Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Cancanta (Kashi na 22 - 27)

Na Cancanta (Kashi na 22)

A washe garin ranar da na dawo Aunty Asma'u ta dawo daga Katsina da zallar abunda yafaru dani acan ta dawo ƙarya da gaskiya, haka suka tattara maza da mata a gidan suna maida yadda aka yi Abbah ne da yaji Hajiya ta fara zaginshi a kan zancen har tana cewa bai ba mu tarbiyya ba mu tattara mu bar mata gida ba za ta iya ba kar a ɗebo mata abun faɗa a gari ashe shi ne sakamakon komawa kanon da Abbah ya yi saboda mu zamar masa jari yanaso yaji daɗin mu zama 'yan iska har yaran 'ya'yan masu kuɗi suna sona inba da lalata ba dame za su so ni ina 'yar matsiyata tana sake jaddada za su ga ƙaryar Hamid Fatima za su haɗashi da ita suga ko gaskiya yake yi zancen ni dama munsa ba lalata a Kano bincikeshi za suyi inko suka samu bahaka ba ne Kuma yaƙin amincewa da Fatima to ita ma ba da yawunta ba a kan Abbah ya aura ma Hamid ni saboda ban cancanci aure a zuriyya irintasu Hamid ba, su Aunty Asma'u da Abbah Jafar ƙanin Abbah ba ne shi ma sai Abbah Imran suke sake zuga Hajiya suka rufarwa Abbah da cin mutuncin su Aunty Luba kuwa su tunzurawa sukeyi da sake cin mutuncin Mamanmu suna faɗin sun yafeshi ga Hauwa'u, ina tsakar gidan ina share bangaren Hajiya nake jiyo zancen nasu har na gama ba su gama ba, shiko Abbah sun hanashi tasowa dama na yi tunanin haka za ta faru ko fiye da hakan maganar wayar da banji anyi ba tunanina ya ba ni ko ba su san zancen ba inako Shirin barin wajen na ji Aunty Asma'u na cewa” Ai iskancin Sumayya harda tsohon saurayina ƙanin wannan matsiyaciyar matar ta Yaya Hashim, matsiyata ne fa ba suda komai indai ba lalata sukeyi da Sumayya ba, ina xai kwashi maƙuda kuɗi ya siya mata waya iPhone kunsan tulin kuɗin da ake siyan wayar kuwa”

Hajiya na ji tana ƙoƙarin rushewa da kuka” Abdullahi yanzu mazinaciya kake ƙoƙarin maida 'yar ka ta tabbatar shi ne dalilin turata Katsinan ke nan, Hashim kuma yayi min waya namanta ma ya ce ko ku fito masa da ɗansa ko ya maka ku ƙotu"

Abba murya rau rau na ji yana cewa” Hajiya Dan Allah ku daina jifan 'yata da kalma Mai muni kalmar zina, duk talaucinmu da halin da muke ciki da rashin taimakonku insha Allah ba zan haifi mazinaciya ba, koni nasa ta ta yi zina dakaina ni uba, danasan abin da Hashim zai sakamin da shi ke nan da ban amince Samir ya daukarmin 'yata ba, sun tozartata a ƙarshe ya Mata dukan da koni uba ban taɓa yimata ba, Kuma yana jifana na boye masa ɗa, ina kiranshi ya zo ya yi min duk abunda yaga zai iya yi, kuma Ni ban taɓa ma 'yata sha'awar aure nan kusa ba bare ma mai kuɗi”

Abba Imran na ji muryarshi yana kuma tafa hannu"dama Abdullahi ina zaka yi sha'awar aurar da Sumayya kana ƙoƙarin maidata karuwa tana kawoma kuɗi, wallahi Hajiya fitinar da ke damun al'umma ke nan yara 'yan 17, 18 zuwa sama sun zama karuwai ƙarfi da yaji saboda sun haɗu da uba mai matattar zuciya, kuma mata da maza yaran manyan ke wannan shaiɗancin dasu wayasan mai Mahmud ɗin ya yi da ita ya bata wannan wayar"

Hajiya tasake rushewa da kuka” Abdullahi ka cuceni kuwa ashe da mazinaciya nake zaune a cikin gida, shegiya munafukar yarinya kalar uwarta, tun da na haifeka abun goma ba zan ce wannan ɗana Abdullahi ya ba ni ba, wallahi ba zan iya zama da ku ba inko na zauna daku tsinke na daina daukewa saidai mazinaciyar 'yar ka ta yi shi”

Abbah a fusace na ji ya fara magana” Hajiya ki dakata iya nan da izinin ubangiji ban haifi mazinaciya ba kaf 'ya'yan da na Haifa da zuriyyar su Kuma ba Wanda cikinku nake bi da baƙin baki, Kuma rashin taimakon da kuka kasa yi min, aiki kuka kasa samarmin bai hana Ina kyakkyawar rayuwa ba Mai tsafta zama cikin ku Kuma na barshi ke nan, ke uwata ce amma kan talauci na gaji da munanan kalman da kike jifana da shi da matata harda 'ya'ya ma yanzu, kuma ni Hauwa'u ko wacce 'ya za ta haifarmin wallahi ta fiyemin harke a gurina na gaji da cin mutuncin da kukeyi min, ba ni na halicci kaina ba, kuma 'ya'ya na wallahi sun fiyemin kaf 'ya'yan ku daga yau Zan iya cewa babuni babu ku gida kuma ku Bari mai gidan ya zo ya koreni da kanshi ba zan rasa inda zan tsugunna ba da talaucin nawa, za a karɓe ni”

Kofar ɗakin na je na tsaya ina zubar da hawaye ina jin yadda Abbah ke faɗa a fusace ban taɓa jin haka daga Abbah ba yana juriyar abunda ke faruwa kai kace bai San wani abu ba'cin rai bare yadda akeyi ba

Maganar Abbah Imran a tsawace, tasa ni ni ma tsorata "Abdullahi kayi haukane Hajiya da ta haifeka kake faɗa wa magana haka saboda ba kada tarbiyya ba ka san mutuncin iyaye ba ba ka san zafin haihuwar da ta sha ba”

Tsaki Abbah yaja” ita wace ce Imran ka fita harkata haihuwata ta yi bata halicceni ba, tarbiyyar da ta ba ni nake gwadawa yau aina yi haƙuri ma kuda kullum kuke cikin gwada musu ita fa amma kune mutane ni talauci ya maidani bare, yaranku sai su bangajeni ma a haya saboda ina yawo a tsiyace, abun ya wuce nida matata ina koƙarin bawa 'ya'yan da na haifa tarbiyya kuna ƙoƙarin iskantamin Sumayya indai ta lalace to duka 'ya'yan da na haifa haka suke da yardar ubangiji ba za mu ga haka Kuma ga 'ya'yan ku ban muku fatan suga haka, dan zina babban illah ce ga rayuwar namiji ma bare mace”

Abbah Imran na ga ya dauke Abbah da mari "mu kake faɗa wa haka Abdullahi”

Abbah a zafafe ya ɗago ya wanke Abba Imran da marin shi ma

"Imran na faɗa ma kuma zan ci gaba da faɗama kowannenku muddin cin zarafin da kuke mana nida matata bai isheku ba Kun daura min da yarana, kunsan hukuncin zina a addinance, maiyi hukuncinshi ko Sumayya kuka kama tana yi muraran saiku fallasata ku ƙaramin wani masifar da ya haɗarmin na samun iyayena da 'yan uwana amatsayin ba ku ƙaunata saboda abunda ban isa na yiwa kaina ba”

Dakin na faɗa na rungume Abba ina kuka ina” Abbah ka kyalesu dan Allah mun fisu laifi da muke ƙoƙarin zama dasu da shiga cikinsu duk da ba mu cancanta da haka ba” rarumar da aka yomin ta baya ya sa ni sakin Abbah na yi ta baya baya, Aunty Maimuna na gani ta zabgamin mari” Sakeshi dan uwar uwarki, matsiyaciya munafuka masu laɓe kun rabamu da ɗan uwanmu wallahi ko ba Abdullahi kuka nememu a dangin uba sai kun tabbatar da mun daɗe da yankeku a cikin jininmu"

Abbah a zuciye shi ma ya wanke Aunty Maimuna da mari haka Abbah ya ja hannuna jiri na ƙoƙarin ɗibarshi na kakkamashi dan ko abincin safe a yau dinma bai ci ba har ukun rana tayi, ina riƙe da shi muka ƙarasa ciki Mama muka samu tana kuka Kamar ƙaramar yarinya ko ni na yi dauriyar ƙinyi sai hawaye bare ita danasan daga ɗaki take jiyo hayaniyar ka sancewar dakunan da muke jikin na Hajiya ne, gurinmu ta nufo ta kamashi ta shigar da shi falon sai da muka zauna Mama ta dubeshi

"Haba mana Abdallah zakaje ka sawa kanka wani ciwan a banza ba ka da mai damuwa da hakan, tun da suka fara ka fito mama amma kamar, an dasaka”

Tari Abbah ya fara, na tashi na dauko masa ragowar pure water na bashi Mama ta amsa tana cemin"Jeki kawo masa abincinsa a kitchen, kitchen na nufa na kawo masa haɗe da cokali na saka a ciki” lokacin da na dawo ya tashi zaune

Mama ya kallah bayan Fara cin abincin"Hauwa'u na gode miki da halaccin da kike min da kyautatamin na ƙoƙarin zama dani cikin wannan halin da hantarar 'yan uwana ita ce gaba da komai a yanzu gareki abun ya wuce wajenki har wajen Sumayya, Hauwa'u familyna basa tare dani saboda ni ɗin bawani ba ne, face talaka, abun yana damuna, ban san ya abun zai daura ba idan bana nan"

Mama hawaye ta share ni ma ta ɓangarena haka ne

"Dan Allah Abban Ahmad ka daina wannan maganar wallahi ina jima tsoron hawan jini, yanzu ya zama abun da ya zama abun kasa ba ne, da abunda ke faruwa, kafiso ka ɗaga hankalinka muka ɗaga mana”

"Hauwa'u dole na damu da yawa wannan fitinar tasu yau taron dangi kina ji sukayi min ya kamata ma, ku bar musu gidan ki tafi gidan Gwaggo, yanzu ni na riga nawa ne, Zan fiki juriya kawai na san nuna min kike kina jurewa, "

Mama jin maganar Abbah ta ɗago ta na kallanshi” Amma Abban. . . . "katseta ya yi da cewa” Dan Allah Hauwa'u karkimin musu ku tafi ke da Sumayyah tun da yara nacan ma, idan suka gama shuka tsiyartasu zuwa dare suka tafi sai ku dawo kin san Asma'u sai ta shigo har ciki ta faɗa miki magangana, ga Mubaraka ma sun haɗu،ni kin san ba bakin komai nake a wajensu ba ni nasu ma bareke sunajin haushinki”

