Ticker

6/recent/ticker-posts

Daurin Harafin ‘n’ a Rubutu

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

Ɗaurin Harafin ‘n’ a Rubutu

135.  ‘M’ an kammala ta komai ya saitu,

 Ita ko ‘n’ tana da tsari na rubutu,

 Sai fa a lura kar a ruɗe ga karatu,

 Ɗaurin na da ƙaida tai ta rubutu,

  Sai a biyo ni sannu domin ganewa.

 

136. Zanka tunawa ko da yaushe kiyaye,

 In aka ɗauri ‘n’ ga kalma a kiyaye,

 Matuƙar bai karo da dokar ‘m’ saye,

 To ita za a sa a huta kai waye,

Harafin duk da zai biyo ta ga zanawa.

 

137. Duk na biye a yanzu kam to ya kyautu-

A ce mun gane ƙa’idar ‘n’ ga rubutu,

 In harafin yana cikin leɓantattu,

 To dole a sauya ɗaurin ga rubutu,

  Ba a rubuta ‘n’ a nan ‘m’ aka sawa.

 

138. Waiwayi baya can a ɗaurin ‘m’ kanta,

An yo sharaɗi da zai daɗa an inganta,

Duk yanayi na ƙaidar don ka rubuta,

 Bayan su a ko’ina aka ɗaure ta,

  Za a rubuta ‘n’ kwatancin furtawa.

 

139. Dangana sanda ba shi yi sai mai sanda,

 ‘N’ nan ta gabata kafin sautin da,

 ‘n’ ita yak kamata kalmar ɗansanda,

 Kalmar gangami, kwatanci, ɗansanda,

  Randa, runduna da rance, runtsawa.

 

140. Malam dakata a nan ga wani zance,

 Don mun bayyana a can dai a rubuce,

Ba duka ko’ina ba ‘m’ za ta kasance,

 In kuma ta fito tsakanin saɓi-zarce,

Sun ka zamo kamar guda gun zantawa.

 

141. Ga misali kamar ka ce ‘Wandon baba’,

Ko kuma dai a gun faɗin ‘Gandun Buba’,

Tandun Balki babu kwalli na duba,

Dandin Mahe[1] za ni ba sai kun ce ba,

  Ko ‘gonan Bashar’ haki na tasowa.

 

142. Duk nan ba ka zana ‘m’ ƙarshen wando,

 Haka Gandu gabansa ‘n’ bari kirdado,

 Ko tandu na Balki ‘n’ ce ko Indo,

 Dandin Mahe ba a sa ‘m’ haba dodo,

  Ko gona, a cana duk bai dacewa.

 

143. Kalmomin daban-daban ne ga rubutu,

 Ba a haɗe su ko kaɗan nan ga rubutu,

 Sa su daban-daban a hutar da karatu,

 Kowace na da nata ‘yanci don hutu,

  Ba a haɗe su ko ga harshen furtawa.

 

144. Don bakinka na faɗin “wandom baba”,

 Ba a rubuta ‘m’ gurin ba ka gane ba,

 Ko da ka ji an faɗa,  “Gandum Buba,

 Nan ma ba a sanya ‘m’ in ka duba,

  “Wandon baba” mai rubutu ke sawa.

 

145. Ba kuma za ka sanya “Dandim” ba jaye,

 “Dandin Mahe” za ka sa kan ka a waye,

 Haka “Tandu” da ‘n’ kawai zai tai raye,

Ba “Gonam Bashar” ba, kai dai ka kiyaye,

Sa “Gonan Bashar” ka zan mai ganewa.

 

146. Lura da kyau a ko’ina aka ɗaure ‘n’,

 Ba a cire ta, ba a sa ‘m’, sai dai ‘n’,

 Ita ce ƙa’ida a kauce a yi ɓarna,

 Naso ɗai ka sa a kore sautin ‘n’

  Za ta fito da kanta ba ta nashewa.[1] Dandin Mahe wata gunduma ce da ke ƙaramar hukumar Yabo a jahar Sakkwato a Nijeriya.

Post a Comment

0 Comments