Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Shan Maganin Kara Girman Nono Ko Ɗuwawu

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin ya halatta mace ta sha magani don Nonuwanta ko kuma Ɗuwawunta suƙara girma ko ta kara kiba idan ta kasance ramammene?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Dangane da hukuncin shan magani domin neman ƙara ƙiba ajiki ko kuma dan saboda wani sashe na jikin Mutum yaƙara girma kamar misali Mace tasha magani danufin Nonuwanta kokuma Ɗuwawunta suƙara  girma, bayanin da Malamai sukayi akan haka shine, akwai wanda yahalatta agareshi yasha maganin ƙara ƙiba, akwai kuma wanda haramunne agareshi yasha wannan magani, wato ya dangantane da niyya ko sababin da yasa za'ayi amfani da wannan magani.

Idan yaka sance Mutum yana da wani aibu ko naƙasa ajikinsa wanda yawuce irin wanda aka saba ganin Mutane da shi abisa al'ada, kamar misalin Mutumin da yayi asari (Accident) wani sashe na jikinsa ya lalace ko wanda haƙoransa suka fito waje dayawa zaƙo-zaƙo, ko yaka sance Mutum arame yake sosai irin ramewar da tawuce wadda aka saba gani a al'ada, kuma koda yanacin abinci maigina jiki haka yake baya ƙaruwa  to ayanayi irin wannan Malamai sukace idan masana kiwon lafiya (Likitoci) suka bashi shawarar cewa yasha maganin ƙara ƙiba to ya halatta yasha, kokuma ayiwa Mutum aiki dan akawar da wannan aibu ko naƙasar dake tare dashi, domin anyimasa hakane danufin akawar da wannan naƙasa dake tare dashine kawai danhaka babu laifi.

Amma idan yaka sance babu wata naƙasa ajikin Mutum irin naƙasar da tawuce wadda aka saba gani abisa al'ada, Saidai kawai Mutum zaisha maganin ƙara ƙibane danufin yaƙara masa kyau, kokuma Mace tasha magani danufin Ɗuwawunta suƙara girma ko danufin Nonuwanta suƙara girma idan yaka sance ƙananane, kokuma arage musu  girma idan sun kasance Nonuwanta manyane sosai, domin taƙara kyau dan tariƙa burge Mutane:, kokuma saboda kasancewar Mutum bashi da jiki sosai acikin abokansa sai yakeso yasha magani danufin jikinsa yakoma irin nasu, da dukkan wani wanda zeyi amfani dawani magani danufin yaƙara kyau bawai wata larura bace mai tsanani tasa yabuƙatu da dole sai yayi hakanba, to dukkan waɗannan abubuwa da makamantansu haramunne aikatasu, domin yashiga ƙarƙashin hukuncin masu jirkita halittar Aʟʟαн() domin dama Shaiɗan yafaɗa cewa sai ya umarci Mutane suna jirkita halittar Aʟʟαн() kamar yadda Aʟʟαн() Yafaɗa acikin wannan aya:

وَلَآمُرَنَّهُمْ فَلَيُغَيِّرُنَّ خَلْقَ اللَّهِ ۚ

Sai na umarcesu da suriƙa jirkita halittar Aʟʟαн() (sūratun Nisá'i : 119)

Danhaka abune mai matukar haɗari haka kawai Mutum yace zaisha maganin kara kiba danufin yakara kyau, yakamata asani cewa, duk yadda Mutum yakaiga rena kansa to ahakan shi abin sha'awane awajen wasu Mutanen, hakanan kuma duk yadda Mutum yakaiga jirkita halittarsa danufin yakara kyau, to ko rabin-rabin kyaun wani bazai taɓa kaiwa ba, danhaka garama Mutum ya hakura da yadda Mahaliccinsa ya halicceshi sai yazauna lafi lafiya.

Don neman karin bayani sai aduba wannan littafi kamar haka:

" فتاوى إسلامية" (4/412)

WALLAHU A'ALAM

AMSAWA:

Mυѕтαρнα Uѕмαи 08032531505

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments