𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
Alaikum, Malam yakake ya gida ya ijtihaadi? Allah ya albarkaci rayuwarka Ameen.
Malam ni madunki ne wato tela inason insan mene ne hukuncin amsar kuɗin jinga ko wani kaso
daga cikin jinga wato (advance) tun kafin in kammala ɗinkin da aka kawo mini?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus
salam wa rahmatullah.
Bisa Ƙa'idah ba za ka karɓi kuɗin jinga gaba ɗayansa ko wani sashe daga
cikinsa ba, har sai ka kammala aikin da aka baka, kuma bisa siffar yadda kuka Ƙulla yarjejeniyar aikin
akansa.
Idan ma baka da kuɗin sayen zare ne, to sai dai ka karɓi aron kuɗin da zai isheka. Shi
kuma wanda ya baka aikin yana da damar karɓar
aikin bisa lokacin da kuka alkawarta da shi idan har aikin ya yi daidai da
yadda kukayi yarjejeniya. Amma idan aikin bai yi daidai da siffar da ya ce ayi
masa ba, yana da damar ya umurceka ka gyara masa.
To kaga duk
wannan ba zai yiwu ba, idan har ka riga ka karɓe
kuɗinka tun farko.
Wajibi ne masu sana'ar hannu su rika kula da ka'idodin addini acikin sana'arsu
tare da cika alkawuran da suka ɗaukar
wa jama'a.
WALLAHU
A'ALAM.
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.