Ticker

6/recent/ticker-posts

Aya

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

408. Aya dai abin nufi kammala zance,

 Wato dai cike bayani a taƙaice,

 In ta zo ka gane ba sauran zance,

 In da ka sa ta dole ne sai ya kasance,

  Jimla ta cike ga tsarin zanawa.

 

409. Masana sun ka ce, ashe aya kanta,

 Babu ta Hausa, dole sai an ka aro ta,

 An ka saka ta ƙa’ida don a rubuta,

 Can asalinta tun ga tsarin tushenta,

  Larabci ya zo da shi gun Hausawa.

 

410. Ƙur’ani ya zo da su gun makaranta,

 Su aka bi a gane komai a karanta,

 Sannan anka sa ta domin a rubuta,

 A rubutunmu an ka sa don a karanta,

  Ga su daki-daki wurare na tsayawa.

 

411. Bayan an aro ta sai aka Hausanta,

 An mata tanadi da tsari na nagarta,

 An kuma nuna yadda za a rubuta ta,

 Suna an ka ba ta an ce ita aya ta,

  Don ta zamo cikin alamun zanawa.

412.  Ta kasu ukku kan alamu na sifarta,

 Kowace ma da yadda za a rubuta ta,

 An mata tanadi na doka ga zubinta,

 In ka lura kowace da muhallinta,

  A wajen ƙa’ida suna sassaɓawa.

 

413. In ka ga ɗan ɗigo alamar aya ce,

 Sai ka kula a nan an ƙure zance,

 Duk harafin da zai biyo to ya kasance,

 Babba ka fara sa shi jimlar a rubuce,

  Ita ce babba don ka zan mai ganewa.

 

414. Sai ta biyunsu sa ta motsin rai ke nan,

 Ita ma in ka gan ta ai aya ce nan,

 Amma ka sani akwai bambanci nan,

 Siffar tasu ta gwada doka ce nan,

  Ɗan layi da ɗan ɗigo aka tarfawa.

 

415. Ta ukun tambaya idan an yi rubuce,

 Ayar in ta zo cikin kowane zance,

 An yi nufin a tambaya nan a karance,

 Wato tambaya ta zo nan a katabce,[1]

  Ayar tambaya wurin za a dasawa.



[1] “Katabce” ararriyar kalma ce daga harshen Larabci (kataba) da ke da ma’anar rubutu.

Post a Comment

0 Comments