𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Wanda ya samu
raka'a biyu ko uku da liman, sai ƙabli
ko ba'adi ta kama liman, idan yabi liman sukayi ƙabli
shikenan, ko bayan ya idar zai sake yi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Idan Mamu ya
samu dukkan Sallah tare da liman, sai liman ya yi mantuwa, wajibine mamu yabi
liman wajan sujjadar (rafkanwa) Ƙabli
ce ko ba'adi.
Idan Kuma Mamu
an tsere masa raka'a ɗaya
ko biyu ko uku, sai Liman ya yi Mantuwa awani ɓangare
na Abunda ka riska acikin Sallah, to:- -Idan Liman Sujjada Ƙabli ya yi za ka yi
sujjada tare da liman, sannan ka tashi ka cikaso sallar ka, sannan bayan ka
idar da Sallarka sai ka sake yin wata sujjadar, domin wacce kayi tare da liman,
kayi tane ba'a muhallinta ba, domin ba'ayin sujjadar mantuwa lokacinda ake
cikin yin sallah, sai dai a ƙarshen
sallah akeyinta, sujjadar da kayi da liman bin limanne kayi kawai.
Idan kuma
sujjada Ba'adi ce takama liman, kai da ka riski wani abu a sallah ba za ka bi
liman ayi sujjadar da kai ba, za ka tashi ka cikaso sallarka kayi sallama,
sannan sai kayi sujjadar kai sallama.
Idan an tsere
maka wani abu a sallah, sai liman ya yi Mantuwa a raka'ar da baka sameta ba,
idan ya yi sujjada Ƙabli
za ka bishi, sannan sai ka cikaso sallar ka, ba za ka sake yin sujjadar a ƙarshen sallar ka ba,
domin baka riski raka'ar ba hukuncin mantuwar bai Shafe kaba.
Idan Kuma
liman sujjada Ba'adi ya yi ba za ka bishi ba, kuma ba za ka yi sujjadar aƙarshen sallar kaba, domin
liman ya yi mantuwar ne kafin ka samu raka'ar.
Waɗannan halayen gaba ɗaya suna gudana idan
mantuwar daka bangaren liman ne. Amma Idan Mamune ya yi mantuwa, kamar ace ka
samu dukkan sallah, amma Sai kayi mantuwa, kamar kamanta tasbihin da'akeyi
acikin ruku'u ko sujjada, babu sujjadar Mantuwa akanka, liman ɗinka ya ɗauke maka. Amma Da za ka
yi Mantuwar da take ɓata
wata raka'a cikin raka'o'i, kamar kamanta karatun fatiha, anan idan liman ya yi
Sallama za ka tashi kazo da raka'ar data lalace saboda mantuwar da kayi, sannan
Sai kai tahiya kayi Sujjada Ba'ad. Dan Samun cikakkun Bayanai akan Sujjadar
Mantuwa acikin Sallah, Duba Wani littafi na Shaik Usaimeen Mai Suna Risala Fy
Ahkami sujudus sahawi.
WALLAHU A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀��👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.