Ticker

6/recent/ticker-posts

Alamar Bude Magana (“)

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

512. Zancen duk da za ka kawo ga rubutu,

 In dai wani ne ya yi shi in za ka rubutu,

 To sai ka yi yadda za a gane a rubutun

 Zance wani za ka sanya ga rubutu,

  In ba naka ne ba tilas nunawa.

 

513. Don a fahimci kai ruwaya kaka yowa,

 Zancen nan da an ka yo ga rubutowa,

 wani ne yay yi, sai ka zo ga ruwaitowa,

 Ba zancenka ne ba, su ka karantowa,

  Kai aikinka nan wurin ɗai zanawa.

 

514. Tun farko ka sa alamar buɗewa,

 Yo haka “ shi da za shi karantawa,

 In ya gan ta zai fahimci ruwaitowa,

 Ce kaka yi batun da kai ka rubutawa,

  Shi zai nuna babu hannunka ga cewa.

 

515. Don malam ya ce; “ɗabi’ar yaranta,

 Ko mai kyau, irin ta koyon malanta,

 Koko akasinta mai awa dai da mugunta,

 In ko biyu ka haɗe da ƙeta da mugunta,

  In aka girma kan ta ba ta sauyawa.

516. Allah ya faɗa; “Waman ya ‘amal” lura,

 Sannan Ya ce; “ Faman ya’amal”  lura,

 Ayoyin biyun ga an nuna su a sura,

 Az Zalzalah, ka duba su ka lura,

  Komai kay yi ran gamo za ka ishewa.

 

517. Duk zancen da mun ka kawo ka kiyaye,

 Wani yay yo shi, don hakan sai a kiyaye,

Kuma mun bayyana gudun kar mu kuranye,

 Sannan mun ka buɗe zance mu tumanye,

Gun buɗe shi ‘yan alamun ka gwadawa.

Post a Comment

0 Comments