Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Cancanta (Kashi na 17)

A zaune na sameshi kan ɗaya daga cikin kujerun robar dake farfajiyar gidan gabana ya yanke ya faɗi idanshi na kaina har na ƙaraso inda yake da rawar jiki na ja kujerar na zauna ina

"Yaya Samir gani”

Shiru ya yi kamar ba zai amsamin ba kafin ya ja dogon numfashi” Sumayyah kin kyautamin ke nan ko na ce kin kyautawa kanki, na daukoki dan kisamu kyakkyawar rayuwa ki zama Kamar Fatima, a raina na baki matsayin da yama zarce na fatimah, ni na san ciwan ki, nafi dacewa ki tunkara da kowacce damuwa ko matsalar ki amma malaminku da Kika tsinta rana tsaka shi ne zaizo har inda kike, a cikin rayuwar da nine nafi dacewa da ke, Sumayyah, ko da aurenki na ce zan yi ban yi laifi ba, duk tattalin da nake inaso na samu kusanci da ke ne”

Hawayen na ji suna zubarmin masu ɗumi na ɗago na kalleshi ba Zan jure kallan yaya Samir ba idanunshi sun Fara rinewa na yi saurin cewa” Yaya Samir Kaya haƙuri, baxan sake ba insha Allah"

"Dago ki kalle ni Sumayyah ki amsamin tambayata”

Dagowa na yi ba dan ina so ba na kalleshi da hawayen da ke ci gaba da fitowa daga idanuna

"Sumayyah ina San aurenki be, kece macen da na fara so da ƙauna tun ban san meye soyayya na, Sumayya ta Samir ce, na jawoki rayuwata ki saba dani da sauran Familynmu, duk da ni dake abu ɗaya ne amma babu sabo tsakaninmu, dan Allah karki kalli Abbah ni da shi ba ɗaya ba ne ki amince min, Dan Allah ki bawa wancen haƙuri idan soyayya ce tsakaninku ba dan Allah Sumayyah, idan ba kisan aurena ba zan miki dole ba”

Shiru na yi kawai tun da ya fara maganar Yaya Samir dai ba shida wani makusa a ina sanina shi duk wani shashanci ba shi cikinsa Yaya AbdulMalik ne dai komai da ruwansa, na san ba wai da Abbah ko Ummi zan zauna ba hayaniya kuma tunma daga kan AbdulHamid Abbah Hashim ya fara ta, bare Yaya Samir inasan Yaya Samir saboda halayyar shi, Amma ya zan yi da AbdulHamid ya ba ni dukkan yaƙini akaina, ya zai ji idan na kawo masa wani zance daban, gaba ɗaya lissafina ya dagule so nake na bar musu rayuwarsu gaba ɗaya hankalina ya koma gida idan na koma gaba ɗaya wayarma Banga anfaninta ba, ba nida wata mafita anan, maganarshi ta katse ni

"Ba ki cemin komai ba Sumayyah, baki Sona ko?, ban da ce a soni ba ko?, kifadamin?, Dan Allah Sumayyah wancen ya fini matsayi da cancanta ko?, ki faɗamin mana”

Kuka na fashe da shi amma ba mai sautin sosai ba, waini Yaya Samir yakema wannan magiya abin kunya ne a wajena Yaya Samir ya zo neman alfarma na kasa yi masa, ni Sumayyah cikin kukan na Fara

"Yaya Samir dan Allah ka maidani gidanmu gobe, dan Allah"

 

"Daina kukan Sumayyah ko yau kike so zan maidake kin gaji da zama Dani ko bakison ganina yanzu, wani ya rigani ko Sumayyah, shike nan, zan maidake gida, Ina jiranki amma dama ko da yaushe na rayu cikin jiranki saboda Jininmu ɗaya, kuma na dace dake Sumayyah a nawa tunanin nfi kowa sanin ciwanki, fatana ki samu rayuwa me kyau sumynsamir, dan Allah ki yarda dani Sumayyah"

Maganar nama gaji da jinta wani ɓacin rai yake tasomin, ciki na miƙe zan shiga, Yaya Samir ya biyo bayana

"Sumayyah ki tsaya ki share hawayen ki dan Allah, Kuma yanzu gaban Abbah din Zan nunaki matsayin matar da nakeson aure, ke ce na tsaya jira a duk shekaruna, ke ce matata insha Allah tun kafin a haifeki din zuwa yanzu"

Ko kallonshi din ban tsaya yi ba bare ci gaba da saurararshi saboda komai ya kwancema lissafina da tunanina, kayana nakeson haɗawa kawai katsina tamin zafi a yau da ya fi na sauran kwanakin da na yi cikinta kofar falon na buɗe na shiga a zaune na samesu Kamar dama jira na suke yi Abbah Hashim da nake koƙarin shigewa ciki ya dakamin tsawa

"Ke Sumayyah zo nan"

Hawayen da suke fitomin suka ci gaba da zubowa na dawo jikina na kyarma na dawo na tsugunna ƙasan carpet kaina na ƙasa Ina jiran tanadin Abbah Hashim akaina

Cikin alamun faɗa ya fara” karki ƙara kiramin kowanne namiji kofar gidanƙ bare cikin gidana, ki kumayi gaggawar bararmin gidana idan ba da ubanki na siyeshi matalautan banza Kun kasa zuciyar tsayawa ku ne ma ku samu, ubanki na tare da uwarku dangin tsiya kaf dangin Hauwa'u matalautane, gadon ta kukayi ƙashin tsiya garesu, na yi Kuma rantsuwa Abdullahi da sisina ban taimakonshi sai ya rabu da uwarku ya auro wata ko ya zauna babu matar, kuma Fatimah ta dace da auran wancen yaron bake ba, yadda ubanku yake sai dai ku samu irinshi ku aura bana muku fatan ci gaba, idan har ubanku bai haƙura da wannan matar ba uwarku"

Ummi ta miƙe tsaye Kamar Mai Shirin faɗa ta ɗaga murya

"Haba Hashim me ita wannan abar ta sani ita ce Abdullahi ko ita ce Hauwa'u, Abdullahi shugaban ƙasa ya zama na yi imani ba zai wa ɗiyarka Fatima haka ba, Kuma 'yata ba da yawuna ba wallahi Fatima tafi ƙarfin a cusata Dan ba koma baya bace, addu'a nake mata Allah ya sa ta gane waye ke Kai ta daina biyema, ni ma da naso biye ma wacce riba naci, 'yan uwana da suke rufamin asiri so kayi ni ma na zama kamarka mu ɓata, arziƙinka naka na yaushe ne da ba ka da shi har ubanta ya taimakeka, bare 'yan uwana amma sune abokan adawarka ba ka san na zauna dasu, ai sun rufamana asiri yanzu budinka, ya zo"

"Khadijah ki dakatamin kan wannan yarinyar ni Kika miƙe kina faɗawa magana san ranki” Abbah Hashim ya yi maganar yana ƙarasowa gaf dani dukan da yafaramin ba abun wasa ba ne ball yake dani yana "yau ko, Abdullahi ne gidannan sai ya barmasa gida, bare 'yarshi”

Maganar Yaya Samir na jiyo duk da dukan da akemin yana

"Abbah ka kyaleta haka za ta koma gidansu yau din nan ni na kawota Kuma zan maidata, tabarwa Fatima wanda kake magana kanshi, ni zan aureta, Abbah zan kawo maslaha dan Allah ka barta haka na ji duk maganar da kakeyi ka yafe mata ta yi kuskure kar ka illatata Ummi ta yi magana ba ita ba, Abbah ka saketa ni zn aureta”

Abbah ne ya sakeni Ina kuka yayo kan Yaya Samir a zabure

"Samir me kake cewa za ka aureta ita Sumayyah za ka aura masu ƙashin tsiyar Abdullahi kakeson zama ke nan, wannan yarinyar har tana da abin da za ka so wajenta har kayi girman tunkarata da maganar kanasan auren ɗiyar Abdullahi, ni Samir, wallahi muddin ka kafe kan maganar ka na zare komai da nake ma, Zan barka kaje gaka gatanan Abdullahi ya zama ubanka ba dai ni ba, karka sake ka nemi taimakon sisi na”

Ummi ta ja tsaki

"Wai Hashim yaushe akai dare garin ya waye, Ni Zan wuce masa gaba, indai tana sanshi ko za ka la'anceshi wallahi sai ya yi niyyar alkhairi gareshi Bata sharri ba Kuma na fika kusanci dashi, Ni ce na haifeshi nina raini cikinshi na haifeshi na yi duk dawainiya dashi, ƙaryar arziƙi kakeyi ɗan baƙin ciki da hassada 'yan uwanka ga sunan ba daɗinka suke ji ba bare Abdullahi ya sa rai da yake nesa da zama daku"

Abbah Hashim ya nuna Ummin yana” Khadijah ya ishe ni haka tun da ba ku ganin girmana kuje ku yi abunda za ku yi ku gani, Abdullahi ba zai ba ku 'yar shi ba tun yanzu na ga alamun jari yakeson maidata, tafi karuwa iya karuwanci”

Ummi dariya ma dagaji maganar ta bata” Hashim kanada lafiya kuwa ko dai hassadar takai haka ne, fatanka iya kan kanka zai ƙare, 'ya'yana ba zai jefesu ba tun da ba ka da tunani har kake ma ɗiyar ƙaninka fatan karuwanci da 'yarka mace budurwa gabanka, tuni nadawo rakiyarka, iyayenka ma ba zan shaidar daɗin ka suke ji ba

Abbah Hashim yana huci Kamar za ki ya fara koƙarin barin falon

"Na faɗa muku karna dawo na tadda wannan matsiyaciyar yarinya gidana, karkiga kina magana San ranki wallahi na dawo na tarar daku ranku zai mummunan ɓaci”, daganan ya sakai ya fice

Ummi ta bishi da kallo wajena sukayo ita da Yaya Samir suna lallashi na da ba ni baki a haka na shiga ɗaki na haɗa kayana Yaya Samir yana jaddamin na yi sauri na fito, wayata da take yashe gado na kalla, Hamid ya faɗomin raina ya zaiji idan ya samu labarin bana Katsina din da labarin kudirin Abba akanmu zai amince da Fatiman a madadina ko kuma zai haƙura ne gaba ɗaya wayata na ɗauka hannuna na rawa na danna lambarshi wajen message rasa ma me Zan tsaya rubutawa na yi na daure nasa

"Kaya haƙuri” ita ce kawai kalma Mai saukin da ko tunanina ba zan wahalar ba, wayar na kashe na yi ƙoƙarin turata ƙasan jakar karamar ma da ba Wanda yasanni da layin haka namata raina ina iPhone ɗin banza ma bata da sauran anfani a duniyata.

Ina kuka Abid mutumina yana yi, Ummi na bawa Abid baki tana za ta kawoshi da kanta wajena ana hutu, Yaya AbdulMalik da Fatima ko leƙowa basuyi ba Yaya Samir ya ja motar muka bar gidan a lokacin 12:30pm.

Rayuwar nake tunani yadda komai yake tafiya yake ci gaba da tafiya ba nida tabbacin zan riski farin ciki a rayuwata haka kawai nake ji duk da ina tuna ubangiji shi ne majiɓancin lamuran ko wanne bawa, amma na rasa dalilin da ya sa rayuwar batamin daɗi wajen wasu wannan ƙaramin matsala ne, Ni Kuma da take damu babbar matsala ne a nawa bangaren, na san idan na yi linƙaya duniyar wasu din suna da labarai mabanbanta da zanma ubangiji godiya duk da ko yaushe cikinta din.

 **** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604
Na Cancanta

Post a Comment

0 Comments