𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
Alaikum. Shi wai zato (suspicion) yana daga cikin manyan kaba’irai na zunubi
ne?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus
Salaam Wa Rahmatul Laah.
Zato iri na
biyu ne: Kyakkyawan zato da Mummunan zato.
(1) KYAKKYAWAN
ZATO shi ne: Yi wa musulmin da ba a san shi da wani mummunan aiki ba kyakkyawan
tunani, da kawar da duk wani zargi na aikata ba daidai ba daga gare shi har sai
abin ya bayyana a fili ƙarara daga gare shi. Kamar abin da Allaah ya faɗa a kan ƙissar
ƙazafin
da munafukai suka yi wa Nana A’ishah
(Radiyal Laahu Anhaa) cewa:
لَّوۡلَاۤ إِذۡ سَمِعۡتُمُوهُ ظَنَّ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَٱلۡمُؤۡمِنَـٰتُ بِأَنفُسِهِمۡ خَیۡرࣰا وَقَالُوا۟ هَـٰذَاۤ إِفۡكࣱ مُّبِینࣱ
Meyasa a
lokacin da kuka ji shi muminai maza da mata ba su yi zaton alkhairi ga
rayukansu ba, kuma suka ce wannan kiren ƙarya ne mabayyani? (Surah An-Nuur: 12).
Kuma
Al-Bukhaariy (6061) ya riwaito daga hadisin Sahabi Abu-Bakrah (Radiyal Laahu
Anhu) cewa: Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« إِنْ
كَانَ أَحَدُكُمْ مَادِحًا لاَ مَحَالَةَ فَلْيَقُلْ أَحْسِبُ كَذَا وَكَذَا . إِنْ كَانَ يُرَى أَنَّهُ كَذَلِكَ »
Idan ya zame
wa ɗayanku lallai
sai ya yi yabo ga wani, to ya ce: ‘Ina zaton sa kaza da kaza.’ Idan yana
tsammanin shi haka ɗin
ya ke.
Waɗannan nassoshin sun nuna:
(i) Haƙƙin
musulmi ne a kan sauran musulmi su kare mutuncinsa, kar su amince da duk wani
zargi na zubar da mutunci da ake yayatawa a kansa, har sai abin ya bayyana a
fili ƙarara.
(ii) Ba a
yarda musulmi ya zaƙe wurin yin yabo ga wani musulmi ba, don kar ya cutar da shi
ta hanyar ɗaukaka
shi da ƙoƙarin
wanke shi, wanda hakan kan iya kai shi ga hallaka.
(iii) Yi wa
musulmi na-gari kyakkyawan zato har a lokacin da ya aikata kyakkyawa, domin ba
a san haƙiƙanin
abin da yake ɓoye na
al’amuransa ba.
(2) MUMMUNAN
ZATO kuwa shi ne: Yi wa musulmin da aikin sharri bai bayyana daga gare shi ba
tunanin cewa yana munana aiki a ɓoye.
Daga nan kuma a cigaba da mu’amalantar sa a kan hakan. Allaah Ta’aala ya ce:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اجْتَنِبُوا كَثِيرًا مِنَ الظَّنِّ إِنَّ بَعْضَ الظَّنِّ إِثْمٌ ۖ وَلَا تَجَسَّسُوا
وَلَا يَغْتَبْ بَعْضُكُمْ بَعْضًا ۚ أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ
أَنْ يَأْكُلَ لَحْمَ أَخِيهِ مَيْتًا فَكَرِهْتُمُوهُ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ
ۚ إِنَّ اللَّهَ تَوَّابٌ رَحِيمٌ ٢١
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku
nĩsanci abu mai yãwa na zato. Lalle sãshen zato zunubi ne. Kuma kada ku yi
rahõto, kuma kada sãshenku yã yi gulmar sãshe. Shin, ɗayanku nã son yã ci naman ɗan´uwansa yanã matacce?
To, kun ƙĩ shi (cin nãman). Kuma ku bi Allah da
taƙawa.
Lalle Allah Mai karɓar
tũba ne, Mai jin ƙai. (Surah Al-Hujuraat: 12).
Kuma Muslim
(6701) ya riwaito daga hadisin Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) cewa: Manzon
Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce
« إِيَّاكُمْ وَالظَّنَّ فَإِنَّ الظَّنَّ أَكْذَبُ الْحَدِيثِ »
Ku yi nesa da
zato. Domin dai zato shi ne mafi ƙaryar labari.
Waɗannan nassoshin kuma sun
nuna:
(i) Ma’anar
Sashen Zato shi ne mummunan zato ga musulmin da ba a san shi da bayyana munanan
ayyuka ba.
(ii) Bai
halatta ga wani musulmi ya yi wa irin wannan musulmi mummunan zato ba, balle
kuma har ya je bincike da neman sanin halinsa.
(iii) Malamai
sun nuna wajibi ne a nisanci irin wannan zaton a kan irin wannan musulmin da ba
a ga wata alama a kan yana munana ayyuka ba.
(iv) Ƙin
bin wannan umurnin na nisantar irin wannan mummunan zaton ya zama haram kenan
ga musulmin da ya aikata shi.
(v) A ƙarƙashin
wannan, maganarsa cewa: Zato Zunubi ne ya zama babban zunubi kenan, ba ƙaramin
zunubi ba, irin waɗanda
sallah da sadaka suke kankarewa.
(vi) Kodayake
wannan irin zaton bai shiga cikin mafiya girman zunubai masu fitarwa daga
musulunci kamar shirka da kafirci ba, amma dai dole mai aikatawa ya yi tuba da
sharuɗɗanta kafin
mutuwarsa.
(vii) Yana
daga cikin siffar Imani mutum ya nisanci irin wannan mummunan zaton ga musulmi,
idan dai ba wani abu ne da ya bayyana a fili ba.
Allaah ya ƙara
mana kariya.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh
Muhammad Abdullaah Assalafiy
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.