Ticker

6/recent/ticker-posts

Alamun Tashin Alkƙiyama

Alamun Tashin Alkiyama

1.
Kullum alamu
nuni suke duniyar 
nan ta zo k'arshe.

2.
Yau yaƙi a nan
gobe girgiza ƙasa
can harshen wuta.

3.
Ba rana ɗaya
da za ta zo ta wuce
ace ba "Wayyo!"

4.
Fad'in Manzo ne (SAWS)
Ba za a yi tashin ta 
ba sai an busa.

5.
Kafin nan fa 
sai an yi auren jinsi
Zina ta fantsu.

6. 
Kwanaki su yi 
ta gudu wal Juma'a
zuwa Juma'a.

7.
A tafka kisa
Mai kisan bai da dalil
Gawar ma haka.

8.
Dajjal zai wanzu
Al-jannarsa duniya
Bi shi ka samu.

9.
Imaninka rau
kamar garwashin wuta
a tafin hannu.

10.
Adabi birjik
Ko'ina in ka duba
har Yanar gizo.

11.
Hoto, majigi
kai dai sayi damarka
Yalo ko d'ata.

12.
Rahayil aini
Idonka ya ganema
kunne jiye mas.

13.
Cututtuka fa?!
Sabbi fil da babu su
sanin iyaye.

14.
Tafiyar wata
a yini na kwana a
k'iftawar ido.

15.
Tafiya ake
Ba tsari babu tsaro
Shugabannin "now".

16.
Rana ta fito
ta yamma k'arshen tuba
In ka sha ka sha.

17.
Karambatan ku 
Musulmi da Yahudu 
Babu makawa.

18.
Nasara taku
Alkawarin Allaah ne
Ba Ya sa6awa.

19.
Zuwan Annabi
Isa (AS) ya kar alade
Haramta jizya

20.
Zuwan Mahadi
na cikin alamomin
Yajuj wa Majuj

21.
Allaah Ya ba mu
sa'a da rabo Ya sa
mu wanye lafiya.

From the Archive of:

Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +2348067062960

©2023 Tijjani M. M.


Post a Comment

0 Comments