Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Cancanta (Kashi na 20)

Misalin ƙarfe goma na safe na kammala shiryawa, Halimah ma ta shirya dan Yaya Baffa zai kaini Tasha tako ce lallai sai ta bishi an rakani da ita Faisal ya dauki jakata ya kaita napep dake kofar gida, Abban Halimah da mamarsu kuɗi suka ba ni na yi kuɗin mota da inada niyyar ƙin amsa Halimah kuwa ta karɓe ta ce su bata ta bani, tasan halina na musu godiya duka gaisuwa suka ba ni na yiwa su Mamah da ƙannenah, haka muka fito ina sake jin ƙaunar Halimah da ahalinta a raina muna tafe a mota Halimah tana jana da fira har ni kam hankalina baya wajenta tunanikane kala kala a raina ga uwa uba kewar Halima da nake yi ga Batul ma ba mu haɗu ba babu damar hakan hankalina ya yi gida ne, Halimah ta kalle ni

"Haba mana Sumayya sai zance nake kinmin shiru"

"Yi hakuri Halimah ban jiki ba”

Yaya Baffa ya ɗan juyo ya kallemu

"Haba keko Halimah tunanin gida take yi barta ta yi abunta, na san ji take kamar ta yi tsuntsu ta jita gida, na dauka zakuce ma za ku biya gidansu Batul ai, na ga munzo unguwar"

Kamar jira muke yi ya yi zancen Batul cikin haɗin baki muka amsa

"Zamuje mana Yaya Baffa”

Kwanar layin gidansu Batul ya yi ba wata tafiya mai nisa sai gamu kofar gidan nasu, Dan ƙaramin gida amma jikin family house dinsu yake Batul ta ce mana duk cikin family house din nasu aka yi gidan nasu, Kamar jira muke napep din ta tsaya mukayi saurin ficewa a motar, Yaya Baffa na koramana kashedin kada mu daɗe, da Batul muka ci Karo zauren gidan nasu muna tura kofar, wani ihun murna ta saki

"Sumayyah oyoyo ashe kin dawo ba labari, ƙila ma kina Kano shekaran jiya da mukayi waya, mu shiga ciki”

Halimah ta kalleta

"Ke malamah sauri fa muke da Yaya Baffa muke, kin san ashe su Sumayya sun koma Gwarzo fa, ni ma sai jiya da Sumayya ta zo na ji labari, ita ma batada masaniya a gidanmu ta kwana ma, yanzu Gwarzo za ta wuce muka biyo, muje mu gaishe da Mama dai mu fito"

Batul ta harari Halimah

"To aku mai bakin surutu aina dauka ma gaishe da Maman ma ba za a shiga yi ba, Abbah ma yana ciki, amma banji daɗi ba Kamar na yi kuka”

Da haka muka ƙarasa ciki Halima na faɗin "Nima haka na ji Batul ya zamuyi an saba, kamar na yi kuka nake ji”

"Ke dama uwar kuka ba”

Duka dariya mukayi ban da Halimah da ta haɗa fuska a tsakar gida brander muka sami iyayen Batul zaune a ƙaton tabarma da ƙannenta duka ka sancewar Batul ita ce babba ita ma, kamarni, gaisawa mukayi Batul ta shiga koramusu jawabi cewar mun tashi mun koma garinmu Abban su Batul cikin rashin jin daɗi ya kalli Batul

"Amma ba jimawa dai da hakan, da ai ba za ayi haka ba, indai matsalar haya ne ga gidan Abbahnku sai su zauna har Allah ya hore musu, aikinma ban da abun Abdullahi ai nema akeyi ba’a zama haka, amma banji daɗi ba”

Maman Batul ta girgiza Kai da damuwa fuskarta

"Nima haka Abban Batul gashi duk sun saba, za a rabu Kuma, ƙila shi ma yana da buƙatar komawa, shi ya sa ba labarin kome”

Cikin jin daɗin yadda iyayen Batul suka nuna jimamin komawar na rashin Jin daɗin su na yi magana

"Ai mamah mai gidan da muke hayarne ba zato ya zo ya ba da notice Abbah na san bai samu lokacin tsayawa wani tunani ba sai haɗa kaya kawai suka koma gidan duka”

Abban Batul ya dube ni

"Haka ne amma kwanaki baya mun haɗu ya fara jan napep ya cemin Alhaji Yassar ya samu daga wajenshi, Ahmad ma ya samu yake ja”

Halima ce tasa baki lokacin

"Ai Abbah napep din Faisal ya ce ta lalace ba kuɗin gyara shi ne ya maida musu kayarsu"

"Aini Abdullahi na rasa irinshi tun da yara sun haɗa mu ba'abun yana boyemin abubuwa da yashafemu duka ba ne, ko ya zo wajena ko mun haɗu ba wata magana da za a taru a jajanta ko abunda ya shafi buƙatar taimako da zai faɗamin na rasa wannan abun nashi, tafiyar Sumayya ma sai bakin Batul na ji yanzu ai an zama ɗaya, dama ɗaya ne tun da school ɗaya ma mukayi a lokacin da yake yin masters"Abbah ya ƙarasa zancen da alamun damuwa

Haka duka jikinmu sanyaye muka miƙe sosai na san halin Abbah shi kullum maganarshi 'yan uwanshi su kasa taimakonshi inaga wasu abokai kowa yana ta iyalanshi da familynshi, shi kanshi Abban Batul din ba wata dama gareshi ba sai da muka shiga JS3 muka fahimci akwai sanayya tsakanin Abbanmu da nasu Batul ɗin duk da kawai zaman aji ne ba wata gaisawa ake ba ayi lecture ne a fito saiko assignment ya haɗa ko presentation ko wani research ɗin a irin wannan Abbah yasan Abbah Ahmad ɗin

Batul hanyar falonsu ta yi a maimakon mu ƙarasa fita waje Halima ta Kira sunanta” mu kam ba falon da za mu shiga”

Batul taja hannuna

"Kin ga Sumayya zo mu shiga dan Allah, kyale wannan Haliman ta jira mu a wajen, na san saboda Yaya Baffa kada ya Mata banbami take wannan"

Ummansu Batul ta kalle ni

"Au wai ba ku kaɗai ba ne?, ya kamata ku kyale Batul ɗinnan, Kuma zo ku rakata sai ku dawo da Haliman su ajiyeki”

Halimah ta yi saurin amshe zancen

"Eh Ummah mu da Yaya Baffah ne kuma ya ce sauri yake yi saboda muma ya yi lattin fita”

Ummah da take Shirin sake magana Batul ta yi saurin marairaice murya

"Ummah dan Allah wata kawai 'yar magana fa zamuyi minti uku ma ya yi yawa”

Ummah ta maka mata harara

"Tatsuniyar gizo dai na san bata wuce koƙi zancen dai Yasir ne”

Abbah dariya ya yi wa Ummah

"ai Batul da Yasir ban san wa ya fi san wani ba, har ni ma na ƙosa na musu auren nan, zance kullum saboda yana ganin shi ɗin dan gidane”

Da wannan muka shige falon muna zama a kujerun Batul dariyar data kunso ta fara yi, Halima ta dube ta

"Kin ga ba musan hauka fa malama meye wai dama aje mu kikayi ki dinga dariya”

Batul ta haɗa rai kamar ba ita ta ke dariya ba

"Kin ga Halimah bafa ni nakai zomon ba, Ni na ce ki ɓata da naki saurayin mai kan kwakwa”

Halimah da masifa ta dubeta

"Kin ga Batul ki fita idona da cin mutuncin Aliyu fa, Kuma gwara shi ke naki saurayin kan giginya gareshi”

Ni abun nasu dariya ya ba ni na kallesu"kunga ya isa haka dan Allah, Halimah barta ta yi maganarta kin san Yaya Baffa na jiranmu dai ku nake jiyewa karya juyeku a Rijiyar za ki ya kwashi passenger ko ya dinga yawo da ku da passenger kuma a motar, ko biyu yake samu ya rage zafin ɓata masa lokacin da kukayi”

Batul ta makamin harara "Aniyar ki ta biki mai baƙin fata, insha Allah ke Za ki hau rigwagwaar mota ban da munafinci ina Kano ina Gwarzo amma tun goma Za ki ce za ki wuce saboda kin gaji da ganinmu, babu amana, ban san ya za ki koma kikayi aure ba Hamid ya kwasheki Katsina ya kaiki ya ajiye”

Halimah ta kalle ni kafin ta kalli Batul

"Kin ga wanne Hamid ai anbar yayinshi ga Samir nan yayanta kin ga ko banza Abbah Hashim ya mareta ta wata rana idan bata Kai ga dukan ba”

Batul ta kalle ni” Subhallah meya faru kumin bayani haba ni dai na san ba lafiya ba, tun da na ga Sumayyah haka ayam"

"Uhm ina ko lafiya matsiyacin mutumi nan ya kama Sumayya ya mata shegen duka, yanzu ma saida ta gasa jiki da ruwan zafi” Halima ta yi zancen ta ƙarasa bawa Batul labarin komai

Batul ta kalle ni cikin tausayawa”, Kuma yanzu kin amince da Samir din, gaskiya ki yiwa Hamid adalci da babu Hamid ko dan Abbah Hashim da saiki amince da Yaya Samir ɗin amma kin bawa Hamid dama tun farko"

Na kalli Batul"nifa Batul wallahi komai ya fita raina fa, na rasa tunanin da ya dace dani Dan Allah ma kada ku bawa Hamid labari game dani, ni dagashi har Yaya Samir na haƙura da su, idan na ƙi karɓar Yaya Samir saina kega na yi butulci duk da shi ɗan uwana ne, tun ina yarinya nake jin labarin irin son da Yaya Samir ya nuna min, wajen Mama kafin su koma Katsina mu dawo Kano da na mantashi da kanshi ya daukeni kawai dan na tunashi wannan abun da ya faru ƙaddara ce kawai, da na san da cewa Yaya Samir na Sona ba zan iya amsawa Hamid ba saboda ban san shi ma daga gareshi mai zan tarar ba”

Batul ta dafani” Dan Allah ki daina wani tunani ki yi addu'a insha Allah za ki samu mafita, addu'a ita ce mafita kawai Allah ya zaɓa mafi alkhairi, kuma ni kaina ban san me zan cewa Hamid ba idan ya tanbayeni game dake kin riga kin gama masa magana kince ya yi hakuri, tun da Kuma ga ƙudirin Abbah Hashim a kan hakan kin san halin wasu mazan idan yaga Fatimah ta fiki a wajenshi zai fi amincewa da ita ƙila a hasashena fa tun da zumun cin naku ya zama ga irinshi, ni kin ga Yasir babanshi yana da kuɗi sosai amma ba wani wanda yakai korafin Abbanmu a kan shi talakane kada Yasir ya aureni, kin san ko da muke 'yan uwane da danginkune sai sun yi, yanzu haka kin ga Yasir har ya kawo kuɗin aurena ma, shi ne zancen fa da zan muku"

Fatan Alkhairi da addu'a muka mata, kuma na ji daɗin kalaman Batul sosai, sai na ji zuciyata ta nutsu

Halima ta kallemu"kunga ku taso dan Allah kun cikamu da zancen soyayyah ni wayata ma kashe take kada ma ki yi tunanin Hamid zai kirani blocking nashi ma zan yi dan ban san me zance masa ba, nifa tun da Aliyu ya ba ni haushi kowanne namiji ciki nake dashi”

Tsaki naja mata” kin ga kin damemu Aliyu Aliyu dai kawai idan da gaske yake ya turo muyi dai mu gama faɗa kuma ta yiyu ke kika ja tun da ke ɗin zuma ce sai da wuta wani lokacin, sanda Kuma za ku shirya ba mu sani ba”

"Allah kina wasa ko Aliyu ya ba ni haushi ba kaɗan ba ku tanbayi Faisal ku ji ma shi na ce ya fita ya ce kada Aliyu ya sake zuwa ƙofar gidanmu"Halimah ta yi maganar tana miƙewa

Batul ta galla mata harara” kin ga mu fa ba muda lokacin shiriritarnan taku, tun yaushe kike cewa Kun ɓata Kuma a zo a shirya mu tuno miki zancen ki ce baruwanmu, yanzu na gane ma ciwan so kikayi kwana biyu"

Halimah ta hararemu duka duk da ni ɗin bance wani abun ba” wallahi ku duka ku fita idona, Kuma ni zazzabi na tun kafin muyi faɗa nake yi kada ma ku min wata fassara”

Da wannan muka fito waje Abbah kuɗin mota shi ma ya bawa Batul ta ba ni godiya muka musu suna mu gaida su Abbah Abban Batul ya ce zaima kira Abbahnmu insha Allah, abin da muke gudu muka tarar munsha faɗa wajen Yaya Baffa ya faɗa wa su Halimah saidai ya ba su kuɗi su hawo wata napep su juyo gida shi ya makara ma yanzu, Ni dama na san za a rina indai Yaya Baffa ne, har cikin Tasha muka ƙarasa sai da na shiga mota na zauna Yaya Baffa ya biya kuɗin motar kafin suka wuce ba dan naso ba sai dai ya zama dole na rabu da ƙawayena masu ƙaunata a dalilinsu na yarda akwai ƙawayen da sun zarce ƙawaye saidai akirasu 'yan uwa sun dauki matsalata kamar tasu, abin da muka rasa daga 'yan uwan mahaifinmu, da su ya fi cancanta su kula damu da tarbiyyarmu, a hakan wata 'yar kulawar saboda Abba ce akeyi mana ita kaina na ƙasa Ina zub da kwalla har motar mu ta ɗaga jin mun Fara tafiya na yi addu'a na ci gaba da tunanin da nake yi

**** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604
Na Cancanta

Post a Comment

0 Comments