewa dashi

Abbah da kwallah ta taru idan shi

"Haba mana Sumayyah ki bar kukan haka za ki sake tayarmin da hankali kina tasomin da abunda ya yi shekaru yanacin zuciya ta Ina ƙoƙarin rayuwa kamar kowa da aza farin ciki a rayuwata, na sani tun asali 'yan uwana basa ƙaunata hatta da iyayena da matsalolin rayuwa ta janyomin haka, da na San haka za ta faru da ban turaki gidan Hashim ba, duk yadda na nisanta kaina dasu Samir ya janyo hakan da wata ɓaraka a tsakaninki da Samir ta faru da ba zan iya yafewa Samir ba, na rasa ina zan yi na samu rayuwar yadda nake mafarkin samunta, da ba mamarku ban san ya duniyata za ta ka sance ba amma ubangiji ya sa ta zama mata ta ta bawa yarana tarbiyya a halin da muke ba su taɓa daukemin magana da za ta tadamin hankali na, na san Allah na tare damu da duk mutanan ke cikin mawuyacin hali irin Wanda muke ciki”

Ahmad da shi ne kaɗai bai tashi ba dan duk su Rumaisa na waje, suna Shirin wanka, muka fara zancen Ahmad ya kalli Abbah

"Dan Allah Abbah kada kayi kukan kaike sake kwantar mana da hankali idan ba ka ciki namu ba zai kwanta ba, ku muke kallo muji hankalinmu na ƙara kwanciya kuma a halin samu da rashi muji za mu iya rayuwa ko mun ci ko da ba mu ci ba ɗin"

Mama takallemu Ni da Abbah"Haba dan Allah kun ta samu kunata hawaye da kuka kuna tuna abubuwan da ba su da anfani kuna nema ku jefawa kanku wani ciwan daban, idan kun yi waye zai taimakeku bayan ubangiji, yanzu rayuwa ta canza kowa kanshi ya sani sanda kake da buƙatar taimako ba’a yima shi, idan kuna tunani haka ciwo za ku sawa kanku, waye cikinmu abun baya damunshi, amma mun tuna ubangiji is there for us"

Sainake jin zancen Mama kamar ba’a hayyacinta take ba Kamar ba da jin daɗi ita ma take ba, kasa cewa komai na yi, sai Abbah

"Na gode Hauwah, insha Allah na daina, dama daɗewar da kikaga na yi ban dawo ba gidan haya na fita nema, Baba ya ce yana buƙatar bangaren shi Asma'u za ta zubamasa kayan furnitures ne, toh shi ne dalilin jimawar tawa, na ba da cigiya, wajen Musa abokina, kuɗin hayar a hankali na biyasu, ke kuma saiku Kama sana'a da yaran nan ko awara duk gatanan yara na yi bakin titi waɗanda sunfimu rufin asirin ma zama ba wata sana'a ba daɗi yara ƙara girma sukeyi, ga karatun Sumayyah ma sai ko Neco kafin Fara biya a samu hanyar Allah nada yawa sai a biya mata ta zana takardun nada anfani ai, an fara a kammala daɗi”

Mama na gani tana share hawayenta ta maida kallanta ga Abbah"Yanzu shi ma Baba hardashi a irin wannan maganar idan ba ka ban san yadda rayuwarmu za ta ka sance ba, na ji nadamar dawowa ta, har gwara a fiddo mana kayan waje ba za mu rasa na Allah da za su taimakemu su ba mu matsugunni, wallahi zumun ci da iyaye a rayuwar ka da ta 'ya'yan ka ta kasa tasiri, Kaya haƙuri ko ubana ya yi hakan zan faɗa da zafin zuciya, yaushe yama maganar ba ka faɗa min ba?"

Abbah ya ce” da safe ne zan fita mukayi karo da shi shi ma zai fita gaisuwar ma tawa bai ansa ba sai ƙudirinshi da yake cin shi”

"Bakomai gasu ga Asma'u nan da sauran insha Allah watarana za mu samu canjin rayuwa ko ma Ya ne, ubangiji na tare damu, ba za mu taɓe ba madogarar duk lamura Allah, waman yatawakkal Alallahi fa huwa hasbuh"faɗin Mama

Mama tana da ilimin addini matuka, Kai kace ta yi haddar Alƙur'an zallar biyece da tasa harta kusa haddar saboda tilawar Alƙur'an, shi ya sa rayuwar mu ta zama kafin mu kalli kowa a lamuranmu tom ubangiji muke fara kallo, shi ne mahaliccinmu majiɓancin lamuranmu, saina ce Abbah ya yi dacen mata matuka, Kai duk ma 'yan uwan mama haka rayuwarsu take sunasan taimako musamman garemu ba su kyashin su yima Mama komai suke da shi, dama saina ce zamanmu a nan ɗin ya fi mana daɗi a kan kanon matsalar su Hajiya ya sa Abbah kwashemu, a nan ma ina cikin ƙawayena sa'annina da suke familyn mama ne, Dan ni ba ma kowa na sani a familynsu Abbah dan duk tafiyar tasu kalar ta guda ce su dai ba su ƙaunar talaka, babu laifi suna da rufin asiri, ne shi ya sa, miƙewa na yi Kamar an tsikareni bedroom na shiga na lalubo jaka ta na ciro wayar da kawun yaya Samir ya ba ni da kuɗin da Yaya Samir ya ba ni na dawo na ajewa Abbah su a gabanshi kallona ya yi da firgici

"Sumayyah ina kika samo wayar nan iPhone 11promax na ga an rubuta a kwalin sai wannan kuɗin za suyi 20k"

Murmushi na yi na yiwa Abbah bayani tare da faɗar abunda na ga ya cancanta ayi dasu

Murmushi ya yi Abban da Ahmad ya dauki wayar dake cikin kwali yana dubawa

Abba ya ce” Kai Ahmad ajiyeta haka, ka san babba ce, yanzu shi Mahmud ya miki wannan kyautar haka, lallai Mahmud ya yi kuɗi sosai Asma'u taƙi shi, gashi sanadinta ya miki wannan kyautar, dama Mahmud banji zai jure halin Asma'u, dan sai addu'a, Asma'u arziƙi na mata hayaƙi a kan nan nata, Allah ya sa kada labari ya sameta Mahmud ya siya miki wayarnan sai ta ce za ta yi wata maganar"

Ahmad ya ce” Kuma Abbah sai ka barta ta yi, irin wannan wayar muka Saida ai mun warke insha Allah, ina ganin ta a wayar abokina hotonta, Abbah shegen tsada gareta na ba ka labari wannan wani Mai amanar zaka sa ya Saida mana”

Mama ta ce” Ai koni kan wayarnan idan Asma'u ta ce za ta yi wani haukan ban kyaleta, yawwa sai Abbah Musa ka bashi ya siyar tun da ya fika sanin garin yanzu"

"Haka ne Hauwa'u shi zan kaiwa, Sumayyah ki cire layi idan akwai a ciki”

Da toh na amsa na karɓi wayar na cire, saida na cire na kunnah nagoge message da na turawa Hamid call logs ma ban kalleshi ba banji inada matsala da shi "

Mama Kam da Abbah ubangiji suka riƙa yiwa godiya da ɗaga hannunsu ubangiji mai taimakon mutum ba da saninshi ba, ji muke kamar talaucinmu ya yanke a dalilin hakan, lallai na ga ribar taimako ba ka san mai zai haifar ba ko ya kayi shi a dalilin kyautar da mutumin ya yi a zuwan ba komai ba ce, mu tana shirin zamar mana komai ɗin, Ni kaina a mafarki bantaɓa tunanin zan taɓa danna babbar iPhone haka na dauketa sai dai na ji ta a novels budurwa mai aji da nasaba da kyau da kuɗi ta riƙe wadda ita a wajenta bakomai ba ce amma a wajena ta zama komai, ni kam waya tazama jarina, ko da za mu faɗi amma za ta toshe mana wasu kafofin da damuwoyin da suka tunkaromu, da hatta iyayen Abbah sun kasa magance mana koƙarin tura mu suke ma. . . . . . . . . . . . . . . .

 **** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604
Na Cancanta

Post a Comment

0 Comments