TAMBAYA (49)❓
Assalam
alaikum warahmatullah wabarakatuh. Barka da Jumu’ah Malam Ya aiki, ya Iyali da
hidima da jama’ah. Mal don Allah tambaya ce dani, Dan Uwanane, abubuwanshi basa
tapia kamar na kowwah karatu wurin sau 4 daya fara sai abu yaƙi dadi dole ya dawo gida,
kuma yana da ƙoƙari Alhamdulillah abun
yana damunmu sosai sai nake tambayanshi mene ne Matsalan ya ce sam shima ya
rasa dalili, amma yana ganin kamar idan ya yi addu’ah Allah baya kar6a, sai
hakan ya tayar min da hankali na tambayeshi 6angaren addininsa duk da abinda ya
bayyana garemu yana da riƙon
addini kuma bamuga Chanji ba, sai na kuma tambayanshi ƙila akwai laipin da yike daga shi sai Allah
yikeyinshi, ya tabbatarmun da Babu nace to ya yawaita Istighfari kafin na
tambayi Malamai akan abin, tunda nasan tabbas Allah baya ƙin kar6an addu’ar Bawa ko
dai bawan ya yi gaugawan ganin bata amsu ba, ko Allah ya chanja mishi da mafi
alkhairi ko kuma Allah ya ijiye mishi ladan. Mal Inason sanin don Allah mai ya kamata yayi. Nagode sosai. Allah ya ƙara lapia da imani
AMSA❗
Abinda ya
kamata ya yi anan shi ne ya yawaita Istighafari domin kuwa idan Allah
(Subhanahu wa ta'ala) yana fushi da shi to silar yawaita Istighfarin zai so shi
kuma ya cire masa wannan damuwar, kamar yanda ayata 222 cikin Suratul Baƙara ta tabbatar da hakan;
إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ الْمُتَطَهِّرِينَ )
البقرة (222) Al-Baƙara
Lalle ne Allah
Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakẽwa.
Sannan kuma
kada mu manta cewar dukkan abu mara kyau da ya samemu to kada mu jinginashi ga
Allah (Subhanahu wa ta'ala) sai dai mu tuhumi kanmu domin kuwa Allah (Subhanahu
wa ta'ala) ya ce;
( مَّا أَصَابَكَ مِنْ حَسَنَةٍ فَمِنَ اللَّهِ ۖ وَمَا أَصَابَكَ
مِن سَيِّئَةٍ فَمِن نَّفْسِكَ
النساء (79) An-Nisaa
Abin da ya
sãme ka daga alhẽri, to, daga Allah yake, kuma abin da ya sãme ka daga sharri,
to, daga kanka yake
Sannan kuma a
nusar da shi cewar mai yiwuwa matsalar da yake samu a karatunnasa shi ne
alkhairi a gareshi domin kuwa wani abun muna son shi amman sharri ne a garemu
haka kuma za kaga mun tsani abu amman kuma wannan abun shi ne alkhairi a garemu
kamar yanda Allah (Subhanahu wa ta'ala) ya fada;
( كُتِبَ عَلَيْكُمُ الْقِتَالُ وَهُوَ كُرْهٌ لَّكُمْ ۖ وَعَسَىٰ أَن
تَكْرَهُوا شَيْئًا وَهُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ ۖ وَعَسَىٰ أَن
تُحِبُّوا شَيْئًا وَهُوَ شَرٌّ لَّكُمْ ۗ وَاللَّهُ يَعْلَمُ
وَأَنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ )
البقرة (216) Al-Baƙara
An wajabta yãƙi a
kanku, alhãli kuwa shi
abin ƙi
ne a gare ku, akwai fãtar cẽwa ku ƙi wani abu, alhãli shi ne mafi alhẽri a gare ku, kumaakwai fãtar cẽwa
kuna son wani abu alhãli kuwa shi ne mafi sharri a gare ku. Kuma Allah ne Yake sani,
kuma kũ ba ku sani ba
Shawarar da
zan bashi a takaice shi ne abunda na fada a farko wato ya gyara alaƙarsa da Allah (Subhanahu
wa ta'ala), domin kuwa batunma babu wani laifin da yakewa Allah a fili ko a
boye ma bai taso ba saboda ai daman shi ba zai iya fada miki laifin da yake a
boye ba tunda ya tabbata a cikin sahihin hadisi wanda Annabi (Sallallahu alaihi
wasallam) ya ce kowanne dan Adam yana laifi sai dai wanda ya fi a wajen Allah shi
ne mai yawan tuba, a sanarda shi cewar ya yawaita Istighfari, in sha Allahu
silar hakan sai kiga Allah (Subhanahu wa ta'ala) ya kawar masa da damuwar ta sa
Muna roƙon Allah (Subhanahu wa
ta'ala) ya kawar mana da damuwarmu baki daya
Wallahu ta'ala
a'alam
Amsawa:
Usman Danliti
Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.