Binciken Da Aka Gudanar A Sashen Harsunan Nijeriya Da Kimiyyar Harshe Na Jami'ar Sule Lamiɗo Da Ke Garin Kafin Hausa, Jihar Jigawa, Domin Samun Takardar Shaidar Kammala Digiri Na Farko (B.A HAUSA), 2023
Falsafar Bahaushe Cikin Littafin Tatsuniyoyi Da Wasanni Na Ibrahim Yaro Yahaya
NA
HABIBA
ABUBAKAR IBRAHIM
TABBATARWA
Na tabbata cewa, ni na rubuta
wannan kundin bincike da kaina, mai suna "Falsafar Bahaushe cikin
littafin tatsuniyoyi da wasanni na Ibrahim Yaro Yahaya". A ƙarƙashin jagorancin Dr. ABDULƘADIR Ginsau. Kuma duk bayanan da aka samo daga wata madogara an ambato
madogarar a cikin matani da kuma manazartar da aka ratayo. Babu wani sashe na
wannan aiki da aka taɓa gabatarwa a wani
wuri a matsayin kundin digiri ko diploma ko kuma maƙala a cikin mujallu wadda wannan bincike ya riska.
SHAFIN
AMINCEWA
Wannan kundi mai taken‚ "Falsafar
Bahaushe cikin wasannin gargajiya" ya sami karantawa da dubawa da
samin amincewa a matsayin wani ɓangare na cika sharuɗɗa da ƙa’idar samun shaidar digiri na farko (B.A Hausa) a
tsangayar Adamtaka, sashen Nazarin Harsunan Nijeriya da kimiyyar harshe ta
Jami’ar Sule Lamiɗo da ke Kafin
Hausa, Jihar Jigawa.
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan bincike ga mahaifana
Mal. Abubakar Nasalla, da Umma-kaltume Muhammad (Mama), da Mal. Harisu Babale,
da kuma sashen harsunan NIjeriya, da sauran ƴan uwana, da
ma ɗaukacin
musulmi baki ɗaya.
GODIYA
Ina godiya ga Ubangijin dukkan halittu, godiya
ga Allah (S.W.T) da kowanne al'amari ke komawa gare shi, mai kowa, mai komai,
mahaliccin sammai da ƙasai da abin da yake tsakaninsu,
ya kuma daidaita a al’arshinsa. Godiya ga Allah (S.W.T.) wanda yake saukar da
ruwan sama, kuma yake tsara al'amuran bayinsa yadda yaso. Godiya ga Allah
(S.W.T.) da ya samar da ilimi, ya arzurtawa bayinsa , ya yi musu baiwar
dawwamar da shi a ƙwaƙwalansu,
sannan ya ba shi hikimar yin tunani a kowanne irin al'amari. Tsira da aminci su
ƙara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi
Muhammad (S.A.W.) da iyalansa da Sahabbansa da waɗanda suka bi
tafarkinsu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Jagoran duba wannan kundi, Dr. ABDULƘADIR
Ginsau, haƙiƙa ya cancanci
godiya ta musamman, saboda jajircewarsa wajen ganin wannan kundi ya kai gaci,
ya yi matuƙar ƙoƙarin
nusarwa da ba da shawarwari masu matuƙar
muhimmanci, Ina roƙon Allah (S.W.T.) ya ƙara
masa lafiya da haƙuri da karamci, Allah ya ɗaukaka shi ya
kuma ƙara masa ilimi, Allah ya kyautata rayuwarsa
da ta iyalinsa, Allah ya biya masa duk buƙatunsa na alheri,
Allah ya yi masa sakayya da gidan Aljanna.
Godiya
ta musamman ga Jami’ar Sule lamiɗo ta Kafin Hausa, wadda ta ba ni
gurbin gudanar da wannan karatu. Farfesa Aliyu Mhammad Bunza yana sahun farko a
mutanen da suka ba ni ƙwarin gwiwar gudanar
da wannan bincike . Ina miƙa godiyata a
gareshi da kuma ɗumbin jama’a
da suka taimaka yayin da nake tattaro bayanai da kuma rubuta wannan kundi.
Gudummuwar da na samu a wurin jama’a ta taimaka wajen warware matsaloli masu
yawa, kuma ta kawo mafita ga hanyoyin da aka bi aka tattaro bayanai .
Wannan godiya ba ta manta da malamai na Sashen
Harsunan Nijeriya ba na Jami’ar Sule Lamiɗo ta Kafin Hausa.
Gudummuwar da Dr. Mu'azu Sa'adu kudan da Dr. Ɗahiru Abdulƙadir,
Dr. Habibu Abdulƙadir, Dr. Abdulƙadir Ginsu,
Mal. Muhammad Sani, da kuma sha kundum wanda ya ɗora mu bisa
hanyar aiwatar da bincike, ya nusar damu ta hanya mai kyau Mal. Yusuf Nuhu
Inuwa, haƙiƙa wannan
bincike ba zai manta da irin gudummawarsa ba da jajircewa wajen ganin an iya
kuma ya yi kyau, Allah ya biya su da kyakkawan sakamako.
Haka kuma ina miƙa godiya ga
manyan malamai masu ziyartar wannan sashe, Farfesa Bashir Aliyu Sallau, da Dr.
Salisu Garba Kargi, saboda shawarwarinsu da haƙuri da suka
yi wajen gabatar da tambayoyi da neman ƙarin bayani
ga abubuwan da suka shiga duhu a wannan bincike. Allah ya haɗa mu a
Aljanna baki ɗaya. Ba zan
manta da Farfesa Ibrahim Garba satatima ba, shi ma ya bada gudummawa sosai a
wasu ɓangarori na
wannan binciken Allah ya biya su da gidan Aljanna..
Masu iya magana sun ce, 'Hannu da yawa maganin
ƙazamar miya.‛ Ina miƙa godiya ta
musamman ga Farfesa Sa’idu Muhammad
Gusau, haƙiƙa farfesa ya
bada gudunmawa marar iyaka a wajen aiwatar da wannan bincike, tare da nusarwa
da shawarwari harma da wasu guzuri duk da za su taimaka binciken ya kai ga
kammaluwa cikin nasara, Allah ya biya shi da gidan Aljanna.
Godiya ta musamman ga mahaifana, marigayi
Malam Abubakar Nasalla, da kuma Ummakaltume Muhammad, saboda haihuwa da raino
da kuma tarbiyya da suka ba ni har Allah ya kawo ni wannan matsayi, Allah ya
saka musu da mafificin alheri, ya yi musu rahama ya kyautata ƙarshensu,
shi da ya rasu Allah ya masa gafara, ita kuma Allah ka dawwamar dafarin ciki a
rayuwarta ka sa aljanna ce gidanmu na ƙarshe baki ɗaya.
Ina godiya ta musamman ga yayyena da kuma ƙannena
saboda haɗin kai da
goyon bya da nake samu a wurinsu. musamman babban yayana Yakubu Adamu da ya ɗauke duk wata
ɗawainiyar
karatuna tun daga matakin farko, Allah ubangiji ya saka da alheri ya kuma bamu
ikon kyautata musu, Sauran ƴan uwana da suka
ƙunshi: Maryam Abubakar, Asma'u da Khadija
duka Allah ya haɗa mu a gidan
aljanna.
Godiya ta musamman ga Malam Harisu, Uba ne
tamkar mahaifi a gurina ya bani gagarumar gudummawa a rayuwata da ta mahaifiya
ta, Ubangiji ya saka masa da mafificin alheri yasa aljanna ce gidansa na ƙarshe.
haka kuma ina godiya ga yayyena da ƙanne,
Babannan, Faruq, Yahaya, Habu, Shu'aibu, Abdurrahman (marigayi), Sulaiman,
Adamu ,Nura, Aishatu (babbar yaya), Rabi, Bilkisu, Fatima,Maryam, Rahama,
Hauwa'u, Allah ya haɗa mu a gidan aljanna
Abokai
sun taimaka min sosai a wannan aiki, musamman Malam Yusuf Mukhtar (Ɗawisu)
Babban abokin karatu kuma mai bani shawarwari a fannoni daban-daban. Da kuma
Maryam Aliyu Usman, Zainab tijjani, da sauran abokan karatu da abokan arziƙi
na cikin makaranta da wurin kwana (hostel), Allah ya saka da alheri ya sa
ilimin da muke yi mai amfani ne .
TSAKURE
Wannan
bincike mai suna Falsafar Bahaushe cikin littafin tatsuniyoyi da wasanni:
Nazari ne daga Adabin Baka da ya nazarci tunanin Bahaushe da ke cikin
Tatsuniyoyinsa da wasanni da ya riƙa
aiwatarwa a rayuwarsa, binciken ya mayar da hankali a kan yadda Bahaushe yake
sarrafa tunani da hikima da basira da kuma yadda ya ci moriyar kowannensu. Daga
cikin tunanin da wannan bincike ya riska a waɗannan
rassan na adabin Bahaushe akwai: Muhallin da yake gina su da kuma Taurarin da
suke aiwatarwa da duk wasu al'amuran da suka jiɓanci
rayuwarsa da zamantakewarsa. Binciken ya nazarci tunanin Bahaushe ne cikin waɗannan muhimman rassa na adabin baka (wasanni da tatsuniya
). Tunani wani abu ne da ɗan’adam yake amfani da shi mai matuƙar tasiri wajen gudanar da harkoki da
suka shafi zamantakewa a cikinsa, yana kuma gudanar da al’amuran da suka shafi
tattalin arziki da shugabanci da sauransu. Bincike ya yi magana a kan tunani
yana nusar da mutum da abinda yake nufi a zuciyarsa. binciken ya ƙuduri aniyar cike giɓin da nazari a tunanin Bahaushe ya bari. ya kuma fito da
dangantakar adabi da tunanin Bahaushe a ɓangarori daban-daban, sannan ya yi ƙoƙarin
tabbatar da Bahaushe yana da nasa tunani a cikin wasanni da tatsuniyoyi .
Binciken ya bi hanyoyi da dabaru iri daban-daban wajen tattaro bayanai da
tantance su a wannan aiki. Binciken ya zaɓo nau’o’in adabin baka, kuma ya yi
amfani da zaɓi na kusanci a lokacin da ya zaɓi wasanni da tatsuniyoyi wadda duka suke da makusanciyar
alaƙa, a inda ya ziyarci manyan ɗakunan karatu a makarantu daban-daban na wannan yankin.
ya kuma yi hira da manyan masana da tsofaffin masan harshe da adabi ,
ziyarce-ziyarce na cikin hanyar tattaro bayanai, binciken ya yi amfani da
nazarin littafin tatsuniyoyi da wasanni gaba ɗayansu.
A ƙarshe, binciken ya gano adabin baka na
Hausa maƙunshin tunanin
Bahaushe ne a kan al'amura da dama. Binciken ya gano akwai tasirin tunanin
Bahaushe ga tarbiyyar ƴaƴansa, kuma al’ada tana da muhimmanci wajen gina waɗannan rassa na adabin baka na Hausa. Adabin baka na Hausa
yana yin duba a kan da’irar rayayyun halittu wajen fito da idon zucin al’umma a
kan zamantakewarsu a wurare daban-daban da suke rayuwa a cikinsa. Idon zucin
Bahaushe a adabin baka yana kimanta rayuwa wajen suranta ta da yanayin da
Bahaushe ke tafiyar da al'amuransa ta hanyar amfani da tunani a fuskoki daban-daban.
ƘUNSHIYA
TABBATARWA--..II
AMINCEWA-III
SADAUKARWA----.IV
GODIYA…-....V
TSAKURE-....IX
ƘUNSHIYA-.XI
BABI NA ƊAYA
GABATARWA
1.1- Shimfiɗa-..1
1.2 Manufar bincike----2
1.3- Dalilin bincike----.3
1.4- Hasashen bincike----.4
1.5- Muhimmancin
bincike--...5
1.6- Farfajiyar bincike----.7
1.7 Naɗewa---8
BABI NA
BIYU
BITAR AYYUKAN
MAGABATA
2.1- Shimfiɗa-..9
2.2- Hausa da Hausawa
da ƙasar Hausa--..10
2.3- Falsafar
Bahaushe (Tuntuntuni)-.26
2.4- Wasanni-.43
2.5- Tatsuniya--....49
2.6- Naɗewa-..64
BABI NA UKU
HANYOYIN
GUDANAR DA BINCIKE
3.1 Shimfiɗa-..65
3.2 Hanyoyin tattaro
bayanai--..65
3.3 Babbar hanyar
tattaro bayanai---67
3.4 Ƙaramar
hanyar tattaro bayanai-...68
3.4.1Tattaunawa------68
3.4.2 Ziyartar
Dakunan karatu--69
3.5 Naɗewa-...71
BABI NA HUƊU
FALSAFAR
BAHAUSHE CIKIN LITTAFIN TATSUNIYOYI DA WASANNI
4.1 Shimfiɗa-..72
4.2 Dangantakar
falsafa da adabin baka--..72
4.3 Falsafar Bahaushe
cikin Tatsuniyoyi da Wasanni------...79
4.3.1 Muhalli-.81
4.3.2 Al’amuran
Rayuwa--....82
4.3.3 Taurarin
Tatsuniya--86
4.3.4 Waƙa-....90
4.4 Tatsuniyar Gizo
da ɓaure--93
4.5 Tatsuniyar Dan
Sarki ya zama maciji--98
4.6 Tatsuniya Na-goma--102
4.7 Wasannin Ka-cici-ka-cici...105
4.9 Wasanin Bata---------110
4.10 Naɗewa----113
BABI NA BIYA
NAƊEWA
5.1 Shimfiɗa-114
5. 2Taƙaitawa--....114
5.3 Sakamakon bincike--117
5.4 Shawarwari--.121
5.5 Kammalawa--125
Manazarta-....126
RATAYE NA1--.135
RATAYE NA 2--137
RATAYE NA 3--154
BABI NA ƊAYA
GABATARWA
1.1 SHINFIƊA
Fannin adabi, fanni ne mai faɗin gaske
wadda ya ƙunshi ɓangarori da dama da
ake gudanar da nazari a cikinsu da suka haɗa da waƙoƙi,
azancin magana, karin magana, tatsuniyoyi, labarai har ma da wasanni kwaikwayo
iri-iri da kan zo a ƙarƙashin
adabin Hausawa, ba ma iya waɗannan kaɗai ba, domin
kuwa akwai wasanni daban da suke aiwatarwa waɗanda suka haɗa da wasannin
yara na manya harma da ƴammata da kuma samari
wadda har ta kai ga manazarta suna rubuta su da killacesu a littattafai. Haka
kuma abu ne sananne cewa kowacce al'umma da yadda take kallon rayuwa, da kuma
tafarkin da take bi wajan tabbatar da al'ummarta, ta yanda take son su yi riƙo
da ita. Wannan ya nuna cewa kowace al'umma da yanda take gina mu'amalarta
tsakanin al'ummarta, amma duk da yadda ake kallon abubuwan rayuwa, tushen
ma'aunin ɗaya ne, wato
Tunani. Tunani na ɗaya daga cikin darajojin da ya bambanta mutum
da dabba da ma sauran halittu da ke doron ƙasa, da
tunanin gane daidai da akasin haka ɗan Adam ya ƙara samun
fifiko wajen yunƙurin kyautata rayuwarsa da kuma taimakawa ƴan
uwansa bil'adam ta fuskoki daban-daban, domin su samu nutsuwa da jin daɗin rayuwa,
hakan ne yasa galibi cikin hanyoyin da tunananin ɗan Adam
(musamman al'ummar Hausawa) ke kai shi ga daɗaɗawa abokin
zamansa akwai Wasa.
Ba haka kawai Hausawa ke aiwatar da wasanninsu
da kuma tatsuniyoyinsu ba da har ake iya gudanar da nazarce-nazarce game da su,
akwai wasu dabaru da hikimomi har ma da fasahohi masu tarin yawa da suke cuɗanyawa
cikinsu, wannan dalili yasa wannan aiki ya ƙudiri aniyar
binciko irin hikimomi da falsafofin da ke cikin wasannin na gargajiya da kuma
tatsuniyoyi, hakan ne ma kuwa ya sa aka zaɓi sanya wa
binciken ko batun suna da "Falsafar Bahaushe cikin littafin tatsuniyoyi da
wasanni na Ibrahim yaro yahaya". domin kuwa wasanni da tatsuniyoyi abubuwa
ne da suke da matuƙar tasiri a wurin
al'ummar Hausawa, kasancewarsu abubuwa ne da ke killace da harshenta da kuma
al'adunta hakan yasa ba za a rasa wani ɓoyayyen tunani
cikinsu ba, don haka binciken zai yi ƙoƙarin
fito da falsaafar da ke cikinsu.
1.2 MANUFAR
BINCIKE
Babu wata al'umma a doron ƙasa
da ba a aiwatar da bincike a cikinta ta hanyar amfani da dabaru domin adana duk
wani tunaninta. Bisa ga wannan masaniyar yasa kowanne abu a duniya da za a
aiwatar akan aiwatar da shi bisa manufa ta musammam. Wannan binciken na da
manufofi kamar haka:
v
Fito da hikimomin da ke ƙunshe cikin
wasannin Hausawa da kuma tatsuniyoyinsu na gargajiya.
v
Nuna yadda Bahaushe ke gudanar da al'amuransa
cikin falsafa ta hanyar wasannin gargajiya.
v
Gwada yadda Hausawa ke amfani da wasanninsu
da ma labarai na tatsuniya wajen ilimantar da ƴaƴansu
da kuma nuna musu yadda ake tarbiyya da mu'amalolin rayuwa.
v
Fayyace yadda tunanin Bahaushe ya ke a cikin littafinin.
1.3- DALILIN
BINCIKE
Duk wani al'amari na duniya da ya faru ko kuma
aka aiwatar da shi ba ya rasa wani dalilin da ya yi sanadiyyar faruwarsa ko
aukuwarsa. Lura da wannan yasa kowanne bincike ake ɗora shi bisa
tarin dalilai da ya haddasa gudanar da shi, to haka abin ya kasance ga wannan
binciken, domin kuwa ba haka kawai aka tarki gudanar da shi ba akwai wasu tarin
dalilai da suka haddasa gudanar da shi da suka haɗa da:
v Da farko an
zaɓo littafin
wasanni da tatsuniyoyi ne saboda kasancewarsu sanannu a wurin al'ummar Hausawa,
bayan saninsu da aka yi kuma har ila yau akan koyar da su takanas a ƙananan
makarantu domin kuwa sune kan gaba wajan samuwar adabin Bahaushe.
v Dalilin da ya
sa aka zaɓi amfani da
adabin baka na Hausa a ɓangaren tatsuniyoyi da wasanni domin fito da
hikimominsu shi ne, duk wasu al'amuran Bahaushe na taskace a cikin adabinsa.
ita kuma hikima tamkar jagora ce cikin al'amuran Bahaushe, wadda yake amfani da
ita wajen bayyana al’adunsa da kuma kyautata al'amuran rayuwarsa. Domin haka ne
aka zaɓi yin nazarin
falsafar cikinsu.
v Domin ɗaga darajar
wasannin musamman na gargajiya da ke neman ɓacewa gaba ɗaya, saboda
rashin ire-iren waɗannan ayyuka da za su ke ɗaga
darajojinsu da fito da saƙonninsu.
v Daga cikin
manyan dalilan aiwatar da wannan bincken shi ne ido bai kai ga wani aiki da aka
gabatar game da falsafar Bahaushe akan wasannin gargajiya ko tatsuniyoyinsu ba,
bisa nazari da wannan bincike ya yi a ɗakunan karatu na
wannan jami'a da ma sauran jami'o'i daban-daban da sauran fannonin ilimi .
Aikin ya samu bayanai akan wasannin gargajiya da dama cikin littattafai da
kundaye da mujallu, amma babu wani da aka riska wanda ya taɓo falsafar
Bahaushe cikin littafin tatsuniyoyi da wasannin.
Wannan su ne manyan dalilai da suka tunzura
mai gudanar da wannan binciken zaɓar wannan batu.
1.4 HASASHEN
BINCIKE
Akwai
hasashe da dama da aka gina game da wannan binciken da suka daɗa da:
v wannan
binciken na hasashen cewa akwai wani dalili da ya sa Hausawa suke gina falsafa
a cikin tatsuniyoyinsu da wasanninsu.
v
Tatsuniyoyi da Wasannin gargajiya a wurin
Bahaushe na daga cikin hanyoyin da ya ke bi wurin gyaran zamantakewa da kuma
kyakkyawar mu'amala, wannan yasa ba za a rasa hikimomi ƙunshe cikinsu
ba.
v
Binciken na hasashen cewa ba iya cikin saƙon
wasa ko tatsuniya Bahaushe ke sanya hikimarsa ba, galibi akan samu wasu
hikimomin ga abubuwan da aka gina tatsuniyar da su, kamar wurare, taurari da sauransu.
wasu kuwa sai an yi nazari mai zurfi ake gane hikimar da ke cikinsa.
v
A Ƙoƙarin
gano irin yadda falsafa ta kutsa cikin adabin baka na Hausa, duk da cewa suna
da dangantaka ta jini. Ana hasashen cewa idan manazarta suka dubi wannan aiki,
lalle za su fahimci cewa falsafa na matuƙar bayar da gudummawa
wajen haɓakar adabi.
v
A wannan aiki, ana hasashen cewa irin waɗannan
hikimomi da Bahaushe ke sakawa cikin adabinsa babu su a wasannin wannan
zamanin, Tabbas wannan ya kawo koma-baya ga tarbiyyar yaranmu da kuma samun
kyakkyawar mu'amala.
1.5 MUHIMMANCIN
BINCIKE
Wannan binciken na da matuƙar
muhimmanci ƙwarai da gaske, kasancewarsa wani yanki daga
cikin katafaren fagen adabin Hausawa wanda ke tafiya da zamaninsa na dauri,
saboda haka binciken zai amfanar da masu gudanar da nazarce-nazarce kan harkar
adabin gargajiya a fannoni daban-daban.
v
Binciken zai ƙara ƙaimi
da kuma sha'awar cigaba da aiwatar da ire-irensa a yanzu, domin ƙara
samun wasu darrusa da hikimomi da ke cikinsa musamman ga yara da kuma matasa.
v
Binciken zai taimaka wajan sanar da al'umma
irin gudunmawar da wasannin gargajiya ke bayarwa a harkar tafiyar da zamantakewar
al'umma da kuma irin tasirin da yake da shi a rayuwarsu.
v
Binciken na da muhimmanci sosai a ɓangaren
adabin Hausa, domin kuwa an yi ayyuka da dama da suka shafi Harshe wanda shi ne
makwafin nahawu a larabci, haka kuma abin yake a fannin Aruli da balaga, amma
ita falsafa an ɗan taƙaita
mata nazari wajan shigar da ita sosai domin a yi nazarinta.
v
Haka kuma binciken na da muhimmanci sosai ga
abinda ya shafi al'ada, domin kuwa wasu hikimomin da Hausawa ke sanyawa a cikin
wasannin da tatsuniyoyi ba sa wuce al'adunsu da suka shafi zamantakewarsu ta
yau da kullum don haka ake ganin a ɓangaren al'ada ma binciken zai taka
muhimmiyar rawa.
v
A ɓangaren harshe ma binciken na da
muhimmanci, domin kuwa Hausawa na amfani da salo iri daban-daban wajan sarrafa
harsensu yayin aiwatar da labaransu na tatsuniya da kuma wasanni domin su ƙayatar
da kuma ƙara musu ƙima. Wannan
ma abu ne mai muhimmanci ga masu nazari akan harshe harma da dabarun sarrafa
shi.
v
Bugu da ƙari binciken
zai taimakawa ɗalibai
musamman na sashen nazarin Harshen Hausa a manya da ƙananan
makarantu wajen yin nazari musamman kan abinda ya shafi falsafa, da wasanni ko
labaran tatsuniyar da kuma shi kansa Bahaushen.
1.6 FARFAJIYAR
BINCIKE
Hausawa na cewa "Daidai ruwa daidai
tsaki" to haka abin yake a harkar gudanar da bincke, domin kuwa a duniyar
ilimi duk wani aiki da aka tarki yinsa dole a samu iyakarsa kamar yadda aka
farar da da shi.
Farfajiyar wannan binciken ta taƙaita
ne ga fannin adabin Hausawa, fannin adabin ma kuma ɓangaren
labarun zube da kuma wasannin na gargajiya. Wasanni da tatsuniyoyin gargajiya
suna da yawan gaske don haka binciken ya iyakance kansa ga wasu Tatsunioyi da
wasanni guda biyar da suke rubutce cikin littafin Tatsuniyoyi da wasanni na
Ibrahim yaro yahaya a littattafai na ɗaya zuwa na shida,
saboda su ne suke da kamantacceniya wajen aiwatarwa da kuma irin muhimmancin da
suke da shi a rayuwa, za a yi nazarinsu wajen fito irin falsafar da Hausawa ke
sanyawa cikinsu, saboda haka wannan aikin zai yi ƙoƙarin
binciko hikimomin na Hausawa cikin waɗannan Taatsuniyoyin
da wasannin guda biyar kacal, tatsuniyoyi uku, wasanni biyu saboda masu nazari
a gaba su ɗora daga inda
aka tsaya.
