TAMBAYA (41)❓
Assalamu Alaekum warahmatullahi wabarakatuhu. Patan malam yana lpy, Dan
Allah ina d tambaya
Dan Allah idan mutun ya yi tunani ko ya yi karatun littatafae ko kuma ko ya
kallali wani abun d yatayar masa da sha'awarsa, shin sae mutun ya yi wankan
janaba kafin ya yi ibada ko kuma kawae tsarki mutun xaeyi?
Sannan miyake wajabta wankan? Allah ya ba da daman amsa minmin
AMSA❗
Waalaikumus, Warahmatullahi, Wabarakatuhum
Alhamdulillah
Idan har silar karatun littafin ko kuma kallon sai maniyyi ya fita to ya
zama dole mutum ya yi wankan janaba
Amman idan ba abin da ya fita to ba za ki yi wankan ba
Domin kuwa wankan yana wajabtuwane ga kowanne baligi namiji ne ko mace
silar fitar maniyyi a mafarki ko a farke
Abubuwan da ke wajabta wankan janaba sun hada da fitar maniyyi silar
mafarki ko kuma sha'awa, zubar jinin haila ko kuma boyuwar kaciyar namiji a
gaban mace duk waɗannan
suna wajabta wankan janaba
Rashin yin wankan sabawa umarnin Annabi SAW ne domin kuwa Mala'ikun rahama
ba sa shiga gidan da mai janaba yake ciki har sai ya kasance cikin tsarki
Haka kuma kallon abin da kan tada sha'awa ko kuma karanta littattafan da za
su gayyato sha'awa suma duk haramun mutum yake aikatawa saboda fadin Allah SWT
( وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ )
المعارج (29) Al-Ma'aarij
Da waɗanda
suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa:
Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www. facebook. com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.