𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mutum ne yazo
masallaci ana sallar isha'i shi kuma baiyi magariba ba, liman ya yi raka'a uku
sai ya yi tahiya ya yi sallama, yakabbara ya miƙe
yasauran isha'i ɗin
meye matsayin sallarsa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله وحده لا شريك له.
Sallarka tayi,
daman ko dai kayi tahiya kajira liman kuyi sallama tare ko kuma ka sallame
araka'a ta uku, sannan sai kai sallar isha'i ɗinka.
Wannan ita ce
mazhabar imamu shafi'i rahimahulla, kuma ita ce ɗaya
daka cikin maganganun Imamu Ahmad, Mardawi Acikin Inshaaf ( 4/413) ya ce: Wasu
daka cikin daliban imamu Ahmad Sun zabeta, daka cikinsu Akwai shaikul islam
ibnu taimiyyah da kakansa Majid bin taimiyyah.
Imamun Nawawi
rahimahulla acikin Majmu'u fatawa (4/143) ya ce: Da mutum Zai niyyaci Sallar
asuba abayan wanda yake azahar mamu ya cika sallarsa ta Asuba, idan yaga dama
zai jira liman azaman tahiyarsa suyi sallama tare wannan shi ne ya fi, idan
yaga dama zai kyale liman ya yi sallamarsa, Anan Sallarsa bata ɓaci saboda yariga liman
Sallama ba babu Saɓani,
saboda Uzurin mutaba'a, haka cikin Sauran salloli waɗanda sukai kama da haka. Kamar yanda malaman
lajnatul da'imah suka bayyana ( 7/407).
Saɓanin niyyar mamu data
liman bata cutar da shi, a ingantacciyar magana cikin magan-ganun Malamai.
Dan haka wanda
ya yi haka tareda liman ya yi dai-dai Sallarsa ta yi babu wani abu akansa.
WALLAHU A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.