Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Cancanta (Kashi na 16)

Da tunanin wayarmu da Hamid na farka na Fara yini na da ita ina sake jin shi kamar mun jima da Fara soyayya daga haɗuwar mu zuwa yanzu na bashi matsayi mai girma nake ji a raina, zullumina ɗaya a yau ɗin wani kallo zai samu daga ni harshi wajen Abbah Hashim da tunanin na cire ta gumin da na yi na shiga toilet wanka na yi na yi alwalar sallar walha, dan kafin na shiga na ga 9:30am lokacin Kam yama daɗe dayi, shirina na yi cikin riga da siket atamfa mai black da coffee, batik ban tsaya dogon kwalliya ba, na fara tada sallahr sai da na idar na shafa powder da lipgloss a baki nasa brush na gyara girata kwalli ma ban tsaya nemanshi ba, dan ba ni da ma shi Dan kwali na yi zaman daurawa na nemi farin mayafi na aje gefena, kiran da na ji wayata ya sa gabana faɗuwa sunan ubangiji na kira kafin na duba na ga mai kiran, Yaya Samir ne hakan ya sa na yi saurin ɗagawa

"Kin manta da break fast yau ke nan na ga baki fito amsa ba ko duk murnar wayar ne”

Murmushi na yi kafin na ba da amsa na ji muryar Fatimah

"Yaya yaushe kuma ta yi waya, Ni inata fama ko Kai ko Abbah wani ya siya min sabuwa kunƙi, na san ma kaine za ka siyama ta”

Tsaki na ji yayi” Tambayata kikeyi ko meye idan za ki yi shiriritarki ku yi da AbdulMalik"

Naji yana "kina jinah Sumayyah kizo ki dauki abincinki”

Murya a sanyaye "toh Yaya Samir"

Wayar ya katse ni ma na cire wayar kunne ina kallanta a raina ina sake ayyana ni da ma ya barta, ni ta kamaimai ban san anfanin da za ta yi min, gani ma ina da gudun rigima a kan waya, dama duka suna Yaya Samir ya fi sona a kansu, tom Ina ga sunji kawunsu yama siya min wayar gwiwa a sake na miƙe na fita a ƙaton Dining Table na wuce su ina gaida Ummi da Abbah da Yaya AbdulMalik, Yaya Samir, duka da lafiya suka amshe dama na san Yaya Samir baya tsawaita amsa gaisuwa duka harara suke miƙamin musamman Abbah da Fatimah, ita dama exactly halin babanta gare ta, har gwara Yaya AbdulMalik ya fi da na Umminsu, kawai saboda Fatimah ne da yadda Abbah ke nuna min suma suka fara tom bai nuna ina da muhimmanci ba a wajenshi bare su, har na shiga kitchen na gaishe da Baba Indo na dauki abincina na fito, zan wuce na na koma ɗaki na ji muryar Yaya Samir

"A'a Sumayyah shigo ki zauna falo, na ga ma kinci kwalliya haka Abid ko yau ma Ummi za ta aike kune”

 

Ina koƙarin ƙarasawa na zauna Ummi ta fara” Samir ba ni son iskanci fa a aiken zan ƙare, sun janyomin Mahmud na tamin sababi na aikesu cikin rana na san ana matsalar abin hawa unguwar nan, ni kuma na san da mashiririciya na haɗa aiken ka ga uwar kwalliyar da take fa” ta nuna masa ni ina ƙoƙarin zama da dai mamaki tom tun da ni mashiririciya ce baga Fatima ba ta aiketa maganar Fatiman na ji

"Ummi sai da na ce ki Bari zanje, ni da mai ma ban tsaya shafawa, gashinan ai ta yi sabar waya wa ye ya sani ma ko Kawu Mahmud ya siya mata saboda Aunty Asma'u, an bi an damemu suna Kama, har banasan zancen muka je Gwarzo ma, su Khairat su bi su damu mutane, ni Aunty Asma'un ma haushinta nake ji”

Ummi na ji ta fara magana cikin faɗa” Kin ga fatima ki kiyayeni da zancen Asma'u karta kirani waya ta nemi cimin mutunci ki tsaya kan Mahmud shi take wasa daku, kin san halin Asma'u batun waya ko ta millions zai siya mata ba ruwana, a cikin ku idan akace da munafukin da yake shirin faɗawa Asma'u ma ke ko recording za su iya yi, har Abban naku da kike biyewa, indai maganar Asma'u ne ware ki zai yi, ba zan iya da halin Asma'u ba, shi ya sa hanyar gidantama bana so na sani”

Abbah na ji ya fara” Kin ga Khadijah, idan kina magana da 'yar ki ki daina sani a ciki, kunfi kusa da Asma'u da ta zauna nan wanne shiri ba ku yi ba, sai yanzu, dan bata auri naki ba ki ka san da rashin mutuncinta”

Ummi na ji ta daura” To ni dama ai na sani, Asma'u ba tada mutunci, da na ga Kamar da gaske za su dai daita da Mahmud ne da farko, tom ta raina arziƙinshi lokacin ana zugata ana sai mai wasu trillions gefe, gashinan Mahmud shi ma yana dasu, har ya siyawa 'yarku waya da kuka kasa ubantama ba ku rufamasa ɗakuna ba, a cikin gidanku ya dawo ya zauna, sai nan gaba kunu na iko kan 'ya'yan shi, sun gama wahalsu"

AbdulMalik na kai doya baki na na ji ya fara magana” Haba Ummi ya kike mana haka yarinyarnan tanaji fa ba bataji ba, yanzu ma meya ruwanki da familyn su Abbah, kinata maganar za a samu maiyin recording na san dani kike ni Asma'un banza da wofi me za ta bani, waye baya zaginta a family, din, ni mai zwn aje layinta na yi mata ma”

Ni dai dariya ma suka koma ba ni yau anyi walƙiya an gansu a rana kafin anjima su sake haɗa kai, anjiman idan Hamid ya zo, Abid da Yaya Samir abincinsu suke ci suna kallansu, dansu da alama sunma ƙoshi da abincin shi ya sa suke hayaniyar su

Kwanan na kai bayan na gama ci Yaya Samir ya ca na sameshi waje

A tsaye na sameshi a inda ya saba tsayawa na tsaya kusa da shi kallona yake Kamar ba zai cire idanshi akaina ba duk da ɗinkin ba wai kamani ya yi ba sai duk na ji kunya dan ko mayafi ban saka ba, dan ba wai girman jiki ma gareni ba, gyaran murya na ji ya yi na dawo daga tunanina na kalleshi ni ma ni ya sake kallo

"Sumayyah!, hankali na ya kasa kwanciya da kwalliyar nan taki, kiya haƙuri amma duk da ba yawa ta yi ba, ina za kije na san haka nan kamar yanzu ma baki isa wanka ba ma”

Inda inda na fara Ina” Zan. . . . uhm. . . eh. . "

Tsawa Yaya Samir na ji ya dakamin sai da na tsorata ya fara” Ina wasa dake ba magana nake maki ba, ina za kije dama yawo kike ficewa ke nan ko, gidan waye kike zuwa, waye naki a nan bayan mu duka nawa ne kike wai, faɗa min gaskiya?"

