𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Yaya ake yanke
farce asunnah, shin mutum zai fara da ɗan
yatsarsa na dama ne ko hagu?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله.
Yanke farce
sunnah ne daka cikin Sunnonin fidira kamar yanda hadisai ingantattu suka nunar,
Anaso farawa dayanke farcen dama saboda hadisin da yatabbata daka A'isha Allah
yakara mata yarda ta ce: Annabi sallallahu Alaihi wasallam yakasance damaitawa
tana burgeshi cikin dukkan Al'amuransa wajan ( sanya takalmansa datafiyarsa da
dukkan al'amuransa) Bukhari (163).
Nawawi acikin
al-majmu'u (1/339) ya ce: Malamai sun yi ijma'i akan yanke farce sunnah ne, akan maza da mata na hannuwa dana
kafafuwa, Mustahabbine mutum yafara
yanke na hannun dama sannan na hagu, sannan nakafar dama sannan ta hagu.
acikin sharhin
muslim (3/149) yasake cewa: Anso mutum yafara da hannun dama, yafara da karamin
ɗan yatsarsa sannan
mai bi masa har nakarshe.
Sannan sai ya
koma kafarsa ta dama yafara da karamin ɗan
yatsarsa, Sannan Sai kafarsa ta hagu ita kuma zaifara da babban ɗan yatsarsa yakare
dakaramin ɗan
yatsansa.
Hanabila
sukuma sun ambaci wani tsarin nadaban wajan ɗan
yatsan daza'a fara yankewa dawanda za'a kare da shi yayin yanke farce, sai dai
cewa bai tabbata daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ba.
Al'iraƙi rahimahullah acikin
Darhul tasreeb ( 2/77) ya ce: Babu wani hadisi daya tabbata daka Annabi
Sallallahu Alaihi wasallam wajan yanda za'a yanke farce daza'ai aiki da shi.
Ibnu hajar
rahimahullahu acikin fat-hul bari ( 10/345) ya ce: Babu Wani hadisi daya tabbata daka Annabi
sallallahu Alaihi wasallam wajan tsarin yanda za'a yanke farcen wani ɗan yatsan akan wani,
Sannan ya ce ibnu daƙeƙil Eiid ya yi inkarin
yanda ake yanke farce wanda imamu gazali ya ambata da waɗanda suke tare da shi, dukkansu basu da
asali, farar da mustahabbanci bashi da dalili, abune munnuna awajena asanina,
koda mai riyawa zai riya cewa farawa da yatsar dama saboda darajarta, sauran
kuma ba zai riya musu hakan ba.
Hakane farawa
da hannun dama da yatsar dama yanada asali, saboda damaitawa tana burge Annabi
Sallallahu Alaihi wasallam.
Saboda haka
dai maganar imamu nawawi rahimahullahu tana da asali wajan yanda za'a yanke
farce domin yagina fatawarsa akan hadisi ingantacce wanda damaitawa yana daka
cikin Sunnah.
Saboda haka
yankan farce za ka fara da hannun dama da karamin ɗan yatsa, sannan hagu da babban ɗan yatsa ka kare da
karamin ɗan
yatsarka, hakama kafafuwa.
WALLAHU
A'ALAMU.
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.