1.7 NAƊEWA
Bisa lura na tsanaki game da bayanan da suka
gabata a wannan babin za a ga cewa kamar yadda batun binciken ya nuna an yi fiɗar biri har
wustiyarsa, domin kuwa an fayyace rukunin da wannan aikin ya shafa a fagen
ilimi wato "adabi" an kuma kawo asalinsa da kuma bayyana yadda shi
kansa adabin ya kasu tare da bayyana kowanne daga cikinsu har ma da fayyace ɓangaren da
tatsuniyoyin da wasannin gargajiyar suka karkata, wanda suka zo ƙarƙashin
gabatarwar babin. Bugu da ƙari babin ya tattare
duk wasu bayanai da binciken ya ƙunsa ta ɓangaren yadda
za a aiwatar da shi, domin kuwa an zayyano manufofi, da kuma dalili da suka
haddasa aiwatar da binciken, daga bisani kuma an nuna ko kuma fito da hasashen
da aka hasko game da makomar binciken da ma irin muhimmancin da binciken ke
tattare da shi, sannan kuma aka toge haɗe da katange iyakacin
inda aikin zai taka birki domin gudun ko ta kwana da kuma kaucewa shiga shirgin
da bai shafi binciken ba, a wannan babin ne aka tattare tsaki da tsakuwar duk
wani abu muhimmi da yazo a ɓangaren mai gudanar da bincike da kuma
binciken kansa.
BABI NA BIYU
BITAR AYYUKAN
MAGABATA
2.1 SHINFIƊA
A Harshen Hausa an bayyana kalmar bita da
himmatuwa wajan nemo ayyukan magabata a kuma zauna a nazarce su, wanda kuma
nazarin ke tattare da kiyaye dokoki da dalilai da aka sarrafa a wani binciken
da wani marubucin ke son ya tabbatar, ko ya ƙago, ko ya
kare, ko ya ƙara masa tsawo ko ya yi tankaɗe da rairaya
(Bunza,2020).
Wannan babin cikin kowanne bincike shi ake
yiwa laƙabi da "Waiwaye" domin kuwa a babin
ne mai gudanar da bincke ke bayyana ayyukan da ya bibiya masu alaƙa
da bincikensa kama daga littattafai ,Mujallu, Muƙalu, Kundayen
bincike da sauransu kamar yadda Bahaushe kan ce "daga na gaba ake ganin zurfin
ruwa", haka shi ma wannan binciken zai bibiyi irin rubuce-rubucen da
magabata su ka yi masu alaƙa da wannnan
binciken a matakan ilimi daban-daban domin fahimtar inda suka ɗauko da kuma ɗorawa daga
inda suka tsaya. wannan yasa binciken zai bibiyi ayyukan da aka gabatar game da
Hausawa da tunaninsa da kuma falsafarsu, har ila yau binciken zai waiwayi
nazarce-nazarcen da aka yi a ɓangaren adabin baka musamman ɓangaren
wasannin gargajiya da tatsuniya domin gujewa nanata aiki iri ɗaya cikin
fagen nazari ɗaya. Don haka
babin na biyu zai tattaro duk wasu bayanai cikin nazarce-nazarcen magabata
wanda ya shafi Hausawa da Harshensu, Ƙasarsu da
falsafarsu tastuniyoyinsu da kuma wasanninsu na gargajiya a ƙarshe
kuma a ƙarƙare babin
tare da bayyana duk wani abinda aka tattauna cikinsa a taƙaice.
2.2 HAUSA DA
HAUSAWA DA ƘASAR HAUSA
Ma'anar Hausa a idon Hausawa da manazarta tana
da yawa, akan danganta ma’anarta da harshen Hausa ko ƙasar Hausa ko
al’umma da suke zaune a ƙasar Hausa da
kuma azanci da Hausa ta ƙunsa.
Bahaushe shi ne wanda ya gaji Hausa ta wurin mahaifinsa ko mazaunin ƙasar
Hausa da ba shi da wani harshe sai Hausa. Ana iya samun Bahaushe ya danganta
kansa da wata ƙabila, domin akwai ƙabilu masu
yawa a ƙasar Hausa kuma wasu al’umman na kusa da nesa
sun yi wa Hausa tasiri. Hausa ta yaɗu a wurare daban-daban saboda addini
da zamantakewa da kuma tattalin arziki da siyasa. Hausawa suna da tsarin
zamantakewarsu a gida da waje, suna zayyana muhallinsu daidai da sauyin zamani,
kamar yadda cuɗanyarsu da
Fulani da Barebari da Larabawa da sauransu ta haifar da sauye-sauyen rayuwa da
bigiren da suke rayuwa a cikinsa. Kusan maganar Hausa a yau ta wuce a ce Hausa
Bakwai da Banza Bakwai, domin Hausa ta mamaye ɗaukacin waɗannan wurare
ta tsallaka cikin wasu yankunan da ba ƙasar Hausa ta
asali ba. Harshen Hausa yana cikin rukin manyan harsuna a duniya idan ana
maganar yawan masu amfani da shi a rayuwa ta kafafe daban-daban.
Skinner, (1989). ya ce asalin kalmar ta samu
ne daga mutanen Sangai (Songhai). Sanyawa sukan kira duk al’ummar da suke gabas
da su da sunan HAUSA ko AUSSA, wanda daga nan ne sai Hausawa suka riƙa
yi wa kansu laƙabi da suna Hausawa. Sai dai Zarruk da wasu
(1982) tambaya suka yi shin Hausawa ƙabila ce? To
amma duk wanda ya tsaya ya bayyana ma’anar ƙabila sosai,
sai ya ga Hausawa sun shiga ciki, misali, bisa ga bayanin marubuta ƙabila
mutane ne masu asali da harshe ɗaya da al’adun gargajiya da kamanni ɗaya. Ita kuma
kalmar Hausa a gun Bahaushe tana nufin harshe ne, ta yadda har ma akan ji ya ce
ban ji wannan Hausar ba, wato bai ganSe wannan harshen ba ko yaren ba, ko kuma
ya ce "Na ji ana wata Hausa‛" wato ya ji ana magana da wani harshe.
Amma a fahimtar Gusau (2008) ga Hausa, kalma
ce mai ma’anoni da dama kuma mabambamta, wadda akan danganta ta da muhalli ko
harshe, misali idan mutum ya ce ni a Hausa, wato ni a harshena ko nufina ko
ma’anata. Ta fuskar muhalli kuma Kalmar Hausa takan ɗauki ma’anar
wuri ko farfajiya ko yanki, wato kamar a ce ƙasar Hausa,
ma’ana yankin ƙasar Hausa ko
farfajiyar ƙasar Hausa.
A tunanin
Magaji,(1986:2).kalmar Hausa daga mutane masu hawa Sa take. Wannan ya faru ne
sakamakon Hausawa masu kiwo Shanu ne, wai daga ƙarshe sai ake
kiran mutanen da Hau+Sa = Hausa, wato daga hawan Sa.
Kabo,
(2016). cewa ya yi an samo asalin kalmar Hausa ne daga kalmar Habasha kafin
daga baya ta koma Habsa sannan ta zama Hausa. Goyon baya a kan wannan ra’ayi
shi ne maganar Mahammadu (2006), wanda ya ce asalin Hausawa daga Habasha su ke,
domin idan aka duba salon bautar Bahaushe ta gargajiya wadda yake bautawa rana,
za a ga cewa lallai al’amarin ya yi daidai da bautar rana da al’umar Habasha
suke yi, domin suna bautawa ubangijinsu mai suna 'Ra‛ shi ne suke cewa ‘Ra’ Na (Ra+na)
wato ubangijina. Zamu rufe da ra’ayin Bello
(2015) da ya bayyana cewa kalmar Hausa ta samo asali ne daga Buzaye, saboda ita
ce kalmar da suke kiran mutanen da suke zaune a Arewacin kogin Kwara, wato
Hausa. A taqaice dai kalmar Hausa tana nufin harshe kuma tana nufin mutanen da
suke magana da harshen Hausa a matsayin harshen uwa, kamar yadda take nufin ƙasa
ko muhalli ko farfajiya ko wurin da wannan mutane suke zaune.
