Ticker

6/recent/ticker-posts

Ma'anar Sunan Haniya Da Nasreen

TAMBAYA (48)

Assalamualaikum. Dan Allah memene ma'anar sunan (Haniya and nasreen). Ngd

AMSA

Waalaikumussalam warahmatullahi taala wabarakatuhum

Alhamdulillah

Nasreen suna ne na larabci wanda yana nufin fulawa (wild rose) mai kamshi musamman koriya kokuma ja hawur, anfi samunta a yankin kasar Pakistan

Shi kuma sunan Haniya asalinsa sunan larabci ne wanda yake nufin wajen da mutum zai samu farin ciki da annashuwa, wasu suka ce a cikin wannan duniyar tamu wadda batada tabbas, radawa jaririya sunan Haniya ko kuma Chanya a yaren Hebrew yana daya daga cikin kyauta ta musamman a gareta wanda a yaren Hebrew ke nufin yardar Allah

Sunan Haniya ya fito (ba kai tsaye ba) a cikin Ƙur'ani: Tur ayata 19 dakuma Al-Haƙƙa ayata 24

Akwai wadanda na san sunansu dayawa ya bisu, wani za kaji ana kiranshi da shaidan kuma za kaga yanata shaidanci ya fitini al'umma, wani kuma rasta za kaga yana shaye-shaye kala-kala wani kuma pastor ma naji yara suna kiransa kuma gaba daya baya maida hankali wajen aiwatarda ibada ga addininsa (shiriyarsa shi ne fatanmu)

Haka kuma akwai wani sanannen labarin wata mata da mijinta ya sakawa jaririnta suna Muhammad matar ta ce ita bata son sunan, ta ce ita sai dai ta rinka kiransa da sunan babanta marigayi, haka akai, amman Allah da ya tashi nuna ikonSa, silar hakan sai yazamana duk sanda za'ayi wani taro a danginsu sai aga ta tashi tana ta tiƙar rawa a gaban iyaye ba kunya alhalin da can kuma mai kunyace, sai Allah ya cire kunyar saboda illar canza sunan mai sunan

Abu Dawud ya ce: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya canza sunayen Al-'As, 'Azeez, Atalah, Shaitan, Alhakam, Ghurab, Hubab, da Shihab wanda ya maida shi Hisham. Ya canza sunan Harb (Yaki) zuwa Salam (Aminci). Ya maida Almudtaji' (Wanda yake kwantawa) zuwaga Munba'ith (Wanda yake tashi)

Ya maida sunan garin 'Afira (Kasar da bata karbar shuka) zuwaga Khadirah (Koriyar kasa ma'ana mai karbar shuka), ya canza sunan dutsen Shi'b Ad-dalala (Hanyar dutsen kuskure) zuwaga Shi'b Al-huda (Hanyar dutsen shiriya), ya canza sunan al'ummar Banu Az-zinya (Yayan zina) zuwaga Banu Ar-rishda (Yayan shiryayyu), haka kuma ya canza sunan al'ummar Banu Mughwiyah (Yayan matar da ta yi nisa wajen aikata sabo) zuwaga Banu Rishdah (Yayan shiryayyiyar mata)"

Sannan kuma yana daga cikin dabi'ar Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) cewar baya son wucewa ta wajen da aka radawa suna mara kyau kamar wani lokaci da yazo wucewa ta tsakanin wasu manyan dutsuna sai ya tambayi sunayensu sai aka ce masa Fadhih (Danasani) dakuma Mukhzin (Rashin kunya), sai ya dawo ya fasa bi ta hanyar duwatsun

(A duba littafin Zaadil Ma'ad wallafar Ibn al-Ƙayyim)

Yakamata duk musulmi idan zai rada sunan yar da aka haifa masa ko da, ya yi koyi da addini don ganin ya radawa abinda aka haifa masa sunan da yake tattare da alkhairi a tarihance musamman ma sunayen yayan Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) dakuma sunayen annabawa da manzanni dakuma sahabbai guda 10 wadanda aka yiwa bushara da gidan Aljannah tun anan duniyar

Hakama a bangaren yaya mata ayi koyi da wadanda suka bawa musulunci gudunmawa kamar mahaifiyar muminai, Nana Aisha RA da yayan Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) kamar Nana Fatima RA. Da kuma sunayen sahabbai 10 da akai musu bushara da gidan Aljannah irinsu Abubakar, Umar, Usman, Aliyu (Allah ya kara musu yarda baki daya), da sauransu

Ya Allah ka bamu zuri'a dayyiba wadda zamu sakawa suna mai ma'ana

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments