𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin ko akwai
dalilai na shariah da suke halatta mace ta juyar da mahaifarta ko kuma ta samu
tazarar haihuwa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
To ɗan'uwa
amfani da abin da zai kayyade iyali, ya kasu kashi biyu:
1. Ya zama zai
hana ɗaukar cikin
kwata-kwata, a nan bai halatta ba, saboda ya saɓawa
manufar shari'a na yawaita al’uma, kuma ‘ya’yan da take da su za su iya mutuwa
sai ta koma mai wabi.
2. ya zama an
tsayar da shi ne na dan wani lokaci, kamar mace ta zama tana yawan haihuwa kuma
cikin yana wahalar da ita, sai ta yi nufin ta tsara haihuwarta ta yadda za ta
haihu duk bayan shekara biyu ko makamancin haka, to wannan ya halatta in dai
miji ya bada izini kuma ba zai cutar da matar ba, dalili akan haka shi ne
sahabbai sun kasance suna AZALU a zamanin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam don
kar matansu su ɗauki
ciki, kuma ba’a hana su ba, kamar yadda Bukari ya rawaito daga hadisin Jabir
mai lamba ta: 4911.
Abin da ake
nufi da AZALU shi ne idan namiji yana saduwa da matarsa idan ya ji maniyyi zai
fito sai ya fitar da azza karinsa ya zubar da maniyyin a wajen farji.
Duba
Dima'uddabi'iyya na Ibnu Uthaimin shafi na 57.
Sannan kuma an
haramta: VASECTOMY wato kashewa 'ya'yan maniyyin namiji. Idan aka yi ma namiji
irin wannan aikin, to zai iya yin Jima'i amma har abada ba zai haihu ba.
TUBECTOMY
shima haramun ne. (Daurewa bakin mahaifar mace, ta yadda Ƙoyin halitta ba zai samu
damar shiga ba). Idan aka yiwa mace irin wannan aikin, to har abada ba za ta
sake haihuwa ba. Domin kuwa Ƙwan
halitta ba zai samu damar shiga ba, ballantana har maniyyi ya yi fertilizing ɗinsa.
Ba'ayi sai dai
idan matar ta kasance anyi mata operation sau da dama, kuma likitoci sun bada
tabbacin cewar ba za ta iya rayuwa ba idan aka sake yi mata wani operation ɗin.
Hakanan irin
allurar da ake yiwa mata domin kashewa Ƙoyin
halittar ɗan adam
(gaba ɗaya) daga
cikin mahaifarsu. Itama haramun ce.
Abinda ya
kamata kayi, in har matarka tana da larurar da addini ya amince ayi family
planning saboda ita, sai kaje ka tuntubi kwararren likita, musulmi wanda kuma
yake da fahimta irinta addini domin ku tattauna, ya baka shawarar da ta dace.
Amma kafin nan
ya kamata ka san cewar duk waɗannan
kwayoyin da alluran tsarin iyali ɗin,
suna da mummunan SIDE EFFECT ga ita matar taka. Musamman ma idan tsufa yazo.
Babu mamaki ta
samu mental problem (hauka) ko mummunar mantuwa. Ko shanyewar jiki, ko kuma
jijjigar gaɓoɓin jiki. Ko kuma sankarar
mahaifa, ko cancer acikin bladder ɗinta.
*** ***
HUKUNCIN FAMILY PLANNING
(TAZARAR HAIHUWA)
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Aslm malam barka da dare,
malam mene ne hukunci mace mai yin family planning? shin akwai laifi yinsa ko
ya halarta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumusalam
warahmatallahi wabarakatuh.
Hakika malamai sun yi saɓani
akan halaccin yin family planning sai dai an samu hadisai da suka nuna
amincewar Annab (Sallallahu Alaihi Wasallam) ga sahabbansa akan su yi AZALU
wato zubar da maniyyi yayin saduwa ba tare da ya shiga jikin mace ba. Ko shakka
babu wannan ma family planning ne, sai dai inda malamai sukayi saɓani
shi yin family planning ta hanyar shan magani, duk da wannan saɓanin
wasu suna ba da uzuri idan mahaifiyar na yawan ɗaukar
ciki musamman waɗanda suke ɗaukar
ciki sau biyu a shekara kuma wannan yakan haifar da rashin lafiyar yayanta.
Rashin ingantacciyar lafiyar mahaifiyar, idan yakasance sai an yi operation a
kowane haihuwa. wannan wasu suna ga yana zama uzuri macen ta yi family planning
domin samun koshin Lafiyar ta da yayanta.
Amma wadanda suke yin family
planning domin kauracewa haihuwa na har abada, tsoron talauci, kwaikwayon
yahudawa, tsoron karyewar tattalin arziki, to anan malamai sun ce baya halatta
ayi family planning akan waɗannan dalilan.
Yin Family planning ba shi
daga cikin manufar aure a musulunci, hakika bayan haramcin yinsa haka kuma yana
tattare da Matsalolin masu dinbin yawa.
Allah ya faɗa a
cikin Alƙur'ani Cewa, “Kada ku kashe ‘ya’yanku
don tsoron talauci, Mu muke azurta ku ku da ‘ya’yan naku.”
Yahudawa maƙiya addinin Allah ne suka kawo mana shi
domin su rage yawan mu. Kuma duk wanda ya ke bincike ya san ƙasashen da suke zuga mu da mu yi Family
Planing su ba sa yi.
Lalle yana daga cikin
ni’imar Allah ga Ɗan
Adam da Ya ba shi ni’imar
‘ya’ya, duk wanda ya yi aure bai
samu ɗa
ba, to baya cikin kwanciyar hankali.
Abin da zai ƙara nuna mana mahimmancin ‘ya‘ya shi ne
yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi wa Anas bin Malik (RA)
addu’ar Allah ya ba shi yawan ‘ya‘ya, Allah ya amsa addu’arsa ya ba shi ‘ya‘ya ɗari
da ashirin da biyar (125). Lalle wannan kaɗai
abin yiwa nazarine.
Idan muka koma gun Manufar
aure ita ce domin a hayayyafa yadda manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam)
zai yi alfahari da yawan mu ranar kiyama kamar yadda ya zo a hadisi Cewa, Wani
mutumi ya zo wajen manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Ya
RasulalLah na sami mata kyakkyawa ‘yar dangi amma ba ta haihuwa. Sai ya hana
shi auren ta.
Ya ƙara dawowa karo na biyu ya ƙara maimaita maganar auren ta, amma
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya hana shi. Ya ƙara zuwa a karo na uku sai Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce masa, “KU AURI WAƊANDA KUKE SON SU, SUKE SON KU (wadanda
suka iya soyayya) MASU HAIHUWA DOMIN IN YI ALFAHARI DA YAWANKU A RANAR TASHIN
ALƘIYAMA”.
Musulunci addini ne mai
tausayi da jinkai hakika Malaman musulunci sun yi ƙiyasi (yarda) akan tsarin iyali, amma da
sharadi;
1. Na Farko, Ya zamana
Mahaifiyar ba ta samun isasshen lokacin da za ta shayarda jaririnta.
2. Na Biyu, Ya Zamana
Mahaifiyar na shan wahala wajen haihuwa, anan an yarda ta tsaya ta huta.
Hakika ajiye haihuwa don
tsoron talauci Haramun ne, Domin Allah (swt) yana Cewa, "KADA KU KASHE
'YA'YANKU DON TSORON TALAUCI, MU MUKE AZURTA KU, KU DA 'YA'YAN NAKU".
Wasu sukan ajiye Haihuwa wai
don a samu isasshen lokacin tarbiyantar da yara, hakika shi ma wannan ya Saɓawa
koyarwar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). Domin Sayyidina Anas bin
Malik (RA) ya shekara ɗari da hamsin (150) a
duniya, saboda dadewa har sai da ya makance. Yana cikin makantar tasa ne ya
kira babbar ‘yarsa mai suna Umainatu ya tambaye ta yawan ‘ya’yansa. Sai ta ce
sai an ƙirga. Da aka ƙirga ne aka samu ɗari
da ashirin da biyar (125) kuma duk sun hardace Ƙur’ani.
Shin idan yawan 'ya'ya na
saka a kasa tarbiyantar da 'ya'ya ya Sayyidina Anas ya yi da 'ya 'ya har guda ɗari
da ashirin da biyar (125) kuma duk mahardata ƙur'ani?
Babu shakka wannan kalubalene ga iyayen mu masu wannan rubabbar dabara.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.