Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
Ɗaurin Harafin ‘M’ a Rubutu
124. Ya zama wajibi a sa ma ga rubutu,
In ta doshi sautuka leɓantattu,
Ko an karya ƙa’ida nan ga karatu,
In ‘m’ ta shigo a tsari na rubutu,
Ba wasali gare ta mai sa motsawa.
125. Ma’ana ga baƙi, wasal sai kuma ga
ta,
Sannan a gabanta ba wasal don ta da ta,
Kalmar tambaya muna
da misalinta,
In ta zo hakan ga to an ɗaure ta,
Ba motsi gare ta balle walawa.
126. Bayan ɗaurin baƙi yakan zo gaba sannan,
Sai a kula baƙin da zai zo gaba ke
nan,
Don dokar da ke hawan
kan shi
wannan,
Wato baƙin da ab
biye dai ke nan,
Wanda ka bi wa ‘m’ ga
kalmar zanawa.
127. In sautin baleɓe ne ba wani can ba,
‘M’
ke bin sa kar a sa wani ba ‘m’ ba,
Leɓawa a sautukan
Hausa ku duba,
In ya zamto ‘f’ walau ‘m’ koko ‘b’,
Ko ya zamto ‘ɓ’ ka zan mai ganewa.
128. Dukkanninsu su huɗun nan ka fahimta,
Leɓawa suke ga tsari na
mafurta,
In sautin gabansu leɓe ka rubuta,
In haka ne aboki ‘m’ za a rubuta,
Ba a rubuta ‘n’ wurin ko farawa.
129. Duba misalansu bi da bi za mu gaya ma,
Kalmomin ga ko ina an ɗaure ‘m(a)’,
Ka ga su jimɓiri da jamfa
da su hamma,
Kalmar tambaya da famfo ko gwamma,
Ko yumɓu kake buƙatar zanawa.
130. Ga dambu, gumba babu kalmar ‘danƙo’,
Ga gambu da Gambo
babu ‘m’ kalmar ‘sanƙo’,
In an lura ɗanƙo ba baleɓe har
sanƙo,
Ga tumfafiya da tambo jambaƙo,
Ga Ɗambatta, Ɗambala ƙara kulawa.
131. Damɓa da Malumfashi duk ba su kauce
ba,
Dambuwa, Dambo, dambala
ba reni ba,
Damben Ɗanbala a sada shi da temba,
Ɗamba, Dambazau
da Ɗambar
Ɗambaba,
Dumfaman ga dambalallen
Hausawa.
132. Kadan mun duba
kana mun ka fahimtu,
Baleɓen duk da yat taho nan ga rubutu,
To ba a sanya ‘n’ gabaninsa rubutu,
Duk dangin baƙi gidan leɓantattu,
In ‘n’ ta biyo su ‘m’ za ta zamowa.
133. Nan ne ƙa’ida na ‘m’ za mu taƙaita,
Kun ji abin da
malamai sun ka hukunta,
Sai mu bi ƙa’idar ga kar ko mu
sake ta,
In mun zo cikin rubutu
mu rubuta
Saɓaninsa malamai na sokewa.
134. Ba a rubuta ‘n’
wurin duk a kiyaye,
Ko ka ji kamar da ‘n’
a gurbin sanye,
Kai dai ka bi
ƙa’idar
kurum don ka kiyaye,
Kar da ka saɓa ƙa’ida ko ka yi
tauye,
Daina kula da yadda sauti ka fitowa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.