Shiru na yi ina ƙoƙarin haɗa kalmomin da zan faɗa masa ya yarda dani dan tsoron shi ma na Fara ji

"Dama Yaya wani malamin mu zai zo nan Ni da Abid muka haɗu da shi wajen hanyar gidan Aunty Ramlah"

"Sai akace ki ce ya zo nan ko?"yayi maganar yana sake kallona

Na yi saurin girgiza Kai” A'a saƙo zai ba ni Halima ta bashi ya kawo min ya je Kano ne wancan satin"

Kai ya girgiza ya fara ƙoƙarin tafiya” ya miki kyau baki Fara sanar dani, baruwana ke da Abbah ai yana gidan"

Hankalina ya tashi Kamar na yi kuka jin an anbaci Abbah Hashim dama ya lafiyar giwa bare ta yi hauka, na Fara magana” Yaya Samir I'm sorry dan Allah ba zan sake mistake haka ba, kama Abbah bayani”

Juyowa ya yi ya kalle ni yana hararata” kin ga by mistakenly Kika sake cemin wani abu haɗuwar mu ba za ta miki kyau"

Na sake "Yaya dan Allah Kaya haƙuri”

Idanshi har sun fara ja ya ɗago ya sake juyowa” shout up your mouth, kin ji ko, wuce ki ba ni waje, sannan ya zo na ga kin wuce minti biyu ma, za kiga yadda zamuyi, wato 'yan iskan malamai kuke kulawa a makarantar har layinsu kike ajewa akanki ma ke nan, Halima kike min magana ko waye duk za su shigo hannuna”

Da wasu hawaye fuskata na koma ciki na buɗe kofata na shiga daƙina, gado na faɗa ina kuka wiwi, ya zan yi ne ni Sumayyah, Yaya Samir ya kasa tsayawa ya fahimceni maiyasa ne ni, me na yi meye laifina anan, wayata da take ƙara ko kallanta ban yi ba na ci gaba da kuka na, ƙofar na ji an buga da ƙarfi Yaya AbdulMalik na wai go na gani ranshi a ɓace ya fara

"Fito munafuka, za ki San kin shigo gonar Abbah ne yau, baki Fara kuka ba ma”

Idona na shiga toilet na wanke har fuskata, bayan ficewarshi da ya ja ƙofar da ƙarfi, wayar na duba missed call a ƙalla 6 duk na Hamid na gani dama a within lokacin na tsammaci zuwan nashi, amma na san zuwan zai ƙaramin ɓacin ran ne da Yaya Samir ya sani yanzu ga Abbah Kuma kafin na ƙaraso falon na ji muryar Ummi ta na

"Ni ka ga Hashim yarinyata Fatima ba neman mijin aure take ba kuma ba wanda zaisa ta fita waje saboda ba ita ake Kira ba, ɗiyar ƙaninka da ba ku sonshi shi da matarshi bare 'ya'yan shi to su masu arziƙin Katsina suke kira ba 'yata ba bana baƙin ciki bare jin haushi 'ya'yan naka ma da ɗai da ɗai za su gane halin naka na baƙin ciki da kyashi, kai a gidanka nufinka arziƙi zai ƙare ko mene ne, Asma'u ma data yaudarar min ƙanina aka haɗa baki da Kai data samu gidan da kuke mata hangen kaf cikin familyn mu har Mahmud murna muka mata bare kuma Sumayyah 'yar cikina. . . "

Da wannan na ƙarasa shigowa n durƙusa gaban Abbah ina "Abbah gani”

Wani mugun kallo Abbah ya bini da shi "kece ko Fatima wanene cikinku ya haɗu da Hamid Saraki, gidan Muhammad Saraki”

Ummi na ji ta yi saurin dakatar da shi haka "A'a ya za ka dauko wani zance dogo haka iya Hamid kace ai za ta gane ni banasan rashin gaskiya”

Ummi ta kalle ni "ke ce ko?"

Na ɗaga kai, ta nuna min hanya "ki fita yana jiranki a waje ki shigo da shi har ciki”

Naji ta ci gaba kafin na ƙarasa fita” Abin kunya, uba na yiwa 'ya hassada, danni ko a mafarki ban yi tunanin ko ɗan shugaban ƙasa zaizo wajen ɗiyar ƙaninka Abdullahi za ka yi haka ba, meye ubanta baiyi tsaya ya yi da guminshi, da 'yan kuɗinshi ya yi ma ba, amma ba kada tabbas a kan alaƙarta da yaro, ba ka san asalin uwarta ba, ba ka tunanin ko familyn Hauwa'u nema kazo kana abubuwa haka gaban yara. . . . "

Da wannan na ƙarasa ficewa ina goge hawayen idona, ummi ba tada laifi dama tun farko yadda taga Abbah Hashim na nunawa ya sa bata nuna kulawarta a kaina, dama ance naka ke ba da Kai amma na ji matsayin Ummi ya ƙaru da ganin martabarta, Yaya Samir na tuno ina ji kamar na koma na fara bashi haƙuri amma na san ba zai saurareni ba, ko dai hasashen su Halima ya tabbatar shi ma Yaya Samir sona yake yi ya zan yi da Hamid gabana ya faɗi, idan na san cancanta ne Yaya Samir ya cancanta na aureshi fiye da kowanne namiji amma ya zan yi da Abbah Hashim shi ne ba zai amince ba ko da Hamid na ce masa ga Fatima yadda na ga Abbah Hashim yake so, na san ba zai bari da yawunshi na auri Samir ba duka ɗinma nawa nake amma ina jina wata daban a yau din kamar ba ni ba kofar gate na buɗe na fita a tsaye na hangoshi da waya hannunshi ya sa ta a speaker ina jin ringing na san wayata yake ta Kira da damuwar da na hango a fuskarshi na ƙarasa inda yake

"Assalamualaikum"

Saurin ɗagowa ya yi

"Sumynah, da na yi tunanin ba za ki fito ba” ya yi maganar yana nuna min wayarshi "kin gani na miki missed called a ƙalla 15 ma, duk da Abbah ya cemin kina zuwa, amma na ji yana Fatima dai ko na ce ma sa, Sumayyah nake kira na kiraki ma missed Called 6 baki ɗagaba to ya shiga yana kokwanto wace ce Fatimah?"

Na murmushi kawai kafin na ce” kaya haƙuri kaina ya yi ciwo shi ya sa ban ɗaga ba, Fatimah sister na ce, ɗiyar Abbah Hashim ɗin ce yayan Abbahmu ne, ka ga sune a nan ɗin, dangin mamarta kusan kaf suna nan ɗin, kowa bashi zai yi wajenta a kazo, ni Kuma na manta ban yiwa Yaya Samir maganar ba, ya faɗawa Abbah"

Hamid ya kalle ni "Ayya sorry sannu ba daɗewa zan yi ba saiki kwanta kisha magani amma, baki ba ni labarin Fatima ba jiya”

Na ce "na manta Ummi ta ce ma ka shigo ciki”

Hamid ya girgiza kai” A'a zan koma zan dawo wani lokacin"

Shiru na yi ina tunanin ko Abbah Hashim ya masa wata maganar ne ban sani ba na dai daure na ce” Amma kuma danni fa ka zo"

Murmushi ya yi "kin ga Sumy ai Zan dawo ne da abin mamaki ma Zan dawo ba dai na zo din na ga sumynah ba, yawwa Abbah ya ce min idan ina sanki na fito kawai, bai dai gane ba ya ɗauka wajen Fatima na zo ne, yana mamaki ne nake tunani yadda Kika faɗamin kin ga Fatima ce anan, ke Kuma baƙuwa ce to da mamaki”

Gabana na ji ya yanke ya faɗi na yi jim kafin na ce” Amma dai kuma. . . dai. . . "nama kasa maganar

Yayi dariya ya Fara kwaikwayata” Amma dai kuma dai Kuma me oya faɗamin ya yi kusa ke nan kome, na yi laifima da na fara zuwa ƙofar gidanku ba tare da magabatana sun Fara zuwa nemarmin izini ba, tom kin san zamani ne gaba ɗaya nama kasa tunanin ya kamata sai yanzu da Abbah ya nuna min, insha Allah da kawuna ya dawo, za su zo, Sumy ina tsoron rasaki, ke fa?"

Ido na rufe ni kam ya ba ni kunya ma gashi ya tsareni da idanunshi

"Au ba za ki magana ba, mene na kunya a nan oya ɗago fuskarki, kimin magana ki ce ni ma Ina tsoron rasaka” yayi maganar yana sake kallona yana sake lumshe idan shi ina hango hakan duk da rufe fuskar da na yi na dai daure

"Tom ni ma haka”

Murmushi ya yi "yawwa ko kefa yaɗan yi ba laifi, Zan tafi?"

Na ɗan ɓata fuska na ce” haba mana AbdulHamid ka shigo ciki kaƙi, Ummi ba zataji daɗi ba”

"Oh Sumynah zan shigo fa, har cikin falo ma Amma ba yau ba, ko kawu bai zo ba, zan ma Hajiya magana, Abbahna da kanshi zaizo ko sati biyu ma bance miki za ayi ba ɗaya ma ya yi yawa a gurina insha Allah, ki mana addu'a kawai, Allah Ni a shirye nake fa, zan tafi fa, Zan biya gidan Auntyna maman Halima da na baki labarinta” ya yi maganar yana kara kallona

Na ce” tom shike nan, Allah ya kiyaye hanya agaida Halima da mamarta”

Murmushi da ya zamar masa jiki kusan zan iya cewa ya sake yi ya ce” Yawwa Sumy zan wuce, kin gama na manta ma ne, zan Kai Hajiya unguwa to bata san, kowa ya yi driving nata sai ni”

Sai lokacin na lura da motar da aka Parker ta gefen gate ɗin gidan Abbah Hashim da ga gefe a rubuce jikin motar na karanta sunan motar mercendes ce White color ban yi wani mamaki ba dan dama tuni zuciya ta ta rayamin hakan tun daga kallan farko da na yiwa Hamid ɗin su Halima da Batul ne banjin sun fahimta, keys ya ka ɗa shi ya dawo dani daga tunani na ya ce

"Yadai Sumy baki so na tafi ko, sorry Zan dawo fa, baga waya ba ban maga wayar ba, idan na dawo karki manta ki fito da ita na gani”

Na ɗaga Kai kawai a haka mukayi sallama ya ja motarshi ya tafi, shidai a gefenshi na san iya gaskiyarshi da yardarshi ya aza a kaina ni Kuma abubuwan da ke danƙare a tunanin gobena ba ma ta soyayya ba nake ina dauka ta Hamid kamar me sauƙi ce a kan tawa, ina tunanin kawai shawarar da Zan yanke ne kawai inason ci gaba da samun farin ciki a cikin yana yin rayuwata yadda ta fara, ana cewa kwaryama tabi kwarya na san da Hamid ya gama fahimtar wace ce ni ni ma a farko na gama fahimtar waye shi babu soyayyar da za ta haɗa mu, jina nake kamar ba Ni ba mema ke shirin faruwa dani ne ma, ƙoƙarin mai da kwallar idanuna nake kar ta ci gaba da zubowa a lokacin da banajin ta da ce ta zubo ƙarar buɗe kofar dake jikin gate din ta fitowa ya dawo dani tunanina na juya na ga mai buɗewar Yaya Samir na gani fuskarsa ba yabo ba fallasa ya ce

"Idan kin gama kizo ina San magana dake”

Yana shigewa ba ni da zaɓin da ya wuce na bi bayan shi, ina jin takaicin ma komaima na rayuwar duka ma nawa ne nake, Amma matsalar rayuwar da muke komai cikin godiyar Allah, yanzu Kuma ni Sumayyah wai soyayya ban ma san ƙarfin halin da ya sa na saurari Hamid ba, wai harna ƙirƙiro kalaman da suka da ce na furta, oh ni Sumayyah da wannan tunanin na ƙarasa shigewa gidan. 

**** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604
Na Cancanta

Post a Comment

0 Comments