Adalci Tsakanin Mata

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    ina da mata biyu, ɗiyar talaka da ɗiyar mai kuɗi, shin ya halatta na yiwa ɗiyar talaka tufafi masu araha, ita kuma ɗiyar mai kuɗi na yi mata masu tsada?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Akwai hujjoji daga Alƙurani mai girma da Hadisai ingantattu da magan-ganun malamai akan wajabcin Miji yaciyar da Matansa, wannan kuma ya biyo bayan gwar-gwado dama da ikon da yake da ita. Kuma ba ya yiwuwa ya bar ta ta ciyar da kanta ko da kuwa mawadaciya ce, sai dai idan da yardarta akan za ta ciyar da kanta.

    Kuma wannan ciyarwar da za'a yiwa mace daga ciki akwai tufatar da ita, lokacin sanyi da zafi, bawai sai kowacce shekara ba, da kowane biki ba, a'a zai yishi ne ko da kuwa tana da tufafin, ba maganar sai ya ga tufafinta sun lalace, sannan ya yi mata ɗinki, A'a tufatarwa na kasancewa ne gwar-gwadon bukatar matarsa ga tufafin kuma gwargwadon karfi/ikonsa, ba tare da kuma ya yi fifita wata akan wata ba, 'yar Masu kuɗi da 'yar talaka, lura da Alƙur'ani mai girma cewa hakan zai kasance ne da kyautatawa kuma gwar-gwadon Wadatarsa:

     ۚ وَعَلَى الْمَوْلُودِ لَهُ رِزْقُهُنَّ وَكِسْوَتُهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ ۚ لَا تُكَلَّفُ نَفْسٌ إِلَّا وُسْعَهَا ۚ

    "Wajibine akan wanda ake yiwa haihuwa (miji) ciyarda Matansa da tufatar dasu bisa kyautatawa, Bamu kallafawa rai sai abin da za ta iya" (Suratul Baƙara:233.)

    Ibn Kaseer Allah ya yi masa rahma ya ce: "Ana nufin ciyar dasu irin abinda al'adar mutanen gari take cewa shi ne Abunda ake ciyar damata da shi gwar-gwadon arzikinsa garinsu ke tafiya akan shi, ba tare da bannatar da dukiya ko  noketa, gwar-gwadon dai samunsa da wadatarsa" Tafseer Ibn Kaseer (1/634)

    Anan abinda ya fi zama maslaha shi ne ko wace ya siya mata irin abin da ya siyawa ɗayar gwar-gwadon arzikinsa.

    Domin Adalci Allah ya ce Ayi, matsayinsu ɗaya awajanka kowacce matarka ce, kasonsu ɗaya acikin gadon dukiyarka koda kuwa Ubantane ya fi kowa wadata aduniya, inka mutu da ita da wacce Ubanta ya fi kowa talauci aduniya ɗaya suke wajan Allah saboda haka nema yaraba gadonsu dai-dai babu ban-banci idan ka mutu.

    Bai halatta kayi wannan Shaiɗanci tsakanin Matankaba, kuma lallai kasani yin hakan kunna wata gobarar dajice agidanka wanda bakasan iyakacin ɓarnar dazatai acikin gidanka da zurriyarka baki ɗaya ba.

    Maganace Mummuna kuma Koda kaji koka karanta awani waje cewa hakan yahalatta, katabbar kuskurece, ta saɓawa Ayoyin Alƙur'ani da hadisan Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam da tunani mai kyau.

    Wajibine katsayar da adalci tsakanin matanka, haramun ne kafifita wata akan wata, wajan tufafi ko kayan kwalliya ko yanayin irin Abuncin dakake ciyar dasu.

    Wajibine kadunga yi musu tufafi masu kima ɗaya daraja ɗaya, haka abunci haka wajan kwanciya haka gida dole kabaiwa kowacce dai-dai da ɗayar.

    Inka saya wa ɗiyar masu kuɗi tufafin dubu biyar, wajibine ɗiyar talakama kasai mata tufafi mai darajar datakai dubu biyar, balalle su zama kala ɗaya ba, amma darajarsu da tsadarsu dole ne suzamto dai-dai.

    Waccan in kullum kana saimata lemuka da nama da dukkan wani Nau'in Abunci mai kyau kona Sha, ɗayar ma wajibin kane kadunga sai mata irin wannan abunci mai daraja iri ɗaya dakuma karin kuzari da inganta jiki irin wacce kasaiwa ɗiyar masu kuɗin da ka auro.

    Haka in ka baiwa ɗaya gida mai dakuna uku da firji da setlight da kayan kawa, itama ɗayar dole ne kasai mata gida irin na ɗayar maicike da kayan kawa da more rayuwa irin na ɗayar babu ban-banci.

    Wannan shi ne zai tseratar dakai agaban Allah rannar Alkiyama daka shiga wuta.

    Bayan haka yana daga abinda ya fi zama maslaha yayin da mutum zai yi aure ya duba MUKAFA'AH wato dai-daito tsakanin miji da mata, domin duk lokacin da ya zamto miji daba ya iya hidimawa matarsa wajen kiyaye mata abincinta, muhallinta uwa-uba bashi da karfin siya mata mai wanda zai gyara mata fatar jikinta kamar yadda take a gidan iyayenta, to dole ne a samu matsala. Don haka yana da kyau idan son samu ne ya auro dai-dai da shi ko kuma wacce ya fita.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.