Assalam alaikum. Gaisuwa gare mu marubuta da makaranta da duk wasu ma'abota harkar adabi.
Na san da yawa an sanni da rubutu na zube da waƙe har da zaurancen Haiku cikin harsunan Hausa da Turanci. Sai dai ba a sanni da rubutu na wasan kwaikwayo (dirama ko film script) ba.
Abin dake faruwa ko in ce abin da ya faru shi ne tun farko ni a gaskiya ban
so harkar fim ba duk da shi ke na ta6a zuwa na yi gwajin a sa ni cikin wata
dirama da fitaccen marigayin furodusan nan Tijjani Ahmad na CTV ya gaiyace in
zo a yi da ni a tashar wajen 1990 ne ina jin.
A gaskiya gwajin da na yi wato auditioning ya kar6u inda nan take aka kaure
da tafi bacin na gama nuna irin kwaikwayon wanda zan zama a diramar wato wani
ne mahaifinsa ya rasu ya bar masa ƙanne maza da mata wanda hakan ta sa dole ya
daina karatun boko ya koma dawainiyar gidansu.
Sai dai a gaskiya ban sake komawa cikin 'yan diramar (cast) ba. Don kamar
yadda na ce da farko ne fim ba ya daga cikin abubuwan da na so in dinga yi a
midiya. Shi ne kawai na koma harkata ta gidan radio.
Dalilin da ya sa nake kawo muku wannan zance da kuma tarihi shi ne akwai
dirama sikirif da na ta6a rubutawa wajen 1990 koma kafin nan da na tsinto a
cikin rumbun ajiyata da zan so wasu ƙwararru a harkar fim irin su Ado Ahmad
Gidan Dabino, Anas Bala Babinlata, Fauziyya D. Sulaiman da dai ire-irensu su
karanta mu ji me za su ce akai.
Kamar yadda ku ka gani a sama taken wasan kwaikwayon shi ne 'YAR DAMISA
kuma na ƙudiri niyyar in kawo rubutun nan don na tabbata ba za a rasa waɗanda
za su so su karanta shi ba. Sannan za a d'auki darussa daga cikin labarin. Ban
da nunawa y'an baya yadda rayuwa take a da wajen shekaru 30 baya.
Sai ku kasance tare da bangona na Facebook, WhatsApp, Instagram don bibiyar
wannan labari ta sigar salon rubutu na dirama da da yawa ba kasafai za ka ga
marubutw na amfani da shi ba wajen ilimantarwa, faɗakarwa, wa'azantarwa,
nishad'antarwa da dai sauransu.
Sai kuma don Allaah a kiyayi haƙƙin mallaka don ba zan lamunci satar fasaha
ba. Ku biyo ni mu je - Shafi Na Farko
From the Archive of:
Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +2348067062960
©2023 Tijjani M. M.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.