Umar, (1977). kalmar Hausa tana nufin masu yin
magana da harshen, ko a ce al’ummar da suke amfani da harshen a matsayin
harshen sadarwa, waɗanda ake kiransu da Hausawa. Kenan Hausawa
al’umma ce ko rukunin mutane ne da suke gudanar da furuci ko magana da harshen
Hausa. Haka kuma, su ne jama’ar da ƙasar Hausa
ita ce muhallinsu tun daga iyaye da kakanni, kuma Hausa ce yarensu na asali ta
yadda a sakamako haka ne ma ake kira mutanen da suka shaƙu ta fuskar
al’ada ko suka taso cikin halaye iri ɗaya da suna Hausawa.
Duk da cewa ana samun ɗimbin Hausawa da masu magana da harshen Hausa
a ciki da wajen Afirka, musammman a yankin Afirka ta Yamma, amma an fi yin
amfani da harshen Hausa a Arewacin Najeriya da Yammacin Jamhuriyar Nijar.
kalmar Hausa na iya ɗaukar
matsayin harshe, wanda shi ne yaren da Hausawa da waɗanda su ke
iyaka da su su ke yin amfani da shi wajen sadarwa a zantukansu na yau da
kullum. A taƙaice dai Hausa shi ne Hausanci wato yaren da
Hausawa suke sadarwa da shi a matsayin harshen da suke fara koya ko tashi da
shi tun daga ƙuruciya har zuwa ƙarshen
rayuwarsu. Har ila yau, Hausa takan zamo harshe na biyu ko na uku ga wasu
mutane waɗanda ba
Hausawa ba ne.
Gusau,(1982) cewa ya yi Hausa ita ce ta
tuntuntuni da ake ginin tasirinsa cikin azanci na zantukan Hausawa, wanda yake ɗamfare a
cikin harshen nasu. Tuntuntuni na nufin falsafa, wato gudanar da zuzzarfan
tunani domin warware matsala ko kuma kyautata magana, wato ƙayata
zance. Amma azanci ta fuskar ma’ana shi ake
kira da hikima, wato dabarun sarrrafa harshe a cikin magana da ma a rayuwa gaba
ɗaya, wanda
harshen Hausa yana ɗauke da dabaru na sarrafa harshe (Gusau
1982).
Abdullahi,(1987).Wata ma’anar da kalmar Hausa
ta ƙunsa ita ce wadda ake jingina ta ga yankin ƙasar
Hausa. Abin nufi a nan shi ne muhallin da aka tabbatar a nan Hausawa suka zauna
tun tali-tali a cikin garuruwa da birane da suka kewaye yankin. “ƙasar
Hausa ita ce farfajiyar da Hausawa suka zauna a cikinta, wadda take cike da
manyan garuruwa da fitattun birane. ƙasar Hausa a ƙarnukan
baya kafin zuwan Turawan mulkin mallaka a dunƙule take wuri
ɗaya, duk da
cewa kowacce ƙasa tana ƙarƙashin
babban sarki mai ‘yancin kansa amma sakamakon mulkin mallaka da ya cinye
Hausawa da yaƙi, sai ƙasar Hausa ta
rabu zuwa gida biyu, inda aka samu Hausawa da suka tsinci kansu a Nijar ƙarƙashin
ikon faranshi, yayin da wasu kuma suka tsinci kansu a Nijeriya ƙarƙashin
mulkin Ingilishi.
Yayin da ake maganar kalmar Hausa ta fuskar
nazari, to ana batu ne a kan karantar Hausa a matakin ilimi daban-daban a
duniyar yau, wato koyar da Hausa tun daga matakin firamare har zuwa jami’a
(Abubakar, 2015). Wannan bayani ya ja hankalin Junaidu (2011) ga bayanin Hausa
a matsayin wani ɓangare na
nazari da ake karantawa kuma ake karantar da harshe da adabi da al’adar Hausawa
a sassa daban-daban na nazarin harsunan Najeriya a jami’o’i da manyan
kwalejojin ilimi da jami’o’in Afirka da ƙasar Amurka
da ƙasashen Turai da jami’o’in Asiya.
Shi kuwa Adamu,(1978). ya fayyace ƙasar
Hausa musamman inda yace "akasarin Hausawa suna zaune a farfajiyar da suke
rayuwa har sai da sahara ta sabbaba gobirawa suka yi ƙaura zuwa
kudu". Hausawa da al'adun Hausawa suna walwalarsu a ƙaƙashin
gobir da kabi, da daura da katsina da zamfara da kano da rano da garun gabas ko
biram. Haka Muhammad Bello ya bayyana Hausawa da ƙasar su a
imfaƙhul-maisur.
Moughtin,
(1964). ya ce ƙasar Hausa tana da ingantaccen tsarin kasuwanci
da mulki da fasahar ƙere-ƙere,
tun kafin zuwan turawa. Masanin ya ce zai yi wuya ya yi wa Hausawa da ƙasarsu
kuɗin goro, amma
a zariya daga an fito ganuwa sai tudun wada, wato mazaunin baƙi
musulmi, kuma yawancin mazauna tudun wada gine-ginensu iri ɗaya ne da na
gargajiya.
Smith,(1961
a). ya ce, taswirar ƙasar Hausa tana
shimfiɗe a kan
digiri na 10½º da 13½º a Arewa da kuma digiri na 4º da 10º. Amfani (2012) ya ƙara
da cewa, ƙasar Hausa ta fara daga Azbin har zuwa
Arewa-maso-Gabas na tsaunukan ƙasar Jos, ta
Yamma kuma ta dangana da Kogin Kaduna, ta Arewa-maso-Yamma kuma ita ce har
Kogin Kabi, sannan ta dangana da Arewa-maso-Gabas ta yi Azbin. Masanin ya ci
gaba da cewa, ƙasar Hausa tana cikin arewacin Nijeriya da
kudancin Jumhuriyar Nijar, kuma Hausawa sun zauni wannan wuri sama da shekara
dubu ashirin. Inda Hausa ta laƙume wasu ƙabilu
da asali ba Hausa ba ne. Masanin ya ce, Hausa ta gawurta a wuraren ƙarni
na sha biyar zuwa na sha bakwai. Amfani (2012) da Adamu (1978) sun ce, Hausa
harshe ne a cikin harsunan iyalin Chadi wanda ya tsira daga rukunin
Afro-asiatic. Amfani (2012) ya ƙara da cewa,
tarihi ya adana bayanin ƙeƙashewar
Tafkin Chadi, wanda ya sabbaba yin ƙaura, kuma ƙaurar
da mutane suka yi ta dangana da Gulbin Kebbi a Yamma, wasu mutanen da suka yi ƙaurar
iyakacin su tsaunukan ƙasar Barno. Masanin
ya ce, Hausawa da Bolawa da Ngizim da Manga da Margi da Kotoko su ne manyan ƙabilun
da suka yi wanna ƙaura. Kuma sun daɗe a wannan
farfajiya, amma an san su sosai ne a wurin ƙarni na sha
biyar. Masanin ya ce, Hausawa sun fi sauran ƙabilun yawa,
kuma sun fi su watsuwa.
Amfani,
(2012). da Adamu (1978) sun yi tarayya wajen fayyace ƙasar Hausa,
musamman inda Adamu (1978) ya ƙara da cewa,
akasarin Hausawa suna zaune a farfajiyar da suke rayuwa har sai da sahara ta
sabbaba Gobirawa suka yi ƙaura zuwa
kudu. Hausa da al’adun Hausawa suna walwalarsu a ƙasashen Gobir
da Kabi da Daura da Katsina da Zamfara da Kano da Rano da Garun Gabas ko Biram.
Muhammadu Bello ya bayyana ƙasar Hausa a
Infaƙul-Maisur kamar yadda Yusuf(2013), ya
fassara. Mafassarin ya ce, Infaƙul-Maisur
jigo ne wajen adana tarihin ƙasar Hausa da
jihadin Shehu Ɗanfodiyo.
Smith (1961 a) ya ce, ƙasar Hausa ta
tsinci kanta a tsakanin Daular Barno da ta Songhai, waɗanda suka yi
mata kyakkyawan tasiri; musamman inda Songhai ta ƙarfafa siyasa
da sadaukantaka da addini da kuma tattalin arziki. A zamanin Muhammadu Rumfa
(1465-99) aka kafa wata kasuwa baya ga wadda Usman Kalmana ya assasa, sannan
Sarkin Kano ya ci gaba da gina ganuwa, ya gina sabuwar fada tare da samar da
tara ta Kano da sauransu.
Smith,(1961). ya ce, an sami sauyi a zamanin
Rumfa sosai, inda Musulunci ya yi ƙarfi, aka ari
wasu al’adun Barebari da sauransu. Masanin ya ci gaba da cewa, ƙasar
Hausa ta sauya, domin ƙananan garuruwa sun
bunƙasa, sarakuna sun ɗaukaka,
sarauta ta koma gadon tsatso, darajar Hausa ta gusa daga ƙabila zuwa
al’umma.
Usman,
(1981). kuma ya ce, mazauna Durɓi-ta-kusheyi na farko wasu mafarauta
ne kamar yadda mazauna Kwatarkwashi na farko suka kasance mafarauta. Masanin ya
ce, ana kiran waɗannan
mafaruta da suka zauni Durɓi-ta-kusheyi da suna Adawa, wato
mutane ne masu girman gaske. Masanin ya ƙara da cewa,
irin waɗannan mutane
su ne suka zauni tarin jigawar da ke kewaye da Bugaje da Muduru. Masanin ya ce,
tarihihi ya nuna cewa an ji ƙuriyar zaman
irin waɗannan mutane
a ƙasar Zazzau da Zamfara da Kano da kuma Barno.
Haka kuma akwai irin wannan tarihihi da yake
nuna wanzuwar irin waɗannan mutane a sassa daban-daban na duniya. Masanin
ya ce, Durɓi-ta-kusheyi
kufan mutanen farko ne kamar yadda Dala da Gaya a Kano suka kasance kufayin
mutane da kuma cibiyoyin noma da haƙar tama da ƙere-ƙere.
Ƙaraye,(2003). ya yi bayanin irin zamantakewar
Hausawa da iyalansu wanda ya ƙunshi, maigida,
matar gida, ƴaƴa. Maigida ya
kan ware sashensa, haka ma mata da ƴaƴansu.
C.H.N.H,(1971). sun bayyana yanayin cuɗanyar Hausawa
da wasu al'ummomi a sanadiyyar yaƙe-yaƙe,
da ƙaurace-ƙaurace, har
ma da kasuwanci, littafin dai ya karkata ne ɗungurungum ga
yadda Hausawa suka yi rayuwa da sauran al'ummomi.
Adamu,(1964).
shi kuma cewa ya yi Bahaushe kan tsara hanyoyinsa wanda galibi sukan ɓille zuwa
makarantunsu, ko masallatansu da kasuwanninsu ko kuma dandalin hira, wasu
hanyoyin ma har jaki kan iya wucewa.
N.N.P.C, (1982). sun kawo bayanai game da
yadda Bahause ya ke aiwatar da al'amuransa na zamantakewar rayuwar kamar abinsa
na gargajiya suturunsa da dai sauransu.
HAUSAWA
Ƙamusun Hausa
na jami,ar bayero(2006) an bayyana cewa Bahaushe shi ne haifeffen mai magana da
harshen Hausa da rayuwa irin ta Hausawa.
Abdullahi smith, (1987) ya bada ra'ayin cewa
" Bahaushe" mutum ne da ke zaune a ƙasar Hausa a ƙarshen
ƙarni na sha biyar 15 a lokaci mai tsawo wanda
ba a iya tantancewa ba. Ko da yake karkasuwarsu cikin wani yanki babu shakka ta
sauya saboda tashe-tashen da ake yi cikin ƙasar Hausa da
kuma daga wajen ƙasar Hausa.
Masanin
ya ƙara da cewa, kusan ba ya yiyuwa a ba da
sassauƙan bayani a kan wa za a ƙira Bahaushe
? saboda koyaushe mutane daban-daban a wurare da lokuta daban-daban suna amfani
da ma'auni daban-daban wajen tantance wane ne Bahaushe, Haka kuma dangane da
abinda ya shafi muhallin Hausawa shahararren Malamin nan mai suna Malam
Abdullahi Usman Ɗanfodiyo a cikin Algaita journal ya nuna cewa
duk wani mazaunin ƙasar Hausa, kamar shi
kansa ya cancanci a karɓe shi a matsayin Bahaushe saboda ba zai iya
kuɓuce wa harkar
al'adunsu ba.
Haka kuma akwai masana da suka tofa albarkacin
bakinsu wajan kawo ra'ayoyi game da wanda ya dace a kira Bahaushe kamar haka:
v Wasu na ganin
cewa Bahaushe wanda yake da al'ada da addini irin na Hausawa.
v Wasu kuwa sun
ce Bahaushe shi ne duk wanda bai da wani harshe sai harshen Hausa. Masu wannan
ra'ayin na nufin duk wanda ya taso a ƙasar Hausa,
kuma ba shi da wani harshe sai Hausa to shi ne za a kira "Bahaushe"
ko da kuwa iyayensa ba Hausawa ba ne.
Abdullahi.U(1994) cewa ya yi Bahaushe shi ne
wanda iyayensa asalinsu Hausawa ne, ya ke yin magana da Harsen Hausa, kuma
al'adunsu na Hausawa ne, kuma addimin musulunci ya yi cikakken tasiri a
kansa".
Adamu,(2011) ya siffanta Bahaushe da cewa ba
shi da dogon gashi kai irin na mutanen songai, amma ƙirar jikinsa
da kamanninsa daidai yake da na al'ummar arniyyawa (Aryan), waɗanda a da suke
zaune a tsakanin ƙasashen turai da Asiya kafin su yi hijira su
warwatsu a gurare daban-daban na duniya. Ya ƙara da cewa
Bahaushe manomi ne mai ƙwazon noma da tara
abinci, sannan a fagen yaƙi jarumi ne
mai juriya. sa'annan sananne ne a matsayin mai sana'a da sauran ayyukan ƙodago
Adamu,(1997).ya ƙara da cewa
kusan galibi adon Bahaushe namiji ba ya wuce riga da wando,musamman fanjama da
takalmi faɗe ko sau-ciki
da hula kube ko dankwara ko zita ko haɓar kada, idan kuwa
saraki ne ko malami ko dattijo ya kan sa rawani. Adon mata kuwa, zani ne da
riga da gyauton yafawa ko gyale da kallabi da ɗan tofi ko
mukuru da ƴan kunne da dutsen wuya wato tsakiya ko
murjani da warwaro a da can suna ɗan hanci amma yanzu wannan adon ya
kau.
Al’umar Hausawa dai al’umma ce da take zaune a
Arewacin Najeriya da yammacin Jamhuriyar Nijar. Al’umma ce mai ɗimbin yawa,
waɗanda suka
bazu a cikin ƙasashen Afirka da yankunan Larabawa. A
al’adance Hausawa mutane ne masu matuƙar hazaƙa,
sai dai ta ɓangaren zubi
baƙaƙe ne da wankan
tarwaɗa da kuma
farare jifa-jifa sannan suna da gajerun gashi. Hausawa sun sami kafa daularsu
ne tun daga shekaru 1300, sa’ad da suka sami nasara a kan dauloli kamar Mali da
Sanwai (Songhai) da Barno da Fulani. A farkon shekara ta 1900 lokacin da Hausawa
suke ƙoƙarin kawar da
mulkin aringizo na Fulani, sai Turawan mulkin mallaka na Burtaniya suka mamaye
Arewacin Najeriya.
Ta fuskar sana’a kuwa, noma shi ne babbar
sana’ar Hausawa, ta yadda har ma suke yi masa kirari da cewa "Na duƙe
tsohon ciniki kowa ya zo duniya kai ya tarar". Akwai wasu sana’o’in kamar jima
da rini da saqa da sassaƙa da farauta
da sauran sana’o’i da dama. Ginshiƙin al’adun
Hausawa sun haɗa da matuƙar
jarumta da ƙwarewa ta fuskar ƙere-ƙere
da sanayya ta fuskar kasuwanci fiye da sauran al’ummar da suke kewaye da su.
Mafi
yawan abincin Bahaushe kuwa ana yin sa da gero ko dawa ko maiwa, sai kuma
sauran abubuwan haɗawa kamar su gishiri da barkono da daddawa da
albasa da kuka da kuɓewa da tumatur da kalkashi da lalo, da tafasa
da ɗata, da kuma
kayan marmari, su wake da shinkafa da acca da ibiro da kuma kayan rafi da
saransu.
Yawancin Hausawa Musulmai ne kuma suna amfani
da Hausa a matsayin harshen sadarwa. A taƙaice dai
Hausawa al’umma ce da suka ɗauki harshen
Hausa a matsayin harshen uwa kuma suke zaune a ƙasar Hausa da
al’adu irin na Hausawa masu matuƙar
muhimmanci da daɗaɗɗen tarihi mai
cike da jarumta da kuma gwaninta. Asalin Hausawa abu ne da masana suka sha
kai-komo a kansa, sai dai abin takaici har yanzu ba a samu cikakkiyar amsa mai
gamsarwa ba, kowa-da-kowa ra’ayinsa yake bayarwa gwargwadon fahimtarsa game da
lamarin. Bari mu duba ra’ayoyi kamar haka dangane da asalin Hausawa:
Mahammadu,(2006).a wata ƙasida ya nuna
cewa akwai wata ƙaura da ta auku daga gabas zuwa ƙasar
Tukururu, wadda ta yi sanadiyar samuwar Hausawa da harshensu, kuma ƙaurar
ta faru ne a tsakanin 900-1000 miladiya. Dalilin ƙaurar kuwa
shi ne Larabawa ne suka yaƙi mutanen da
suke Arewacin Afirka, sai suka baro wannan waje zuwa ƙasar Hausa.
Amma Adamu,(2011). ya tafi a kan cewar akwai
dangantaka tsakanin al’ummar Hausa da mutanen Cadi, amma sun raba hanya a
shekaru 1000 da suka wuce, kuma akwai Tukururu da suke zagaye da tafkin Cadi
har zuwa inda ake kira da Sahara, saboda suna Arewa maso gabas wato inda
Hausawa suke. Wannan ra’ayi na nuna cewa akwai alaƙa tsakanin
harshen Hausa da harsuna iyalan Cadi.
Usman,(2008) ya yi bayanin taƙaitaccen
tarihin Hausawa inda yace " ƙasar Hausa
tana shimfiɗe a Arewacin
Nijar a can afrika ta yamma, daga gabas ta yi iyaka da ƙasar Barno
daga yamma ta yi iyaka da ƙabilun Gwari,
ƙasar Hausa tana da girman ƙwarai
da gaske, daga kudu ,ƙasar ta fara daga
Azbin har zuwa kusurwar Arewa maso gabas ta tsaunukan ƙasar jos.
Daga nan sai ta kwasa ta yi yamma har zuwa inda kogin kaduna ya yi babban doro.
Daga nan kuma sai ta buga ta yi arewa maso yamma sai da ta dangana da wani ƙaton
kwari na gulbin kebbi. Daga wannan wuri sai ta karkata ta nufi Arewa maso gabas
har azbin. Wannan zagaye shi ya nuna iyakokin ƙasar Hausa a
gabas da yamma kudu da Arewa wadda kuma har zuwa yau su ne iyakokin ƙasar
Hausa, wannan ƙasar Hausa ita ce ƙasar da
Hausawa suke zaune fiye da shekaru (20,000).
Akwai wata ƙasida da wani
Malami ya buga a jaridar gaskiya tafi kobo ta ranar 22 ga watan 10 a shekara ta
1985 mai suna ‚ " Asalin Hausawa da harshensu‛.
Inda Malamin ya tafi a kan cewa asalin Hausawa daga Masar suke, kuma sun fito
ne daga sashen ƙibɗawa, mutanen Fir'auna; har ma ya ƙara
da cewa daga cikin Fir’aunonin Masar
da aka yi akwai baƙaƙe
a cikinsu har lokacin sarautar gida na 24. Mutanen Masar su ne suka yi ƙaura
zuwa Afirka ta yamma, sun fara zama a bakin tafkin Cadi wanda a wannan lokaci
cike yake da ruwa. Farar fata na Hamada sukan kawo musu hari, wannan ta sa suka
sake wurin zama kuma suna ɗauke da harshensu na Masaranci wanda
daga baya ya sauya ya zamo Hausa.
Kabo, (2016). ya nuna cewa asalin Hausawa daga
Habasha suke sannan kalmar Bahaushe daga Bahabshe take, misali Bahabashe zuwa
Bahabshe zuwa Bahaushe. Goyon bayan wannan ra’ayi shi ne maganar Maitama-Sule
(2007), har ma ya tafi a kan cewa asalin Hausawa daga Habasha suke, domin an
samo tarihin da ya nuna cewa Habasha tsohuwar ƙasar baƙaƙen
fata ce kuma sarakunansu baqar fata ne, kuma sun bazu ne sakamakon fari da
yaqi. Manazarcin ya cigaba da cewa ‘ya’yan sarki ne (maguzawa) su uku suka yi ƙaura
daga ƙasar Masar zuwa ƙasar Hausa, a
cikinsu akwai ‘Kano’ wanda ya sari Kano, sai 'Gayya' wanda ya sari Gaya, sannan
sai 'Ranau' wanda ya sari Rano.
Jinju,(1985). ya yi bayanin inda Huasawa suka
samo asali a inda ya kawa ra'ayoyin masana daban-daban da suka yi tsokaci game
da asalin nasu ,da kuma bibiyar labaru da tarihi masu alaƙa da
asalinnsu.
Khalid,(1999). cewa ya yi Hausawa da Harshensu
sun yaɗu ne a duniya
ta hanyar shige da fice da suka riƙa yi wurare
daban-daban na nahiyar Afirika,da yadda suka riƙa
mu'amalantar al'ummomi daban-daban a duniya.
Amfani,(2011). ya fayyace yanayin Huasawan da
da na yanzu ta hanyar kawo ire-iren halayyar Bahaushen da kuma Hausawan yanzu
har ma da hasashen yadda Hausawa wani lokacin mai zuwa za su iya tsintar kansu,
ta hanyar bayyana dalilai da kuma misalai masu kama hankali.
Adamu,(2000). ya gabatar da takarda mai taken "Tarbiyyar
Bahaushe" mutumin kirki and Hausa prose fiction: towards an analytical
framework" a taron samina na tsangayar nazarin yaren turanci, jami'ar
Bayero kano.
Ita ma wannan
takardar ta yi bayani ne game da irin kyawawan halayya da Bahaushe ke da shi,
da kuma irin yadda yake da ƙarfin tarbibiyyar
da ahalinsa, da kuma ƙoƙarinsa
na ganin ya girmama na samansa da kuma shuwagabanninsu.
2.3 FALSAFAR
BAHAUSHE (TUNTUNTUNI)
Kalmar falsafa an aro ta ne daga yaren
Larabci, duk da yake wannan ba zai sanya a ce Hausawa sun rasa hikima ba, domin
sukan ce‚ Magana jari ce, Kuma hikima da azanci tubala ne da ake gina karin
magana ta Hausa da su. Falsafa hanyar tunani ce wadda take ƙoƙarin
tattaro bayanin kusan dukkan al’amuran da suka shafi duniya da ɗan’adam da
inda mutum ya sanya gaba. Haka ya sanya manazarcin ya tsakuro ma’anonin falsafa
daga cikin Encyclopedia of Religion and Ethics, (1953, shf. 844) inda aka ce
"falsafa ta samo asali daga Girkanci wato ‘Philo’ - ƙauna da
'sophy‛ – hikima, watau gwari-gwari ƙaunar
hikima ke nan. Ma’ana ƙoƙarin
zurfafa tunani tare da nazarin dukkan abin da yake kai komo a sararin Subuhana
tare da hikimar bayinsa‛ (Amin, 2004, shf. 209).
Bergery,(1933) ya bayyana ma'anar falasa da
kawo abinda ya gabata wato mayar da saura ta wani abu da ya wuce , ko kuma
hasashe na abin da ya gabata ko wanda zai zo" ya kuma ƙara
da cewa wannan kalma ta falsafa wata manufa ce da ake auna abu bayan zurfafa
bincike ta hanyar amfani da ƙwaƙwalwa
yanda kuma hankali zai ɗauka.
Nasir,(1982)
ya dubi kalmar falsafa a musulunci don haka ya ce: falsafa na nufin hikima tare
da ƙoƙarin nazartar
dukkan al'amari a bisa kyakkyawar shimfiɗar tauhidi.
Popkin da Stroll,(1993). sun ce, falsafa fagen
nazari ne da ya ɗara sauran
fagagen ilmin wahala, saboda nazari ne da yake tu’ammali da zuzzurfan tunani.
Mafalsafan sun ce, wasu sukan danganta falsafa da tunani a zantukansu, duk da
yake batu ne da ya shafi ƙaunar hikima.
