Ticker

6/recent/ticker-posts

'Yar Damisa (Kashi na 2)

Alhaji Damisa:

Ba za ta iya shiga jami'a da shi ba ne?

Hajia Jummala:

Ba dai a yadda yake ba. Amma idan na samu Kawun ta dake Jami'ar jihar nan zai iya sama mata

Alhaji Damisa:

A'al ba dai y'a ta ba. Ta bayan fage?! Inaa. Ina take Lau... (Ya kama kiranta ke nan aka kwankwasa kofar gidan tare da sallama. Suka juya baki daya suka dubi kofar)

Hajia Jummala:

A'ah, waye wannan da sanyi safiyar nan?

Alhaji Damisa:

Ban sani ba amma bari in duba in gani (ya daga murya) Alaikumus-salam (Ya tashi ya nufi kofar ya bud'e)

Direban Kamfani:

Yalla6ai barka da asuba (cikin ladabi da biyayya)

Alhaji Damisa:

Barka ka dai Liman mai ya faru?

Direba:

Yalla6ai sabon injin nan ne ya tsaya a ma'aikata tun jiya da daddare. Anyi anyi a gyara abin ya citura shi ne MD ya turo ni maza in zo in kirawo ka.

Alhaji Damisa:

Injiniyan kamfani bai zo ba ne mai yasa bai gyara ba?

Direba:

Yana nan tun da karfe biyar na asuba amma injin bai gyaru ba. Anyi iya kokarin da za a yi a tada shi ya k'i tashi.

Alhaji Damisa:

Tun yaushe Manajan Darekta ya zo Kamfani? Don me ya sa ba a bugo min waya ba?

2>3


'Yar Damisa - Gabatarwa

From the Archive of:

Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +2348067062960

©2023 Tijjani M. M.


Post a Comment

0 Comments