Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Namiji Ya Yanke Wa Mace Farce

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mene ne hukuncin matan da suke miƙa hannuwansu da ƙafafunsu ga maza domin su yanke musu farce?

𝐀𝐌𝐒𝐀

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Hakan ya halatta ne kawai idan namijin muharraminta ne, kamar mijinta ko mahaifinta ko ɗanta ko ɗan’uwanta da suka haɗa uwa da uba ɗaya ko uwa kaɗai ko kuma uba kaɗai. Sai dai in akwai tsoron aukuwar wata fitina a tsakaninsu, ko kuma idan ana tsoron hakan zai kai ga aukuwar alfasha a tsakanin shi da wata wadda ba ita ba, to a nan ba za a yarda da ya kale ta ko ya taɓe ta ko ya shafi jikinta ba.

Kuma idan shi ba muharraminta ba ne, to a nan ma bai halatta ba, kuma haram ne a fili ƙarara macen da ta kai a yi sha’awarta - ko da ba matar aure ba – ta yarda wani namiji ya taɓi jikinta, ko da me ko don me! Sai dai in da wata larura ce ƙaƙƙarfa, kamar likita a asibiti. Shi ma haka ɗin sai ya zama a daidai wurin da larurar ta ke ne kawai, kuma a kan idon wani muharraminta, ba wai a keɓance su kaɗai a bayan labule ko wani wuri ba! Don haka, bai halatta likita ya sa mace ta tuɓe ƙirjinta ba don yana son duba mikin da ya ke a wuyanta, misali. Haka kuma bai halatta ya taɓa, ko ya shafi wurin da larurar aikinsa ba ta tilasta masa shafawa a jikin nata ba.

Daga waɗannan bayanan na sama ya fito fili cewa: Yanke ƙumba, ko gyaran gashi, ko goge kaushi ko faso, ko kuma awon ɗinki a wurin tela, da sauran hanyoyin yi wa ango ko amarya ado da kwalliya, duk ba larura ba ce da za ta halatta wa wani namiji ya kalla ko ya taɓa, balle kuma ya shafi jikin wata macen da ba muharramarsa ba. Kamar yadda ita ma macen, ba ya halatta ta shafi jikin wani namijin da ba muharraminta ba, in dai ba da larura ba.

Waɗannan dokoki da hukunce-hukunce duk sun shiga ƙarƙashin dokar Ubangiji Taaala ne mai cewa:

 وَلَا تَقۡرَبُوا۟ ٱلزِّنَىٰۤۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَـٰحِشَةࣰ وَسَاۤءَ سَبِیلࣰا

Kuma kar ku kusanci zina. Haƙiƙa! Ita alfasha ce, kuma mummunar hanya ce. (Surah Al-Israa: 32)

Ka ga a nan kusantar zinar ce ma Allaah ya hana, ba ma wai ita kanta zinar ba. Ma’ana: Duk wani abin da zai iya kusantarwa ko ya sawwaƙe hanyar da ke kai wa ga zinar shi ma Allaah ya haramta shi. To, ina kuma ga kasantuwar ga shi an samu nassi ƙarara da ke nuna cewa wasu gaɓoɓi da suka haɗa da hannuwa ma suna yin zinar?! Kamar maganar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da ya ce:

الْعَيْنَانِ تَزْنِيَانِ ، وَ الْيَدَانِ تَزْنِيَانِ ، وَ الرِّجْلَانِ تَزْنِيَانِ ، وَ الْفَرْجُ يَزْنِي

Idanu suna yin zina, kuma hannuwa suna yin zina, kuma ƙafafu zuna yin zina, sannan kuma farji ma yan ayin zina. (Sahih Al-Jaami: 4150).

Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daga Abu Hurayrah (Allah ya yarda da shi) Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: ”Allah yana rubutawa ɗan Adam kasonsa na zina, zai riski wannan kason babu makawa, zinar ido ita ce kallo, zinar kunne saurara, zinar harshe zance, zinar kafa tafiya, zuciya ta yi buri ta yi sha’awa, farji shi zai yarda ko ya karyata”

Allaah ya ƙara tsare mana imaninmu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒��𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments