Dokokin Dauri

    Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

    About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

    Dokokin Ɗauri

    106 Ɗauri na da ƙa’ida in mun lura,

     A gaɓar Hausa mai baƙi wasali tara,

     Saka sauti gaban wasal ɗuko ƙara,

    Duk ɗaurin da za a yi Hausa a lura,

    Kar ya wuce tsawon gaɓoɓin Hausawa.

     

    107. Dokoki na ɗora ɗauri ba kushe,

     Ɗauri na zuwa ga kalma koyaushe,

     Bai da wuri guda da ya bar shi a yashe,

     Ba a yi shamaki ba farko ko ƙarshe,

      Ko farkonta, ko tsakan, ko a tuƙewa.

     

    108. Duba za mu faɗaɗa ga misali ne,

     Babba-da-jikka zanƙalelen dabba ne,

     Can ga fukafukan baƙi ne ba zane

     In kun lura dukkansu misali ne,

      Farkon kowanensu ɗauri aka sawa.

     

    109. Lura Babarbare, barunje da mayanka,

     Makarantar da malami ke dukan ka,

     Rundawa ka ba da fata ga maɗinka,

     In aka duba inda ɗaurinsu ya sauka,

    Ɗaurin nasu duk tsakansu yake zo wa.

     

    110. Wasa ag gare mu Misau[1] wai girjim.[2]

     Akwai ɗauri a ƙarshenta wato dai -jim,

     Na ga baƙi-ƙirin da jajir aje tinjim,

     Zan kula, -rin da -jir da ƙarshen -tinjim,

    Sai ƙarshen gaɓa a nan muka ɗaurewa.

     

    111. In mun lura yadda ɗauri ka tahowa,

     Farko ko tsakansa koko ga tuƙewa,

     Furuci ko rubuce duk zanka kulawa,

     Wato dai zubi da tsarin ɗaurewa,

      Kalmomi a gun su ne aka ganewa.

    112. Sharaɗi nai a sa baƙi wasali daidai,

    Su kasance a jere, komi ya yi daidai,

    To kuma sai su zo da ɗaurin sauti dai,

    Za a saka gaban wasali ɗin dai,

      Kana a sa baƙin da ɗaurin ka riƙewa.

     

    113. Baƙi, wasali jere ai gaɓa ta cika sosai,

    Kuma buɗaɗɗiya ake ce mata, to sai-

    Zancen a rufe ta gum! Baƙi zai zo sosai,

     Ko wasali ya zo ya ɗaure baƙi sosai,

      Acca, Annaboro, ankwa, arbawa.

     

    114. Keken Ammani ya zube can ƙasa kancau!

     Ankara, Anka, Andarai, Indo, Ancau,

     ‘In’ da ‘an’ cikin Indo da Ancau,

     Da misalin da yat taho jinkar ‘kancau’!

      A misalan ga duk baƙi aka ɗaurewa.



    [1] Misau ƙaramar hukuma ce a jahar Bauchi a Nijeriya.

    [2] Girjim wata wasa ce da ake aiwatarwa a garin Misau (da ma wasu wurare watakila). A duba rataye na 1 domin ganin bayanin wannan wasa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.