Ticker

6/recent/ticker-posts

Littafi

Madubin rayuwarka,

Littafin ayyukanka.


Kar ka ruɗu da duniyarka,

Kai asarar lahirarka.


A Fesbuk kai ta shuka,

Tsiya har kai wa kanka.


Daina zagin 'yan uwanka,

Ko sharri da masu ƙinka.


Bar biye wa masu sonka,

Kar su sa Shaiɗan ya ja ka.


Shagalta kai ta harka,

Ba ka duban gabanka.


Igiyar zarge wuyanka,

Harshe yatsun hannunka.


Masu zayyana furicinka,

Na alheri tsiyarka.


Gaɓɓan da suke jikinka,

Ba mai ƙarya wajenka.


Gujewa zuciyarka,

Kan sui shaida gare ka.


A ranar za su bar ka,

Da dalar zunubanka.


Masoya masu binka,

A Tiwita suna zuga ka.


Guda bai taimakonka,

Kai da shirgin zunubanka.


Ran ƙiyama dai halinka, 

Alƙali ne fa naka.


Tun da sauran lokacinka,

Lafuza da mu'amalarka.


In kai kiwon abin ka,

Ka sarrafa lamuranka.


In ka bi Ubangijinka,

Nasara ta zo gare ka.

Post a Comment

0 Comments