Ticker

6/recent/ticker-posts

Rabon Da Ya Kusance Ni Tun Kafin Azumi, Mene Ne Matsayin Auren Mu

TAMBAYA (44)

Aslm. Malam inada miji amma munsamu sabani abin kamar shiga tsakani ya daina kulani ya daina cin abincina inyashigo dakina a falo kantabarma yake kwana rabon da ya kusanceni tun kafin azumi meye matayin aurenmu. Wlh ban san menayi mishiba malam baya kulani kwatakwata sai dai na jisu da abokiyar zamana. Ita ce kominshi ita ce mai fada aji

AMSA

Waalaikumus, Warahmatullahi, Wabarakatuhum

Aurenku yana nan daram, in sha Allah

Saidai yana tangal tangal kuma sauran kadan shaidan ya yi nasara akanku

Nasarar ita ce ya samu saa a kan mijinnaki ya sakeki. Babban burin shaidan ke nan, ya raba aure

Haba, baiwar Allah, magana kikefa ta tsawon watanni 6 cur bai kusanceki ba. Wannan wanne irin laifi ne ya shiga tsakaninki da shi haka ?

Dole akwai dalili kam

Na farko dai ki tuna can baya a lokacinda yake sakar miki fuska kuna raha sosai

Sannan kuma ki tuna mekikai masa wanda lokaci daya kawai ya juya miki baya

Zata iya yiwuwa laifi kikai masa

Sai ki sameshi a tsanake ki tambayeshi cikin siyasa

Ni kam baban wane, me na yi maka ne na ga kwana biyu ba ka sakar min fuska

Idan laifi na yi maka ka sanardani sai in gyara

Kada ki sake ki yi tunanin zuwa wajen malamin duba domin kuwa a kan wannan gabarne za kiji shaidan yana raya miki kije wajen dan duba ya dubo miki dalilin sauya miki fuska da yayi

Idan kika kuskura kika je kuwa to sallarki ta kwana 40 ba zaa amsa ba

Don haka kamar yanda na fada miki dincan a shawarce ki kwantarda hankalinki ki tambayeshi mene ne laifin da kikai masa wanda bakisani ba har ya sa ya daina kusantarki alhalin yana mijinki halak malak

Wallahu a'alam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments