Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Cancanta (Kashi na 16)

Sai da ta gama ringing number din Hamid da na Kira harta katse ba’a ɗaga ba tunanina ɗaya biyu ya ba ni ko dai baya ɗaga baƙon number ko baya kusa da ita, wayar na ci gaba da dannawa, ina jin mamaki wai wannan wayar ce ta haura hamsin ta tafi ɗaruruwa, kuma an kashesu ba a ji wani ɗar ba, ni Kam da kuɗin aka ba ni ai ba ni ba, harsu Halima da Batul sai sun san Ina da kuɗin, amma ga abunda ya kamata suyi min da kuɗin su ɓige da siyamin waya ba zance ban gode ba dai hakan ma da sukamin yana cikin kulawa, amma babbar kulawar da nakeso ba ta ma shige da waya, ni iPhone ma saving number sai dai dake na iya karatu, duk inda zan shiga zan karanta shi, ni tunanina ma ni kam na koma Kano ya zan yi da wayarnan ai ajeta kawai zan yi, jigilar jonata caji ma ya ishe ni, ina ji Ruƙayyah Muhammad na labarin yadda yayanta ke jigilar jona tashi caji ko kaiwa a class namu, ta ce dole ya saidata ya canza wata, amma ya ce kuɗi na zauna masa zai sake siya tana da daɗin anfani to ni dai har zuwa yanzu banga daɗin anfaninta ba, da tunane tunanen nawa na ji karar wayata number din Hamid ce ɓaro ɓaro da kyar na lalubi yadda zan ɗaga kiran na ɗaga da sanyin muryar da tafi ta wa haɗa kalmomin da zan haɗa na bashi idan ya tanbayeni wace ce ni

"Assalamualaikum"na furta na yi shiru ina jiran abin da za a furta ɗaya ɓangaren dan na kasa tantance waye ma zai fara yin sallamar na yi hanzarin farata duk da Mai kiran naka zai fara yin ta

"Wa'alaikumussalam Sumynah"

Murmushi na yi jin ya gane ni ce Mai kiran, da muryarshi mai daɗin saurara ya daura

"Ai ban yi tsammanin za ki kirani ba, yanzu na gama waya da Halima jiran ta turomin number naki, sai na ga baƙon number an kirani ɗaya wayar, na mayi mamaki ba kowa ya sanni da layin ba, tom gwara ma Batul last week ta kirani da wancan layin da suke dashi, ba kati ban tsaya siya ba ta bank na kirata da wannan ɗin ashe har ta yi saving, Batul ke nan, ba ruwanta, kin ji daɗi ke Kam"

Na sake sakin murmushi jin kalmar ƙarshe ta Hamid ya sani saurin cewa "Daɗin mene Malam ni ko na ji haka”

Ya ɗan yi 'yar dariya mara sauti "Ah to kin ji daɗi mana Sumy, a'a ba dai Malam ba AbdulHamid Za ki faɗa min, aini ɗalibinki ne”

Na jinjina maganar Hamid ɗin kafin na ce” Uhmm uhmm ban yarda ba Allah ina kunyar faɗar sunanka, yawwa ni dai faɗamin mene na yi na jin daɗin"

Ya ce "kalle ni Sumynah"

Dariya ya ba ni zancen nashi taya zan kalleshi ban ganshi kusa da ni ba

"Au dariya ki kemin ko?, saboda ɗalibi ya ce malamarshi ta kalleshi, Allah gaske nake na daina amsa Malam, haba dai nifa dama can ɗalibi ne, tom Sumynah me zan faɗa miki kawai fa kina jin daɗi nace, na san kina kwance ne kina hutawa yanzu haka ko ba haka ba?"

Ni dai duk zancen na shi ya dabaibayeni na dai daure” tom shike nan Abdul"

Ya ɗan min muryar shagwaɓa

"Uhm uhmm gaskiya Sumynah Abdul to na waye ba ki ce Abdul ɗinki ba, ko dai ba ki yarda da soyayyata ba ne, na ga kinata shamin ƙamshi ne, Sumy da gaske nake ina ƙaunarki ba ma iya so ba dan Allah ki ba ni dama, Ya Abid na faɗa dai dai ko?"

Na ɗaga kai Kamar yana kallona duk ya kashemin jikina daga fara 'yar firar tamu na daure” tom Abdul I'm sorry kunyarka nake, ka sa zuciyarka kawai na ce ne, yana lafiya lau"

"Tom ya zance miki tun da ƙinƙi faɗamin, a gaidashi yaushe ne zanzo nifa ko yanzu ma a shirye nake da zuwa”

Na dai yi murmushi” zaiji a'a fa yau fa muka haɗu ka dai saka ranar dai ban da gobe amma”

"Saboda me Sumayyah kuma yaushe raban na ganki Sumayyah ko dai da matsala ne baki so na ko, na haƙura shike nan idan kince hakan zan yarda amma kuma ban sani ba ko wani ne ya rigani karki ji nauyina kin ji”

Murmushi na yi kawai saina ji jikina duk ya yi min sanyi Hamid ke nan ni kam banga wani abu da zance na gani tare da shi ba, kawai na ga Kamar yana tsoro ne, ganina ni ɗin ba wai 'yar wani ba ce ba” A'a fa bahaka ba ne, amma ko goben kazo shike nan"

Da farin cikinshi da na ga alamu a muryarshi” Yawwa Sumynah ko da yaushe ina ƙara sanki ina addu'ar Allah y ba ni ke matsayin mata, ban wai taɓa jin a guri kusa ma zan Fara soyayya ba sai akanki, ji nake Kamar almara ne, lallai kam yau Hajiya zan ƙarasa yini ina ma hirarki fa, kin san a nan ina wajen iyayen mamana da zama ne, ina tunanin ma ai na faɗa miki”

