Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Yana Bawa Kishiyata Ranar Girkina

TAMBAYA (42)

aslm malan barka da warhaka. da fatan maln yana cikin koshin lfy. mln dan allah ina da tamba ya akwai abun da ya kullemin kai. dan allah inason awar waremin. a kan mijin mune inada abokiyar zama

amman malm dan ace yau girkina ne sai yadau lokacina yakai mata kokuma ya je gidan ta da janaba ya yi wanka acan kuma ya ce dan ya sadu da ita baharamun ba ne saiyace mun ni ma in inason hakan zai kwanta dani ni akullun ina ce mishi ahaka ake haifar shege amman ayau na ce barina ji tabakin malam kohakan kuskure ne

AMSA

Waalaikumus, Warahmatullahi, Wabarakatuhum

Tabbas ba haramun ba ne ba idan ya sadu da ita tun da ai matarsa ce ta sunnah, saidai kuma idan kun yi alƙawari da shi cewar zaku dinga raba kwana ita 1 kema 1 to a nan ya saba alƙawarin kuma ya zamo munafuki domin kuwa saba alƙawari yana daya daga cikin suffofin munafukai kamar yanda Annabi SAW ya fada

(Sahih al-Bukhari 33, Sahih Muslim 59)

Batun a haka ake haifar shege kuma ai bai taso ba ma, domin kuwa shege shi ne wanda aka haifa ba ta alaƙar auratayya (auren sunnah) ba, kin ga kuwa ai ita kishiyar taki ai yar uwarki ce musulma kuma matarsa ce halak malak to me ya kawo batun shegantaka a nan ?

Idan har ranar girkinki ita ce ranar da zai kwana a gidanki to bai kamata ya dinga dan waken zagaye yana bullawa gidan abokiyar zaman ki ba harma yana bata aron lokacinki na kebantuwa, hakan yana nuna ba zai iya adalci a tsakaninku ba

Idan kuma har ba zai iya adalci din ba to bai kamata ma ya auri mace sama da 1 ba

Allah SWT ya ce:

( وَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تُقْسِطُوا فِي الْيَتَامَىٰ فَانكِحُوا مَا طَابَ لَكُم مِّنَ النِّسَاءِ مَثْنَىٰ وَثُلَاثَ وَرُبَاعَ ۖ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُوا فَوَاحِدَةً أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ ۚ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَلَّا تَعُولُوا )

النساء (3) An-Nisaa

Kuma idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba a cikin marãyu, to, (akwai yadda zã a yi) ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba

Shawara a nan ita ce: Ki bashi shawara a ilimance cewar abin da yake baya kyautawa a addinance, domin kuwa duk wanda baya adalci tsakanin iyalansa to a ranar lahira zai tashi ne tsagin jikinsa a shanye (paralyzed) kamar yanda hadisin ya tabbatar

(Sahih Muslim)

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments