Ticker

6/recent/ticker-posts

Matsalar Rashin Jin Dadin Saduwa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀                     

Assalamu alaikum. mlm tambayata ita ce Yar'uwata ta kasance shekara 3 da aure tunda take mlm ba ta taɓa jin wani daɗi tsakaninta da mijinta ba shi ne sai sukaje Asibiti likita ya ce mata haka Allah ya halice ta to wai damman ana iya sa.?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum Salam.

Na'am wasu sukan samu irin wannan Matsalar tundaga halittarsu amma wannan rashin Lafiyace danhaka in suka nemi magani zasu samu in Allah ya yarda. Domin ya danganci abubuwan da takeji ajikinta.

Dayawa wasu Abubuwane kan haifar da irin waɗannan matsalolin, sun haɗa da Abubuwa kaman: Sihiri, Aure da wani Aljani (Jinnul Ashiƙ), Wasu kuma Basur, wasu kuma Infection, wasu kuma Ƙarancin Ruwan Farji dadai sauransu.

Ga ɗan taƙaitaccen bayani akan wasu dagaciki:

1. BASUR: idan cuwon basur ya shiga jikin mace kuma ya yi kaka-gida, zai iya ɗauke mata dukkan wata ni'ima irin ta 'ya mace, kuma za ta samu irin wannan rashin jin daɗin.

2. STD: Wato irin cututtukan da ake ɗauka ta hanyar Jima'i. idan mace ta taɓa fama Gonorrhea ko Syphilis, ko ciwon sanyi, da sauran makamantansu, kuma ta bar cutar ta daɗe ajikinta ba tare da magani ba, shima zai iya haifar mata da irin wannan matsalar bayan ta warke ɗin.

3. INFECTIONS: Sauran cututtukan da suke kama al'aurar mace koda bata da aure, suma idan suka daɗe ajikin mace ba tare da an magancesu ba, suna kawowa Mutuwar karshen jijiyoyin da ke cikin al'aurar mace. (nerve endings) waɗanda su keda alhakin ɗaukar sako daga cikin al'aurarta zuwa ga kwakwalwarta. Su waɗannan jijiyoyin sukan samu matsala ta dalilin yawan amfani da yatsa, ko kuma wani abu acikin al'aurar mace. Musamman ma budurwa. hakanan yawan amfani da sabulu mai zafi wajen wanke al'aurar shima yana haddasa wannan matsalar.

4. JINNUL ASHIƘ: Wato Aljanin Soyayya. idan ya shiga jikin mace, yakan zauna ne acikin al'aurarta, ya ɗauke mata ni'ima, ya hanata jin daɗin saduwa da mijinta. Amma shi Aljanin zai rika zuwa acikin mafarki yana saduwa da ita. kuma abin mamaki, idan a mafarkin ne sai ta rika jin daɗi.

5. ƘARANCIN RUWAN FARJI: Idan farjin mace babu Ni'ima sosai to wannan yakankai ga rashin jin daɗin saduwanta wani lokaci amemakon taji daɗi sema taji akasin haka wanda wani lokacima har namijin yakanji saduwar da itama babu daɗi, domin wannan ni'iman daga cikin dalilan da Allah yayishi shi ne dan ya gyara saduwar aure.

 MAGUNGUNA:

1. Ki samu ALMUMTAZ daga Islamic chemis yana magance Kurajen gaba, yana magance buɗewar gaba (kamar matan da sukayi haihuwa da yawa). Kuma yana Ƙara ma Ma'aurata jin daɗi yayin saduwa.

Ki rika yin matsi da ALMUMTAZ, sai bayan kamar awa guda sai ki wankeshi da ruwan dumi. sannan ki samu ingantancen Garin Hulba ki dafa ki juye acikin robar wanka sannan ki rika zama aciki. In Shã Allãh zaki ji chanji sosai. zaki samu waraka da izinin Allah. Kuma koda akwai Jinnul Ashiƙ ɗin ze ƙone da izinin Allah.

2. Idan kuma basur ɗin ne, ki nemi sassaken Ararrabi, Sassaken dinya, Sannan ki dafasu tare da tafarnuwa. ki tache ki rika sha. In shã Allahu zaki samu waraka da izinin Allah.

Ki samu Man Shammar, ko Man Jirjeer ki rika shan cokali guda acikin ruwan shayi da safe alokacin breakfast. da daddare kuma after dinner. Ki yawaita amfani da kunun aya, kankana, da sauransu.

3. Inkuma Sihirine dama munyi karatu akan warware sihiri in kikayishi in Shã Allahu ze warware.

4. Inkuma Rashin Ruwan Farjine, to Farko, za a iya samun Lemon-tsami kamar guda biyar, a matse su. Bayan kin juye ruwan a kofi, ki samu kanumfari kamar cikin cokali, ki daka, ki jika a ruwa, shi ma ki tsiyaye ruwan kanumfarin, sai ki haɗa da ruwan lemon tsami da ki ka matse, sai ki juye Madarar gwangwani na ruwa a ciki, ki kuma sa zuma mai kyau ta asali, sai ki riƙa sha a kai a kai. Da yardar Allah za ki samu karin ni’ima.

Abu na biyu kuma shi ne, ki samu man Hulba, man Yansun, Habbatus-sauda, man Zaitun, ( OLIVE OIL) man Zogale, man Ridi, man Tafarnuwa, Kanumfari cokali ɗaya, zuma kamar cikin gwangwanin madarar Peak na ruwa, sai ki daka Kanumfarin ya zama gari, sai ki haɗa su a roban Swan ki girgiza su a hankali har sai sun haɗe, sun narke. Sai ki adana a Fridge, ki rika sha, misali, cokali (3) uku a rana, ki daure har ya kare.

Allah yasa mudace.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments