Kundin neman digiri na farko (b.a. Hausa) a ƙarƙashin sashen nazarin harsuna da al’adu, jimi’ar tarayya gusau, jihar zamfara, nigeria, AUGUSTA, 2023
ALH. ABDU ƊANGUNDUWA KAGARA DA WAƙOƙINSA
NA
BABANGIDA AHMAD BARAU
TABBATARWA
Na tabba cewa, ni na rubuta wannan kudin bincike da kaina mai
suna, ALH. ABDU ƊANGUNDUWA KAGARA DA WAƙOƙINSA . A karkashin
jagorancin Dr. Musa Fadama Gummi. Duk bayanan da aka samo daga wata madogara to
an Ambato madogarar a cikin matani da kuma manazarta, da aka ratayo. Babu wani
sashe na wannan da aka water a wani wuri a matsayin kundin Digiri ko Diploma a
cikin mujallu,
AMINCEWA
An amince da wannan
kundin bimcike naBabangida Ahmad
Barau (1710104008) a kan cewa, ya cika duk ƙa’idojin kammalawa da aka shimfiɗa dangane da neman
takardar kammala digiri na farko (B.A. HAUSA) a Sashen Nazarin Harsuna da
Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan
kundi ga iyayena wato Malam Barau Abubakar da Mahaifiyata Malama Nana Firdausi
Barau Abubakar Kagara.
GODIYA
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai. Tsira da mincinSa su ƙara tabbata ga shugaban halitta manzon tsira
Annabi Muhammadu (SAW) da
iyalansa da sahabbansa. Ina ƙara gode wa Ubangiji (SWT) da ya ba ni damar
kammala wannan kundi cikin nasara.
ALHAMDULILLAH!
Bayan haka ina miƙa godiya ta musamman ga jagoran wannan aikin,
watau Dr. Musa Fadama Gummi a kan namijin ƙoƙarin da ya
yi duk da tarin ayyuka da suke gabansa amma kuma ya jajirce wajen ganin cewa,
aikin ya samu kammaluwa cikin nasara da kuma irin ingancin da ake buƙata aikin ya samu. Allah ya saka masa da
mafificin alhkairinsa. Amin.
Bayan haka, ina miƙa godiyata ga ilahirin Malaman Jami’ar Tarayya, Gusau musamman waɗanda suke a Sashen
Nazarin Harsuna da Al’adu. Ina jinjina musu a kan ƙoƙarin da suka
yi na ganin cewa, mun samu tarbiyya da ilimi ingantacce kuma nagartacce. Waɗannan Malaman kuwa su ne
kamar haka: Prof. Aliyu Muhammad Bunza da Prof. Magaji Tsoho Yakawada da Prof.
Muhammad Lawal Amin da Prof. Dumfawa Atiku da Prof. Ɗantumbishi Muhammad da Dr. Nazir Abbas Ibrahim da Dr. Adamu Rabi’u
Bakura da Dr. Musa Fadama Gummi da Dr. Tahir Rabi’u Muhammad, da Malam Aliyu
Rabi’u Ɗangulbi da
Malam Musa Abdullahi da Malam Isa Sarkin Fada da Abu-ubaida Sani da Malam
Muhammad Arabi da Malam Bashir Abdullahi da Malama Halima Kurawa. Da sauran
ma’aikatan sashen Nazarin Harsuna da Al’adu na Jami’ar Tarayya Gusau. Ina
godiya ga kowa da kowa.
Haka kuma, ina godiya ga Malam Barau Abubakar da Mahaifiyata
Malama Nana Firdausi Barau Abubakar Kagara. a kan goyon bayansu a gare ni da
addu’oinsu da taimakonsu a kan dukkan abubuwan da ya shafi rayuwata, haƙiƙa ina matuƙar godiya, Allah ya saka musu da alheri. Bayan haka, ina godiya ga
yan uwana musamman Dr. Lawal Musa Kagara da Malan Abubakar Sani Kagara da Hon.
Sani Barau sa Shuaibu Barau Kagara ganin irin kulawar da suka bani ta hanrar
shawarwari da abin hannunsu domin ganin wanannan yayi nasara. Haka kuma bazan
taba mantawa da malan Danlami A Garba Morai shima duk da yana sashen Faransanci
amma ya taka rawar gani ga gudum muwa da yake bahaushe ne mai kishin Harshen
Hausa bias ga haka yayi daka domin ganin cewa ya taimaka.
Tsakure
Wannan kundi na bincike ya kunshi ma’anar waƙa ire-iren waƙa, Tarihin
Alh. Abdu Ɗangunduwa Kagara da yadda ya fara
koyon waƙoƙkinsa da kuma yadda yake shirya waƙoƙinsa da kuma
nau’oin waƙoƙkinsa da
kayan da yake amfani dasu da kuma wasu daga cikin waƙoƙinsa.
KUNSHIYA
Tabbatarwa- - - - -ii
Amincewa- - - - -iii
Sadaukarwa- - - - -iv
Godiya- - - - -v
Tsakure- - - - -vii
Kunshiya- - - - -viii
BABI NA DAYA
GABATARWA
1.0
Shinfiɗa-
- - - --1
1.1. Manufar Bincike- - - --2
1.2. Hasashen
Bincike- - - --3
1.3. Farfajiyar
Bincike- - - --3
1.4. Matsalolin
Bincike- - - --4
1.5. Muhimmancin Bincike- - - -5
1.6. Hanyoyin Gudanar Da Bincike- - --5
1.7. Nadewa- - - - -6
BABI
NA BIYU
BITAR
AYUKKAN DA SU KA GABATA
2.0 . Shinfiɗa- - - - --7
2.1. Bitar ayukkan da suka gabata-
- --7
2.1.1. Bugaggun Littafai- - - --8
2.1.2. Kundayen Bincike- - - 10
2.2.Hujjar cigaba
da bincike- - - 16
2.3. Naɗewa- - - - -16
BABI NA UKU
FASHIN
BAKI A KAN MA’ANONIN DA SUKA SHAFI TAKEN BINCIKE
3.0. Shinfiɗa- - - - -17
3.1. Ma’anar waƙa- - - - 17
3.2. Ire – Iren waƙoƙin baka- - - 20
3.2.1.Waƙoƙin Baka Na Yara- - - 20
3.2.2. Waƙoƙin Baka Na manyan
Mata - - -21
3.2.3. Waƙoƙin Yara Maza- - - -21
3.2.4. Waƙoƙin ‘Yan Mata- - - -22
3.2.5 Waƙoƙin Daka - - - -23
3.2.6. Waƙoƙin Reno- - - -24
3.2.7 Waƙoƙin Daɓe-
- - -25
3.2.8 Waƙoƙin nika - - - -25
3.2.9 Waƙoƙin Talla- - - -26
3.2.10 Waƙoƙin Baka Na Cikin Labarai Da Tatsuniyoyi- 27
3.2.11 Waƙoƙin Baka Masu Tafiya Da kaɗe-kaɗe- -27
3.2.12 Waƙoƙin Jama’a- - - -28
3.2.13 Waƙoƙin Maza- - - -28
3.2.14 Waƙoƙin Sana’a- - - -29
3.2.15 Waƙoƙin Fada- - - -29
3.2.16 Waƙoƙin Bandariya- - - 30
3.2.17 Waƙoƙin Sha’awa- - - -30
3.3 Nazarin Waƙar Baka- - - 31
3.3.1. Hanyar Nazarin Waƙar Baka- - -31
3.3.2. Salsalar Waƙa- - - -32
3.3.3. Shekarar Da Makaɗi Ya Fara Waƙar- - 32
3.3.4. Yawan Ɗiya a Waƙa - - - 33
3.3.5. Tarihin Makaɗi a Taƙaice- - - 33
3.3.6. Bayanin Wanda Aka Yi Wa Waƙa- - -33
3.3.7. Turke Da Warwaransa- - - 34
3.3.7.1. Muhallin Turke- - - -34
3.3.7.2. Taƙaita Turke (Turke a gajarce) - - 34
3.3.7.3. Warwara Da Tsattsefewar Turke-
- 35
3.3.7.4. Tubalan Ginin Turke- - - 36
3.3.8. Awon Baka- - - - 36
3.3.9. Yawan Layuka A Ɗa- - - -37
3.3.10. Tsarin ɗan waƙa- - - -38
3.3.11. Tsarin Rerawa- - - -39
3.3.12. Takiɗi a ɗiyan
waƙa- - -
40
3.3.13. Ƙarin Murya - - - -41
3.3.14. Amsa Amon Kari- - - -41
3.3.14.1. Gidan Dara Na Kari- - - 41
3.3.15. Salon Sarrafawa Da Adon Harshe-
- 42
3.3.16. Adon harshe- - - -43
3.3.17. Zaɓen Kalmomi- - - -43
3.3.18. Karin Harshen Waƙa- - - 44
3.2.19. Gini Jimla Da
Tsarinta - - -45
3.3.
Naɗewa- - - --45
BABI NA HUDU
ABDULLAHI DANGUNDUWA KAGARA DA WAKOKINSA
4.0.
Shinfiɗa- - - - -46
4.1. Taƙaitaccen tarihin Alhaji Abdullahi Dangunduwa
Kagara-47
4.1.1. Ƙurciyarsa da Tasowarsa da
Neman Iliminsa- -48
4.1.2. Koyo da fara waƙoƙinsa- - --49
4.1.3 Yaransa- - - --52
4.1.4. Yawace - yawacansa-
- --53
4.1.5. Shirya Waƙoƙinsa- - - -54
4.1.6. Kayan kiɗansa- - - -56
4.1.7 Nau’oin waƙoƙinsa- - - -58
4.1.8. Rasuwarsa- - - --62
4.2. Matsayin Alhaji
Abdullahi Dangunduwa Kagara a Tsakanin Mawaƙan Da da Na Yanzu- - - --63
4.3.
Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa- - -64
4.4.
Nazarin waƙoƙinsa- - - -65
4.4.1.
Turken Waƙoƙinsa- - - -65
4.4.2. Zubi da Tsari waƙoƙinsa- - --68
4.4.3. Turken waƙoƙinsa- - - -70
4..4.4. Warwarar Turke- - - -72
4.4.5. Salon Sarrafa Harshe-
- --82
4.4.6. Salon Amshi- - - --87
4.4.7. Zubi Da Tsarin waƙoƙinsa- - - 90
4.5. Naɗewa. - - -
- 92
BABI NA BIYAR
SAKAMAKON
BINCIKE
5.0.Shinfiɗa- - - - 93
5.1. Sakamakon Bincike- - - 93
5.2. Shawarwari- - - - 95
5.3. Naɗewa- - - - -96
Mazarta - - - - -98
BABI NA DAYA
Nazari bisa ayyukkan adabin Hausa ya ginu ne ta hanyar yin tsokaci da
tarke da fiɗa don a fito da armashi ko rashin armashin abin da ake
nazari a kai. Nazari ne wanda yake duba adabi ta fuskar lugga da nahawu da
yadda aka sarrafa harshe a cikinsa,
da balaga da hikima. Haka kuma da fito da yadda halin zamantakewa da tattalin
arziki da sha’anin addini da siyasa na al’umma suke ƙunshe a cikinsa da sauran manufifi da dangogin hikimomin da
aka ɗora shi a kansu.
Wannan binciken ya
waiwayi wasu daga cikin waƙoƙin Alhaji
Abdullahi Ɗangunduwa Kagara domin ya ba da
haske da jagora ga fahimtar irin gudunmawa ta fasaha da hikima wadda Alh.
Abdullahi Ɗangunduwa Kagara ya bayar don bunƙasa adabin Hausa. An yi ƙoƙari a ruwaito wasu daga cikin waƙoƙinsa, bisa taƙaitawa domin
a yi nazarin su. Acikin aikin an zo da aƙalla waƙoƙi daban – daban guda uku kamar yadda muka
faɗa cewa wasu daga ciki. Domin haka ne aka laƙaba wa kundin sunan Nazarin Wasu Daga Cikin Waƙoƙin Alh.
Abdullahi Ɗangunduwa Kagara. Kusan a iya cewa wannan kundin
yana daga cikin kundayen da za su iya taimakawa ɗalibbai da ma
su shawar nazarin adabin Hausa.
Shi dai wannan aiki ya zama fitila ne kawai, domin haka, ina kira ga
dilibbai yan’uwana da masu shawar ganin harhsen Hausa ya ci gaba da mu tashi
tsaye, mu daɗa kyautace wannan nazari.
Manufar
wannan bincike ita ce samar da wani kundi da zai gano jigogi da salailai na wasu daga cikin waƙoƙin Alh.
Abdullahi Ɗangunduwa Kagara, tare da zayyana irin rawar da waƙoƙinsa ke takawa cikin, adabin Hausa. Nazari a kan waƙoƙin Noma ko kaɗan
ba su kama ƙafar
sauran takwarorinsu na waƙa ba, misali waƙoƙin sarauta wadanda har zuwa yau akwai masu ƙoƙarin nazari da bincike a kan wani abu daga cikinsu domin bunƙasa su, wannan dole, shi ya sa muka ga ya dace mu yi wani ƙwaƙƙwarar nazari a kan
wasu daga cikin waƙoƙin Alh. Abdullahi Ɗangunduwa Kagara, gwargwadon ikonmu. Bayan haka tabbas manufar wannan
bincike ita ce taimakawa wajen raya adabin Hausa, da kuma bar ma na baya tarihi
da abin koyi da ƙara
harzuƙa su
dan su tashi tsaye gadan-gadan domin ganin anci gaba da raya wannan adabi na
Hausa.
Muna hasashen cewa, idan wannan aiki na bincike ya samu
kammaluwa zai taimaka wajen haɓaka
da raya harshen Hausa, dan haka ya sa mu muka zaɓi rubuta kundinmu game da nazari a kan wasu daga cikin waƙoƙin Alh.
Abdullahi Ɗangunduwa Kagara. Domin waƙoƙin Hausa na da muhimmanci ƙwarai ga rayuwar Hausawa. Waƙa ta baka ko rubutacciya, kamar yadda muka sani tun ba yau
ba, ita ce hanya mafi sauƙi da ake bi wajen isar da saƙo ga Jama’a.
A ƙarshe, muna hasashen bincikenmu zai ba mu damar cika ƙa’idoji da a ka gindaya
na neman takardar shaidar digiri (B.A. HAUSA) asashen Nazarin Harsuna da
Al’adu, Jami’ar Tarayya, Gusau.
Aikin binciken da za a gudanar ya
shafi waƙoƙin baka na makaɗan Hausa. Saboda haka za a yi nazari
ne a kan wasu daga cikin waƙoƙin Alh. Abdullahi Ɗangunduwa
Kagara daga farko har
karshen aikin.
Haka kuma, aikin
zai tsaya a farfajiyar jigogi da salai-lai waƙoƙinsa. Haka binciken zai zaƙulo
Taƙaitaccen tarihin da kuma yadda
yagudanar da rayuwar Alh. Abdullahi Dangunduwa Kagara, musamrnan yadda
ya koyi sana’arsa ta waƙa da ire - iren
waƙoƙinsa. Duk
da kasancewar aiki zai gudana a fannin wasu waƙoƙinsa.na noma da kuma sarauta.
Kamar yadda aka sani
cewa babu wani aiki da za a gudanar ba tare da an ci karo da matsaloli ba nan
da can, musamman a kan aikin bincike.
Abdullahi Dangunduwa Kagara, ya yi fice a kan kawo cigaban harshen
Hausa ta fannin adabin baka. Manazarta da masu bincike a kan harshen Hausa ba su
mayar da hankali ba wajen bincike ko nazari a kan Abdullahi Dangunduwa Kagara da waƙoƙinsa. Kuma ko da an yi ba su yi yawa
ba. Wannan ya sa na ci karo da matsaloli daban – daban a kan wannan binciken.
Ganin irin matsalolin da na fuskanta
wajen wannan bincike, ya ƙara ba ni ƙarfin guiwa ganin
cewa manazarta ba su yi yawa ba wnnan fagen binciken. Dan haka wannan aikin zai taimakama na tafe masu sha’awar nazari a kan Alh.Abdullahi Dangunduwa Kagara da waƙoƙinsa.
1.5. Muhimmancin Bincike
Muhimmancin
bincike shi ne zai daɗa
fitowa tare da zaƙulo
hikimomi da ke cikin waƙoƙin baka na Hausa. Ba wannan kaɗai ba, aikin zai daɗa faɗaɗa ayyuka adabi a matsayinsa na madubin al’umma. Aiki
binciken zai taimaka wajen adanawa da kare waɗannan waƙoƙi masu ɗauke
da tarin hikimomi daga salwanta, Salwantarsu kuwa ba ƙaramar hasara ba ce ga harshen da ma al’umma ta Hausawa.
Dalili kuwa shi ne cewa waƙoƙin Alh. Abdullahi Dangunduwa Kagara, wani babban madubi ne
na kallon rayuwar Hausawa.
1.6. Hanyoyin
Gudanar Da Bincike
Hanyoyin da aka bi don gudanar da wannan bincike su ne :-
1. Ganawa da tattaunawa da abokan sana’arsa ido-da- ido mai suna
Hussaini Ɗanbaraka a Kagara
2. Haka kuma kamar hira da mukayi da wani yaron Alh. Abdullahi Dangunduwa Kagara da ake
kira Bashar Maidaura Kagara 085/02/2023 a gidansa da ke garin Kagara.
3. Sa’annan kuma an
gana da wani yaronsa kuma mai yi ma sa banbaɗanci mai suna Namaimuna 06/3/2023.
4. da kuma hirar da muka yi da Babban ɗansa wanda ya gade shi 27/3/2023.
Wannan
babi wanda shine na farko a cikin tsarin wannan aiki an kawo abubuwa da dama
wanda suke sune muhimman bayanai na shimfiɗa. Da farko an kawo gabatarwa da Shinfiɗa,
Manufar Bincike, Hasashen Bincike, Farfajiyar Bincike, Matsalolin Bincike,
Muhimmancin Bincike, Hanyoyin Gudanar Da Bincike da kuma Naɗewa.
BABI NA BIYU
Wannan babi ya bibiyi
tarahin irin wannan nazarin ko kuma mai kama da shi wanda aka aiwatar domin
raya adabin Hausa dangane da lokutta daban – daban. Wannan babi wanda shi ne na
biyu a cikin tsarin wannan aiki za mu
kawo abubuwa wanda suke sune muhimman bayanai kamar haka ; Shinfiɗa bitar ayukkan da su
ka gabata, hujjar cigaba da bincike, da kuma naɗewa.
2.1. Bitar ayukkan
da suka gabata
Hausawa na cewa
“waiwaye adon tafiya” duk aikin da za a yi, ya kamata a yi bitar ayyukan masana
da manazarta da su ke da alaƙa da wannan aiki ko
su ka yi kama da shi, da nuna hanyar da su ku bambanta da wannan aiki. An
nazarci kundaye, mujallu da kuma littattafai. Ayyukan da aka nazarta waɗanda ke da nasaba ko
alaƙa da wannan aiki su
ne:-
2.1.1. Bugaggun
Littafai
Akwai wallafaffun
littafai da dama masu alaƙa da wannan bincike waɗanda masana da manazarta da dama suka yi a baya. Daga cikin littatafan akwai:-
Yahaya, (2001: 289) a
littafinsa mai suna “Salo Asirin waƙa” ya yi bayanin ma’anar salo a cikin waƙa. Sannan kuma ya bayyana muhimmancin salo, bayan wannan kuma
ya yi bayani kan sauran dabarun sarrafa
harshe kamar, Jinsarwa, kamance, kinaya, zayyana da makamantansu. Wannan aiki
na da dangantaka da nawa, sakamakon salo da za a kalla a cikin waƙoƙin Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara da kuma kawo ma’anar shi
salon.
Bunza, (2009:45) a
Lttafinsa mai suna “Narambaɗa” ya kawo tarihin Narambaɗa da ƙoƙarinsa, da fito da
ma’anar Salo da ire – irensa. Da sauran abubuwan da ake iya samu cikin waƙa.
Wannan aiki yana da alaƙa da nawa duk da cewa
kan Narambaɗa aka yi shi, amma
tun da an kalli salo da ma’anarsa to ya na da alaƙa da nawa sosai da
sosai saboda ya kawo tarihin Narambaɗa da ƙoƙarinsa, sai dai ni a
kan nazarin wasu daga
cikin waƙoƙin Alh. Abdullahi Ɗangunduwa Kagara aikina zai gudana.
Gusau, S.M. (1986 16)
Ya rubuta littafi mai suna “Jagoran Nazarin waƙar baka”. A cikin littafin
marubucin ya yi tsokaci a kan abubuwa da dama musamman waƙoƙin baka na gargajiya.
Marubucin ya tattauna sosai da sosai a kan ire – iren waƙoƙin baka kuma ya yi ƙoƙarin rarrabe su zuwa
rukuni – rukuni inda ya kai
kowane kaso a cikin rukunin da ya fi dacewa da shi. Ya tattauna a kan ma’anar
waƙar baka, da karani da dai sauransu. Saboda haka, littafinsa da
wannan kundin bincike suna da aalƙa da juna kasancewar su duka bangaren
waƙoƙin baka na Hausa.
Gusau, S.M. (2009:
285) Ya rubuta littafi mai suna “Diwanin waƙoƙin baka,” zaɓaɓɓun matanonin na waƙoƙin makaɗan baka na Hausa. Alaƙar wannan littafin da wannan
kundinbincike ita ce dukkansu sun shafi waƙoƙin baka na Hausa.
Gusau ya yi akan waƙoƙin baka na Hausa na
maza da matagaba ɗaya shi kuma wannan
binciken ya shafi waƙoƙin maza ne kawai kuma
ko a maza ya shafi waƙoƙin Alh. Abdullahi
Dangunduwa Kagara ne kawai.
Gusau, S. M. (1995:
7) Ya rubuta littafi mai suna “Dubarun Nazarin Adabin Baka,” Shi wannan littafi
ya waiwaiyi sassan hanyoyi da dubarun nazarin adabin Hausa daga makarantunsu
mabanbanta ya fito da su a dunƙule don ya ba da haske da jagora ga
fahimtar manyan matakan nazarin adabin baka na Hausa.Musamman ga ma su nazarin
waƙoƙin makaɗan baka na Hausa. Alaƙar wannan littafin da wannan kundin bincike
ita ce dukkansu sun shafi waƙoƙin baka na Hausa. Wannan binciken nawa
ya shafi wasu daga cikin waƙoƙin Alh. Abdullahi Dangunduwa Kagara .
2.1.2.
Kundayen Bincike
Mashi, (1982:32) A cikin kundin bincikensa na digiri na
farko mai suna “Gudummuwar Hajiya Barmani Coge Mai Amada ga adabin Hausa” wanda
aka gabatar a sashen fasaha da nazarin Al’amuran Musulunci, jami’ar Bayero,
Kano.
Ya yi bayani sosai a kan irin gudummuwar da Barmani Coge ta
bayar a wajen bunƙasa
adabi da harshen Hausa. Kundin bincikensa yana da alaƙa ta kusa da wannan kundin binciken ta fuskar waƙoƙin baka na Hausa. Mashi, ya yi a kan ɗaya daga cikin mata mawaƙan baka na Hausa wato mawaƙiya Sa’adatu Barmani Coge. A wannan kundin binciken kuma, an yi shi
ne a kan Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara. Don haka suna da alaƙa da juna kasancewar dukkan su an yi
nazari ne a kan mawaƙan baka na Hausa.
Hadiza, (2007: 41) A cikin kundin bincikinta na neman digiri
na farko mai suna “Waƙoƙi a Kan Mata” A cikin wannan kundin binciken, ta yi bayani
cewa mata su ne suka fi yin amfani da waƙa domin isar da saƙo ko kuma domin nishaɗantatwa a tsakaninsu a cikin aikin nata ta bayyana ma’anar
waƙar
baka da ire- iren waƙoƙin baka na Hausa. Haka ta yi bayanin ire-iren mawaƙa inda ta nuna cewa a cikin mata akwai
waɗanda suka shahara wajen isar da saƙonni a waƙoƙinsu zuwa ga jama’a. Hakazalika ta nuna yadda matsayin mace yake ga Bahaushe
da kuma sharhin wasu daga cikin waƙoƙin mata.
Garba Keku (1992:10) a kundinsa da ya rubuta a kan rayuwar
Salisu Jankidɗi, ya yi tsokaci ne a kan waƙoƙin Salisu Jankiɗi,
a inda aka yi bayanin asalinsa, haihuwarsa, ƙuruciyarsa da kuma tasowarsa, fara waƙarsa da kuma shahararsa. Haka kuma an yi bayani a kan
sarakunan da ya yi zamani da su, da kuma sarautar da Sarkin Musulmi da ya naɗa shi.An kuma bayyana yadda yake shirya waƙoƙinsa tare da matsayin waƙoƙinsa ga wasu sauran waƙoƙi, sannan an yi bayanin shahararsa a wajen kida da kuma
jigon waƙoƙinsa wadanda su ka ƙunshi yabo, zambo, habaici, zuga, da
kirari da kuma salon waƙoƙinsa na mai-maitawa da aron kalmomi.
Shi kuma Alhaji Lawal
Faruku (1997:13) a kundin da ya rubuta a kan “Rayuwar Ƙwazo Bagega da Waƙoƙinsa”, nazarin waƙoƙin Ƙwazo Bagega aka yi, a
inda aka bayyana tarihinsa tun daga haihuwarsa har tsufansa. An bayyana yadda
yake tsara waƙoƙinsa da jigogin waƙoƙinsa da salon waƙoƙinsa ta fuskar sarrafa harshe, daga ƙarshe aka kawo jerin wasu waƙoƙinsa.
Yayin da Abdurrahaman da Ahmad na Baba Tsafe, da Attahiru
Rufai Gwandu (1993:21) a kundinsu da suka rubuta akan rayuwar Sani Sabulu na Kanoma
da waƙoƙinsa a inda aka bayyana tarihinsa tun
daga haihuwarsa har tsufansa, an bayyana yadda yake tsara waƙoƙinsa da jigogin waƙoƙinsa da salon waƙoƙinsa ta fuskar sarrafa harshe. Daga ƙarshe aka kawo jerin wasu hikimominsa
Har ila yau mun dubi
wani kundi na Muhammad Y. Nasarawa da na Muhammad Khalid (1997: 23) mai taken “Nazari
A Kan Alhaji Abdu Inka Bakura da waƙoƙinsa”. Anan ma an bayyana yadda yake tsara sana’arsa ta waƙa da jigogin waƙoƙinsa da salon waƙoƙinsa ta fuskar sarrafa harshe dagaƙkarshe aka yi fashin baki a kan waƙoƙinsa.
Ashiru (2001: 48)
kundin digiri na farko mai taken: “Jigon Kishi A Cikin Rubutattun Waƙoƙin Soyayya” wannan kundi ya yi tsokaci kan kishi da abin da ke
haifar da kishi, tsakanin namiji da mace. Wannan aiki yana da alaa da nawa
domin kishi jigo ne a cikin jigogin soyayya. Bayan haka kuma a waƙoƙin soyayya da za ayi nazari akwai jigon kishi, amma waƙoƙin wanɗanda Sadi Sidi Sharifai ya yi ne.
Saboda haka wannan aiki ya sha bamban da nawa aikin.
Muhammad. (2010:34)
kundi mai taken “Kalaman Cikin Waƙoƙin Soyayya, Gaskiya ko Ruɗi”
An yi wannan aiki ne don neman digirin farko a sashen koyar da Harsunan
Nigeriya Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato. A cikin wannan aikin an yi ƙoƙarin bayyana irin
rawar da marubuta da masu rera waƙoƙin soyayya na Hausa ke takawa, musamman wajen salo a cikin waƙoƙin. Shi ma wannan aiki yana da alaƙa da nawa tun da a
kan wakokin soyayya ya gudana. Amma ni nawa ya sha bamban da shi, saboda a kan
wakokin Alhaji Danbalade da waƙoƙinsa ne na Sarauta, Noma da kuma Dambe. zan yi shi.
Umar, (2011:63) a
cikin kundinsa na neman digirin farko a sashen Harsunan Nigeriya Jami’ar Usmanu
Danfodiyo Sakkwato, mai taken “Salo da Sarrafa harshe a cikin waƙoƙin Ibrahim Aminu Dandago, na Aliyu Magatakarda Wamakko. A
cikin wannan aiki, an yi ƙoƙarin fito da salailai
daban – daban da ma’anar Salo da mahimmancinsa da Sauransu. Shi ma wannan aiki
ya na da alaƙa da nawa ta fuskar salo kawai duk da
cewa shima a kan waƙoƙin wani ya yi. Ni kuma a kan waƙoƙin Sarauta, Noma da Dambe nawa aikin zai gudana, inda za
a kalli jigoginsu da salailansu.
Hamza, (2011:25) a
kundinsa na neman digirin farko a sashen koyar da Harsunan Nigeriya Jami’ar
Usmanu Danfodiyo Sakkwato, mai taken Salo da Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Aminuddeen Ladan Abubakar (ALA). Aikin ya bayyana Salo da
ire – irensa duk a cikin waƙoƙin Ala. Shi ma wannan ya yi tarayya da nawa aikin ta fuskar
salo, sai dai shi wannan a kan waƙoƙin ALA ya gudana, ni kuma nawa a
kan wakokin Alhaji Danbalade Morai zai gudana.
Bisa la’akari da
ayyukan da suka gabata, na kundaye har zuwa littattafai, za a samu cewa ba wani
aiki da ya yi daidai da nawa, saboda an yi wasu ayyuka a kan wasu mawaƙa
daban, ko ma a kan wani abu da ya shafi Soyayya.
Dan haka, ko da akwai
wasu bambance- bambance a tsakanin su, wadannan makaɗa da Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara kaɗan ne, Saboda shi dai makadin ‘yan dambe ne kuma sana’ace ta
maza. Amma Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara yana waƙoƙin. Sarauta da kuma fawa , duk da ya fi ba da ƙarfi ga waƙoƙin noma domin gare su ya yi fice har duniya ta san shi..
Daga ƙarshe mun dubi wadannan ayukka ne domin mu ga yadda magabata
suka gudanar da bincike da kuma abin da bincike ya ƙunsa da irin hanyoyin da ya kamata mai bincike ya bi da kuma
kariyar harshe daga salwanta.
Za
a ci gaba da wannan bincike ne, Sakamakon ba wani aiki da aka taɓa samu wanda aka
aiwatar a kan wannan fasihi, duk da cewa an yi aiki a kan wasu daga cikin waƙoƙinsa , da dama, amma ba a yi a kan Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara ba.Kuma ko da har in
an yi Ni nawa nazarin ya sha bamban da na sauran manazarta.
2.3.
Naɗewa
Wannan babi a cikin
sa ne aka kawo bitar ayukkan da su ka gabata, a inda a ka fara shi da shimfiɗa, a ka yi tsokaci a
kan wasu kundayen kammla karatu da Littafai na magabata, duk a cikinsa ne a ka
kawo hujjar cigaba da wanan binciken, da kuma naɗewa.
BABI
NA UKU
FASHIN BAKI A KAN MA’ANONIN DA SUKA
SHAFI TAKEN BINCIKE
A wannan babi, za a kawo ma’anonin waƙa daga bakin masana
da manazarta kamar yadda suka bayyana raayoyinsu daban-daban dangane da
ma’anar waƙa da
kuma sauran abubuwan da suka shafe ta.
Mawaƙan
baka na Hausa maza da mata suna ba da gagarumar gudunmuwa wajen inganta
harshen, domin yana ɗaya
daga manyan rukunnai na raya al’adu da adabin ko wace al’umma ta duniya.
Saboda haka, daga cikin abubuwan da za a tattauna a wnnan
babin akwai ma’anar waƙa da kuma ire-iren waƙa tare da jawabin naɗewa a ƙarshen babin.
3.1. Ma’anar waƙa
Masana da dama sun yi ayukka
daban-daban sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma’anar waƙar baka ta Hausa da ma rubutacciyar waƙa kaɗan daga cikin su akwai:
Ahmad,
I. M. (1982: 36) acikin nazarinsa na kundin Digiri na biyu wanda ya yi a
Jami’ar Bayero dake Kano, wanda zamu iya cewa duk sun haɗu kan cewa waƙa wata maganar hikima
ce. Tsara ta ake yi, ana zaɓen
kalmomi da za a gina ta da su.
Gusau, S. M. (1984:47) Ya ce “Waƙa wata abu ce da ake shirya maganganu daki-daki cikin azanci
da nuna ƙwarewar
harshe”.
Yahaya, A.B. ( 2001: 56) Ya na cewa “Waƙa ita ce tsararriyar maganar hikima, da
ta ƙunshi
saƙo
cikin zaɓaɓɓin
kalmomi masu azanci, da aka auna don maganar ta reru, ba wai a yi faɗarta ba kawai”.
Dangambo, A (.2017: 54).
“Waƙa wani
salo ne da aka gina shi a kan tsarriyar ƙa’ida ta baiti, ɗango,
rerawa, ƙari,
(bahari), amsa-amo (ƙafiya) da sauran ƙa’idojin da suka shafi dai-daita kalmomi, zaɓaɓɓu da
ake amfani da su cikin jigogin da ba lallai ne haka suke a maganar baka ba.
Umar, (1987: 64) Ya bayyana ma’anar waƙa da cewa “Waƙa ita ce nau’in guduwoyin zance da ake kira ƙayyadajje, kuma ake rerawa da wani irin sautukan murya na
musamman”
Gusau, (1993: 45) Ya ce “Waƙa magana ce ta fasaha a cure wuri ɗaya a cikin tsari na musamman”.
Sa’idu, (1981:76) Ya ce ”Waƙar baka ita ce wadda ake rerawa don jin
daɗi, a ajiye ta aka a kuma yaɗa a baki”.Saboda haka a waƙar babu amsa amo na harafi kamar na rubutacciyar waƙa.
Dangambo, (1982: 76) Ya bayyana waƙa da cewa “Waƙa wani saƙo ne da aka gina kan tsararriyar ƙa’ida ta baiti da ɗango
da ake rerawa a kan ƙari da amsa amo da sauran ƙa’idojin da suka shafi daidaita kalmomi”
Muhammad, (1980: 68) Cewa ya yi “Waƙa Magana ce cikin sarrafarfiyar murya
wadda ake rangaɗawa bisa wani tsari”.
Idan muka yi la’akari da abin da masana
suka faɗa dangane da ma’anar waƙa, za a iya cewa: waƙar baka wani zance ne na azanci wanda ake yi ta hanyar zaɓen kalmomi da lafuzza tare da daidaita sautin murya da zaɓen kalmomi waɗanda
ake rerawa da fatar baki cikin sautin murya mai daɗi”.
3.2.
Ire – Iren waƙoƙin
baka
Farfesa Sa’idu M. G., (1983:92) ya ce
“waƙoƙin baka na Hausa sun shiga ko’ina a dukkan ɓangarorin rayuwar Bahaushe. Waƙar baka takan yi ruwa ta yi tsaki a duk inda ta ga Bahaushe
ya jefa kafarsa. Kasancewar waƙoƙin baka suna da wannan halayya ta ratsa kowane zango na
rayuwar Hausawa ya sa suka zama suna tafiya daidai da rayuwar yara ƙanana da matasa da kuma manyan mutane,
maza ko mata. Za a iya karkasa wakokin baka na Hausa zuwa gida-gida kamar haka:
3.2.1.Waƙoƙin Baka Na Yara
Wannan nau’i na waƙoƙi ya ƙunshi sassan waƙe-waƙe da yawa waɗanda
yara ‘yan maza da ‘yan mata suke gudanarwa da suka haɗa da waƙoƙin wasannin dandali da wasannin tashe da wasan kwaikwayo da
bikin aure da sallar takuutaha da roƙon ruwa da sauransu. Ga wasu misalansu:
Kai rawa kai malan kai rawa
Dagemun nawa
3.2.2. Waƙoƙin Baka Na manyan
Mata :
Waƙoƙin
baka na manyan mata su ne waƙoƙin da yawanci mata suke yin su a lokacin da suke aiwatar da
wasu ayyukan gida. Manyan mata suna yin waƙoƙin a lokacin daka ko raino ko dabe ko nika ko wanke-wanke da
sauran lokuta na gudanar da wasu hidimominsu na yau da kullum. Farfesa Sa’idu
M. G., (1983) ya ce “waƙoƙin baka na Hausa.
3.2.3. Waƙoƙin Yara Maza
Waƙoƙin
yara maza su ne waɗanda
suke shiryawa a lokacin da suke wasansu na dandali. Irin waɗannan Waƙoƙi kan
sami jagora mai bayarwa, sauran yara kuwa suna karɓawa, kamar a waƙar sha
burburwa:
Bayarwa: Shaburburwa,
Amshi: Sha.
Bayarwa: Kowa ya bace,
Amshi: Sha.
Bayarwa: A sha shi da kulki,
Amshi: Sha.
Bayarwa: Kulkin kira,
Amshi: Sha.
Bayarwa: Ba na aro ba,
Amshi: Sha.
Bayarwa: Ku ba shi gidanai,
Amshi: Sha.
Bayarwa: Har ya kawo,
Amshi: Sha.
( Gusau, S.M. (1983).
3.2.4. Waƙoƙin ‘Yan
Mata
Waƙoƙin ‘yan mata su ma nau’i-nau’i ne, kuma su ne ake kira wakokin gaɗa ko na bojo. Su ma ‘yan mata suna gudanar da wasanninsu ne
a dandali ko a wasu wurare na musamman kamar a wajen bikin aure ko bikin sallar
takutaha ko lokacin rokon ruwa ko tashe a watan azumi da sauransu. Misalan waɗannan waƙoƙin akwai kamar haka:
Waƙar
Talle
Bayarwa:
Amshi:
Maina ya kone,
talle
Ba da talle ba,
talle
Jirkita mani,
talle
In ciwo kashi. talle
( Gusau, S.M.., 1983)
Waƙar
Sabara:
Bayarwa:
Amshi:
Na tai tsarince,
Sabara
Magarya tai mani jar tsikara, Sabara
lye, lye, lye Sabara
Magarya ba haka nan akan yi ba, Sabara
lye, iye, iye,
Sabara
‘Yar bakin gulbi, Sabara
Ta yi liya-liya,
Sabara
Ku yayyafa mata ruwa, Sabara
Shaf, shaf, shaf, Sabara
Ka dauko naka ka tura daka, Sabara
Ka dauko dan wani kai ta damfara Sabara.
Forofesa Sa’idu M. G., (1983) ya ce “waƙoƙin baka na Hausa
3.2.5 Waƙoƙin Daka :
Waƙoƙin daka su ne waƙoƙi waɗanda
mata suke yi lokacin da suke daka inda za su dinga gwama tabarya da turmi, sai
su ba da sautin da ake kira lugude ko mama, misalin waƙar daka ita ce:
Ana lugude ana mama,
Cikin shigifa cikin soro,
Mama ba habaici ce ba,
Salon daka a haka nan,
Ga macen da ba a so ta haihu,
Ta haifi kwandamin da namiji,
Shugaban daka shi ka daka,
‘Yan tanyo kissa su kai,
Sukus-sukus sai su aje,
Gidan Marafa kaji ka daka,
Tarmani na izon wuta,
Angula na kirba dawo.
( Gusau,
S.M., 1983)
3.2.6. Waƙoƙin Reno
Waƙoƙin reno su ne waɗanda
mata suke yi a lokacin da suke rainon yara suna yi musu tawai don su yi shiru
su bar kuka a kwantar da hankalinsu a sanyaya musu rai. A cikin waƙoƙin akan faɗi
nasabar yaro da ayyukan da ake yi a gidansu da yabon masoya da zambo da habaici
ga maƙwabta
in akwai su. Misali:
Yi shiru bar kuka,
Ku taho ku gane shi,
Ku yo ziyara,
Dan yaro sai dai a bi ka.
Gusau, S.M., (1983)
3.2.7 Waƙoƙin Daɓe
Waƙoƙin dabe su ne waƙoƙin da manyan mata suke yi a lokacin da suke aikin daɓe. Yawanci waƙoƙin daɓe
sukan ƙunshi
bege da zambo da habaice-habaice da kalmomin batsa da na zage-zage da sauransu.
Ga misali:
Ina Lumu shege,
Mai malmala ga munta,
Kare bakin bahwade,
Ya hana mu walawa.
(Gusau, S.M., 1983)
3.2.8 Waƙoƙin Niƙa
Waƙoƙin niƙa su ne waƙoƙin waɗanda
mata suke yi lokacin da suke nikan tsaba a kan dutsen nika na gargajiya.Waƙoƙin sun ƙunshi begen miji ko wani masoyi ko habaici ga kishiyoyi ko
uwar miji ko ta hanyar shagube ko ambaton juyayin nakuda da dai sauransu. Misali:
Waƙar Naƙuda:
Wayyo naƙuda ta tashi,
Ciwon naƙuda ya tashi,
Kuma ciwon naƙuda ya motsa,
Yau kam babu zama zaure,
Wayyo inna ki cece ni,
Da kis sha daɗinki,
Shin wai ke tuna inna ta cece ki?
Ko ko Ke tuna da baba ya cece ki?
Wayyo naƙuda ‘yar ziza,
Ciwon naƙuda horo ne,
Ko ko naƙuda hauka cc?
(Gusau, S.M. 1983)
3.2.9 Waƙoƙin
Talla
Waƙoƙin talla su ne waƙoƙi waɗanda
ake yin su a lokacin da ake tallan wani abu. A cikinsu akan zuga sana’ar da ake
tallar tare da fito da kwarjiinta ko amfaninta. Misali:
Ku sai dawon gero da barkono,
Furata da ‘yan yaji rankanɗam,
Sai da nid daka nib burke,
Harda gudajin nono.
(Gusau, S.M. 1983)
3.2.10 Waƙoƙin Baka Na
Cikin Labarai Da Tatsuniyoyi
Gusau, (1980) ya ce
haka kuma akwai wasu ‘yan waƙe –waƙe da ake sakawa a cikin labarai ko tatsuniyoyi don ƙara musu armashi ko jawo hankali da
tunanin mai sauraro. Ga wani misali daga tatsuniyar Maɗaci da Yarinya:
Yarinya: Maɗaci,
Maɗacci
ubana,
Gare ka anka ban ni,
Gare ka za ni tsira.
Maɗaci:
Ishunki, ishunki ɗiyata,
Gare ni anka bakki,
Gare ni za ki tsira,
Mutum ɗari
da goma,
Manzo dai kan kai gida.
(Gusau, S.M. 1980)
3.2.11 Waƙoƙin Baka Masu Tafiya Da kaɗe-kaɗe
Gusau, (1980) ya ce " waƙoƙin baka masu tafiya da kaɗe-kaɗe waƙoƙi ne waɗanda
makaɗan baka suke shiryawa. Waƙoƙin makaɗan
baka sun karkasu dangane da ire-iren makaɗan da ke aiwatar da su, ko ta hanyar kayan kiɗan da ake amfani da su ko kuma ta yanaye-yanayen waɗanda ake yi wa su. Waƙoƙin baka masu tafiya da kaɗe-kaɗe sun
haɗa da:
3.2.12 Waƙoƙin
Jama’a
Waƙoƙin jama’a su ne waƙoƙi waɗanda
ake yi wa attajirai da ma’aikatan gwamnati da sauran jama’a. Makaɗan da ke yin waƙoƙin jama’a suna da yawan gaske, sunayen wasu daga cikinsu sun haɗa da Mamman Shata da Danmaraya Jos da Abdu Karen Gusau da
Mammalo Shata da Garba Supa da Shehu Ajilo da Sabo Saya-Saya da Musa Danba’u da
Aliyu Gadanga da Haruna Uji da Hassan Wayam da Sani Dan’indo da sauransu. (Gusau,
S.M.,1980)
3.2.13 Waƙoƙin Maza
Gusau, (1980). ya kawo cewa waƙoƙin maza, waƙoƙi ne da ake yi wa wasu rukunin jama’a da suka haɗa da ‘yan dambe da ‘yan tauri da ‘yan kokawa, da ‘yan baura
da sauransu. Daga cikin makaɗan
wannan sashe akwai Kassu Zurmi da Alhaji Danbalade Morai da Muhammadu Bawa
Dan’anace da Isa Danmakaho da Illon Kalgo da Muhammadu Gambu da makamantansu.
3.2.14 Waƙoƙin
Sana’a
Waƙoƙin sana’a, waƙoƙi ne waɗanda
ake yi wa masu sana’o’in gargajiya kamar wanzamai da mahauta (runji) da manoma
da masunta da maƙera da
majema da masaka da sauransu. Yawancin makaɗa na rukunin waƙoƙin maza su ne suke shirya waƙoƙi na rukunin waƙoƙin sana’a kamar Dan’anace da Alhaji Danbalade Morai. (Gusau, S.M.,1980)
3.2.15 Waƙoƙin Fada
Waƙoƙin fada waƙoƙi ne waɗanda
ake shirya wa sarakuna da sarautunsu na gargajiya. Wasu daga cikin fitattun
makaɗan fada sun haɗa
da Ibrahim Gurso da Ibrahim Narambaɗa
da Salihu Jankidi da Abubakar Akwara da Buda Dantanoma da Muhammadu Dodo
Maitabshi da Musa Dankwairo da Abdu Inka Bakura da Aliyu Dandawo da Sani
Dandawo da Alhaji Danbade Morai da sauransu. (Gusau, S.M., 1980)
3.2.16 Waƙoƙin
Bandariya
Waƙoƙin bandariya, waƙoƙi ne waɗanda
ake aiwatarwa domin nishaɗantarwa
da yi wa rai yayyafi. Daga cikin makaɗan ban dariya akwai ‘yan kama da ‘yan gambara da ‘yan galura
da sauransu. (Gusau, S.M., 1980)
3.2.17 Waƙoƙin Sha’awa
Waƙoƙin sha’awa su ne waƙoƙin da ake shirya wa abubuwan da suka ba mutum sha’awa ko suka ƙayatar da shi. Da wuya a ware makaɗi daya daga cikin makaɗan Hausa a ce waƙoƙin sha’awa kawai yaƙe shiryawa, amma akwai wasu makaɗan da suke tsarma ire-iren waɗannan waƙoƙi jefi-jefi a cikin waƙoƙinsu kamar Haruna Uji
da Mamman Shata da Danmaraya Jos da Hassan Wayam da Sani Dan’indo da sauransu. (Gusau, S.M.., 1980)
A dunƙule, waƙoƙin baka na Hausa suna nan jibge kuma sun ratsa dukkan sassan
rayuwar Hausawa ta fuskar zamantakewa da siyasar zama ko tattalin arziki ko
addini ko ta hanyar al’adu ko wasanni da sauransu.
3.3 Nazarin Waƙar Baka
Waƙar baka aba ce wadda take buƙatar shiryawa da tsarawa , wato tsara batutuwa a samar da
gangar jikinta cikin a zanci da hazaƙa da naƙaltar harshe da ake amfani da shi.
Yahaya (1984) Ya ce “Waƙar baka maganar hikima ce da ake rerawa
ba faɗa kurum ba wadda ke ƙunshe da wani saƙo da ke ɗauke
da wasu kalmomi zaɓaɓɓu, tsararru kuma zaunannu”
Dangambo, (1982) ya bayyana ma’anar waƙar baka kamar haka “Waƙa wani furuci ne wato lafazi ko saƙo cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da
dai-daita kalmomi cikin wani tsari ko ƙa’ida da kuma yin amfani da dabaru ko salon armashi.
3.3.1.
Hanyar Nazarin Waƙar Baka
A wannan sashe an harhaɗo, tsofaffin hanyoyin nazarin ne da kuma sababbin a tayar
wannan hanyar ta nazarin waƙoƙin baka na Hausa. Wani abun ƙoƙari a nan shi ne matakan nazarin da ake yin amfani das u a
wannan hanyar za su fi dacewa da waƙoƙin baka wadanda makaɗan baka suka aiwatar.
A ƙarƙashin wannan hanyar ana buƙatar mai nazarin waƙar baka da ya fara gabatar da waƙar da ya ke yiwa sharhin yin bayani game da waƙar abubuwan kamar haka:
3.3.2.
Salsalar Waƙa
Mai nazari zai bayyana ainihin sunan wanda ya yi waƙa da wanda ake yi wa ita, da abin da
ake yi amfani da shi wajen kiɗan
waƙar
wato (abin kiɗa). Wato ana buƙatar mai nazari ya bayyana kayan kiɗan da makaɗi
ke amfani da su, sannan ana son mai nazari ya bayyana hanyoyin da aka bi, ko ya
bi ya sami waƙar ta
zo hannunsa. Samar da waɗannan
bayanai yana ƙara
tabbatar da ainihin waƙar da ƙarfin ta da madogararta.
3.3.3.
Shekarar Da Makaɗi Ya Fara
Waƙar
To ana buƙatar mai nazari ya faɗi shekarar da makaɗi ya fara rera wannan waƙa ya dace kuma a faɗi lokacin da ya yi ta, da kuma wurin da aka rera ta.
3.3.4.
Yawan Ɗiya a Waƙa
Sannan yana da kyau a bayyana yawan ɗiya da waƙar ta ƙunsa, tare da tabbatar da cewa an yi la’akari da mabanbanta lokuttan rerawarta,
banbancin lokuttan rerawarta kan sa yawan ɗiya ya ƙaru ko ya ragu.
3.3.5.
Tarihin Makaɗi a Taƙaice
Sanin taƙaitaccen tarihin makaɗi yana taimakawa ga fahimtar waƙoƙinsa. Ashe kenan yana da alfanu ga mai nazarin ya zo da dunƙulallen tarihin rayuwar makaɗin waƙar da zai yi wa sharhi.
3.3.6.
Bayanin Wanda Aka Yi Wa Waƙa
Kafin a shiga nazarin gundarin waƙa, ya dace a zo da bayanai masu gamsarwa game da nasaba da
tsakuren tarihin rayuwar wanda aka shirya wa waƙar. Wannan zai taimaka wajen fahimtar inda makaɗi ya dosa da gundarin saƙo ko saƙonnin da waƙar take ɗauke
da su. Idan sha’awa ce ta ɗauki
makaɗi ya yi wa wani abun da aka yi wa waƙar ta fito da halayensa da ɗabi’oinsa da sauran makamantan waɗannan bayanai.
3.3.7.
Turke Da Warwaransa
Turke shi ne abin da waƙa ke Magana a kan sa wanda ya ratsa tat un daga farkonta har
zuwa ƙarshenta
wato dai turke shi ne ainihin manufar waƙa, wasu abubuwa da ake dubawa don ƙara fito da turke a waƙa sune
3.3.7.1.
Muhallin Turke
Muhallin turke wani wuri ne ko wasu wurare da yawancin makaɗa ke bayyana takamaiman saƙon da waƙa ke ƙunshe da shi. Makaɗi yakan jefa saƙon waƙa ko wureren da aka bayyana gundarin saƙon waƙa.
Misali a cikin waƙar Danmaraya Jos ta “Aure” akwai inda yak e cewa”Jawabin aure zai yi”.
3.3.7.2.
Taƙaita Turke
(Turke a gajarce)
A wannan ɓangare
na taƙaita
turke ana buƙatar
fito da bayanan waƙar ne a taƙaice. A na iya ɗaukar
ɗiyan waƙa rukuni – rukuni a fito da muhimman abubuwan da suke magana a kai. Ga
misali daga waƙar
Danmaraya Jos ta “Karen
mota”.
Ɗa na 1 – 2 Bayanin maƙasudin waƙar kuma inda aka bayyana muhallin turke.
Ɗa na 3 Wasu halayen
Karen mota da siffofinsa
Ɗa na 4 Rashin sa’ar Karen mota da yadda ya zama macuci.
Ɗa na 5 – 19 Ci gaba da ambaton siffofi da halayen Karen
mota.
Ɗa na 20 Ssiddabarun da Karen mota ya ke yi idan wani abu ya
auku a mota da fito da ƙwarewar makaɗin
waƙar ta
fuskar fahimtar sassan mota.
3.3.7.3.
Warwara Da Tsattsefewar Turke
A nan mai nazari yana da babban aiki saboda a nan ne ake so
ya tsattsefe bayanan da waƙa ta ƙunsa ya fito da su daki – daki za a yi sharhin waƙa na gaba ɗaya tare da fito da manyan da ƙananan saƙoninta. Sannan kuma a bayyana abubuwan da makaɗi ya kafa hujja da su a cikin waƙarsa’
3.3.7.4.
Tubalan Ginin Turke
Yawancin waƙoƙin baka, idan mai nazari ya duba zai tarar da an jajjefa
wasu abubuwa a cikin su bayan manyan saƙonnin da su ke magana a kai waɗannan abubuwan da makaɗi ke sanyawa ƙari ne ga babban turke, kuma su ake kira tubalan ginin
turke, kenan tubalan ginin turke na nufin wasu magangannu da aka bi aka ƙulla waƙa da su don ta ƙara tsawo amma ba su ne babbar manufar waƙar ba.
Daga cikin abubuwan da za a iya kawowa a nan su ne:
Ambaton addinin, asali ko nasaba, ƙaramcin kyauta, iya shugabanci, tsarin sarauta, jaruntaka,
alfahari, ko ma kan tarihi, roƙo, zuga, kambamawa, zambo, yabo, da dai sauran abubuwa makamantan
waɗannan.
3.3.8.
Awon Baka
Shi wannan fagen nazari ne da ya shafi yadda makaɗi ke shirya waƙa a cikin zubin ɗiya
da dabarun karin murya . A wannan ɓangaren
ana duba zubin layuka da yawan ɗiyan
waƙa da
tsarin rerawa da karin murya da amsa amon kari da sauran abubuwan da suka shafi
awon baka.
3.3.9.
Yawan Layuka A Ɗa
Makaɗan
baka suna da walwala ta musamman dangane da shirya layukan ɗiyan waƙoƙinsu. Wasu sukan tsara waƙoƙin ne nan take wato a lokacin da suke a wajen kiɗa, wasu kuma sukan shirya waƙoƙin ne tun daga gida layuka ba su ɗaukar yanayi bai ɗaya
a tsarin ɗiyan waƙoƙin baka na Hausa. A kan shirya ma layi ɗaya ko biyu ko uku ko huɗu ko biyar koma fiye da haka a waƙa ɗaya.
Domin haka a waƙa ɗaya akan samu ɗiyanta
su zamanto masu ƙunshe
da yawan layuka daban – dabban. Misali a cikin waƙar “Ma su garin mazan gabas ta tsayayye ta sarkin Rafin Kurya
Dambo wadda Ibrahim Naranbaɗa
ya yi kamar haka:
Jagora: Ai kurya ta Dambo ce Makauru yannan.
Yan amshi: Zamfara babu Bagare kamarshi.
Jagora : Ai da takobi da garkuwa da mashi.
Yan amshi: Mai sulki Dambo na da yaƙi, kurya akwai mazan faɗa da arna.
3.3.10.
Tsarin ɗan waƙa
Ɗiyan waƙa tamkar rassa ne na itaciya wadda ake fara hawowa daga
gindin kuma a sauka ta kansa. A kowane “ɗa” za a sami “hawa” da sauka. Hawa shi ne wanda jagora ke
fara yi sannan ‘yan amshinsa (‘yan karɓi) su tarbe shi su iyar da sauka. Haka kuma a wajen tsarin ɗan waƙa akwai “ɗa) mai sauki akwai (ɗa) mai tsauri. Ga bayaninsu kamar haka.
Misalin ɗan
waƙa mai
sauƙi shi
ne
Hawa= In an so ko in ba a so ba,
Sauka = Mai abu dai shi adda abu nai,
Haka a cikin waƙar Narambaɗa
ta sarkin Kiyawa Abubakar Kaura Namoda.
Bayan wannan kuma akwai saukar sauka
Saukar sauka : wuri ne inda ma’ana ta ƙare kwata – kwata, wato wurin da ake gama sauke ma’ana
musamman bayan “takiɗi” ko
ajewa : Wuri ne inda ma’ana take numfasawa , ta ɓangaren tsari kuma ana amfani da waɗannan alamomin ne na ƙwayoyin sauti don fitar da shi a ɗan waƙa kamar haka:
A – (2) amma banda (+) ana
ƙirga ƙarewar ma’ana a cikin ƙaramin saƙo da su. Idan ma’ana ɗaya ce sai a ba ta alamar (A) idan aka ƙara samun wata ma’anar a ɗan
waƙa sai
ba ta alamar (B) Haka dai za a yi ta yi
har ƙananan
ma’anonin su ƙare.
3.3.11.
Tsarin Rerawa
Rerawa wani tsari ne inda makaɗi yake ɗan ƙarin murya cikin ranji mai ma’ana ya furta kalmomi ɗaya zuba cikin ɗiyan
waƙoƙinsa
Akwai wasu dabaru da ake amfani das u wajen fitar da tsarin
rerawa na ɗiyan waƙoƙin baka, su ne kamar haka:
-
Kaɗaita furucin jagora
-
Karɓi furucin yan amshi
-
Kulli wuri ne inda ake fara furta ƙaramin
saƙo a ɗan waƙa
-
Ƙari wuri ne inda ake ƙarasa furta ƙaramin
saƙo
-
Tarbe wuri ne inda ‘yan amshi suke iyar da
ma’ana ƙarama wadda jagora ya fara ta ɓangaren kulli
-
Rakiya wuri ne inda ‘yan amshi suke maimaita ƙarin
da suka riga su ka yi wa jagora zuwa wani ɗan lokaci
-
Karɓeɓeniya dabara
ce ta maimaita furucin ƙari da niyyar yi wa
makaɗi rakiya
-
Bayayyeniya wuri ne inda ake karɓe - karɓen ‘yan
amshin za su dinga maimaita rera abinda duk jagora ya furta ba tare da canza ko
kalma ɗaya ba
3.3.12.
Takiɗi a ɗiyan waƙa
Takiɗi shi ne maimaita abu domin ƙara ƙarfafa shi sannan dalilin da ke sa makaɗi amfani da takiɗi
shi ne: ƙarfafa
nauyin ma.ana ko jaddada ƙaramin saƙo, domin ƙara fito da muhimmancinsa fili. Misali a cikin waƙar “Bubakar sarki na Ma’azu,
-
Gidan Shehu da Bello (waƙar sarkin
taushi Katsina ta sarkin musulmi Abubakar na 111)
-
Ƙulli = kakka
sake a ramma,
-
Ƙari = Sa’idu
shirin ka ya yi ,
-
Takiɗi ƙulli
= kakka sa ke a ramma,
-
Ƙari Sa’idu shirinka
ya yi,
3.3.13.
Ƙarin Murya
Ƙarin murya ko tsayuwar sadaru a ɗiyan waƙoƙin su ta fuskar ƙarin waƙar baka an fi jan gaba mai nauyi ko a ƙarwara ta kangaba maras nauyi wato gaba mai sauƙi . Gaba maras sauƙi wato gajeriya , ita ce wadda ta haɗa baƙi da wasali (BW) DA (BWW) wadda ake nunawa da alamomi kamar
haka [ - ] ko [ ! ].
3.3.14.
Amsa Amon Kari
Amsa amon ƙari shi ne daidaitawar ƙari inda zai iya zamantowa bai ɗaya a gaɓoɓin ƙarshe wato madirar sauti na ƙarshe a saduwar ɗan
waƙa.
Amsa amon ƙari yana daidaita hawa da saukar murya a saduwar su ta fi
jere bisa ƙa’ida. Amma alamomin da ake amfani da su
wajen fitar da ƙari a
waƙa. Ga su kamar haka:
3.3.14.1.
Gidan Dara Na Kari
Wannan wata hanya ce da ke nuna ƙari ta bin hawa da saukar murya a sadurun ɗan
waƙa a fitar da gidan dara na ƙari ta amfani da gubabun ƙari da ginshiƙai. Awajen tantance wannan hanya za’a yi la’akari da wannan abubuwan kamar haka.
-
Ginshiƙi: shi ne
gaba ɗaya na murya
da za a iya wakilta da alama kamar haka [+]
-
Ginshiƙin ƙari
wuri ne da yake ɗaukar ginshiƙi
ɗaya ko biyu .
Idan gaɓa mai nauyi
ce to ta an a matsayin ginshiƙi duga biyu ne, amma a gurbi ɗaya. Misali
{++}
Idan, kuma gaɓa mai sauƙi ce wato marar nauyi tana a matsayin ginshiƙi ɗaya, Ciko wannan shi ne ƙunshiyar gurbi wanda zai iya zuwa gaɓa ɗaya
mai nauyi ko gaɓa biyu marasa nauyi.
3.3.15.
Salon Sarrafawa Da Adon Harshe
Dangane da salo masana sun bayar da ma’ana da dama .
Dangambo (1981:23) Yan a ganin salo shi ne dabarun jawo hankali wajen isar da
saƙo.
Salo a waƙar baka kuma na nufin wata hanya wadda makaɗi ke kyautata zaren tunanensa, ya sarrafa shi cikin azanci
dan ya cimma burinsa na isar da saƙo a waƙa.
3.3.16.
Adon harshe
Adon harshe wata dabara ce wadda ake yi wa harshen waƙa kwalliya. Daga cikin dabarun da ake
amfani da su don yi wa waƙoƙin baka ado akwai:
-
Kamantawa
-
Sinfantawa
-
Jinsarwa
-
Kinaya
-
Alamtarwa
-
Ƙarangiya
3.3.17.
Zaɓen Kalmomi
A wannan fage mai nazari zai yi ƙoƙari ya fito da yadda makaɗi yake zaɓo
kalmomi da yake zubawa a cikin ɗiyan
waƙoƙinsa za a duba a gani, kalmomin nan
tsofaffini ko sababbi ko ƙirƙirarru ko kuma ba ƙire ba waɗanda
su ka shigo harshen Hausa daga wasu harsuna. Ga abin da suke so mai nazari ya
fito da su a wannan ɓangaren.
-
Tsofaffin kalmomi – kalmomin ƙarfafa
ma’ana
-
Ƙirƙirarrun
kalmomi – kalmomin sakaya zance
-
Sababbin kalmomi – kalmomin sakaya ma’ana
-
Baƙin kalmomi –
kalmomin amsa kama
-
Kalmomin kambamawa – kalmomin nishaɗi
3.3.18.
Karin Harshen Waƙa
Makaɗan
baka suna aiwatar da waƙoƙi ne cikin kare – Karen harshen Hausa da ake da su kamar Sakkwatanci da
Gobiranci da Zamfarci da Katsinanci da Zazzaganci da kuma Kananci da dai
sauransu.
Dangane da nazarin Karin harshe a waƙa za’a iya duba waɗannan
abubuwa :
-
Nau’in Karin harshe
-
Kalmomin fannu na Karin harshe
-
Rambun kalmomi
-
Yanayi furuci
-
Yanayin ɗauri da
sauransu.
3.3.19. Gini Jimla Da Tsarinta
Masana adabin waƙa sun nuna cewa lahirar waƙa akan ba makaɗi
da mawaƙi
dammar karya wata doka ta ginin ko tsarin jimla. Amma duk da haka, makaɗa da mawaƙa kan tsara jimloli dogaye da gajeru da kuma
matsakaita.
3.4.
Naɗewa
A
cikin wannan babi mun fara gabatar da shine da taken fashin baki a kan ma’anonin da suka shafi taken bincike, domin kawa yadda
siffar babin za ta kasance da kawo ra’ayoyin masana akan ma’anar waƙa
kuma mun kawo Ire-Iren waƙoƙin Hausa da yadda ake aiwatar da su ackin al’ummar Hausawa
tare da cikakken bayani da misalai na Ire-Iren waƙoƙin Hausa, haka kuma a wannan babi mun kawo mu ku hanyar
nazarin waƙar baka.
ABDULLAHI DANGUNDUWA KAGARA DA WAKOKINSA
A babi na hudu kuma za a kawo
bayanai game da gundarin taken bincike. Wato, bayanai a kan Alhaji Abdullahi
Dangunduwa Kagara da wasu daga cikin waƙoƙinsa a inda muka fara da
shinfiɗa game da taƙaitaccen
tarihinsa, wato haihuwarsa, ƙurciyarsa da tasowarsa da
kuma neman iliminsa. Haka an zo da bayanai dangane da koyo da fara waƙoƙinsa, da
yaransa, da kuma yawace –
yawacensa, da yadda yake shirya waƙoƙinsa, da rasuwarsa, da matsayin Alhaji Abdullahi
Dangunduwa Kagara a tsakanin mawaƙan da da na yanzu, da nau’oin
kayan kiɗansa, da kuma nau’oin waƙoƙinsa.
Babin bai kamala ba sai da aka nazrci wasu daga cikin waƙoƙinsa, inda aka fayyace, jigon
waƙoƙinsa tare da warwarar jigo.
Haka an yi bayanai dangane da salon waƙar Alhaji Abdullahi
Dangunduwa Kagara, aka zo da bayanai dangane da salon sarrafa harshe, da salon amshi, aka kuma yi bayani game da zubi
da tsarin waƙoƙinsa daga ƙarshe
kuma aka zo da naɗewa.
4.1. Taƙaitaccen tarihin Alhaji Abdullahi Dangunduwa
Kagara
An haifi Alhaji Abdullahi
Dangunduwa Kagara a garin
Kagara, ƙaramar hukumar Talata Mafara a cikin jihar Zamfara,
Nijeriya. Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara an haifeshi a shekara ta alif ɗari tara da sittin da shidda
(1966). Sunansa na yanka Abdullahi, wanda ake masa laƙabi da Dangunduwa ya tashi a
cikin gidan makaɗa, saboda makaɗi ne Alhaji
Abdullahi Dangunduwa Kagara ya yi gadon kiɗan ne daga mahaifinsa wato
Ibrahim, wanda makaɗin Tama da fawa, ya na kuma amfani da kayan kiɗa kamar kalangu.
Alhaji Abdullahi Dangunduwa
Kagara ana yi masa wannan laƙabi ne na Dangunduwa tun yana ɗan yaro lokain da ba ya da
baki idan yana jin yunwa sai ya ce a ba shi (gunduwa da wule) ma’anar gunduwa
shi ne abinci wule kuwa miya. Ta nan ne wannan laƙabi ya samo asali tun ya na yaro.
Fahimtar wannan ba zai
kammala ba, ba tare da anbi diddigin tarihin mahaifinsa ba. Mahaifinsa
(Ibrahim) shi dai makaɗin kalangu, kuma mawaƙi ne mai hazaƙa da son
mutane, ya na kuma da ƙoƙarin zagaye domin tafiyar
sana’arsa ta kiɗa da waƙa (waƙar baka) kamar irin waƙar fawa
da ta noma ko tama.[1]
4.1.1. Ƙurciyarsa da Tasowarsa da Neman Iliminsa
Kamar yadda muka yi fira da
wani malami kuma dattijo kusan ɗan shekara saba’in zuwa tamanin mai suna malam
Zakari Kagara kuma ƙanen wanda ya koyar da Alhaji
Abdullahi Dangunduwa Kagara ilimin addinin musulunci ya bayyana mana
cewa, kamar yadda al’adar Bahaushe
take, idan aka haifi yaro ya tasa ya kai lokacin ƙurciya, babansa yana kai shi
makarantar allo domin neman ilimin addinin Musulunci. Alhaji Abdullahi Dangunduwa
Kagara mahaifinsa ya kai shi makarantar allo ta wani malami mai suna malam
Muhammadu domin samun ilimin addini. A sha’anin waƙa kuwa, da Alhaji Abdullahi
Dangunduwa Kagara ake zagayawa duk in da aka je, domin yin amshin waƙa, ta
haka ne ya bi mahaifinsa ana waƙa yana amshi, har ma wata
rana yana yi masa ƙari a cikin waƙarsa.
Tun daga nan mahaifinnasa ya ga cewa shi yaro ne mai fahinta da kuma fasaha.
4.1.2. Koyo da fara waƙoƙinsa
Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara, ya koyi waƙa ne ga
mahaifinsa ta hanyar bin sa sau da ƙafa har zuwa lokacin da Allah
ya sa mahaifinsa ya tuba ya bar waƙa. Bayan mahaifinsa ya tuba
ya bar waƙa, sai ya koma yana bin wani makaɗin ‘yan mata ko da yake ba
wannan sana’a ya koya ba a wajen Abdullahi Bayan ya yi biyar Abdullahi ya kuma
yi biyar ƙanen ubansa wanda ake kira Muhammadu Dan’inna,
shi ma Amadu Danbaƙi tare da Alhaji Abdullahi
Dangunduwa Kagara suka yi biyar Ibahim watau mahaifin Danguduwa Kagara.[2]
To kamar yadda muka faɗa tun da farko cewa Abdullahi
Dangunduwa Kagara mutun ne mai basira mai hazaƙa, haka suka cigaba ya na
biyar ƙanen babansa Muhammadu Dan.inna, suna kiɗa da waƙa tare. A wannan lokaci, Ɗangunduwa
ne tauraro a wajen waƙoƙin. A kan haka Abdullahi
Dangunduwa Kagara yana nan yana biyar ƙanen babansa shi ma sai Allah
ya yi masa rasuwa. Ta haka ne Alhaji ya zama mai gidan kansa.[3]
Waƙoƙinsa Na farko
Waƙar da ya fara aiwatarwa da
kansa ta farko ita ce ta fidda shi waje wato waƙar noma ta Alhaji Amadu
Morai, kamar haka:-
Alhaji Amadu ginshiƙin dutse ,
Tunkuɗa ba ta kasheka ɗan Mamman,
Za mu kai mai kiɗa can garin Morai,
Ya ci gwabron maza ya buwai daji,
Wannan ita ce waƙar da Danguduwa Kagara ya fara ta farko, da ya yi wa wani manomi
Alhaji Amadu Morai. Haka kuma ya yi waƙoƙin fawa da dama, waɗanda suka ba shi
damar zama makaɗin waƙoƙin baka,
duk da kasancewar abin da ya gada ga mahaifnsa shi ne kiɗan fawa da kuma kidan noma.
Bayan ga kiɗan noma yana kuma kiɗan fawa. Bisa al' adar Bahaushe mun san cewa wancan lokaci
ko babbar Sallah ko kuma in aka yi wani
naɗin sarkin fawa. To su waɗannan mutane masu sana'ar
fawa suna da nasu makaɗi na kansu, kamar dai yadda mafi yawan sana'oin
Hausawa suke da su. Ita ma sana'ar fawa ta na da muhimmanci ƙwarai da
gaske, ga rayuwar Bahaushe don hka tana
da nata makaɗa na daban.
Dangunduwa Kagara a fagen waƙa ko ina ya na iya tattaɓawa, ya yi ma sarkin fawa waƙa da sauran maƙarrabansa, a inda yake waƙe sarkin
fawa Abu Kagara kamar haka:-
Sa maza su ji tsoron nama,
Abu Danmiko ka bugi tozon nagge,
Ba gari nama Abu Danmiko,
Ya Allah shi riƙama mahauta.
Kamar dai yadda muka gani cikin bayanin cewa
Dangunduwa Kagara, ra'ayi ne kawai ya sa ya koma makaɗin sarauta, duk da ya yi fice sosai
ga waƙoƙin
sarauta.
Waƙar ‘Sarauta
Waƙarsa ta
farko daya fara yi ta sarauta, ita ce wadda ya yiwa Banagan Morai Alhaji Abdulmali a inda yake
cewa :
“Kai adda Morai riƙa
Allah ya baka Morai riƙa ta da kyau
Malikki ɗan Muh’d
Macciɗo,
Malikki ɗan Abu
Banaga,
Ɗan Farinruwa
ɗan Danau,
Garnaƙaƙi bari tsoron maza,
Na Abu Morai, Ɗanmusa”.
Wannan ita ce waƙa ta farko da Dangunduwa Kagara ya fara yi ma wani
basarake. Wannan shi ne dan takaitaccen bayanin yadda Dangunduwa ya koyi
sana'arsa ta waƙa. Duk a cikin waƙoƙinsa na farko akwai wata
waƙa ta sarkin Morai inda ya fara ta ne kai tsaye:-
"Ya hana gwangwani gwauron Majikira ƙansaƙin Danau,
Alhaji Banaga na jekada Allah kai dai ya zaɓa,
Da girmanai ya hau na malam,
Da halin girma zai sauka
Ya hana
gwangwani gwauron Majikira ƙansaƙin Danau”
A wannan fagen za mu kawo
bayanai dangane da yaransa kuma abokanan sana’arsa ta kiɗa da waƙa.Ya zama dole idan ana zancen
makaɗa Alhaji Abdullahi Dangunduwa
Kagara a yi zancen yaransa, domin su ne masu taimaka masa wajen fito da waƙarsa.
Saboda da yawa za ka ji a cikin wasu waƙoƙinsa idan ya faɗi gindin waƙa, ba
zai ƙara cewa komai ba sai dai ya rinƙa yin shiru,
su ko suna cigaba da waƙar har ƙarshenta, kamar yadda a waɗansu waƙoƙin su kuma yaransa idan suka
yi amshi ɗaya a farko ba su ƙara cewa
komai har sai ƙarshenta ayi amshi ɗaya, wannan yana faruwa ne
domin mafi yawan waƙoƙinsa kamar bayanin wani abu
ne da ya faru yake yi. Kuma ga jerinsu kamar haka :
1. Muhammmadu Ɗanbaraka
- Makaɗi
2. Hussaini Abdullahi Maidiki -
Makaɗi
3. Shehu Abdullahi Dangunduwa -
Makaɗi
4. Sa’idu Tsauni - Makaɗi
5. Ummaru Ɗan’auta – Ɗan amshi
6. Mustapha Abdullahi - Ɗan amshi
7. Haruna Muhammadu Jatau - Ɗan amshi
8. Muhammadu Nagido - Ɗan amshi
9. Abdullahi Ƙwazo – Mai kwazakke
Kamar yadda muka yi bayani
can baya cewa Abdullahi Dangunduwa Kagara mutun ne haziƙi a fagen waƙar Hausa.
Abdullahi Dangunduwa tun farko da shi ake zagayawa ana yawace – yawace a duk
inda aka je, domin yin amshin waƙa, ta haka ne ma Abdullahi
Dangunduwa ya bi mahaifinsa ana waƙa yana amshi, har ma wata
rana yana yi masa ƙari a cikin waƙarsa. Bincike
ya nuna cewa, dangane da yawace-yawace wajen yin waƙa. duk faɗin tsofuwar jihar Arewa Maso
Yamma wadda ta haɗa Sakkwato, da Kabi, da
Zamfara, da lardin Neja har a sauran
garuruwan arewacin Nijeriya da kudaccinta, ba inda bai ƙafa ba a wajen yawon kiɗa da waƙa. Abdullahi Dangunduwa ya yi
yawace – yawace domin isar da sana’arsa ta waƙa, wanda aka shaida mana cewa
a wajen yawace – yawacansa na waƙa har wani masoyinsa ya biya
masa kujerar hajji, bayan alhairan da yake samu wajen aiwatar sana’arsa ta waƙa.
4.1.5. Shirya Waƙoƙinsa
A kowane al’amari ko fanni, ana samun maɗaukaka
da na ƙasa-ƙasa,
saboda bambancin da Allah ya yi tsakanin bayinsa, haka ma a wajen makiɗa ana samun irin wannan banbanci domin
wasu makiɗa sukan tsaya
ne da su da yaransu ('yan amshi)
tun a gida su shirya irin waƙar
da za su je su yi ma wani mutun wanda suke son su yi wa waƙa. Irin
su: Alhaji Musa Danƙwairo Maradun da Alhaji Aliyu Dandawo da sauransu domin su makiɗa ne na sarauta da ke son su zo waje
su burge, ko dai wanda suka yi wa kiɗan
ko jama’a. Amma shi Danbalade Morai mun sani cewa makaɗin maza ne sannan kamar yadda bayani ya gabata cewa shi ba wai ra’ayi da shawa ya sa yake kiɗa da waƙa ba
a' a gadon abinsa ya yi wajen mahaifinsa.
To a takaice dai, Abdullahi
Dangunduwa Kagara shi
makaɗin shawa ne tun lokacin da ya fara sana'ar, har
lokacin da Allah ya amshi abinsa,
saboda haka ba ya shirya komai na waƙa
tsakaninsa da jama'arsa watau (makiɗa da 'yanamshi) domin idan an tafi
daji ko fagen kiɗa, suna
amfani da duk wanda suke da shawar yi wa waƙa, ko wanene ko an san shi ko ba' a san shi ba, misali waƙar wani gwarzonsa da ya yi wa waƙa.
Mai suna
"Haruna Sarkin noman Mayanci. Wannan wani bawan Allah ne da Abdullahi Dangunduwa ya ji labarinsa
ya yi masa waƙa kurum ba don ya
san shi ba, sai bayan shekara biyu da yi masa waƙar sannan ya je ya kai ma sa ziyara.
Wannan waƙar ga ta kamar haka:
"Sarkin noma mai hana aikin gona ya kwan,
Matsa a gama manyan makasa sabra Ɗan Abu,
Haruna Ɗanba’u barker ka da yaƙin tausar yama,
Sarkin noma mai hana aikin gona ya kwan,
Matsa a gama manyan makasa sabra Ɗan Abu,
Gabas ga Mayanci ba ku da daji ko ɗankaɗan,
Sarkin noman yamma ga titi ya kau da shi,
Haruna Ɗanmani,
daure ka yi min kyautar isa,
Ni dai na san ba ka da ruwa ko ‘yar kaɗan”.
Wannan ita ce waƙar da
Abdullahi Dangunduwa Kagara ya yi wa sarkin noman Mayanci tun kafin su haɗu. Akwai
ire-iren waƙoƙin da yawa domin makaɗin tama bai san irin mazan da zai haɗu da su ba sai an je
fagen tama, amma tsayawa a shirya wata
waƙa kafin a fita bai ko taso ba.
4.1.6. Kayan kiɗansa
Kayan kiɗan sun
danganta da irin kiɗan da
mai kiɗa ke aiwatarwa, saboda haka
da yake Abdullahi Dangunduwa Kagara ya keɓanta ga masu sana'ar fawa da tama da
kuma Sarauta, a halin
yanzu, kayan kiɗan fawa
da noma da kuma sarauta
yake amfani da su. Daga da baya ya fara waƙar
sarauta, sai ya sami kotso. Kamar
yadda bayani ya gabata cewa Abdullahi Dangunduwa Kagara, kiɗan sarauta ba gadonsa ya yi ba daga baya ne da ya ga ya shahara fagen waƙa har ya
yi wa Sarkin Morai Banaga Abdul malik Muhammadu waƙa, daga
nan sai Sarkin Morai na yanzu wato Banaga Abdul malik Muhammadu sai ya ga cewa ya kamata ya canza tafashe sai ya saya masa
kotso domin ya riƙa amfani da shi wajen kiɗan sarauta. Kalangu da kwazakke wajen kiɗan fawa da noma.Ga kayan kamar haka :
1. Kalangu
2. Kotso
3. Kwazakke
4.1.7
Nau’oin waƙoƙinsa
Kamar dai yadda ya zo
cikin bayani cewa Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara mutum ne haziƙi da fasaha, kuma ya shahara akan waƙoƙin Hausa, kuma ya yi
waƙoƙi daban-daban; iri-iri,
kala-kala ire-iren waƙoƙinsa su
ne kamar haka:-
Waƙar Fawa
Su kuma
dai waɗannan waƙoƙi na
fawa su na zuga mahauci komahauta su yi bajin ta da sibiri, irin na shan Gumba
ko kuma kamun "Sa" ko su dubi
sa ya faɗi a yanka shi, da sauran waɗan su abubuwa na nuna bajin ta, da kuma nuna
kwarewa ga sauran runji, da bada shawa ga wanda ke kallo ko saurare, muna iya
ganin wasu misallan wadannan waƙoƙi kamar haka :-
“Sai na kai kiɗa gidan sarkin fawa Ummaru,
kai ash
shugaban mayanka shanu kaf ƙasar
Kagara,
Dawo Ummaru ‘yanrujji ai
sun san da ba su yi
In dai Ummaru ya yi magana
ban san mai iya tayar mai ba,
Ai ga wani saunan sakin
fawa,
Shi bai yanka bai alheri,
Sai in sun yi ya dauki kwashi”
Waƙar Noma
Waɗannan waƙoƙi ana
yin su ne domin a cusa ƙwazo da karsashi a zuciyar manoma su motsa, su -girgije, su duƙufa ga noma. A cikin waƙar wani sarkin noma Lawali Anka,. Alhaji Abdullahi
Dangunduwa Kagara yana cewa :
« Lawali na Abu
sarkin noma,
Allah mai san Anka in ga Lawali na Abu sarkin
noma,
Lawali ko ana fari ya fi gaban kakare,
Lawali ka noma ɗari ka kuma noma dubu don mun gani ».
Dama Hausawa ba abin da
suke so irin wannan kiɗa na
noma, ka san halin Bahaushe mazauni karkara ga kiɗa irin
na noma domin ba ya da wata
sana’a da ta wuce noma. Kamar sauran waƙoƙin noma su ma sun ƙunshi jigon yabo, zuga misali a cikin wata waƙa yana cewa:
“Ga wagga ƙasa duk
mai riƙa kalme ya san da kai,
Gabas da yamma ga Mayanci ba su da daji ko ɗan kaɗan
Sarkin noman yamma ga kwalta ya sassabe,
Na Ɗan mani
barkarka da yaƙin noman
hatsi,
Na Ɗan mani
barkarka da yaƙin noman
gyaɗa”.
Waƙar
Sarauta
Waƙoƙin sarauta, galibin su sun keɓanta ga wasu jinsin mutane a cikin al'ummar Hausawa waɗanda suka ƙunshi
sarakuna ko 'yan sarki, ko kuma duk wani wanda sarki ya ke naɗawa ya zama
wani shugaba a cikin al'umma. Waɗannan rukunan mutane ne ake yi wa waƙa irin
ta sarakuna. Waƙar sarakuna keɓantacciya ce, ba kowa ake yi wa ita ba sai irin su
sarakuna da hakimai da ‘ya’yan sarakai. Waƙoƙin sarakuna ana yin su ne domin cusa yabo da zuga ga zukatan sarakuna.
Waƙoƙin suna ƙunshe da jigon yabo,
zugi kwazo da kumaƙauna misali a cikin wata waƙa ta
sarkin Anka waton maimartaba Sarkin Zamfara Attahiru, makaɗa Ɗangunduwa yana cewa:-
Kai maza ka shakka mugun
madambaci Atta
Bai yarda a rammai ba, ba takura jan zaki,
Kai maza ka shakka mugun
madambaci Atta
Alhaji Ɗan Ummmaru giwa ba kikan kula da tarkoba,
Kai maza ka shakka mugun
madambaci Atta,
Maigima mai Kadandaɓa mai BirninTudu da Janbaƙo,
a.