"Eh ka faɗa min ina tare da su Halima lokacin a ce ina gaidata ni ma”

Ya furta” za ta ji, wai sumy na tanbayeki?, gaske ne su Halima iya friends na ki ne”

"Eh mana, friend nawa ne tun daga junior class har yanzu"na yi maganar ina sake sauraronshi

"Ayya gaskiya, ban yi tunanin ba kuda wata alaƙar jini ba, ai har Kama ma kukemin, na kasa yarda Mukhtar teacher na ku na English ya cemin ba familynku ɗaya ba, shi ne ma ya fara faɗamin a gwarzo kuke namasan garin muna wucewa idan na zo Kano zan koma katsina wata Friday a nan na tsaya na yi sallahr Juma'ah ma, tom gaskiya kun wuce ƙawaye dai, sai dai triplets, i mean 'yan uku, tom amma Sumynah ce babba” ya ƙarasa maganar yana dariya

Nima dariyar ya ba ni na yi sama sama” eh haka ne zuwa mukayi, anytime ma za mu iya komawa garinmu, a'a fa ka rabani da Halima ai tuni mun bar mata girman tom ita fa ka san lallai ita abin matured takeson yi Batul harta haƙura da girman, tafa girmema Halima amma ta ce ta bata girman, bare Kuma ni”

Dariya ya yi yana "wayyo ni Hamid ki ce haka kuke fama da ita, ai daga yana yi dai na lura Haliman za ku yi fama, ni ma Muna da Halima yarinyace amma har mun fara fama ɗiyar ƙanwar mamana ce, yini take ƙiriniya idan suka zo, wato ita ce babba na gama alama tom gashi ta shiga zuciyata ta min maganar za ta turomin number naki kafin na furta, hala bata kwace miki position a school ko ni banma taɓa ganin results naku ba, "

"Uhmm Ni Kuma Batul ta turomin ita, ai Halima, Kuma na yi mamaki da ta saba da Kai haka, ah kana da sa'a kam, ko dan saboda Yaya hakim ne dai nake tunanin, duka sunayenku kusan is the same, tana shiriritarta din nan duk wuceta muke, amma ta fimu ƙoƙari fa, kawai ai mu ba muda aikin yi da muke karatu jinta ta ke a higher table wannan da kake kallonta”

Ya sa dariya "Eh haka ne, suna Abdul suma da yawa ke nan ma ƙila ko?, ni ma gidanmu haka ne za ki kwana Abdul ba za a gane wanne ba cikin mu ba, dan ma a nan nake zama, akwai AbdulHalim, Abdulshahid, Abdulra'ouf, gani AbdulHamid shi ya sa idan ba za ki kira in full ba sai dai ki ce ko Hamid, Shahid, Halim, Ra'ouf, yanzu ne ma muke da Mahmud, Amir, wato gifted ce ke nan"

Na ɗan taɓe baki” taɓ wanne gifted shiririta dai, ai Halima mashiririciya ce tun muna biye mata har muka daina, Ayya Suma gidansu Halima ya wanci haka ne sunayen su"

"Ayya Masha Allah, gaskiya kam ta san kan ta ne a karatu da alama, na ji ana mata Mrs Aliyu a class, ina ƙoƙarin shigowa” yayi zancen yana dariya

"Uhm uhmm, stubborn girl ke nan Halima batajin magana duk ƙiriniyarmu ka saba da mu duka zaka san ta wucemu, amma Halima ba dai kirki” na yi zancen ina daurawa da bashi labarin soyayyar Aliyu da Halima yana bina da abin da yaji na dariya ya yi abarsa, a haka ya katse kiran

Sai dare na samu kiran su Ummah gaisawa kawai mukayi Ahmad ya karbe wayar yana koromin jawabi da tambaya faɗi ba’a tanbayeka ba ke nan nasha surutu tun ina biyewa har ya zama daga uhm sai uhm uhmm, saida ya gama zancen Khadijah ta yi saurin karɓewa kafin Rumaisa ita ma surutun nata ta gama ina biye mata, har dai na gaji ita ma, ta bawa Rumaisa ba jimawa mukayi ba ita Kam akwai sanyin hali, ni da ita tafiyarmu tafi zuwa ɗaya, sai Sadiƙ sarkin rashin ji ya amsa da ganan Khalil, daga shi na katse wayar ina ya gaidamin Aisha yana gata na katse kiran Dan na san shiriritar Khalil, gashi na farajin barci

Lokaci ɗaya wata faɗuwar gaba ta zomin bayan katse wayar ba abun na sake Kira ba saboda a yana yi na ji su lafiya da akwai damuwa Ahmad zai faɗa min, duk da na san ummah za ta iya kwaɓarshi addu'a na yi kawai, da tunane tunanen duniya da addu'a Allah ya kawo abunda za a yi a Gwarzo na Alkhairi da za mu je daganan na bi Abbahmu mu koma gida, dan tunani da zullumi kaɗai sun ishe ni a nan ko da babu wata cusgunawa, ga tunanin zuwan Hamid ɗin a goben ya ma abun zai ka sance da ma sauran tunanikan da suke sake zuwarmin barci ya yi gaba dani ka sancewar dama na yi Shirin kwanciyar tawa, harda addu'a kafin ma ta kira su Ummah.

 **** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604
Na Cancanta

Post a Comment

0 Comments