𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum Malam shin ya halatta barin farce?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salam warahmatullahi Wabarkatuh
Yanke farce
yana cikin sunnoni na dabi'a da'aka dabi'antar da mutum akansu saboda faɗin
Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallam ( Abubuwa biyar suna daga dabi'ar da'aka halicci
mutum dasu, kaciya, da aske gashin gaba, da rage gashin baki ga ( maza) da
yanke farata, da tsige gashin hammata) Bukhari da Muslim.
Ya Tabbata
awasu hadisai sunnonin fidra guda goma ne daga ciki akwai yanke farce, yazo
ahadisin Anas dan malik Allah yakara yarda da shi ya ce: Annabi Sallallahu
Alaihi Wasallam ya iyakance mana lokacin yanke gashin baki da yanke farce da
aske gashin gaba da tsige gashin hammata kada mu barshi yahaura kwana arba'in
bamu kawar dasu ba). Ahmd, Bukhari, Nisa'i
Wanda bai
yanke farcensa ba ya saɓawa
sunnah, hikimar hakan shi ne tsafta da kuma fitar da abunda ke karkashinsu na
dauda da datti, da dauke kamanceceniya da wanda basa hakan cikin kafirai, da
kuma kama da dabbobi, Fatawa lajnatul da'imah ( 5/173).
Mafiya yawan
mata ayau sun faɗa
cikin kamanceceniya da dabobi da kafirai wajan tara farce, sannan sai su
rinashi da jan farce baki ko jah, wannan yakai makura wajan muni, da abun kyama
acikin zukata, ga duk wani mai hankali mai dabi'a kubutacciya.
Haka yana daka
cikin mummunar dabi'a wajan wasu mutane saisu bar wani sashi nafarcen ya yi tsawo
bakyan gani, dukkan waɗannan
sun saɓawa sunnah da
kuma fidira ta ɗan
adam, saboda haka bashi halatta tara farce gabaɗayansa
ko barin wani daka cikin faratan domin kamace dakafirai kama dakafirai kuma haramun
ne acikin dukkan komai na al'adunsu.
Muna rokon Allah kubuta daka waɗannan munanan halaye,
Allah yashiryar damu hanyar madai-daiciya.
WALLAHU A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.