Ba yadda muka iya Mama tasa hijabi ni ma na zari mayafina na yafa, ka sancewar mun yi wanka, muna fitowa ɓangarenmu ni da mama muka ƙara sauri muka buɗe get gararau muka fice muna jin Aunty Mubaraka na cewa

"Wanne ɗan iskane ya buɗe mana kofa ya fita da gudu"

Aunty maimuna muka jiyo Muna ƙoƙarin tura gate ɗin tana

"Futa ki gano mana ko barawo ne, ko yaron Yaya Abdullahi ne aka fara sace sace ya na bin yaron nan Shu'aibu na gidan Malam Habu"

Ni abunma dariya ya ba ni su dai lamuransu sai addu'a mama ta kalle ni” ya da dariya Sumayya” Na ce "mama bakiji mai Aunty Maimuna ke faɗa ba” ta ce” naji mana kin san shashasha ce Maimuna, ni dan kar siyo kaina na ƙara saurin nan gwara su ci kansu indai sune kafin kowacce ta tafi sai kin ji kansu batse batse kuwa”

Muna tafe muna fira har muka ƙarasa gidan su Mamah, gidan na ƙasa ne da simintin shi amma da sauri na na riga Umma shigewa da Omm Habibah ƙanwar mamah da Zainab da ita ce ƙaramar ƙanwarsu Mamah na ci Karo a tsakar gidan da na kwaɗa sallamata juyowa sukayi suna kallona da amsawa suka bini da kallo "oh Sumayya anyi girma” Omm Habibah ta kalli Zainab ta ce” ke kin ga Zainab har ta fiki girma ma”

Zainab takalleta” to dama Sumayya ai ta girmeni kusan kece tsararta ma ya kike haɗa ni da ita”

Da wannan Mama ta shigo ita ma sallamar da ta yi muka amsa Omm Habibah ta kalli Mama "yawwa Yaya Hauwah Zainab ce sa'ar Sumayya ko ni”

Mama ta yi dariya” ke ce Mana ki yi zuciya ki yi girma na ga kin maida Zainab ce babba tun da kin maida Sumayya sa'ar Zainab"

Dariya na yi na ce” wallahi Mama tun da nashigo Omm da zancen ta tareni ko ni ce sa'ar Zainab"

Mama ta harareni da cewa” Ƙaniyar ki da Zainab in ba Za ki ce mata Aunty ba ita ma Omm Zainab ce”

Zainab ta ce” barta Yaya ni ma zan hana Ahmad yana cemata Yaya, ba dai na hannun dama na ba ne”

Dariya mama ta yi ta shige ciki ta barni da su Omm Habibah, da suke wanke wanke dama kujera na jawo na zauna kusa dasu hirar littafi suke yi” omm Zainab ta ce "yawwa Ommu an turo without my dreams ɗinnan kuwa Dan Allah Kika anso charge ku ba ni na karanta ni ma, na ji labarin Munira ni kin san ina team din ta”

Dariya na ji omm Habiba tayi” lallai yarinyar nan, tom ko ki canza sheƙa team din Hidaya yafi, saboda mamarta ta nada kirki ita ba Kamar kaltume ba”

Ommu Zainab ta kalle ni” kin ji fa Sumayya ya kamata ki bawa Sumayya ta karanta ita ma, amma Munira ai ta yi ƙoƙari a dai matsayin roll ɗin da tafi to, kuma indai kin san Hidaya kin san Sumayya Kamar fa nida Omm Habiba din ne, kaɗan ya banbanta, su Kuma sa'anni ne ma Kamar twin suke”

Nace "wai Aunty Zainab ba zan gane ba gaskiya adai 'yanmin nkaranta, yawwa ni ko ina wannan book din na Rufaidah da Abdurra'uf akaƙi musu aure sun haɗu ne a super market ShopRite ne ma, tom ba su sake haɗuwa ba sai bikin wata friend ɗin Rufaida Samiha, namanta sunan littafin ya min daɗi Allah ya sa an ƙarasa wancen zuwannamu na tarar ana posting nashi”

Tsaki Aunty Zainab ta yi tace” kin ji fa Ommu kin san littafin da take nufi JININMU ɗAYA, na wannan sabuwar marubuciyar da kika cemin Sadiya Khalil ne ko Halimatu Khalil ne oho ita tasan da wanne take using sai ku masu wayar"

Omm Habiba ta ce” nafa gane shi na ji ana za ta ƙarasa shi yanzu ma duk anma manta shi ƙila sabon updating za ta ƙarayi ko ta daura tasa mutane na neman document din na baya, kin san rubutu na da cin rai inji su dai masu ƙoƙarin yi amma ta iya book wasu ke cewa Kamar irin ta gwanance tun farko da ta fara, tasan me take kamar dai, amma ni yanzu fav ɗina a rubutu marubuciyar without my dreams wallahi, Kuma littafinta ɗaya na karanta wannan da take rubutawa without my dreams"

Ni kam na ce "taɓ ai ni kam ko dan Halima tom Halimatu Khalil ce fav dita a masu tasowa a rubutu, gashi a littafin maman Rufaidah sunan Mama gareta gashi akwai Abdul Abdul a littafin Abdulahid, Abdulmalik waye waye kuma gata sunan Abbanku Abbanta gareshi”

Aunty Zainab ta ce "ke wannan lissafin naki, munji ni bance ina ƙin book nata ba da Habiba, za ki ma, ko yanzu ta yi saban book ommu taga ana poster wa zan ansa na karanta shi, ba laifi ta iya, amma baruwana da lissafin nan ni da ake bawa waya dakyar Ni ba ma na duba sunan marubuciyar ma, nake karantawa, Ni karatun bai dameni ba littafi ana farawa ba continuation ko na tura wayar Gwaggo document wasu ma su damu mutane na kuɗi ne, ni fa ko za su dinga Allah ya isa an karanta saina karantashi kuwa, abin duniyar mu talakawa Ina muka ga kuɗin biya duk ribar da za su ci, Kamar abun samun lada mtsew"

Aunty Zainab uwar jaraba shiru muka mata har tagama zancen, can za ma wani mukayi tun da Zainab ta ɓata firar share wajen na taya su kafin muka shiga dakin Gwaggo muka gaisa aka fara fira su Rumaisa an nausa cikin gari gidan yayar Mamah Aunty Maryam ka sancewar mamah ce ta biyu a gidan nasu. . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . .

Na Cancanta (Kashi na 23)

Humairah da take ta barci a bayan mama tunma kafin a fara rigimar ta fara kuka mama ta sauketa daga bayanta, daga ita sai pant jikinta nan mama ta fara bata nono, Gwaggo dasu Aunty Zainab suka kalleta "lafiya haka Aisha ba kaya jikinta”

Gwaggo ta ɗora” ko Bata da lafiya ko wani abun ya haɗa ki da surikan naki gama dai ansaba, hala ƙannan nasa suka ci miki mutunci ke sakarai Kika kasa ramawa Kika taho mana nan ki tayar wa da mutane hankali, shi ya sa sam banji daɗin dawowarku nan ba kinacan asirinku rufe muma namu haka Atika Kuma na ɗan taimaka muku, da ko da aka koreku kunje gidanta ai zatasan yadda za ta yi a samo muku wani gidan ko a unguwar ne, sai abu ya faru a kasa tunanin da ya dace to kundawo nan din, in dukan kawo wuƙa za su miki nidai da sanina ƙannanki ba za su je ba, inma rigimarce dasun kada Miki da 'yar taji ciwo da paracetamol ba za su taimaka muku ba, wannan jarabbabbun mutane hukuma ma sunfi ƙarfinta, haka suke rigimar su dukansu da surikansu da ƙannan miji da yayye su Mubaraka da Maimuna haka sukeyi danma sun haɗu da daidai su ne abun ke zuwa da sauƙin wulaƙancin su Kuma duk laifin surikan naku ne da basasan laifin 'ya'yansu"haka Gwaggo ta ci gaba da sababi,

Ita dai Mama haƙuri ta bata da cewa” Mama ni ba ma dani suke ba da ɗan uwansu sukeyi shi ne ganin ko kar haushin ya ƙarasa ƙarewa kaina ya ce na taho nan tun da yara suna nan", mama da jajayen ido take ci gaba da maganar, "Gwaggo wallahi na gaji da zama da mutanan nan ko a can ban tsira ba su bar mu ma da talaucin dake damunmu da ubangiji ya sa ka sancewar mu haka maimakon su tausayama na, shi ne dalilin da Allah ya Samar da Mai kuɗi da talaka saboda mai shi ya taimaki mara shi ko da da shawara da kwantar da hankali ne, amma babu dukkansu ba mai taimakon mu sai jifanmu da mugun alkaba'i ba su ba 'yan uwanshi hatta da iyayenshi, wallahi saina ji kamar na zube musu 'ya'yan ko kotu naje a raba auren nan, indai ni ce matsalarsu" ta ƙarasa maganar tana rushewa da kuka mai ban tausayi dan Mama abar a tausaya mata ce, cikin yana yin tausayi su Gwaggo suke bata haƙuri harda Aunty Zainab Gwaggo ta ce” inkin kashe aurenki Hauwa'u kikazo nan wa Kika bawa ajiyar dauke miki duk dawainiyarki su Sha'aban suma buga bugace kina gani ba wanda ko maganar aure ya Fara ma da ya dace a ce sun fara shekaru tafiya suke tayi, kuma kinada tabbacin za su kula 'ya'yan naki sun riga basa ƙaunartaki kuma ba ma kece basa ƙauna ba Abdullahi ɗinne basa so har su iyayen nashi, dan da suna sanshi murna za su yi dake da Allah ya sa ya samu ya yi auren, ya auri matar rufin asiri ai ita mace a wajen miji kamar katanga ce, kuma daraja da haiba take ƙarawa namiji kamar yadda ita ma yake zamar mata, in ba kaso matar ɗanka ba ba ka sanshi ke nan matar rufin asiri, in kin ga ana ƙin surika anawa ganin sai baƙin halin nata yakai iyaka, shi ma a ce tana munanawa ɗan naka shi ne kake ƙinta, amma dan surika ta ta mai sauki ce sai taje inda suke ko ta sauraresu za ayimata, saidai ko fitsararta ta takai ƙarshe, ni yanzu su Jabir nawa suke amma ji nake kamar ko da kaina na samu kuɗin da Zan aurar dasu na huta na ji da su ommu da Zainab, amma su sunfisan ɗaga ma ɗansu hankali bare ke kisa ran naki zai kwanta shi ne basa so ba ke ba”

Jin maganar Gwaggo ya sa ni fara magana” wallahi Gwaggo haka ne basa ƙaunar Abbah ne kawai” labarin komai da ya faru ni da aka yi komai zai iya cewa a gabana na shiga basu, ransu in ya yi dubu ya ɓaci haka suka ci gaba da mamakin su Abbah Imran ɗin amma Gwaggo faɗi take Abbah duk da haka bai kyauta ba da ya farfaɗawa Hajiya maganganu su Aunty maimuna da Aunty Asma'u ya kamata a ce ya zanesu duk abunda zai faru ya faru za ta fi jin ciwan hakanma, Ni dai shiru na yi Mai faruwa ta riga ta faru, haka muka ci gaba da labaran duk na gidanmu ne, ba mu muka bar gidansu Mama ba sai dare har Abbahsu Mama Saida yadawo Gwaggo ta shiga bashi labarin abin da ya faru shi ma duk labarin gidansu Abbahn yana da shi ko tantama baiyi ba yasan fiye da hakan za su iya ma dan Abbansu shi cewarshi harshi Abban namu sai ya samu warwara za a tantance shi nashi halin dan zumun ci yanzu yana samu za su shirya shi ma ya manta aibunsu tun da 'yan uwanshi ne, itadai Gwaggo ta ce wa Malam anya kuwa haka za ta faru kuwa, haka muka tattaro da su Rumaisa muka taho gida, da sallama bakinmu muka tura kofar gidan muka shiga a tsaye kofar dakin Hajiya muka samu Abbansu Abbah yana kallon kofar gidan da alama shigowarmu yake jira tsaiwar da tsumayenmu ta yi kama hasken wutar nefa ya haska mana fuskarta shi da take cunkushe ba alamun fara'a

Mamarmu da muke koƙarin shigewa ciki saboda ganin hakan mama bata masa magana ba dan tasan ba abu mai daɗi zai biyo baya ba tsawar da Abbah ya dakawa mama mukanmu saida muka tsorata

"Ke Hauwa'u "ya ambata cikin daga murya da karaji, Mama a firgice ta tsaya muma muka ja muka tsaya ta ɗago ta kalleshi jikinta na ɓari ta kasa cewa komai ya ci gaba da magana cikin zafin zuciya

"Na sallamawa Abdullahi ke kin zama uwarshi to inaso ki zama ubanshi, babu ni babu shi, ba zan ce ya rabu dake ba saboda girman kuskuren da ya yi mana da butulcin haihuwarsa da mukayi da ya yi saidai mu barshi da ke, alfarmar kwana ɗaya a gidannan na yi muku in ba haka ba, zan muku abin da acan gidan hayar ba’a yi muku ba sainasa an muku taron dangi an fasa muku jiki an wurgar muku da kayanku waje, duk da hakan banji na wuce abin da Abdullahi yayi min bare Kuma na ce uwarshi ta wuce ni kika sa ya wulaƙantani da tarbiyyar da na masa, kika mayar masa da 'ya karuwa saboda kema halinki ke nan"

Cin zarafin na ji ya yi yawa ciki ƙeƙashewar zuciya na kalli Abbahn su Abbah din babu alamun tsoron mai bakin yake faɗa da abin da za a mayar masa ko kuma abunda furucinsa zai ja masa ko da a gaba ne take maganar da kaurarata ya tsaidamin uwa yana maganar san ranshi, Mama na kalla tare da cewa "mama ki taho mu shige ciki idan yana da magana da mu ya biyo mu ciki, in bahaka ba zan masa rashin kunyar karuwai, saboda na lura babu imani bare tsoron Allah a furucin mutanan nan, baki zama Abbah ba kuma ba suda alaƙa dake saboda ba su mayar da ɗansu ɗa bare ke ki sa ka rai za a maida ke ɗan wani abu a ransu"

Banma jira sake jin muryarsa ba da nake jinta tafi komai munin ji a wajena ba dan komai ba sai jifan da akemin da kalma mafi muni banji ba bangani ba

"Ku taho mu shige in kun ga za ku ci gaba da sauraran shashancinsa ku ci gaba” suku ku suka bi bayana har Mama da na san ban da ranta ya ɓaci sai ta mareni kalmar da nake faɗawa Baban musamman ta ƙarshe har muka shige ciki ban ko sake jin tarin shi ba alaƙa damu dama ya yanke ni kaina kan ƙaya zan kwanta gidan na kwana ɗaya sallama mukayi da Ahmad ya yi ƙoƙarin yi mah shirun da muka ji muka ƙarasa shiga muka fara leƙa falo a nan muka samu Abbah da alama gyangyaɗi yake dukanmu da tausayawa muka shiga ciki muka sameshi muka fara "Abbah mun dawo"firgigit ya tashi a rikirkice ya kallemu"Kun daɗe sai kace ba za ku dawo ba, ku nake ta tsumaye, Hauwa'u na yi zaton ko Gwaggo ta hanaki dawowa ta inda yaran za su ɓullo nafi zaman jira da fargabar abunda zan ci karo da shi na Fara gyangyaɗi danni da nake cikin jarrabawar da jiran hukunci da ƙudirar ubangiji a kainah zan ka sance shi ne na yi imani da shika shikan imani yadda da ƙaddarar jarabawa mai kyau ko akasinta ina jin a raina ubangiji yana kusantani da alkhairi ko da bayan raina ga iyalaina, dan kune komai na, duk labaran da nake ji bantaɓa jin kalar nawa ba, a ce abun ya tsaurara haka ban ci musu ba sha musu ba, na rasa ina ma zan saka kaina ne, Musa ya zo bayan tafiyar ku ya maidomin ma wayar nan ya ce ta yi tsadar da za ta zama zargi a kan yadda aka yi aka same ta wani ma zai iya sharrin tashi ce aka sata mutane ba tsoron Allah, ko Kuma a taya ta kuɗi banza saboda za suga ko an matsu da sai dawa, ya ce Sumayyah ta ci gaba da anfani da ita a gabanshi Baba ya cimin mutunci ya ce gobe gobe mu bar gidannan, shi ne bayan tafiyarshi Musan ya ce akwai wani gida inda ya yi haya kafin ya ƙarasa gininshi to bakowa ciki ya ce zaizo da mota a kawoshi kayanmu ko da asuba mukeso mu koma za mu iya saboda gidan a hannunshi yake shi ma rigingimu da ƙannanshi da matarshi ya sa ya bar gidansu ya Kama hayar wannan gidan amma shi abun nashi baikai kwatar wannan ba”

Tun da Abbah ya fara magana har ya kammala hawaye nake yi zuciyata a cunkushe take, a cikinmu ina jin Khalil ne kawai ba zai iya fahimtar abin da ke faruwa ba, nama kasa yarda a kan talauci ake ƙiyayya damu saina kalli abun muddin haka ne a matsayin jahilci babba, saboda suma da suke da shi specific abunda za su kalla suce ya samar mu su da shi ƙarya sukeyi, Abbahnmu ya yi karatu tuƙuru yana da ilimin da ya wuce na kwalayenshi hakan ya sa banjin ko kaɗan karatu ne arziƙi, arziƙin ka da shi ka samu kyakkyawar rayuwa da yawa daga manyan shaharrun masu kuɗinmu na jiya da yau ba suyi ilimi ana wasu da ga cikin na yau ƙwalin SSCE ba su haɗa har zuwa yau ɗin banaji ko familynsu Abbah sun san haka ko fahimtar gaskiya ta rufe musu ido, kalaman Mama ya katseni

"Muma yanzu Baban ya taremu kasa cewa komai na yi sai Sumayyah ta masa magana ita ma ɗin ban yi zaton za ta iya ba”

Abbah ya yi murmushi "Ai ko zaginsu ta yi ba zan musa ba saboda kalamun su musamman akanta yanzu sun yi tsauri fiye da nacan baya, Hauwa'u dan kana babba ba ka da izinin tauye ƙarami, ba za ka ce zakaita shimfida isarka ga ƙarami kuma na zalunci kace ba zai yi magana, ko da ɗanka ne ka ɗabi'ance shi da kyakkyawar daɓia hakki ne akanka ga dukkan mutane duk yadda kake kallonsu a ƙasƙanci ba ka san alaƙar bawa da ubangiji ba wani ba zai ɗaga hannu yana roƙon Allah ayi ruwa ba face bai sauke hannu ba Allah ya ƙaddari hadarin ya haɗu anyi ruwan akwai abubuwa da yawa da za su sa mu hankalta amma bamayi, Allah ya kawo mana mafita kawai”

Mu ka amsa da "Amin"

Shi dai Ahmad tun da aka fara zancen bai sanya baki ba ban sani ba ko ys rasa mai zaice ne ma, da haka mukayi shirin kwanciya barcin sam ni kasa samuwa ya yi a tare dani na ma rasa maike min daɗi ma abubuwan kamar a almarane zance rushewar takai ƙarshe duk dai kan Mama ne zan iya cewa ni kam tausayinsu nake musamman ma Maman da ko rabuwa ta yi da Abbah ba za su iya amsarmu ba saidai su dauki nasu kawai tun da abun nasu haka ya nuna, ji nake zuciyata ta ƙeƙashe ina jin zan zama ne mace kamar namijin da zan kawar da mikin dake tare dasu, kuka nake mara ƙarfi duk dalilina abun ya taso haka kuma dalilin zuwana Katsina ne, sai yau na tabbatar da illar zuwa hurumin da bai dace da Kai ba ko da janka aka yi aka kaika kai ya kamata ka gudo ne da ƙafafunka kabar rayuwa da San birge wanda yake gani ya fika ba za ka taɓa burgeshi ba ina jin ko a 'yan uba aka samu irin wannan matsalar za a jinjina amma uwa kuma uba ɗaya hawaye suke bin saman fuskata ina jin sharewar ba shida anfani saboda wani ne zai sake biyowa, ban san iya lokacin da na dauka ba a haka har barci ɓarawo ya yi awan gaba dani, tashin da Mama tayi min ya sa ni fahimtar asuba ko safiya ta yi idona na buɗe na kalli waje haske har ya fara fitowa mama ta kalle ni

"Lafiya Sumayyah haka kikayi nauyin barci haka, sai Ahmad ya tashi su Rumaisa ke ko yama tasheki baki tashi ba”

Muryata a shaƙe ta alamun wadda tasha kuka "wallahi Mama barcin ne ya kasa daukata saikace mai dannau"

Maman ta ce” Dannau din kuka ba, wallahi Sumayyah ki kyale mutane ubangiji ma baya iyama yawancinmu ki bar kowa da fahimtarshi ko da bahagon tunanin ƙiyayyarsa akanmu a kan abin duniya da ba mu dashi, Allahn da ya raba yaba kowa zai raba ya ba mu idan yaso idan be so ba haka za mu faru mu tafi ba tare da hakan ba Kuma insha Allah dukkan jinkiri alkhairi ne”

Na jinjina maganar Mama dan kaifin basirar ta ka sance mace mai shi kalamanta ga masoyi abun yadda ne da san jin ta yi su, nidai na san bata taɓa nuna mana aikata mummunan aiki ba muna fama da yau da gobenmu ne muna barci da zullumin ya gobenmu za ta Kaya za mu samu abin da za mu ci ko a'a ko sau daya za mu samu kawai shi ya sa ba ma muda lokacin ƙulla wa wani wani abun bare musa ran dan aiken ya dawo kanmu kana girbar abin da ka shuka ne nake kallon abunda duk za ka shuka ne ɗin, na ajiye tunani na ce” Mama kukan ai yana zama sauƙi a kowacce zuciya ne a kan ƙuncin da ta riski kanta a ciki kuma da kuna yi za ku samu sauƙi a zuciyarku na san kuna cikin shi duk da miƙa lamura ga Allah ko ya ya za a samu wani miki a zuciya ne na tunani”

Mama dai ta ce” ci gaba da kukan ki idan hawayenki ya ƙare za ki bari, kuka ma aikine babu wanda yasan kina yi kuma ga mutanan da ƙiyayya ta shafe komai akanmu ba za ki samu sassauci ba”

Na ce ina miƙewa” Mama Kuma ranar da kuka fara naku ba zan hanaku ba abunda kukeson yi tsawan shekaru kuka kasa sai a lokacin na san za ku rage raɗaɗin da zuciyarku take yi” daga nan na fice yin alwala dan Kam gari ya waye ne danma bisa barci na yi rashin sallar lokacin duhun asuba, a dakin na dawo na same ta a falon da muke kwanciya ta zuba tagumi da hannu biyu ne har na dawo na yi sallar na idar bata ji ba sai da muka fara jiyo sallama na ganta firgigit ta miƙe tana dube dube tsayawa na yima kallonta ganin duk ta kiɗime na ce” Mama lafiya kuma?"sai sannan ta daidaita kanta ta ce” yawwa tashi su Rumaisa su fara fitar da kayan na ji sallamar kamar ta Abbah Musa” Ni dai kallan ta na yi tana ficewa na girgiza Kai kawai wannan fitinar kam dole ta gigita mama din tashinsu na yi kawai na fara tashinsu.

Na Cancanta (Kashi na 24)

Haka muka gama kwashe kayanmu da ba yawa garesu b dama muka ƙarasa lodasu a akori kura dukkanmu ba wanda yana yinsa yake cikin daɗi muka bar gidan kafin su fito ma su sake ɓata mana rai a ƙasa muka tafi haɗe da Abbah Musa da shi ne yasan gidan, ba laifi tafiya ce mai ɗan nisa ba ma ɗa ba mai nisa ce ma ba sababbin unguwanni ba ne ba, gidane ginin ƙasa Abbah Musa ya nuna mana shi da muke ƙoƙarin ƙarasowa, ba shida ko filasta ma amma Alhamdulillah ya fi mana gidansu Abbah da suka cire soyayyar iyaye da ɗansu suka wulaƙanta shi kanshi Abbah ma bare mu da mama a ƙofar gidan muka toge muka jira Abbah Musa ya bude kofar da a zauren muka isar da kayanmu harma an kawo su gidan sun juye da Abbah Musa ya ba su ɗaya daga cikin key din gidan gaba ɗaya muka shiga cikin gidan da cikin azama muka fara kinkimar kayan zuwa cikin gidan mai daƙuna uku da banɗaki sai kitchen na langa langa da alama muguwar zuba yake yi kitchen ɗin amma gaba ɗaya muna farin ciki da samun canjin da Abbah ya kasa ɓoyewa ya dubi Abbah Musa” Musa ban san da wanne ido ko kalmomin da zan dubeka ko na furta ma ba na gode sosai ka taimakeni lokacin da nake jin a yadda matsalar ta tasomin nafi kowa buƙatar taimakon"

Abbah Musa ya girgiza kai” Haba Abdullahi ai yiwa kaine duk wanda zai taimaki wani to ya sa a ranshi kanshi ya yiwa ba wani ba, kamar wanda yaƙi taimakon kanshi ya yiwa, ladan bai ishe ni ba ai da zan gaza yi ma taimako dan ko da ƙarfin jikina zan yi ma, muma a harkar karatu ka taimakemu ai kayi karatu amma ka bari muyi exam tare da saboda mu karatun baima dame mu ba, sai gashi mun rigaka cin moriyarshi, Abbah Musa ya faɗa murya raunane da alamun rayuwar tamu ta dameshi da muke ciki” ni da na yi tsaye kusa da su hawaye na ji suna zubomin cikin rashin shiri

Abbah ya dafa shi” Haba Musa karka damu dan Allah samunku ai nawane ba gashi ba ka fahimceni ka dubemu abin da a cikin gidan mu hatta da iyayena sun kasa wannan fahimtar, ni haka rayuwar ta namun daɗi ina fahimtar abubuwan da a cikin yalwar arziƙi ne ya yi kaɗan na fahimta”

"Allah ya mana suttura Abdullahi wucewa zan yi akwai rijiya a makwabta nan gida jikin nan ɗin kusa su samo muku ba matsala batun ruwa sai dai ko su yaran suƙi zuwa danni sai na siya sanda muka zauna yarane masu ƙyuya Allah ya bani” cewar Abbah Musa yana koƙarin ficewa

Abbah ya ce” sunga kana samunka ne niko karsu ɗebo ma su ga ni”

Abbah Musa ya tsaya da fara tafiya "na shafa'a ba muyi sallama da Hauwa'u ba, na san sai tama ciwan baki ka san mata”

Abbah ya yi dariya kawai ya kira Mama ta fito t sake ma Abbah Musa godiya sukayi sallama ya ƙarasa fita Abbah n biye da shi zuwa rakiya waje

Sai sannan na shiga ɗakunan ina leƙawa da babu isassun siminti a ƙasa duk ya cire tabarmi muka shishshifiɗa da ba manya ba ne dandanan muka shiga ayyukan gidan da share share muka yi muka gama su Rumaisa suka shiga ɗebo ruwa ni ma har dani ba laifi daga shigarmu gidan matan gidan suna da kirki gidan kuma mai kyau ne babu laifi ba kamar wanda muke ciki ba akwai yarinya kusan sa'ata a gidan Malika da shiga ta muka fara fira ta nada kirki kamar iyayenta da na ga alamar hakan haka muka dinga kinkimo ruwan saina zauna ma ni ce nake jawowa suna kaiwa gidan Malika dake wanke wanke a gefen rijiyar tana ɗan san muyi fira na dai ɗan sake da ita muna firar makarantah, ita ma mate ɗaya muke bata samun ƙualyfying ba amma shirin biya mata akeyi ma kuma tana tunanin ɗora karatu ma, na ji ina ma ni ce ita haka na taya ta murna tana tambayata wanne course ya kamata idan ta zo jamb tasa ka na yi dariya na aje gugar da na gama jan ruwan

"Wallahi ban sani ba duka fa tare za muyi candy ai sai dai ki tanbayi yayunki da suka taɓa jamb ɗin, suka samu wucewa University ai”

Tayi dariya” ok na tuna fa haka ne, zan tambaya zumuɗi ne fa kawai kin san ba’a tashi farawar ba ma”

Na jinjina kai "Nace haka ne kuma, Allah ya taimakemu, bari na tafi, mungode”

Malika ta ce” Amin tom sai na shigo ko anjima ne, na ƙarasa aiki, kina kitso ne?"

Na yi murmushi” A'a bana yi Mamarmu dai tana yi, inkinaso zan mata magana saikizo ta miki” na lura dai Malika surutu gareta har ya wuce nawa da da ma banwai cika surutu ba

"Kai da kin kyauta min ya fi sati a tsefe na baki labari inata kame kamen mai kitso inda nake zuwa ya yi nisa yanzu na rage san yawan kuma” cewar Malika na bita da "uhmm haka ne sai anjiman to da haka na fice ina mamakin surutun ta haka daga haɗuwa abun har mamaki ya ba ni ma

Ina shiga gida sallama Mama ta amsa min da ta yi shinfiɗa a waje, tana murmushi "Ai su Khadijah sunce min kin yi sabuwar ƙawa a gidan ɗebo ruwan" na zauna gefen Mama ina ce wa” Mama ke dai bari kawai kamata ta ke tare zamuyi candy amma surutu tsiya gareta daga haɗu wata da ita har naso na gaji”

Mama ta harareni” ke kin manta naki surutun cakwaikwaiwa ke nan, kin sake haɗuwa da kalar ƙawayen naki ke nan ai”, jin Mama ta ƙi yarda da zancen surutun Malika na ƙyaleta ai za ta zo gidan za ta tabbatar nata surutun ba irin namu ba ne ba, na canza zancen da "Mama Abbah har yanzu bai dawo ba wallahi na fara jin yunwa”

"Eh na san dai yana hanya insha Allah"Mama bata gama rufe bakin taba mu kaji sallamarshi ya shigo hannunshi ɗauke da icce da na san ba zai wuce na ɗari biyu ba sai leda kuma ita ma a hannun, miƙewa na yi na ansa iccen na yi hanyar kitchen Rumaisa ta ƙaraso ansar leda ita kuma na ji Abbah yana "ƙyaleta Rumaisa fulawa ce a ƙasa saman wayar Sumayyah ce, samo roba a zuba fulawar a ciki ayi ko ɗan wake ne”

Inda muke zaune na dawo na zauna Rumaisa ta wuce samo roba na ɗan ɓata fuska Abbah dake gefen mu ya kalle ni ya kalli Mama” Hauwa'u mai kika ma Sumayyahn taki ne”

Dariya Mama tayi” me zan mata kuwa ka san ba tasan ɗan wake shi ne taji za a yi take ɓata rai”

Abbah ya kalle ni” Au wai shi ne abin ɓata rai bari toh ayi wainar fulawa amma in ba ku ƙoshi ba ruwana” na amsa da toh, Mama ta taɓe baki” ka dinga biyowa yaran nan musamman Sumayyah ma”

Dariya Abbah yayi” toh naƙi biye ma ta, ita da ba yayye gareta da za su biye mata ba, indai inada hali kam hukuncin Sumayyah da ta yanke shi za a riƙa zartarwa a gidannan ba ma na iya abinci ba, kema kika yi wasa saita ƙarasa har kwashe fadar yarda da shawararki a wajena, nifa kin san ba ruwana babba mace ne ko namiji yana nan dai matsayin shi”

Mama ta yi dariya "naji dai ai ni na haifi a bata ba zan ji haushi ba, amma kar a waremin Ahmadi na, duk hankalin Sumayyah shi namiji ne ya fita tunani”

Abbah ya ce” oh my God, ai ni ma namiji ne nafi Ahmad tunani in na tanbayi shawara na ji baiyi ba wadda Sumayyah ta bayar to zan shawarina da kaina, ya bari ta ci fadarta shi ko yaushe muna tare”