4.1.8.
Rasuwarsa
Kamar yadda bayanai su ka zo
daban – daban dangane da Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara, tun daga
haifuwarsa har zuwa ƙurciyarsa da yadda ya gudanar
da rayuwarsa. Abin da aka sani ne cewa kowace rayuwa za ta ɗanɗana mutuwa, haka Alhaji
Abdullahi Dangunduwa Kagara ya rasu ranar Litanin 16 / 10 / 2015. Ya bar mata ɗaya da ‘ya ‘ya kamar
i. Muhammadu
ii. Hussaini,
iii.Ya’u,
iv.Ummaru,
v. Sa’idu,
vi.Nana Fiddausi.
Bayan rasuwarsa, ɗansa Muhammadu shi ya gade
shi kuma shi ke jagoranci aiwatar da wannan sana’ar ta waƙa kamar yadda babansa, watau
Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara ya gada ga mahaifinsa Ibrahim.
4.2. Matsayin Alhaji
Abdullahi Dangunduwa Kagara a Tsakanin Mawaƙan Da da Na Yanzu
Kamar yadda yakan kasance kowane mutun bai rasa
abokanan hulɗa duk fannin da yake gudanar
da harkokinsa na sana'arsa. Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara shi ma yana da
dangantaka da wasu makaɗa da
mawaƙa kamar haka:-
Alhaji Abdullahi Xangunduwa yana da alaƙa makusanciya da wasu abokan sana’arsa. Daga ciki akwai
Alhaji Danbalade Morai. Shahararren
makaɗin fawa / dambe da noma da
kuma sarauta a cikin ƙasar Talata Mafara da Ƙwazo Bagega da Abamu Maradun, mai kiɗan
'yandambe, da Ibrahim Dangulbi, da Musa Ɗangulbi
da Muhammadu Maiturare Wababe. A cikin duk waɗannan
makaɗa, dangantakar da ke tsakaninsa da makaɗa Alhaji
Danbalade Morai ta fi ƙarfi sosai dalilin kusanci da ke tsakanin garuruwan da su ke
zaune. Ko da yaushe sukan haɗu. Hasali ma, sukan ziyarar junansu koyaushe. Hasali ma duk abin da za su yi, sukan shawarci junansu.
A wani ƙauli, cewa aka yi Alhaji Danbalade Morai ne ya fara shawartar Alhaji Abdullahi Dangunduwa
Kagara da ya kai ma sarkin Morai waƙa. Bincike ya tabbatar da
cewa daga baya sun ɗan sami takin
saƙa tsakaninsu. Ana kyautata zaton cewa ganin ɗaukakar
da Alhaji Abdullahi Dangunduwa
Kagara ya samu inda har aka saya masa kayan kiɗan
sarauta ne ya
sa dangantaka tsakaninsu ta yi tsami. Idan kuwa muka koma wajen mawaƙan yanzu Alhaji Abdullahi Dangunduwa Kagara ba ya da wata dangantaka a tsakaninsa da mawaƙan yanzu
domin bai yi wata cikakkiyar hulɗa da su
ba.
4.3. Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa
Kamar dai yadda ya zo
cikin bayani cewa Alhaji
Abdullahi Dangunduwa Kagara mutum ne haziƙi mai fasaha, kuma ya
shahara akan waƙoƙin
Hausa, kuma ya yi waƙoƙi daban-daban; iri-iri,
kala-kala ga wasu daga cikin waƙoƙinsa su
ne kamar haka:-
Waƙarsa da ya yi wa sarkin Mayanchi
Sabon gari Ƙashimu
ga ta kamar haka:-
"Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,
Sabon gari Ƙashiu,
Allah babban mutum ya yi ka,
Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,
Sabon gari Ƙashiu,
Na Anaruwa ƙara gyaran faɗa,
4.4. Nazarin waƙoƙinsa
A cikin wannan nazarinwasu
daga cikin waƙoƙin Alhaji Abdullahi
Dangunduwa Kagara, zai kasance sharhi kan waɗansu waƙoƙi da muka zabo a cikin waƙoƙinsa.
Wannan sharhi zai shafi jigon waƙoƙinsa, warwarar jigo, salo waƙoƙinsa,
salon sarrafa harshe, salon armashi da zubi da tsari waƙoƙinsa.
Daga farko za mu fara da
sharhi akan waƙar sarkin Anka
waton Maimartaba sarkin Zamfara
Attahiru, in da ya ke cewa :
4.4.1. Turken Waƙoƙinsa
Kamar yadda muka sani jigo a
cikin waƙoƙin Alhaji Abdullahi
Dangunduwa Kagara, shima abin da waƙar ta ke tafe da shi ko kuma
abin da waƙar ta ke son ta isar ga al’umma.
Saboda haka ita wannan waƙa jigonta shi ne zuga, watau
a inda yake cewa:
" Kai maza ka shakka mugun madambaci
Atta »
Bai yadda a rammaiba, ba
takura jan zaki,
Alhaji Ɗan Ummmaru giwa ba kikan kula da tarkoba,
Kai maza ka shakka mugun
madambaci Atta,
Maigima maikadandaɓa maibirnin tudu da Janbaƙo »
Idan
muka duba a cikin wannan waƙa daga
baiti na ɗaya har zuwz na biyu, a nan
jigon ya nuna mana cewa sarkin Anka
waton Maimartaba sarkin Zamfara
Attahiru wani
shahararren sarki ne wanda bai yarda da wasa ba, kuma ba a kai masa reni sannan
kuma ya bayyana shi sarkin Anka
waton Maimartaba sarkin Zamfara
Attahiru da cewa idan baya nan
sarakuna suna yadda sukaso, amma idan sun ganai duk sunzan kamar ba sarakuna
ba,. Dan haka Dangunduwa Kagara ke kiransa da cewa:-
“Bai yadda a rammaiba, ba takura jan zaki »
A cikin wannan waƙa, Alhaji
Abdullahi Dangunduwa Kagara ya na nuna mana cewa ko shakka babu, Maimartaba sarkin
Zamfara Attahiru da gaskiya yake yin mulminsa ba da wasa yake yi ba.
Bayan haka, duk a cikin waƙar Maimartaba sarkin Zamfara Attahiru ya fito mana dawani
jigo na nuna bajin ta, da Maimartaba sarkin Zamfara Attahiru ya yi haka kuma ya
bayyana mana shi dai Maimartaba sarkin Zamfara Attahiru duk yawan da ya bamu
labarin jaruntakar shi idan an fito fagen fama, dangane da haka sai a dubi
wannan baiti:-
" Kai maza ka
shakka mugun madambaci Atta »
A nan makaɗa
Abdullahi Dangunduwa Kagara ya na sun ya bayyana mana irin jaruntakarsa, da
kuma nuna sadaukantaka da bajinta da Maimartaba sarkin Zamfara Attahiru yake da ita.
Salon waƙar
To a cikin wannan waƙa ta Maimartaba sarkin Zamfara
Attahiru, Makaɗa ya fara wannan waƙa ta Maimartaba sarkin Zamfara Attahiru kai tsaye ba tare da budewa da komi ba ita
wannan waƙa Dangunduwa Kagara ya fara
tane da:-
" Kai maza ka shakka mugun madambaci Atta »
Haka kuma ya kara da salon danbantarwa ya na
cewa:-
"Alhaji Ɗan Ummmaru giwa ba kikan kula da tarkoba"
Bayan haka, ya yi amfani da salon siffantawa a ya yin da ya siffanta,
shi wannan shahararren dan damben da cewa:-
" ba takura jan zaki".
A nan in muka duba,
Dangunduwa ya kamanta wannan shahararren basarake da wannan baitin, domin ya na
nuna ma duniya cewa wannan basarake shi sadaukin sarki ne.
Bayan haka Abdullahi Dangunduwa Kagara ko shakka ba bu ya yi
amfani da salon yabo kamar haka:-
Idan muka yi la' akari da wani baiti a cikin
wannan waƙa, wurin day a ke nuna cewa a
lokacin day a na aikin gomnati ya kawo wurai – rai daban – daban inda ya yi
aiki Abdullahi Dangunduwa Kagara ya na
cewa “kowa ya yaba da aikinsa”
Bayan haka, kuma cikin wannan waƙa Abdullahi Dangunduwa Kagara ya yi amfani da
salon aron kalmomi, musamman daga harshen larabci har dai in muka yi la’akari
da wannan baiti da ke biye :
‘Ya Allahu Rabbana ba
ni abinda zan faɗa,
Kar yanduniya su rena ni’.
Ko
shakka ba bu idan muka dubi wannan baiti za muga cewa gaskiya ne Abdullahi
Dangunduwa Kagara ya yi amfani da salon aron kalmomi domin wannan kalma ta
Allahu da Rabbana duk ya aro su ne daga harshen larabci.
4.4.2.
Zubi da Tsari waƙoƙinsa
Ita wannan waƙar Abdullahi Dangunduwa Kagara ya fara ta ne kai tsaye tare da nuni
zuwa ga ‘yan sarki ya na cewa: -
« Kai maza ka shakka mugun madambaci Atta »
Haka kuma wannan mawaƙi Abdullahi Dangunduwa Kagara ya kuma tsara waƙarsa ne acikin baiti biyu-biyu, sannan yan mai maita wasu
daga cikin baitocin bayan haka yan amshi su na yi mashi ƙari.
Idan muka yi la'akari da
bayanin da ya gabata da kuma yadda muka yi bayani tun farko cikin
nazarin waƙar Maimartaba sarkin Zamfara
Attahiru, na kawo zubin baitocin waƙoƙin baka
ya sha bambam dana rubutatun waƙoƙin domin
a cikin waƙoƙin baka za mu tarar da
cewa akwai layi biyu - biyu ne, dan haka wanda ya ke a rubutattu ba haka abin
ya ke ba sai dai idan waƙa mai ɗango biyu-biyu zai kasance kowane baiti yana
da waɗannan ɗangwayen wato biyu ko uku ko hudu ko kuma
biyar.
Haka zalika a cikin wannan waƙar Dangunduwa ya fara kai tsaye da kiran sunan
basaraken, yana cewa :
Kai maza ka shakka mugun madambaci Atta
Bayan haka wannan mawaƙin ya tsara wakarsa ne acikin baiti biyu-biyu,
sannan ya na marmaita wasu daga cikin baitocin, bayan haka ‘yan amshi suna yi mashi ƙari.
Zubin layukkan baitocin waƙar baka ya sha bamban da rubutacciyar
waƙa, domin kuwa a cikin waƙar baka ana iya samun baiti mai dangi daya
(gwaron dango) ko baiti mai dango biyu (tagwai ko mai dango uku). (yar uku) ko
hudu (tarbi’i) ko kuma biyar (tahamisa) har ma fiye
da haka ana samu a cikin waƙoƙin baka. Amma ita waƙar da muke nazari, tana da layukka da zuwa biyu
a matayin dango guda misali, 1, 2.
4.4.3. Turken waƙoƙinsa
Kamar yadda bayani ya gabata
cewa duk waƙoƙin Alhaji Dangunduwa Kagara
ba su wuce Muhimman turke guda biyu ba, watau zuga da turken yabo, to shi
wannan jigon yabo shi ma kamar yadda jigon zuga ya kasu kashi biyu shima ya
kasu kashi biyu, domin akwai yabon na musamman watau na Alheri da ake yi masa
sannan akwai yabo irin na koɗawa watau irin wanda ya ke aiwatarwa ga mutanensa watau ‘runji, manoma ko sarauta.
Misali kamar yadda za
mu gani a cikin wasu waƙoƙin fawa
na Alhaji Dangunduwa Kagara , turken kamar yadda muka sani cewa turke a cikin
waƙoƙin shi ne abin da waƙar take tafe da shi ko kuma abin da waƙar take son ta isar ga al'umma. Saboda haka ita
wannnan waƙa turken shi ne zuga, watau a inda ya ke cewa:-
"Sai na kai kiɗa gidan sarkin fawa Ummaru, kai ar shugaban mayanka shanu kaf ƙasar Kagara,
Dawo Ummaru ‘yan runji ai sun sanda ba su yi
Ida Ummaru ya yi magana
ban san mai iya tayar mai ba,
Ai ga wani saunan sakin
fawa,
Shi bai yanka bai alheri,
Sai in sunyi ya ɗauki kwashi”
Idan muka duba a cikin wannan waƙa daga ɗa na biyu har zuwa na uku, a nan jigon ya nuna
mana cewa sarkin fawa Ummaru wani shahararren barunje ne wanda
bai yarda da wasa ba, kuma ba a
kai masa reni sannan kuma ya bayyana shi sarkin fawa Ummaru da cewa”idan Ummaru ya yi magana ban
san mai iya tayar mai ba. Dan
haka Dangunduwa Kagara ke kiransa da cewa:-
Ummaru ‘yanrujji ai sun sanda ba su yi
A cikin wannan waƙa,
Dangunduwa Kagara ya na nuna mana cewa ko shakka babu, Sarkin Fawa Ummaru
da gaskiya yake yin wannan sarauta ba da wasa yake yi ba.
Bayan haka, duk a cikin waƙar Dangunduwa
Kagara ya fito
mana da wani zambo, dangane da haka sai a dubi wannan baiti:-
" Ai ga wani saunan
sarkin fawa,
Shi bai yanka bai alheri,
Sai in sun yi ya ɗauki kwashi”
A nan Dangunduwa Kagara yana son ya bayyana mana irin lalacewa da kuma
nuna komawar baya da wani sarkin fawa ya yi a fagen sana’arsa ta fawa.
4..4.4. Warwarar Turke
Jigo shi ne wani muhimmin saƙon da
mawaƙi yake son isarwa a cikin waƙarsa,
watau manufar ko maƙasudin waƙar. (Gusau,
S.M. 1989).
Shi ma Dokta Tanimu Yar’aduwa
a cikin littafensa yana cewa turke shi ne ginshiƙin waƙa don kuwa duk waƙar da ta
kasance ba ta da turke to ba waƙa ba ce. Akwai masana adabi
ko masu nazarin waƙa sun yi la’akari da
fito da wasu hanyoyin nazarin waƙa wajen nazarin turke :
1. Hanya ta farko ita ce ka
gano jigon wajen sauraron da kake yi, watau mene ne saƙon mawaƙin.
2. Hanya ta biyu ita ce bayan
ka gano abin da mawaƙi yake nufi a waƙarsa sai
ka yi ƙoƙarin bayyana turken mawaƙin.
3. Hanya ta uku ita ce wanda maisauraro zai
warware turkenn ko feɗe turken mawaƙi.
Turken Zuga
Kamar yadda muka sani cewa turke a cikin waƙoƙin baka kamar ta makaɗa
Dangunduwa Kagara shi ne abin da
waƙar ta ke tafe da shi ko kuma abin da waƙar take son ta isar ga al'umma. Saboda haka ita
wannnan waƙa turkenta shi ne
zuga, watau a inda yake cewa a cikin waƙarsa ta
noma:-
"Lawali na Abu Sarkin noma,
Allah mai san Anka inga Lawali na Abu Sarkin noma,
Lawali ko ana fari ya fi gaban kakare,
Lawali ka noma ɗari ka kuma noma dubu don mun gani ».
Ga wagga ƙasa duk
mai riƙa kalme ya san da kai,
Gabas da yamma ga hanya ba su da daji ko ɗan kaɗan
Sarkin noman yamma ga kwalta ya sassabe,
Na Ɗan mani
barkerka da yaƙin noman hatse,
Na Ɗan mani
barkerka da yaƙin noman gyaɗa”.
Idan muka duba a cikin wannan waƙa daga saɗara ta uku
har zuwa ta shida,
a nan turken ya nuna mana cewa Lawali wani shahararren
manomi ne wanda bai yarda da wasa ba,
kuma ba a kai masa reni sannan kuma ya bayyana shi Lawali da cewa Lawali ko ana fari ya fi
gaban kakare, Dangunduwa Kagara ke kiransa
da cewa:-
“Na Ɗan mani
barkakka da yaƙin noman hatsi,
Na Ɗan mani barkakka da yaƙin noman gyaɗa”.
A cikin wannan waƙa,
Dangunduwa Kagara yana nuna mana cewa ko shakka babu, Lawali da gaskiya
yake yin wannan sana’a ba da wasa yake yi ba.
Bayan haka, duk a cikin waƙar, Dangunduwa
Kagara ya fito
mana da wani turke na nuna bajinta, da
Lawali ya yi haka kuma ya bayyana mana shi dai Lawali duk yawan da ya ba mu labarin jaruntakar shi
idan an fito fagen fama, dangane da haka sai a dubi wannan ɗa:-
"Na Ɗan mani
barkakka da yaƙin noman hatsi,
Na Ɗan mani barkakka da yaƙin noman gyaɗa”.
A nan Abdullahi Dangunduwa Kagara yana son ya bayyana mana irin
jaruntakarsa, da kuma nuna bajinta da Na Ɗanmani
yake da ita, idan an fito fagen fama.
Haka kuma Abdullahi Dangunduwa Kagara cikin waƙarsa ta Sarkin Mayanchi, ya fito mana da wani turke
Idan muka duba wannan waƙar za mu
ga cewa turken wannan waƙar ya fito ne a cikin ɗa na bakwai. A nan ya nuna mana cewa, Sarkin
Mayanchi wani shahararran Sarki ne, wanda Abdullahi
Dangunduwa Kagara ya fito mana da turken Juriya ga wannan basarake wato Sarkin
Mayanchi inda yake cewa:
"Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,
Sabon gari Ƙasimu,
Allah babban mutum ya yi ka,
Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,
Sabon gari Ƙasimu,
Na Anaruwa ƙara gyaran faɗa
Tsare aiki cikin gaskiya
Duk mai aikin cikin gaskiya
Yana samun rabon duniya
Yana samun rabon lahira
Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,
Sabon gari Ƙasimu,
Allah babban mutum ya yi ka.
A cikin wannan ɗa,
Abdullahi Dangunduwa Kagara ya nuna mana cewa Sarkin Mayanchi, Shahararren
sarki ne mai gaskiya, saboda zamansa
buwayayye sai dai kallo domin duk yadda ka yi ba za iya ba shi cin hanci ya yi rashin gaskiya ba kamar
yadda mawaƙin ya nuna mana cewa, “Tsare aiki cikin
gaskiya,
Duk mai aikin cikin gaskiya "
To kaga wani ɗan ya
nuna mana cewa mai gaskiya ne, duk abin da ka yi sai dai ka gaji ka barshi wuri
nai.
Idan muka yi
la'akari da bayanin da ya gabata a nan za mu iya cewa wadannan waƙoƙin na
Abdullahi Dangunduwa Kagara na da muhimmin saƙo, wannan saƙon kuwa
nau'i - nau' ne daga cikinsu akwai babban saƙon da ya haifar da a aiwatar da su daga cikinsa akwai saƙon zuga watau. turken zuga ke nan
san nan akwai saƙon yabo watau turken yabo kenan, dan haka turken zuga shi ne
babban turken waƙoƙin Abdullahi Dangunduwa Kagara saboda.
Kasancewar mashahuri a wajen kiɗa, Abdullahi Dangunduwa Kagara na tabbatar mana da
cewa dama shi turken waƙoƙinsa zuga da yabo, domin
a cikin waƙarsa ta
Banagan Morai watau Alhaji Abdulmalik, akwai inda yake rerawa da bakinsa cewa:-
"Banaga
Ubanƙasa mai kwana da martaba,
Dandanau na Bubakar,
Banaga
Ubanƙasa gumbar tsakkuwa,
Wai
wawa da yagguma,
Haure nan yakkatse "
Saboda haka idan muka dubi wannan
gutsiren waƙa ta Abdullahi
Dangunduwa Kagara za mu fahimci cewa wannan zuga ne ya ke yi tsakanin sa
da wani.
Haka a cikin wannan waƙa har
yanzu Abdullahi Dangunduwa Kagara na cewa:-
Ni ka hadawa bani rabawa
Duk wadannan ire-ire zuga ne waton.zuga sarki, shi da wasu
kalmomi domin ya firgice ya ba shi kyauta, ko wani abu mai kama da haka. Kamar yana haɗa shi da wasu ‘yan sarki ko kuma wasu
talakkawa da sauransu, haka kuma wannan zugin yana sa sarki ya ƙara shiri. Misali a cikin waƙar da Abdullahi Dangunduwa Kagara ya yi ta Musa Narabi ta noma akwai inda yake
cewa :-
Sai dare yana daji gonatai,
dawo na Rabi mai kalme wa kilba".
Shi kuma
Jikin sa ya yi kaf da zan-zana sai ya fara kirari kamar haka:-
"Kai Abdu mai kidin
Noma,
Wai na ji kana yabon kanen
su Tafarki,
To gobe in muka game wurin noma,
Rannan sai anyi ba dare ba rana,
In bani ba Abdu kanan su Tafarki,
Rannan in ba a sha ga Gyamdama ta watse,
Ko yaggiya ta tsuke ke shi”.
A takaice
irin wannan zuga a tsakanin sarakuna ko manoma yana da yawa, sai dai mu
kawo irin waɗanda muke
iya kawowa.
Turken Habaici
Habaici
wanda ya ke tamkar zagin kasuwa ne wani jigo ne wanda makaɗa Alhaji Abdullahi
Dangunduwa Kagara ke amfani da shi a cikin waƙoƙinsa domin ya adanta waƙarsa ko ya yi suka ga wani mutum zuwa ga wadansu manoma ko wadansu mutane
na daban. Haka kuma ya kan yi amfani da shi domin ya isar da wani saƙo ga sarki ko wanda ya kewa waƙa. Misali a cikin waƙarsa ta sarki
Morai Banaga Abdulmalik in da ya ke cewa:-
ai ga wani yasha
kashi,
ya iske tumaki kwance,
sai yace ku wadanga ina kwana
ku".
Haka kuma cikin waƙarsa da yawa wannan basaraken in da ya
ke cewa:-
‘Wai wawa da yagguma,
Haurenan yakkatse ".
A cikin duk kan waɗannan misalai guda biyu da mu ka zai
yano zamu ga cewa makaɗa
Abdu Dangunduwa shi na habaici ga wadansu jama'a, haka kuma shi na da kyau a
san cewa shi habaici ya babban ta da zambo , domin ba'a fadin siffar mutum ko
sunan shi, sai dai a yi zagin kasuwa kowa ya doka don kai ne.
Turken juriya.
Haka
kuma Abdu Dangunduwa
ya yi amfani da turken
juriya. Watau anan ana nuna ainihin karfin halin mutun wajen
jurewa wahala ko wace iri ce da kuma nu na cewa idan wani ya sami kansa cikin wannan wahala
to ba shakka ba zai yi raki ba. Misali a cikin waƙar da Abdu Dangunduwa ya yi inda ya ke cewa:-
"Gwarzon
Usmanu ƙara shirin daga,
Sabon gari Ƙashimu,
Allah babban mutum ya yi ka,
Gwarzon Usmanu ƙara shirin daga,
Sabon gari Ƙashiu,
Na Anaruwa ƙara gyaran faɗa »
Turken zambo
Haka kuma Abdu Dangunduwa Kagara ya yi amfani
da turken zambo. Zambo shi ne munana mutum KO kuma muzanta shi, misali a cikin waƙar
Abdu Dangunduwa Yana cewa:-
Dan sarki yakoma kamar mata Yana shapa
hoda da jan baki yara suna cewa koya tafu
Idan muka yi la'akari da wandannan ɗiyan za mu ga cewa ko shakka babu Abdu Dangunduwa ya yi zambo ne ga wasu maƙiyan wannan
basaraken domin ya ƙara rage mu su darajja a
idon jama'a domin shi wannan basaraken ya kara harzuƙa kuma
darajarsa da ƙara fitowa a idan mutane.
Turken Yabo
Kamar yadda bayani ya gabata cewa duk waƙoƙin Alhaji Abdu
Dangunduwa ba su wuce Muhimman turke guda biyu ba, watau zugi
da turken yabo, to shi wannan turke na yabo shi ma kamar yadda turken zuga ya kasu kashi biyu shi ma ya kasu kashi biyu,
domin akwai yabon na musamman watau na Alheri da ake yi masa sannan akwai yabo
irin na koɗawa watau irin wanda yake
aiwatarwa ga mutanensa watau manoma ko sarauta.
Yabon alhairi
Shi wannan turken na yabo da Abdu Dangunduwa ke amfani da shi wajen
yabon mutanen da ke taimaka masa saboda nuna gamsuwar su da irin abin da yake yi kamar a cikin
waƙarsa ta Banagan Morai ya kawo irin su Maudaci da Direban
sarki da Bunun Morai, da sauransu.
Turken Yabo Irin Na Koɗawa
Kamar yadda muka bayyana baya cewa akwai turken yabo irin na koɗawa watau, yabo ne da ake amfani da wasu kalmomi irin waɗan da su sarakuna ko manoma suke son a rinƙa
kiransu da su ko wani aiki wanda za a yabe su da shi a ce su suka yi shi ko da ko
ba su aikata shi ba. Misali, irin waɗannan
kalmomi sun fara ne tun daga sunayensu misali za ka ji sunnan su kamar
haka: zaki, gwarzo, toron giwa da dai sausansu
To dai kamar yadda sunayen nan na su yake
to a kuIlun haka suke son a rinƙa
yabon da ire-ire wadannan ababe misali idan ka dubi waƙar babban
gwarzonsa watau yabo kamar inda ya ke cewa:-
"Gwarzon
Usmanu ƙara shirin daga,
Saban gari Ƙasimu »
Kai abin
sai dai kurum domin idan ka dubi irin wannan yabo ka san cewa daban ne da irin
wanda Alhaji Abdu
Dangunduwa ya ke wa su mutanen Mayanchi da dai sauransu. Inda yake
cewa :
«
Mutan Mayanchi muna godiya zay yawa,
Domin kun yo abin a
yaba ».
Saboda
haka irin waɗannan
kalaman da ya ke amfani da su ga sarakuna ba irin sa ne ya ke yi wa mutanen da
ke bashi alheri ba amma dai duk yabo ne.
4.4.5. Salon Waƙoƙin Alhaji Abdu Dangunduwa
Ma’anar Salo:
Wata
hanya ce ko dabara ce da mawaƙa ko
marubucin waƙa ke
bi domin ya isar da saƙo ga
masu saurarensa.
Ire-iren
salai-lan da yake amfani da su, game gari ga duk wani mawaƙi ko marubuci shi ne salon
siffantawa wani nau’i ne na salo wanda mawaƙi ke amfani da shi ya siffanta wani
abu da ka ganshi ka ce ai wannan
ne. A ƙarƙashin
wannan akwai salo daban-daban misali salo kamanci, salon kinaya salon jinsarwa,
salon alamtarwa da sauransu. (Gusau, S. M..1984).
Saboda haka Alhaji Abdu Dangunduwa ya
fi amfani da salon jinsarwa a cikin
waƙoƙinsa.
Salon jinsarwa: shi ne
wani nou’i na salon siffantawa wanda ke nufin daukar darajar wani a ɗaro wa
wani wato kamar ka ɗauki darajar mutum ka ba
dabba, ko ta tabba ka ba
mutum.To shi jinsarwa saƙo ne
wanda ya kasu gida? (uku) kamar haka:-
1. Matumtarwa
2. Dabbantarwa
3. Abuntarwa
A cikin
waƙarsa wanda ya yi wa Maimartaba Sarkin Zamfara ya yi amfani da
salon kambamawa in da ya ke cewa:-
« Kai maza
ka shakka mugun madambaci Atta,
Ba takura jan Zaki »
Haka kuma Alhaji Abdu Dangunduwa ya yi amfani da salon dabbantawa a cikin waƙarsa ta Mai martaba Sarkin Anka a inda y