Ticker

6/recent/ticker-posts

Satar Fasaha Na Daga Cikin Hanyoyi Samar Da Cigaba Ga Al'uma

Satar Fasaha Na Daga Cikin Hanyoyi Samar Da Cigaba Ga Al'uma

Da yawa muna manta cewa shi fa amfanin ilimi aiki da shi.

Tambaya anan ita ce anya muna aiki da ilimin da muke samu kuwa? Me muke yi na daban bayan mun samu ilimi ko ƙarinsa in an gwada da sanda ba mu da shi ko ba mu da wata sabuwar fahimta daga ilimin da muka ƙara? Sau da yawa ni dai ban gani ba.

Gaskiya akwai tawaya a yadda muke sarrafa ilimin da muke samu. Wasu gani suke samun aiki a dinga biyansu albashi duk wata su ci su sha da su da matansu da y'ay'ansu shi ne mutum ya amfana da iliminsa.

E haka ne amma cimma hakan ai shi ne mafi ƙanƙantar moruwar dake tattare da samun ilimi. Sai dai me mutum ya amfanar da al'umarsa daga sauyin tunanin da iliminsa ya samar shi ne haƙiƙanin amfanin samun ilimi. Amma da yawa ba haka ba ne a gurin su.

Shin wane sauyi ko ci gaba ka kawowa mutanen gidanku layinku unguwarku karamar hukumarku jiharku shiyarku ƙasarku nahiyarku da ma duniya baki ɗaya dalilin samun iliminka? Wannan shi ya kamata kowa ya tambayi kansa.

Na ga kowa ya je makaranta ya samo ilimi mafi akasari maimakon ƙanƙan da kai sai ka ga ƙaruwar ilimin ta sa shi ɗagawa, girman kai, raina duk wanda ya fi yawan ilimi ko da kuwa iyayensa ne. Wannan kuwa ba ga ɗaliban ilimin boko ba ba ga na addini ba.

Ilimi kullum neman sa ake kuma samunsa ake sannan lokaci lokaci ka ji an gano wasu sabbin abubuwa, salo da haske akan wani abun da aka sani da. Amma ka ga mai ilimi ya ce ga wata sabuwar hanya mafi sauƙi na yadda ake yi ko ƙirƙirar wani abu, hmmm ba dai mu ba.

Ku lura da kyau daidai da allurar ɗinki su tsinken sakace ko yadda ake ƙirƙira ko gyara wata na'ura in ta lalace ta fi da kyau, aiki ko ƙarƙo ba za ka ga masu iliminmu sun kawo ire-iren waɗannan sauye-sauye a rayuwar al'uma ba.

Yanzu mu ɗau misalin mulkin damokaradiya da muke amfani da shi wajen za6an shuwagabanninmu. Da yawa fa an gano cewa ba hanya ba ce da take fidda mana waɗanda suka fi dacewa su riƙi ragamar gudanar da al'amuranmu suke mulkan mu ba.

Amma masu ilimin sani halayar ɗan Adam, zamantakewarsa, siyasa, shugabanci, addini da dai sauransu kowa yawo da tunkaho yake da tarin sanin akansa amma babu wanda yake neman yadda za ayi a ɗora al'umarmu akan tafarki madaidaici a cikinsu. Ko meye amfanin iliminsu? Amma fa ban da malamai su kam sai son barka.

To in muka waiwayi komai dake faruwa a ƙasar nan tamu Najeriya a kowanne fannin rayuwa abin da yake faruwa ke nan. Mafi yawancinmu kowa ya ajiye saninsa a gefe ya zama ɗan amshin shata. Babu wanda za ka ga yana amfani da iliminsa a fannin da ya dace don kawo sauyi a rayuwar al'umarmu.

Yanzu tsakani da Allaah meye bambancin masu iliminmu da waɗanda ba su da shi? Sai ka rasa dalilin da zai sa ilimi ya sauya maka tunani, kaifin basira, iya tsari, hangen nesa, matsayi, ɗaukaka da dai sauransu amma sai mutum ya ƙare a neman aikin da za a dinga biyansa albashi duk wata.

Alhali mai ilimin nan ba ƙaramin ci gaba da sauyi mai fa'ida da ingancin rayuwa zai iya kawowa ba sanadiyar samun ilimin nan na shi. Maimakon kowa ya duba ya ga shin da me da mene ne mutane ke buƙata a rayuwarmu ta yau da kullum da ba mu da shi ya samar?

Sai mutum ya kalubalanci kansa ya duƙufa shi kaɗai ko shi da wasu su samar da abin mutane su saya su amfana daga nan su sayarwa makwabta ba a gida kawai ba har ma a ƙasar waje. Aamma ina! Sai ka ga mai ilimi ya shekara wajen biyar wai yana jiran a ɗauke shi aikin duk wata a biya shi albashi.

Sannan wasu na mamakin yadda ake ƙirƙiro abubuwa, na'urori, salon yin abubuwa da gudanar da su su rasa ta wace hanya ake bi? To ai ba komai ake yi ba illa satar fasaha bacin an gudanar da bincike akan duk wani abu da ake so a yi ko a samar.

Samun abu ake yi a bi shi kurfakurfa a yi masa fillafilla a fahimci amfanin kowane bangaren sa sannan, a nemi da me ake yin fannoninsa da in har aka haɗa su za su gudanar da aikin da na'urar take yi. In an tabbatar da samar da ita sai a nemi inganta ta daga bisani a sa mata suna da kuma "Made in Nigeria" Shi ke nan 😄

Yadda ake amfani da ilimi ko masaniya ke nan a ci da al'uma gaba.

From the Archive of:

Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +2348067062960

©2023 Tijjani M. M.

Post a Comment

0 Comments