Ahmad dai bai san wainar da ake toyawa ba yana ɗaki ana sana'ar barci kamar kasa haka yake na san da tuni mun kacame da gaddama, Rumaisa ta dawo da roba da saida ta nemo ta ajewa ta yi aka fara ciromin wayata a kwalinta yadda aka ba da ta Abbah ya miƙamin a bata yana "Ai Abbah Musa na faɗamin kyan wayar nan, da inada kuɗi ai na siya miki n siyawa mamanku da ni kaina kuma” na yi dariya daga cikin kwalin ya cirota ya miƙamin yana” kona kunnata a ba ni aro ma” nidai dariya nake yi muna ƙoƙarin haɗa ƙullun waina ɗin hankalin mu kwance ba muda zullumin komai sai yau da kullum amma ba bu tunanin cin mutumcin kowa duk da dai ba kayan wani muke ci bashi ba amma a wannan rayuwar na dauki cin mutunci basai haka ta faru ba, kawai a kan abin da babu mai yiwa kansa ma sai a ci maka mutunci duk dan ko bahagon tunanin gazawarka ce, haka muka fara soya wainarmu Ni Kam a na cireta daga kasko nake cinta danma fulawar da yawa a ƙalla kofi biyu da na tabbatar ni zan kusa cinyeta ma, da yamma yaran sun fice da Abbah ya samu islamiyya zai kai su ni kam na ce ba yau ba sai an huta gaskiya zan fara zuwa haka dai Abbah da bai cika San takuramin ba ya amince Mama ko sai faɗa take tana aiko ta yarda na yau amma bata yarda gobe ba kuma ni zan wanke wanken gidan rashin dai zuwan baisa na huta ba shi ko Abbah makaranta ya samu iya kuɗin Laraba ake kaiwa kuma yaji ana da karatu yaga gwara ya yi ta maza dan zaman gidan ma bari ta ishesu ma, yaga kuma ga sauƙi ya zo

Sallamar da na ji na yi saurin leƙowa daga ɗaki da nake kwance sallamar Malika na ji amsa mata sallamar na yi ta ƙarasa shigowa ta dube ni

"Yayi Sumayyah barci ma kike yi ko, kitso na zo fah"

Na ce "ya fara ɗauka ta dai, shi go na ma mamarmu magana”, Cikin ɗakin ta shigo ta zauna ni kuma na fito na je na faɗa wa Mama Malika ta zo kitso, a waje mamarmu tasa na yi shinfiɗa na dawo ɗakin ina faɗa mata ta fito

"Ban ga ƙannan ki ba, suna ina” cewar Malika

Na ɗan yi murmushi na ce” Sunje Islamiyya Abbah ya kai su ance bayan gidan nan ce, ba kuɗin term ake biya ba ban san sunan makarantar ba”

Malika ta kalle ni” lah ni ma makarantar nake yi ai, kwarai ta kyauta ce sisi ba’a bayarwa sai goma ashirin kuɗin Laraba, to mu makarantu a nan kusan duk na kyauta ne ma, to kuɗin babu yawa”

Na ce” Allah sarki mu a unguwar da muka zauna a cikin Kano ba laifi da tsada gaskiya”

Malika ta ce” Haka ne ni ma dan da karatu ya sa ba’a canzamin makaranta ba yaka mata kema ki shigo gaskiya”

Nan nake shaida mata ni ma gobe zanje da haka muka fito, Mama da tuni ta fito haka Malika suka gaisa da Mama ta zauna ta miƙa ma kibiya aka fara kitso Malika nada gashi sosai har mamakinshi na yi na kalleta "Dole kiƙi yin kitso da wuri gaskiya”

Tayi dariya kawai na ɗaura da Allah "Masha Allah kina da gashi "

Mama ta ce” oh Sumayyah anga gashi an ruɗe”

Malika ta ce” wallahi kuwa Mama kamar ita ɗin bata da shi”

Kukan A'isha ya sa ni miƙewa naje na ɗaukota Mama ta ce” haɗo da zani ki goyata, yanzu ta yi barcin goyata na yi ina jijjigata, har ta koma barcin, labarin Islamiyyar da Abbah yakai su Rumaisa na ke bawa Mama da cewa nan Malika ma take yi, Mama da farin ciki take cewa "shike nan kin huta kin samu ƙawa ƙila ma a barki a jinsu"

Nace” Wallahi Mama ni ma na ji daɗi sosai da na ji haka”

Sallamar da muke ji kamar daga sama ya sa jiki na daukar rawa kamar mazari Muryarsu Aunty Asma'u nake ji, da ko jiran amsa wa ba su yi ba suka faɗo cikin gidan mama suka shiga nunawa su uku ne Aunty Asma'u, Aunty Mubaraka, Aunty Maimuna, Mama da take kitso kanta na ƙasa dan bata ɗago ba ko da taji sallama nan suka shiga nunata suna cewa” Hajiya ce ta turo mu ta jaddada miki ta yafe miki ɗanta da haka kike so kika kuma shirya, shegiya 'yar gidan talakawa da duk wanda ya auri irinku cikin tsiya yake ƙarewa, kuma ku raba shi da 'yan uwanshi da iyayenshi kuma Yaya Hashim ya ce na shaida muku yana nan gobe zuwa garin, zai shigar da ƙarar tuhumar mijin naki hukuma ya fito masa da ɗansa kuma wani abu ya sa mi Samir sai Sunje ko kotun ƙoli ce a kan hakan, dan mun riga yanzu mun yafewa Abdullahi ke bare kuma yaranki suyi tunanin raɓarmu anyi gadon makirci da mugun abu masu ƙashin tsiya” Haka suka ci gaba da ciwa Mama mutunci kamar su rufeta da duka kai jin shirun nata ma ya yi yawa sai su kayo kanta Aunty Asma'u ta yi kukan kura sai Mama taji saukar duka nan Mama ta zuciya ita ma suka fara faɗa ko kawa ganin haka suka rufarwa Mama mu kam baya mukayi ina kuka sai Malika ce ta fice waje ta kira maza aka fitar dasu daga gidan da kyar ranar kam na ga bala'i na rasa mai muka tsarewa mutanan nan haka muna takanmu da abin da za mu ci sunce abar musu gida an bari amma har nan ma saida sukayi bincike aka musu kwatance, ba wadda nafi mamaki sai Aunty Asma'u kinada yadda za ki yi kina rigima da waɗanda kin fisu da ƙulla musu sharri ba su ji ba ba su gani ba, ba mu tsare musu komai ba Malika mamaki ta shiga yi sosai na abunda ya faru da jin alaƙar mu da su, nan aka cewa Mama za a kaisu wajen hukuma ta ce "a ƙyale su kawai” dan mu kam ta mu ta ishe mu banji ban da wainar fulawar nan za mu sake samun wani abu mu ci ina muka ga ƙarfi ko bakin rigima harda dambe ni saboda baƙin ciki ban ko tanka ba, dan banida bakin magana ga goyon A'isha bayana kawai na barsu da ubangiji ya gaggauta saka mana banida bakin tsiya dan rigimar tasu duk sanka da faɗa to abun nasu yasha kan kowa, Malika harta tafi da mamaki da al'ajabi take kallan abun, duk da ba wai tasan wani labarin akanmu ba, iya abin da ta gani na yau kawai ta sani, ko da Abbah ya dawo haƙuri ya shiga bawa Mama dan shi ma ya rasa yadda zai yi da abubuwan, yadda na hasaso ɗin ba abinci yau ma kwaki gari, muka samu mukaci shi ma ba dan ƙoshi ba ba wai rigimar ce ba za mu iya ba dasu ƙarfin tane ba mu da shi mu ba wani abu garemu ba bare muce muna ci rigima kuwa ai sai ana da yadda za ayi shi ya sa ganin haka ma suke takamu abin da Abbah ya guje mana ya sa ta kwashe mu kusa da shi to ga yadda Ubangiji ya tsara komai nan da tsammanin zuwan dame gobe za ta zo garemu shin Abbah Hashim zaizo da gaske tuhumar Abbah ɗin ko a'a naka sa wani tunani ma bare ko na tuna wata mafita da zan samar mana na har zuwa wayewar gari.

Na Cancanta (Kashi na 25)

3:00pm da misalin ƙarfe uku na rana sallamar da na ji kofar gidanmu da nake tsugunne gefe daya ina wanke hannu na da bakina ka sancewar tuwon dawa miyar kukar da na gama ci ke nan lokacin, da yau ma da safe ba mu samu karyawa ba sai ruwa da muka dinga sha Khadijah da Khalil ko kwanciya sukayi shame shame dan ga yunwar daren jiya ga shi da safen ma ba’a samu anci wani abu ba, sai da Abbah ya lallaɓa ya fita sai gashi da dawarshi kwano uku da kayan miya harda kuka da Maggi duk Abbah Musa ya bashi, ya ce masa kafin ya ɗan bashi jari ya fara juyawa yana ƴar wata sana'a kafin daminar ta zo a fara noman dan noman ma sai da kuɗin tun da ba taɓa yi ya yi ba yanzu zai fara, Abbah Musa ma ya na da kirki sosai a cikin abokan Abbah na nan ya fi sauran taimaka mana, ko da muna ƙanana muna zaune a Gwarzo haka Mama take ba mu labarin Abbah Musa, kuma yanzu dawowarmu bai gaza ba duk da shi ma famar yake amma akanmu kam Alhamdulillah zai ce tun da har yana da ƙarfin halin taimaka mana, ka sancewar shi akwai zumun ci ko Abbah bai zo ba wajenshi shi zaizo dalilin hakan ma tasa ya fi sauran abokansu Abbah fahimtar halin da muke ciki, Abbah Musa mutum ne gaskiya yana aikin gwamnati da noma duk da koyarwa yake albashin ba mai yawa ba ne amma Alhamdulillah

Sake jin kwaɗa wata sallamar ya sa ni dawowa tunanin da na faɗa gaba na na ji yana tsananta faɗuwa nan na fara addu'a, la'ilah ha'illa anta inni kuntu minaz zalimin, haka na ci gaba da ambata a cikin zuciyata ina addu'ar Allah ya sa kada maganar Aunty Asma'u ta tabbata kada Abbah Hashim ya zo tuhumar Abbah ɗan shi, a tafi hukumar da Aunty Asma'u ta anbata daga nina ƙaramar matsala ce amma saina ɗauka tun da ana san wulaƙantamu kotu ma sai a tafi hawaye na ji masu ɗumi na sauka a kan fuskata na rasa gane laifinmu kawai dan muna talakawa sai a dinga wulaƙantamu abin har hukuma mah, a ce tana ƙoƙarin shiga ma wannan rayuwa wacce iri ce mukeyi a cikin ƴan uwan mu, abin ya wuce muke ganin ana ƙin mu a'a abu ne da duk mai hankali zai yi wannan shaidar ko da yana zullumin faɗa to a ranshi tabbas zai yi wannan tunanin, na rasa gane ta ina Maman take da laifi, kasa matsawa na yi daga inda nake a tsugunne na yi dan yadda gaba na ya ci gaba da dukan uku uku, ga wata sallamar an sake dokawa jin sallamar har karo na uku na jiyo Abbah da ga inda nake yana magana

"Ah'a wannan sallamar fa na san dai ba Musa ba ne, Ahmad taso kaje ka gani waye, danni kam yanzu ina tashi daga abincin nan na ƙoshi kuma”

Ahmad da shi yama rigani kammala ci shirin tafiya islamiyya ma ya fara dan uku ta yi harma suna neman makara ni ma Malika nake jira ta kuma cemin sai uku da rabi za mu tafi dan da muka shiga ɗebo ruwa ko wanka bata da niyyar yi makararrace dai danma farkon zuwa ne na biyewa shiriritar Malika ɗin, duk da dai yau rashin samun abinci ya sa dole za mu makaran ma, Ahmad da banji fitarshi ba sai sallamar dawowar shi da ya yi ya sa na sake jin bugun zuciya ta ya ƙaru kasa amsa masa sallamar na yi haka ma su Mama na ji Abbah yana ce masa

"Lafiya wanene Ahmad"

Amsar Ahmad ya sa na ji dum a zuciya ta na dafe kirji nah cikin inda inda na ji Ahmad ya ce wa Abbah

"Eh. . . uhmm. . Abbah. . . Ɗan sanda ne Abbah da kaki na ganshi ya ce na faɗama kazo police station yanzu kai da Yaya Sumayyah, ana san ganin ku"

A zabure na miƙe daga gurin da ni ke na nufosu

"Abbah ɗan sanda ni me na yi kuma” na yi maganar idona ya yi rau rau

Mama ta ce” Mai kukayi dai za ki ce Sumayyah, shi ma Abbahnku ba abin da ya yi musu kawai don a tozarta shi ne, amma ina zai kai Samir inda bai kaiku ba, talauci ai ba rasa imani ba ne”

Abbah ya cire hannu daga cin abincin ya dubi Ahmad ya ce "jeka kace masa muna zuwa yanzu"

Ahmad sai da ya fice ya dawo da dubenshi ga Mama ya ce” Hauwa'u ai a ganina ni ya dace su tuhuma ba Sumayyah ba, tozarcin ya fi dacewa ya tsaya iya kaina yanzu da me garinnan za su riƙa kallon Sumayyah"

Mamah ta goge hawayenta "Bakomai Allah na tare daku kuma ya isar muku ku nemi agajinsa baya zalinci kuma ya haramta zalunci a cikinmu bayinsa ke nan shi mai ji ne mai ganin zahiri da baɗini, na san mun yi kuskuren tura ƴar mu inda kai uban ta ba’a sanka a wajen bare saka ran za aso jininka, Allah dai ya dubemu da niyyarmu" Abbah ya amsa da "Amin" niko ka sancewata a ruɗe ko hijabi kasa shiga na ɗauko na yi sai Rumaisa ce ta ɗaukomin, haka na bi bayan Baba zugui zugui gaisuwar kirki ɗan sandan bai tsaya ya yi da Abba ya ja machine ɗin shi ya yi gaba ganin fitowarmu, da na fi tunanin ko tunani yake Abbah zai nemi wani taimako daga gare shi bayan ga ubangiji da taimakon shi duk muke nema na san a irin yana yin da ya gan mu ba sile ba sisi banjin zai iya taimaka mana ko da yana da hanyar haka a dai yana yin da na ganshi da alama yana cikin waɗanda suka yiwa talakawa kuɗin goro na hassada da ƙyashi da kwaɗayi da maulah da shishshigi da ya yi wa wasu tsiraru cikinmu wannan halin yawa a cikinmu, amma a zahiri na gaskiya matsaloli sunsha mana kai da ba mu da mataimaka a cikin ƴan uwanmu sai dai muna samun taimako daga wajen ubangiji sai ya ka sance ya sadar damu da mutanan kirki masu ƙaunarmu a yadda muke basa tunanin gazawarmu ce ko kasawarmu, basa kallan talaka a matsayin wanda za ka masa rana ya yi ma dare, basa kallan mu a matsayin waɗanda ko nan gaba za a haɗa baki da mu a aika ta musu wani abun basaji ransu za mu ci amanar su sun amince mana ɗari bisa ɗari, tabbas na sani akwai talakawa da ba wai talaucinsu ya damesu ba, amma babu mu a cikinsu kukan rayuwarmu kawai mukeyi ba muda ƙarfin aikata aiki makamancin wannan fatan ubangiji ya ƙara tsarkake zuciyoyinmu kaɗai a ko da wanne lokacin mukeyi, da wannan tunanin kan muka ƙarasa station ɗin da bata cika nisa sosai bah muna shiga muka ci karo da Abbah Hashim sai su Aunty Asma'u, da tun a harabar station ɗin muka ci karo da tsadaddiyar motar Abbah Hashim ɗin da nake tunani cikin tashi motar suka shigo dukansu dan banga motar Aunty Asma'u ba a wajen, cikin kayansu na alfarma suke zazzaune dan Abbah Hashim ma waya yake amsa wa kallansu nake yi sama da ƙasa kafin na maida kaina kanmu dan ko su Aunty Maimuna da suke aure Gwarzo masu rufin asiri sosai suke aure, amma a hakan wai ake tuhumar mu da ɓatan ƙaton saurayi da ya isa ya tara iyali ma kawai dai tozarcin da suke mana a gidan ne bai ishesu ba harda hukuma, saida ya gama wayarsa ya kallemu a wulaƙance duk da gefensu muke tsaye muna kallonsu gefensu saida ya kallemu tas da Abbah wani koɗaɗɗan yadi ne jikinsa ni ce ma kayan nawa masu ɗan kyau cikin kayan su Aunty Abida, da Aunty Malika da suke bani, Abbah Hashim ya fara ma wani ɗan sanda magana ba wanda ya sa a kiramu ba ne wani daban da gani shi ma ba kirkin zai yi ba

"Yallaɓai ga sunan tuhumar su nake shi da ƴar sa kamar yadda na faɗa muku a kan ɓatan ɗana Samir nake tuhumarsu, dan tun da ƴarsa ta fito da halinta a gidana da tajemin hutun jarabawa, ranar da na ce tabar gidana shi ma ranar ya bar gidan wayoyinsa a kashe na kira su ya fi a ƙirga ita ma mahaifiyarshi ta shaidamin ba tasan ina ya tafi ba, na san talakawa da muguwar sakayya shi ne nakeso a bincike min su har sai sun fito min da ɗana ko da gawarsa ce sun tsafeminshi saboda suna so suyi kuɗi, ban sani ba, dan su ba talaucin da suke ciki ba ne ya dame su sun riga da sun nuna hakan tuntuni dan da shi ya damesu ba za su aje mugunta haka bah a ransu"

Yadda ya tsara kalamansa da yadda suka ganshi alamun kuɗi sun bayyana a garesa ya sa ba tare da jin ta bakinmu ba kawai suka kwashe mu zuwa cell suka rufe mu da cewa har sai an samu number nashi kuka na ji ya kwace min a cikin cell ɗin har sai yaushe za mu samu a fitar damu addu'a kawai nake yi da tunanin su Mama a raina ya za suji idan suka ji haka haka su Abbah Hashim suka gama cike cike su kabsr station ɗin da na san yau zuciyoyinsu sun yi wasai dasu.

Na Cancanta (Kashi na 26)

Har yamma gaf da magriba muna cikin cell ɗin, ba wanda ya waiwayemu, banjin Mama tasan tsaremu aka yi ba, ina cikin cell din na ga shigowarta ita da Abbah Musa da kana ganin ta za ka san bawai a hayyacin ta ta shigo ba tambayarsu aka shiga yi "lafiya”, nan na ji Abbah Musa na labarta musu wajenmu suka zo wani cikin police ɗin da a lokacin da muka iso ban ganshi ba ya ɗauki file da case namu yake ciki ya karanta ya kalli su Mama” kunga ku zauna ai case ɗin ba wai babba ba ne sai na ga duk rashin fahimta ne ma, yanzu in kuna da number ɗin yaron ku kirashi” yana yin yadda ya yi maganar na fahimci wannan police ɗin ba shida damuwa

Mama ta share hawayenta ta fiddo wayoyi biyu hannunta tawa da ta Abbah da na san kayana ta bincika ta nemo ƙaramar wayar tawa da ban fara amfani da ita ba, ta nunawa police ɗin"ka ga wayar nan ta Sumayyah da Abbahnsu ɗin ce tun da suka taho nan nake kiran Samir ɗin bana samu"

Ya girgiza kai ya sake duban Mama” ki sake trying Aunty ko za a samu ta shiga jin lafiyar yaron ce za ta fiddasu banji za su yarda a ba da belinsu", jin haka Mama ta sake ɗaukar wayar ta kirasa ta wa ta raruma ta danna tasa a kunne a loudspeaker ta sakata cikin rashin zato ta shiga number ɗin sai aka katse, Mama ta ɗago tace” Ta shiga amma an ka. . . "bata ƙarasa maganar ba kiransa ya shigo, Mama da hanzari ta ɗauka ko sallama bata yi ba ta fara” Samir kana ina ne muna ta kiranka ba ma samunka dan ka kira Abbanku ka sanar masa inda kake hankalin kowa ya kwanta” ka sancewar loudspeaker ta sake danna wa na ji Muryarsa yana cewa” Ummi Hauwa'u ki faɗa min maike faruwa dan Allah, ina ita Sumayyah ɗin"Mama ta ce” Dan Allah Samir ka fara kiran Abbahnku ka shaidamasa kana lafiya” yana ƙoƙarin sake cewa” Toh amma Ummi. . . ", Maman ta katse shi "dan Allah Samir kayi abin da na ce maka hankalin kowa ya dawo jikinsa” daganan ta katse wayar"Mama da sakin murmushi ta furta” Alhamdulillah"Abbah Musa ya kalleta ya ce” Hauwa'u kin ji wani abin mamaki ga yaro ya amsa waya hankali kwance shi bai san da faruwar komai bama, amma ana neman wulaƙanta Abdullahi har abun ya yi tsamari haka”, ɗan sandan da bai gama fahimtar komai ba ya ce "To yanzu dai Alhamdulillah tun da an sameshi a waya Allah ya tsare gaba bari na shiga ciki na sanarwa da dpo ɗin a kira su suzo da wuri dan kwana cikin gurin nan sai dolen dole dan yanzu ma na san zai sa a fiddo su" su Mama suka ɗaga kai” Mungode Allah ya saka da alkairi” da haka yabar wajen Mama da Abbah Musa suka ci gaba da tattaunawa can sai gashi ya dawo yake sanar da su Mama DPO zai kira su Abbah Hashim yanzu a waya a zo a ƙarasa maganar case ɗin ya wuce, sai da Abbah Hashim ya dawo, danshi kaɗai ya dawo sauran nafi tunani daya kwasosu sun tafi gidanjensu, dama Aunty Luba ita ban da ita duk da bata da mutuncin ita ma amma mijinta bai cika barinta unguwa ba, sai sannan aka fiddomu cikin cell ɗin, da sai gaf da Isha ya zo nan ya fara cewa musu yaronsa ya kirashi ɗin, a nan aka kashe maganar sai kuma iyakar da Abbah ya nema da Abbah Hashim ɗin haka sukayi baran baran kamar ba su fito ciki ɗaya ba Abbah ma ya yi haƙuri da shi a dai yadda ya daɗe yana nunawa

