TAMBAYA (43)❓
Assalamu alaikum malam barka da safiya dafatan antashi lfy, Allah yakara
basira ameen. Malam tambayata a nan ita ce. Malam macece tai aure akauye alhali
aburni aka haifeta harta isa aure sai tai aure akauye to malam garin bawani na
gartaccen ilimi saiyaranta da suka haifa aka kaisu wajen iyayenta dan samun
ilimi, malam mijin yaka sance marowacine kuma yanada halinshi daidai gwargwado
maaikacine kuma manomi, baitaba siyen ko da sabuluba yaba iyayen matarshi
maruka yayanshi saidai su sukagabaya siya konayaran sai sukace yadunga saima
yaranshi ana masu wanki, to malam yahalatta matarshi idan zataje gida tadan
kwana2 ta dibi abincinshi tatai da shi sudunga ci saboda iyayenta bahali
garesuba intaje hannu biyu ga yaya haka zaaita wahalar neman abunci, shikuma
idan zataje ba zaice ga ko kudin siyen kokoba haka zatatai da yaya hudu ko da
za suyi sati, yahalatta tadibi danyen abinci tatafi da shi bai saniba dan inya
sani ba zai bariba kuma ta ce tana barar addua Allah yashirya mata mijinta dan
baya cikin na gari baya aikata zina baya shaye shaye amman halayensa basuda
kyau mungode malam Allah yashirya zuria
AMSA❗
Waalaikumus, Warahmatullahi, Wabarakatuhum
Ma'aikaci kuma manomin a takaicedai Allah ya albarkacesa da rufin asiri
amman jahilci ya kewayeshi, mafita a nan shi ne a bullo masa ta bangaren da
yake da naƙasu wato ilimi
Kuskuren ta daya anan, me ya sa ta kai yayan nasa batareda izinin mijinba,
a nan ta yi gaban kanta ke nan ta maida kanta jagora alhalin shi ne jagoran
gidan wanda za ta iya yiwuwa silar hakan ya janye hannayensa daga ciyar da su
da shayar dasu da tufatarwa. Kallon mai kudi amman jahili da dangi suke masa kadai
isa ya sa shaidan ya yi nasarar da zaisa ya zare hannayensa daga lamuran
yayannasa
Dukkansu sun yi kuskure. Ta hanyar da aka bi tanan yakamata a sauko
A shawarce kamata ya yi ta tambayeshi dalilin da ya sa baya taimakawa yayan
nasu idan ya ce meyasa kuka daukesu batareda izinina ba to sai a bashi haƙuri
wanda in sha Allahu silar hakan zai dinga taimaka musu
Idan kuma ya nuna cewar shi haka nan bashida ra'ayin taimaka musu to sai
samu waliyyinki a sanardashi abin da ke faruwa
Rashin maida al'amarin matsalar aure ga waliyyai shi ne babban abin da yake
kawo matsala ga al'ummar wannan zamanin. Wanda ma'aurata a da can za ka ga suna
samun rashin jituwa za su gaggauta miƙa lamarin ga waliyyansu, kuma nan da nan
zakaga an shawo kan matsalar
Don haka idan bai gyara halinnasa ba sai kije ki samu waliyyanki ki
sanardasu duk abin da ke faruwa. Abin da nake jiye miki tsoro shi ne kada kiji
wataran ganki kin daukar masa kayan abinci wanda shaidan zai raya masa ai ta
dade ma tana dauka batareda saninka ba alhalin ke kin dauka ne da manufar
ciyarda yayansa. Ance dai maganin kar ayi kar a fara. Kuma ki godewa Allah SWT
da ya zamana iya wannan ne halin nasa
A karshe muna roƙon Allah SWT ya baki ikon cin jarabawar da kike
ciki tun da daman gaba daya rayuwar kowa jarabawace kamar yanda Allah SWT ya
fada a cikin Suratul Mulk ayata 2, sannan kuma ki dage da tsayuwar dare, In sha
Allahu za ki ga sauyi domin kuwa babu abin da ya gagari Allah SWT kuma ki dauka
wannan ƙaddararkice kuma Annabi SAW ya ce babu abin da ke sauya ƙaddara
sai addu'a kamar yanda hakan ya tabbata a cikin sahihin hadisin da Abdullahi
Ibn Abbas RA ya rawaito
(Duba littafin Tuhfat al-Ahwadhi wallafar Al-Mundhiri hadisi mai lambata 9,
chapter 13)
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa:
✍Usman Danliti
Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www. facebook. com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.