𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mijina ya
kasance ba ya damuwa da ni, ko a wajan mu'amalar aure ba ya gamsuwa da ni, ga
shi mai taurin kai da rashin sakin hannu dasauransu. Muna haka sai na samu
magani da zan sha don karkato da shi zuwa gareni. Kuma maganin na gari ne da ake
sha, a wajan shan kuma za a ambaci sunan mijin. menene hukuncin wannan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Maganin da
mace za ta sha don kyautata alaƙarta da mijinta ya kasu gida biyu:
1. Maganin da
za ta sha don ƙara mata ni'ima da za ta sa mijinta ya ji daɗin muamalar aure da ita.
wannan babu komai idan ya kasance an haɗa
shi ne da sinadarai halatattu kuma ba zai cutar da lafiyarta ba.
2. Magungunan
da ake yi masu alaka da sihirce-sihirce waɗanda
za su juyo da hankalin miji zuwa ga matarsa ba don wani sababi na zahiri da ke ɗaukar hankalin maza ba,
kawai sai don tasirin wannan magani gareshi. Irin wannan yana cikin ababen da
ake kira (Attiwalah) = Mallakau ko bita-zai-zai, kuma hadisi ya tabbata daga
Manzon Allah ﷺ Yace
shirka ne.
A zahiri
maganin da mai tambayar ta ambata ya fi kama da kashi na biyu (mallakau -
Attiwalah) don kuwa maganin da za a ce sai kin ambaci sunan miji wajan shansa,
akwai alamar ba wata ni'ima zai kara miki da za ta sanya mijinki ya so ki ba
ne, kawai dai za a sihirce shi ne ya so ki ba so na ɗabia ba. Duba da haka anfani da irin wannan
maganin bai halatta ba.
Abin da ya
kamata mai irin wannan matsalar ta yi shine ta duba ta ga sababin da ya sa
mijinta ba ya sha'awarta. Idan ya zama sababin wata gazawa ce daga gareta ta
wajan rashin gyaran jiki ko rashin kyakykyawar mu'amala to sai ta yi ƙoƙari
ta gyara kurakuranta.
Idan kuma ya kasance matsalar daga mijin ne
sai ta lura sosai: Ko dai ya zama wasu abubuwa ne suke ɗauke masa hankali sai ta bi hanyoyin da suka
dace a shariance da hikima wajan nusar da shi kula da haƙƙin iyalansa. ko kuma
ya zama sihiri aka yi masa: to sai ta bi hanyoyin da suka dace da shari'ah
wajan warware sihirin, ba ta hanyar shan irin wannan magani da shi ma yake ɗaukar hukuncin
sihiri ba, domin ba a warware sihiri da
sihiri.
Daga Cikin
Hanyoyin Da Mace Za Ta Bi Don Kyautata Alaka Da Mijinta Sune Kamar Haka:
1. Gyara
jikinta a ko da yaushe.
2. Kyautata
kalamanta da sanin abin da za ta faɗa
a gabansa.
3. Lura da
abin da ya fi so na abinci ko abin sha tare da tanadar masa shi gwargwadon iko.
4. Nuna ƙauna
ga iyaye da yan'uwansa.
5.
Tarairayarsa da nuna damuwa da shi fiye da komai.
6. Nisantar
abin da ba ya so wanda bai saɓawa
sharia ba.
dasauransu...
WALLAHU A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.