Abbah Hashim ya kalli Abbah da sauran mutanan wajen kafin ya ci gaba da magana” iyakata ta ƙarshe da kai Abdullahi ka raba ɗiyarka da ɗana dan ko zai mutu ba aure ba zai auri wannan ƴar iskar ƴar taka ba, yaron da suke sheƙe ayarsu da ita tun da na masa zancen Fatimah bai sake neman mu ba”

Abbah da kallo yabi Abbah Hashim"Ai tun da ka nuna ga abin da kake so ni kuma ba zan yi ba, kaje ka cusawa ɗan ka halinka firstly ka nuna isarka akanshi, amma ni ba za ka nuna min isa a kan hakan ba zumun ci shi in yaga zai yi damu ba zan Koresa kona ci mutuncin sa ba yadda ni kama tawa, lalacewa kuma da kake kallan ƴata lalace take da ɗan ka suke lalacewa amma kuma har yanzu ba su taka ƙafarka ba ɗaga ƙafarka ma basuyi ba, kuma maganar yaro da kake yi yaga iskancin da ɗan ka ya koya mata kazo da wanda ya fi nasu, dan na yi imani a yadda tunaninka yake akwai matsalar hankali tare dakai ko akwai cutar raina abin da ubangiji yabaka ga cutar hassada da ba ka ganin samunka saboda rashin godiyar Allah sai talakan talau shi ne kake ganin yana da samun da za ka tsaya jayayya da shi”

Jin maganganun da Abbah ke mayarwa da Abbah Hashim ya sa ya fara muzurai” kungani dai irin cin mutumci da yake min a ƙarasa yi mana iyaka ni dashi”

DPO ɗin ya kalli Abbah Hashim ya na cewa” Alhaji ai an gama muku iyaka, ko da ba'ayi ba inshi yana da hankali ba zai sake shiga rayuwarka ba ko da ya rasa dangin da zai yi hulɗa dasu, saboda ƙaramin case haka ka kawoshi nan an sashi bayan kanta da ƴar shi da na ga fiye da wannan ma za a iya yi a gida a sasanta, mu bi yadda kake so ne saboda bamasan maganar ta yi tsawo tun da ga yarda ƙarin naka ya ce a kan maganar yara ka jawa naka kunne ka faɗa masa abin da bakinka yaso akansu shike nan, dan Allah ku tafi haka bamasan wata hayaniya kuje gida ku ƙarasa maganganunku, ko ku tafi ofishin sasanci mu dai ga iya sasanci da za mu iya yi muku an bi ma haƙƙinka da kake nema shike nan, duk mai gaskiya tsakanin ku watarana za ta bayyana, in kuma rayuwar talauci ce tun da shi ya ɗanɗana ba kaji komai ba, da ya dace ka tausaya musu komai za suma saboda rayuwarku ta banbanta ka kuma taimaka musu taimako na zumun ci da Allah da Manzonsa su sukace ayi shi a sadar dashi, to in ba kayi wasa ba kaima za ka ɗanɗana ko ga kuɗin sukasa amfani a gareka komai mai sauƙin ne a gurin mahaliccinmu"

Da haka dai muka fito ko takan Abbah Hashim ba wanda yabi yanata faɗansa muka wuce ya zo ya wuce mu a mota ya baɗemu da ƙura ya fi motar da ƙarfi ta gabanmu, nidai su Mama ke tattaunawa ni ko har muka zo gida ban iya cewa komai ba da kallo nake bin kowa na gidanmu haka na shige ɗaki A'isha da Mama ta bari gida ta sha kuka har Rumaisa ta goyata abinci Rumaisa ta kawomin ɗaki na ce mata na ƙoshi shi ne maganar da zance na yi tun shigowar mu a zahirin gaskiya ba yunwar ce banaji ba cinne ba zan iya ba ƙwaƙwalwa ta ta kasa aiki yadda ya dace tunanin na kasa yi kukan ma na kasa yadda nake jin labarin depression, a makaranta sai nake ji kamar ina gaf da shiga cikinsa, to gani ke nan inaga Mama da Abbah amma ina jin tausayin kaina a ƙananan shekaruna ina fuskantar hakan kaina da da cikina suka ɗauki ciwo a tare lokaci ɗaya haka nake zub da hawaye kamar ruwa na tsiyaya wata irin azaba nake ji kaina kamar ana dokamin guduma na rasa gane maine ke shirin faruwa dani ina jin labarin mu ko a littafi da film ba’a kwatanta kamarsa ba, saida kan ya lafa na miƙe na yi alwala na dawo na tada sallolin da ake bina suma a zaune ina idarwa ko azkar ban yi ba na kwanta ina jin ko a kwance zan yi addu'ar idan tunanin matsalar dake faruwa ta barni da hakan nake jin Allah ya dubi zuciyata ya kawo mana canji ba wai ni kaɗai ba dukkanmu Allah ya gani an mana zalinci an kasa fahimtar mu saboda talauciy, na fashe da kuka mai cin rai ina ambatar Allah"ya Allah ka dube ni da dukkan Musulmi da Allah ya jarabcesu ta koma wacce fuska ce ka kawo mana canji, Allah ya ba ni ikon ambatonka a zaune a kwance a tafiya a lokacin samu a lokacin rashi, Allah kada ka ba ni ikon kokawa ƙaddarar jarabawoyinmu ko dan kada ka bar mu dasu"nama rasa me zan ci gaba da yi wayata da Mama ta ba ni a hanya silent na dannata ma.

"Yaya Sumayyah ana kiran wayarki tana haske” maganar Rumaisa da na ji cikin barci da dakyar ya daukeni ya sa ni buɗe idona da kyar saboda kaina dake saramin na kuma kasa magana a samo min magani, da na san Mama taji hakan saita min faɗan saka damuwar nan acewarta danaji ta dasu Abbah a hanyarmu ta dawo wa, fiye da hakan ko bai faru ba zai iya faruwa kada wannan ya sa Abbahn damuwa, wayar nakai hannu na ɗauka na duba na ga Yaya Samir ne haka dai na ɗauka jiki a sanyaye na kasa cewa komai na yi shiru, sai shi ne na ji yana cewa

"Sumayyah kina jina ko?", dakyar na amsa da "Eh Yaya” Sumayyah dan Allah kiya haƙuri da abin da Abbah ya sake yi, wallahi ban sani ba amma muna waya da Ummi ai shi ne dai ya ɗauki fushi dani inji Ummi ta ce na bari sai ya wuce na kirashi, ban san abin da zai yi ba ke nan kuma ban san yana kirana ba, wallahi Sumayyah na rasa mai ke damun Abbah, halinsa ya ƙara sauyawa sai kace bashida imani, haba samu ai da rashi na ubangiji ne abarku mana haka” tun da ya fara maganar nake zubar da wasu hawaye masu zafin gaske har ya ƙarasa banajin zan iya magana mai yawa ma ko da a zahiri bare a waya na ce” Yaya Samir sai da safe za mu yi magana”, na ji yo sa yana cewa” Sumayyah kina jin haushina ko babu laifi kiji haushina ai na cancanci hakan, amma ki duba ba laifina ba ne ban san zai yi ba Ummi batasan ya zo ba dan Allah kada ku kamamu a kan laifin Abbah ba muda masaniya ni ɗan uwanki ne, ina ƙaunar farin cikinki da naku duka ni ɗin kamar uwa ubane nake wajenki Sumayyah, tun ranar da na barki hankalina ya kasa kwanciya nata kiranki shiru wayarki, ashe ɗin bakwa yana yi mai daɗi na ji duk abin da su Abbah Imran sukayi da barinku gida ina nan amma banajin daɗin komai dake faruwa na ma rasa wanne mataki zan dauƙa Saddiƙ na Abbah Imran ne y ba ni labarin komai abun babu daɗi Allah ya ganardasu ya muku sakayyah"haka Yaya Samir ya ci gaba da yi min kalaman kwantar da hankali har na ji zuciya ta ta rage zafin da take yi daganan mukayi sallama na kwanta barci mai cike da mafarkai iri iri da na san yana yin da nake yabawa shaiɗan galaba akaina ya sa nake mafarkan kala da kala duk marasa daɗi, irin yadda yana yina yake, Har hakan ya sa na farka a barcin saboda mai ɗumbin mafarkan tsoron da nake yi, addu'a na yi kawai na runtse idanuna hawaye na sake bin kuncina, na rasa ina zan dafa ina zan saka raina mah zafin ƙiyayyar ya yi yawa ban yarda duk a dalilin Mama ba ne, ko wani waje kalar abin da zai yi garemu ke nan, yaushe kukan zai ƙare namu zamuyi farin ciki ya mantar damu ƙuncinmu yaushe waɗanda suka ƙi mu za su ci tamu alfarmar yadda Halimah ta faɗamin Halimah ɗin nakan tunota a duk lokacin da na shiga damuwa musamman irin ta yau da Halimah ya dace ta sani sai kuma Baatul yana yinmu tare da farin ciki nake tunowa muna yin abu irin matured ɗin nan, hawayen dai kam yau da za su ƙare da sun ƙaremin na rasa juriyar da na saba arewa a yau ɗin, tunani nake tabbas akwai masu matsalolin da sunfi nawa tare dasu suma a wannan daren sun kasa runtsawa ɗin, kuma babu damar su samu ƙarfin yin nafilfilu yadda ni ma banida zuciya ta babu ƙarfi irin na sauran lokuta da a wannan yana yin nakesamun damar nafilfilu da kaiwa Allah kuka na, Allah madogara ne na san kuma baya zalinci ya haramta sa a tsakanin mu Allah zai dubi zalintar mu da aka yi Allah yana saurin amsa addu'a na wanda aka zalunta ko dama bai kai ƙarar mutumin da ya yi zalincin gabansa, saboda ya zama abin haramci garemu, ba kuma Sudan tabbacin ta ina sakayya za ta zo taka sance. . .

