Dauri da Dokokinsa

    About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

    Ɗauri da Dokokinsa

    92. Bi ni a hankali aboki ka zan lura,

     Kar ka bari a bar ka baya cikin ƙura,

     Sabon bagire a yanzu shi muka tunkara

     Sa natsuwa da hankali ɗan saurara,

    Don mun doshi gargada sai da kulawa.

     

    93. Ilimi dai yana buƙatar a kwatanta-

     Ai nazarin abin da duk za a rubuta,

     Kar a ɓatar da mai buƙatar ya karanta,

    Farko tambaya mu kai don a taƙaita,

      Mene ne gaɓa ga tsarin Hausawa?

     

    94. Masana sun ka ce gaɓa lafazi ke nan,

     Lura gaɓa iri-iri ce kuma sannan,

     In an ce ‘buɗe’ mai baƙi wasali ke nan

     Wanda take ‘rufe’ baƙi ke farkon nan-

      Ga wasali a sa baƙi sai furtawa.

     

    95.  A buɗaɗɗiyar gaɓa a nan misalinsu,

     Tamkar ba, da ci, da do, ka ji zubinsu,

     Idan kuwa an biya dukkanin tsarinsu,

     Wasali wanda bai da goyo ke bin su,

      Kowane nan gaɓa guda ne a zubawa.

     

    96. Haka ma sau, da kai ƙui! Masu tagwaye,

     Ga goyonsu nan a bayyane kai waye,

     Ko sun ɗauki wanga tsari ba tauye,

     Ba su rufe ba, ko alama, a kiyaye,

      Ka ji gaɓa guda-guda don ƙarawa.

     

    97. Shi ɗauri baƙi a nan in aka ƙara,

     Can ne kan gaɓar da ke buɗe a ɗora,

     Sai a rufe ta kan gaɓar don a sarara,

     In ɗauri ya zo a kan harafi lura,

      Gun ɗaurin a nan gaɓa taka ƙarewa.

     

    98. Lafazin tir da tur da kul duk ɗauri ne,

     Sautin nan na ƙarshe ko shi ƙari ne,

     An ƙara shi ne ka gane tsari ne,

     To ke nan cikin gaɓar nan ɗauri ne,

      Buɗaɗɗiyar gaɓa a nan taka kublewa.

     

    Zubin Gaɓoɓin Kalmomin Hausa

     

    99. To su ko gaɓa-gaɓa akwai maganarsu,

     Kalma kan samu ne idan ka haɗa su,

     Akan sa ɗai, biyu, uku, ko da yawansu,

     Yanzu mu je zubin gaɓa mu ga tsarinsu,

      Kalmomin da kowace za ta haɗawa.

     

    100. Ci, yi, ji, da zo gaɓoɓin duka ɗauka,

    Ɗaiɗaya ne ka daina yin duk wata shakka,

    Kwai biyu ma ajin gaɓar in an sakka,

     Baba da Inna, Kawu, gwaggo, ka sa kaka,

      Bibbiyu ne gaɓuɓuwan sai karyawa.

     

    101. Wansu gaɓarsu ukku ce gun zanawa,

     Ka ga Abuja, auduga ga kamawa,

     Bagudu, Bagudo, bajinta, birgewa,

     Sadauki, jaruma, gwaninta, gogewa,

      Lura gaɓansu ukku-ukku ga zanawa.

    102. In muka zo cikin bayani kuwa sosai,

     Akwai mu da masu tsarin huɗu sosai,

     Makaranta, sarauniya duba sosai,

     Masarauta, madakata ƙyarga sosai,

    Hurhuɗu ne wajen gaɓa babu musawa.

     

    103. Akwai masu gaɓa biyar wurin zanawa,

    Kalmar dunƙulalliya, rirrikitarwa,

    Ko kuma mulmulalliya gun furtawa,

    Ga kuma zanƙaleliya mai miƙewa,

      Kowace ‘yar gaɓa biyar ce ga azawa.

     

    104. Akwai ma mai gaɓa shida can tsarinta,

     Sai dai ‘yan kaɗan suke ga misalinta,

     Ga mu murƙushesheniya a irinta,

     Ita lallanƙwasasshiya in ka fasalta,

      Gaɓɓai shidda ne ka duba da kulawa.

     

    105. Yanzu taƙaice dai idan muka duba su,

     Masu guda-guda, bibbiyu mun sa su,

     Ukku, huɗu, biyar, shida ga jimillarsu,

     Ka ji ajin gaɓuɓuwan Hausa dukansu,

      Masana sun ka ce a nan za su tuƙewa.

    Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.