Ticker

6/recent/ticker-posts

Daurin ‘r’ A Gabar Aikatau

Ɗaurin "r" A Gaɓar Aikatau

223. In aka ɗauri ‘r’ wurin ba nasaba ba,

Ba kuma mallaka ba, to malam duba,

Ba a gaɓar da za ta fayyace muna jinsi ba,

In ba a gan shi nan ga kalmar sunan ba,

  Ba dangantaka ka zan mai ganewa.

224. Wato aikatau yana iya ɗaure ta,

 Za ta taho ga aikatau sai a riƙe ta,

 Ba sautin da za a sa don kwance ta,

 In ta biyo da aikatau a rinƙa kula ta,

  Can ƙarshen gaɓarsa za ta liƙewa.

 

225. Rinƙa kula da ‘r’ idan aka zana ta,

In ta raɓi aikatau ba a taɓa ta,

Ba nashe ta ko a tsarin furucinta,

Kuma ba ƙara harrafi nan bagirenta,

  Ba siffarta ko guda mai sauyawa.

 

226. A wuraren da za a gane misalin shi,

Sautin ‘r’ a nan ka san an ɗaure shi,

A misali akwai fitar da kawar ga shi,

Jefar, can gusar, matsar duk a saka shi,

Ko a ɓatar da shi mayar da na maidawa.

 

227. Ɗaurin ‘r’ akwai misalai aikin ga,

Mai tallar tumaturi ad da waɗanga,

Yaro na biɗar wuƙa don ya yi tsarga,

Mai tafiyar da hamɓarar da hukumar ga,

  Ya horar da dakaru jiya horarwa.

 

228. Kalmar aikatau akwai sauti liƙe,

 Ba sauti gabansa shi ɗai yake liƙe,

 Ba sauya shi, ba a tauye shi a shaƙe,

Duk a gaɓar da kag ga ‘r’ ƙarshe liƙe,

  Abada sai a bar ta nan ba ta gushewa.

 

229. Zana fitad da kuskure ne a kiyaye,

 Ko tafiyad da bai da gurbi a kiyaye,

 In an hamɓarad da gwamna tafi ɓoye,

 Ba a faɗin fitad da domin a kiyaye

  Ɗaurin ne na baki ba a zanawa.

 

230. Horas ko ɓatad da duk kak ka rubuta,

 Horar, ko ɓatar ka daidai a karanta,

 Naso ne kawai ka gane ka kwatanta,

 Tsarin an ka so ka gane ka rubuta,

  Balle hamɓarad a sa ‘r’ nashewa.

 

231. Muddin aikatau da ‘r’ sun haɗu tare,

 In ka gan su nan ga kalmarmu a jere,

 Ko furucin baki ba ka jin ta a ɗaure,

 Ko furucin da kaj jiya ba ‘r’ ɗaure,

  ‘R’ a rubuce tabbata za ta fitowa.

 

232. Duk kalmar da ‘r’ ta zo a misalinmu,

Kalma ce ta aikatau shiga aikinmu,

Tantance ta tabbata ta ga aikinmu,

Kai a taƙaice ‘r’ da ag ga misalinmu,

  Aiki ne ta bayyanar mai bijirowa.

 

233. Ko dai wanda yaw wuce koko a yanzu,

 Ya danganta lokacin duk da ya wanzu,

 Shuɗaɗɗe yak kasantu ko yanzu a yanzu,

 Ko kuma an yi ya wuce tun can ɗazu,

Ko kuma mai zuwa da ɗan jinkirtawa.

 

234. Kalmomin kawar, fitar, duk aiki ne,

 Haka miƙar da zayyanar ma aiki ne,

 Ga su gusar, da tsallakar duk aiki ne,

 Ai shi ma mayar ka san duk aiki ne,

Haka tafiyar da hamɓarar ko horaswa.

 

235. Duk asalinsu kausuwa ne da fitarwa,

 Da mayarwa, da karkatarwa da ciyarwa,

 Kalmar talla, ko ɓatarwa, tafiyarwa,

 Da ɓatarwa, biɗi, kawarwa, da gusarwa,

  Ko tafiya da hamɓara ko horaswa.

 

236. A bayanan da mun ka zano a rubuce,

 Asali dai ga aikatau ‘r’ ta kasance,

 An ɗaure ta ne, buƙata a taƙaice,

 In muka san hakanga ‘r’ ‘yar rakiya ce,

  Ko ita ko rashinta duk bai cutarwa.

 Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa


Post a Comment

0 Comments