Ticker

6/recent/ticker-posts

Babbar Aya (.)

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

416. Ita ga sifarta ɗan ɗigo za a sakawa,

 Haka nan yat taho rubutun Hausawa,

 In maganar ka ta cike gun sheɗawa,

 Sai a saka ta ɗan ɗigo babu daɗawa,

Ƙarshen sheɗawa da duk za a tuƙewa.

 

417. In jimlar da za a yi ta cika sosai,

 Babu ragi bale a yo ƙari to sai,

 Dangwala ɗan ɗigo ka duba dai sosai,

 In saƙo a nan wurin ya cika to sai,

  Sai a yi ɗan ɗigo alamar ƙarewa.

 

418. Ba a saka ta sai bayani yai daidai,

 In saƙon ya jagule to ka sani dai,

 Matuƙar ka saka ta ka kauce daidai,

 Kai kula in da za ta zo dole ya zan dai,

  An tantance babu sauran ƙarawa.

 

419. Kai jama’a ku zo mu ɗan harhaɗa kanu,

 Ita ko duniyar ga sai an tafi sannu,

 Babu batun faɗa da an tsona idanu,

 Ga misali ka ce ma yaro tafi sannu,

Ba a gudu ga gargada daina matsawa.

 

420. Kaji ga su yashe an watse akurki,

 Wai kashin ake biɗa don a yi taki,

 Da isa ta wurin haba sai mamaki,

 Na tafi kasuwa wajen masu awaki,

  Na ishe babu ko guda mai burgewa.

 

421. Wani ya ce da ni aku ya fi ya suda,

 Na bar arhar abin ku na yarda da tsada,

 Magabatanmu sun faɗa mun kuma yarda,

 Mun lamunta mun gani har ga takarda,

  Halayyar uba ɗiya suka ɗaukowa.

 

422. Baitocin ga ɗan’uwa in ka lura,

 Kwai jimla cikinsu, duk an tsattsara,

 Kar fa ka ɗau abin kamar dai almara,

 Bi su daki-daki, ka duba ba saura,

  Duk jimla guda guda suka nunawa.

423. Duk ɗango guda idan ka yi karatu,

 Lura da mai bin sa ɗan’uwa nan ga rubutu,

` Ko na ukunsu ma ka gane ka fahimtu,

 Amma wasu kan idan ka yi karatu,

Gun na biyunsa nan bayanin ka tuƙewa.

 

424. Don haka ne muke buƙatar aya nan,

 In aka sa ta an gama to shike nan,

 Za fa ta taimaka ga masu karatun nan,

 Za a gane ta nan ga rubutun nan,

Don a fahimci nan bayani ka tsayawa.

Post a Comment

0 Comments