Na Cancanta (Kashi na 27)

Suku ku na tashi gaba ɗaya kuma har lokacin kaina bai bar ciwon ba sai dai ya yi sauƙi mun samu ragowar tuwon jiya mun ɗunɗunma mun ci, ƙanne na da aka samu hutun term yau da ta kama monday duk muna gida, tunanin kuɗin da na ba Abbah da yaya Samir ya ba ni na shiga yi dan indai kam ya taɓa su za mu ga sauyi sai dai banji ya taɓa ta yiyu wani abun yake nufin ya yi dasu dan indai ba’a juya ba to ƙarewa za suyi bare ma ba yawa ba ne dasu sosai ba su wuce dubu Ashirin ba a yadda na ƙiyasta nake jin kuma dasu za a samar masa gonar da zai yi noman dan na san ita ma sai anbada wani abun, kowa a wannan lokacin yana fama da abin da ya dameshi, ina ma laifi in mun samu duk da za mu ba da wani abu wani ko nawa za ka bashi bai yarda aci arziƙinsa ba ya gwammace ya aje gonar bai noma ba har damina ta wuce mutane iri iri gasu nan muna rayuwa a tare da su, Allah dai ya azurtamu da manufar alkhairi a zama mutanan kirki, saƙon da Mama ta aiko Rumaisa da shi wajena ya katse tunani na, cewa naje mu tafi ɗebo ruwa gidansu Malika haka na zari hijabi muka fice ba dan wai ina jin ƙwarin jikina ba, dan dai ina cewa ga wata damuwata zan ja Mama ta tsareni a kan damuwa na cireta Ita kuwa na ɗauke ta dole ce ko ba ka so sai ta ziyarceka, haka muka tattara kayan ɗebo ruwan muka fice, gidansu Malika muka shiga muka gaisa da iyayenta muka fara ɗibar ruwa banga Malika ba ban kuma tambaya ba, "can muka ji ƙarar buɗe kofar da nake tunanin nan ne bayin gidan da bucket ta fito jikinta ɗaurin ƙirji ne da alamun ruwa a jikinta da yake shaida wanka ta fito ta kalle ni da nasa Rumaisa da ja ruwan na tsugunna a gefe

"Sumayya ashe za ki shigo yanzu nake niyyar na shirya kafin na wuce inda zani na leƙo gidanku", na yi murmushi na ce” Eh kin ganni dai kaɗan ma za mu ja ruwan za ki iya shigowa ai” Malika ta dawo inda nake ta zauna saman bokkitin ƙarfen ta ci gaba da cewa” kin ga ba fa lallai zuwan na ji labarin mai ya faru, zullumina kar a ce gulma ta kawo ni, yara suka shigo suke faɗa” Ni dai kallan Malika nake kawai banjin ta cancanta na zauna bata labari haka duk da yadda na ga alama daga ita har iyayen ta suna da kirki, amma sai na ga kamar akwaita da sanjin zance ko dake da abu na faruwa ba ka san dalili ba gwara kaji ba'asinsa yadda yake ko ka samu natsuwa kuma abune da za a kallemu bahagon kallo dashi, amma saina ga lokacin ta sani baiyi ba na dubeta da canza zancen

"zafa ki bushe fa kinzo kin zauna haka” Malika ta miƙe "Au namanta saboda zafi mah shi ya sa”

Rumaisah bayan wucewarta ta ce” Yaya Sumayyah wannan Malika ɗin kamar munafuka wallahi” Nasa dariya jin abin da Rumaisah ta faɗa na ce "Ba wani munafunci son jin zance gareta kawai”

Rumaisa ta ce” uhmm aji daɗin ba da labari ba ansan daga A har Z"na girgiza kai na ce” oh Rumaisah ai ba mu tabbatar ba ai, kawai nafi tunanin tana cikin mutane ne da sunfi san suji labari daga farko har ƙarshe don hankalinsu ya ƙarasa kwanciya hakan ma kulawa ce nake gani” Rumaisah ta ajiya gugar gefe” gaskiya dai banga ma yarda da itaba kina gani saboda gulma bucket ta kafa ta zauna”, Ni dai naka sa sanin a inda zan aje Malika ɗin, da haka muka ɗauki sauran ruwan bayan mun musu godiya muka fita, takalma da na gani ƙofar ɗakin Mama ya sa ina aje Bucket ɗin na shige dan na san baƙin namu ne na arziƙi ne waɗannan dasu Aunty Zainab ƙannansu Mama na ci karo a ɗakin Zainab ta kalle ni kafin na ƙarasa zama "To zauna mutanan cell kai Sumayyah ƴan uwansu Abbahnku ba su da kirki, ai yanzu muke tambayar Yaya Hauwa'u ta ce kuna ɗibar ruwa makwabta, gidan ma da ta mana kwatance gidansu Malika Tukur Bello ne ƙawa ta ce ma, a boko, "

Ni dai na zauna gefensu iyayen labari sunzo kuwa kafin na fara bawa su Aunty Zainab labari” Kai kadai bari Aunty Zainab mun sha cell jiya ashe labari har ya kai muku"

Omm Habiba ta kalle ni” lallai Sumayyah ai yanzu mutum ake kiwo duk wani mutsinka a idan mutane yake kuma kaɗan suke jira, Yaya Jabir ya zo da labarin nan, ni nama rasa mai kuka musu ma, wulaƙanci ne kawai, kudai Allah ya kare ku sharrinsu" na ce” Amin", Aunty Zainab ta ɗaura "Allah ya kawo muku canji na alkhairi duk dan ba ku da shi ne, Allah shi ya sa kuma ko a littafi ban ci karo da yana yin wannan zumun ci naku ba uwa ɗaya uba ɗaya hakan ke faruwa, ko littafin Zumun cin Zamani banajin yakai naku labarin ƙunci duk da dai a kan Zumun cin yake magana ai a wannan yana yin fa in fa ba kada shi ba'ayi dakai karka ɗaura ko nauyi ne” Nanfa labarin littafin aka buɗe shafinshi su ne dai masu karantawar ni saidai na ji labari, yadda muke firar ka shigo gidan za ka ɗauka su Aunty Jamila ne suka zo saboda yadda muke firar tare, yini sukayi a gidanmu ka sancewar sunsan yana yin da muke ciki ko ƙorafi ba su yi ba, har Abbah ya dawo da ɗan wani abun dafawar dai, sai da yamma sai ga Malikah ta shigo gidan nan ta shiga mamakin ganin su Zainab gidan bayani suka yi mata, nan fa fira ta ɓalle, Mama ta koramu ɗakinmu, nan muka ci gaba da fira sai lokacin n ski jiki fiye da da Malika ɗin, sai dare suka tafi gida.

Abubuwan yanzu sai na ce sun yi sauƙi ba kamar da ba Abbah ya fara sana'a saida kayan miya duk da ba wata riba musamman ko dan ƙaramin jari garesa ga gasu kayan gwari wasu duk ruɓewa sukeyi da cinikin ba duka kowa yasan yana saidawa ba a kofar gida yake zama, wani lokacin Ahmad a lokacin Mamah ta fara dafamin awara ina soyawa a kofar gida ka sancewar layin mu babban layi ne muna dawowa islamiyya nake fara soyawa Malika kullum tana wajen ita da take 'yar fira hakan ya sa ita ma mamarta ta ce ta dinga mata dankali da zaman da take yi haka muke sana'ar mu asirinmu rufe, muna samu, batun Yaya Samir ba ma wani waya da shi ko yana kirana ban sani ba dan wani lokacin kashe wayar nake yi, ta yi kwana biyu ma kashe babbar ce dai Ahmad ya fi anfani da ita dan shi dama mayen waya ne, niko saidai na yi kallo ko karanta Novels da ita hakan ya sa na maida Sim din da yke ciki a wayar, ganin ban fiya anfani da itaba tafi zama flightmode, Yaya Samir inashan faɗa wajenshi wai in dinga kashe wayata na ce masa matsalar caji ne wai su Halima na ga ya dace na kira tun dawowa ta ba muyi waya ba

Duk muna tare ɗakin Mama ni da ƙannena da ita yau gidan Aunty Maryam yayarsu ta tafi dubo jikinta bata jin daɗi ka sancewar juma'ah ma ya sa jin rashin lafiyar ta ta lokacin za a jiƙa wake Mama ta ce abari ayi gobe insha Allah tun da yau juma'a ma, Ahmad dake game shida Sadiƙ d Khalil a wayata su na kallah na ce” Ahmad ba ni wayar nan na kira su Halimah, tun da na dawo ba mu taɓa gaisawa ba” Ahmad ya sa game pause ya tsaidata ya miƙomin wayar yana cewa” Gaskiya Yaya Sumayyah baki kyauta ba” na amsa ina” toh yaxa'ayi Ahmad hankali ba kwance ba bari na kira dai” duka na yi rashin sa'a wayoyinsu a kashe,

Na miƙa masa wayar "ci gaba da game ɗin ka ba sa'a duka wayoyinsu a kashe suke” amsa ya yi yana cewa” yawwa niko Yaya ana yawan kiranki da wata number idan wayar na wajena ganin baƙon number ya sa bana faɗa miki sai jiya ne ma na ɗaga akace ke ake nema na ce bakya kusa da wayar shi ne ya ce mai kiran in kindawo na ce Hamid ya kira”

Tunma kafin yakai ƙarshen zancen na san Hamid zai faɗa dan Yaya Samir munfi gaisawa a ƙaramar waya tun da na ce masa Ahmad ya fi anfani da babbar da ɗaya sim ɗin shi ko Hamid number na ɗaya gareshi, na dai kawar da tunanin na ce ma Ahmad "Malam Hamid ne fa, da ya mana service a makarantar mu", Ahmad ya ce "Ok na gane shi wanda kuka haɗu a Katsina kwanaki har Abbah Hashim ya dokeki akansa” na ce "Eh shi ne fah"Ahmad ya ce” lallai ai Yaya kwarya bin kwarya take tun da kikaga haka dagaske masu kuɗi ne, gwara ma karki saurareshi, dan kayan saiti ma complete Abbah bashida shi saidai a dangin Mama ayi karo karo" na ce "Haka ne kam, kawai inya ƙara kira kace masa wrong number ne ko kaƙi ɗagawa, kawai a rabu lafiya, Allah ya ba ni daidai dani”

"Haba Yaya Sumayyah yana sanki Allah uncle Hamid Kuma yana da kirki, ba lallai suyi mana yadda su Abbah Hashim sukayi ba, tun da wasu keyi masu kuɗin ba duka suka taru suka zama ɗaya ba” Rumaisah ke wannan zancen

Harara na galla mata rai ɓace na ce” Banza sakarai dake nake magana, in Kuma kin ga ban kyauta ba ki je ki auresa tun da kinfini sanin waye Hamid ɗin"Tsaki na mata nama tashi daga wajen Rumaisah ta na cewa” Allah ya baki hakuri” ko takanta banbi ba na ma shiga ɗakinmu na ɗauki hijabi na shige gidansu Malika da mukai matuƙar sabo yanzu, tana yanka dankali da za ta fitar na same ta.

**** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604
Na Cancanta

Post a Comment

0 Comments