Ticker

6/recent/ticker-posts

Alamomin Rubutu

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

Gabatarwa

402. Tambihi muke ku zam masu kulawa,

 In kun lura ƙa’idojin zanawa,

 Jagora suke ga masu karantawa,

 Ga rubutu akwai alamu kyawawa,

Da ake son a zan kula ga rubutawa.

 

403. Sai an sa su kyan rubutu ka fitowa,

 Sannan za ya taimaka ga karantawa,

 Duk wani yamutsi ka san su ka rabewa,

 Su aka sa cikin rubutun Hausawa,

  Har ma’anarsa sai da su aka ganewa.

 

404. In ba su abin ya kwaɓe sai mai su,

 Sai su jagwalgwale rubutu illar su,

 Su ka dagargaje, fahimta tsarin su,

 Dole a nemi wanda ke ɗan gadonsu,

  Ko shi ai da mamare zai ganewa.

 

405. Ya zama dole mai rubutu ya kiyaye,

 Yai nazari na ƙa’ida ba wani shaye,

 Ga rubutu na Hausa komai kai waye,

 Ya rattaba ƙa’idar rubutu a gwananye,

  Ga wuraren da za a sa su ga tsarawa.

 

406. Su ke gyaran komaɗar nahawun zance,

 Ba a ganin su dole sai dai a rubuce,

 Su ka zuwa cikin rubutu su yi kwance,

 Kuma sun taimaka wa malam a karance,

  Ba don su ba, ƙa’ida ba ta fitowa.

407. Bi ni da hankali ka gane bayanina,

 Zan bijiro da su na ba ka misalina,

Na san ka sani batun ƙara sani na,

Tattaro hankalin ka kai abin alheri na,

  Sa natsuwa ka bi ni su zan nunawa.

Post a Comment

0 Comments