A yau, kusan akan kalli falsafa ta fuskoki masu yawa. Misali idan wani bai
aminta da manufar wani ba, yakan ce masa bai gamsu da tsarin da yake bi ya
gudanar da kasuwancinsa ba. Idan kuma wani ya aminta da tsarin wata hukuma,
yakan ce ya gamsu da manufofin wannan gwamnati. Yin tunani abu ne da ya shafi
falsafa, musamman idan al’amura suka bijiro ko matsala ta auku da mutum, akan
ba shi shawara ya tsaya tsaf ya yi tunani mai zurfi game da abin da ya fi zama
masa alheri. Falsafa iya tantancewa ne da kuma ƙalailaice al’amuran rayuwa domin a samo mafita. Domin falsafa tana
tattare da manyan tambayoyi masu caza ƙwaƙwalwa.
Mafalsafan sun ƙara da cewa,
mafalsafi yakan zauna ya tsara wasu tambayoyi masu fa’ida ga rayuwa, waɗannan tambayoyi sukan
ƙalubalanci matsalolin da al’umma take fuskanta kai tsaye ko a kaikaice. A kan
tsinkayi alherin abu da sharrinsa yayin da ake yin tunani a kansa. Mafalsafan
sun ƙara da cewa, tunanin mafalsafi yakan sabunta
na al’umma, al’umma ta da]a fahimtar kanta da tadodinta, duk da yake ba kasafai
ake aiwatar da ra’o’in da mafalsafi ya gina ba saboda tsaurinsu. Wannan bai
kore fa’idar hangen nesar mafalsafi (game da duniya da mutum da sauransu) ta
amfani al’umma ba.
Abubakar,( 1994).ya kawo ma'anar falsafa da
cewa kalma ce da za a iya bata ma'anoni da yawa waɗanda duka
idan an haɗa su za su
bada cikakkiyar ma'ana guda ɗaya, haka kuma falsafa na iya zama ɗaya daga
cikin waɗannan abubuwa
guda ukun:
v
Wani abu a zuciyar mutum , wanda ya dame shi
kuma har ya sanya shi baƙin ciki ko
farin ciki.
v Mutum ya riƙa
saƙa wani abu a ransa wanda zai aikata ko zai
samu a gaba mai kyau ne ko maras kyau.
v Haka kuma
falsafa na iya zama hikimar ɗan Adam wato tunani.
Aminu
Alan waƙa, a cikin waƙarsa ta
"Uwar iyaye" Aisha, ya nuna cewa tunani wata hidima ce da aka tarawa ƙwaƙwalwa
har ta haifar da shi a zuciya:
Abinda ƙauna za ta
bayar,
Shi biyayya za ta haifar.
Abinda ƙwaƙwalwa
ta bayar,
Shi tunani za ya haifa
Dr
A. Nassar,(1982).cewa ya yi mai da hankali da mutum kan yi wajen tunani akansa,
wanda ya koru ga hankali ya sawwara kansa ya gano haƙiƙanin
mutum da mafarin rayuwa, sai dai kawai a samar da wani nishaɗi a ƙwaƙwalwa.
A dunƙule a iya cewa: falsafa ta ƙunshi
wasu hikimomi da kowacce al'umma take aiwatarwa, Irin waɗannan
hikimomi suna nuna hoton rayuwar al'ummar musamman ta fuskar zamantakewa da
addini da tattalin arziƙi da duk wata hanya
ta rayuwa. Wamnnan shi ne falsafar al'umma , yin nazari mai zurfi irin waɗannan
abubuwan da aka lissafa shi ne falsafa.
Gusau,
(2001). ya kawo ma'anar fasafa da cewa: falsafa wani fanni ne da ake nazarin
tsarin rayuwar al'umma da yadda suka suke wanzuwa da dalilin faruwarsu, da
matsayinsa a zangon nazari mai zurfi. sh- 68.
Momoh, (2000).ya bayyana falsafa ce tushen duk
wata wayewa, ita ce ƙoƙuwar
rufin wayewar al’umma a kusan komai. Mafalsafin ya ƙara
da cewa, falsafa tana haska rayuwar al’umma, idan ta
yi ƙamfa kuma, akwai duhu kewaye da komai na al’umma. Saboda falsafa hikama ce ta ƙoli.
Mafalsafin ya ƙara da cewa, tunanin al’ummar da ba ta da
falsafa yana ƙuƙumce da sarar
bauta, haka kuma zurfin tunanin falsafa yana gaba da na sauran sassan ilmi
Oxford, Dictionary,(2008) an bayyana ma'anar
falsafa da cewa wata manufa ce ko ra'ayi da ke samowa daga ƙwaƙwalwar
ɗan Adam.
Sannan kuma an cigaba da cewa falsafa hanya ce ta sarrafa abubuwa da za a yi
nazarin su ta yin amfani da ƙwaƙwalwa.
Gusau, (2022). ya bayyana falsafa da cewa
hanya ce ta aikata wani abu ta hanyar harshen da mutum yake magana da shi na
tunani ko tafakkuri cikin hikima da azanci ta furuci ko rubutu, ya ƙara
da cewa falsafa tunani ce ta hanyar samo wani abu ko gano ko kuma hango ko
tabbatarwa cikin hikima ta yin hange ko hasashe ko ƙagowa ko
sauwarawa ko kimantawa ko kwaikwayo dangane da muhimman manufofi a rayuwar
mutum.
Spirkin, (1983). ya ce, falsafa tana nazarin
al’adu da kimiyya da fasaha da siyasa da addini da nagarta da sauransu. Waɗannan rassa
na falsafa sun sanya ana danganta ta da hikima, wadda ta ƙunshi kusan
kowane fage na rayuwa. Hakan ya sanya Descartes ya fasalta falsafa da bishiya,
wadda ilmin zahiranci ya tsirarar da na gaibiyya, kuma sauran sassan ilmi suka
zama rassanta; musamman likitanci da fasaha da nagarta. Falsafa hanyar nazarin
tunani ce ko ra’ayi ko wani al’amari da yake wanzuwa a sararin duniya. Falsafa
fagen nazarin duniya ne da halittun cikinta. Falsafa, tunani ne game da rayuwa
da fa’idarta ga mutum, kuma ta karaɗe fagagen ilmin kimiyya da na fasaha.
Falsafa tana ankarar da mutum game da muhallinsa. Falsafa tana ci gaba da ɗora mutane a
kan turbar da za su ƙara fahimtar kansu,
da yadda ya kamata su rayu. Irin namijin ƙoƙari
da ake yi a falsafance wajen amsa waɗannan tambayoyi: Ya ya duniya take?
Mene ne asalin mutum? Ya ya aka a yana gaba da na sauran sassan ilmi.
Gusau,(1999) ya rawaito wata ma'ana daga
Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya a muƙaddimar
littafinsa HANYA ƊAYA, cewa "ita falsafa wani ƙasaitaccen
tunani ce taƙaitacce da ke koyar da hikima da
kujiba-kujibar rayuwa, domin ita falsafa tana bayyana yadda al'amura suke a
tsarin rayuwa, da fasalin aukuwar al'amura ta dalilin faruwarsa ga al'umma,
wato tana samar da makamar rayuwa da hanyoyin da ake bi wajen gudanar da
ita".
Ogungbemi, (2007). ya ce, falsafa nazari ne da
yake fafitikar gano amsoshin wasu manyan tambayoyi da suke da muhimmanci a
rayuwa. Falsafatana haska alƙiblar rayuwa,
a fahimci al’amura a bisa hujjoji. Falsafa takan
sanya wa mutum idon zucin al’amura a
zuciyarsa, kuma takan sanya masa tunani da ƙaimin
tantancewa da rarrabewa a tsakanin al’amura. Mafalsafin ya ci gaba da cewa,
falsafa ba ta zura wa al’amari ido kurum sai ta yi tambayoyi a kansa; tambayar
takan bukaci amsar da ta shafi alherin abu da sharrinsa. Hangen falsafa a kan
al’amura ya sa a da yadda mutane suke tunaninsu na yau da kullum, domin falsafa
fagen nazari ne, kuma ilmi ne da yake tarke rayuwa ya sake gina ta a kan ƙwararan
hujjoji.
Wasu daga cikin manazarta musamman turawa suna
taraddadin cewa ko al'ummar afrika suna da falsafa?, masanan irin su parinder
(1961) da Finnegan (1970) da Bodunri (1981) da Hounrtoudji (1983) da Appiah
(1992) duk sun haɗe kan fau-fau
al'ummar da ba su naƙalci rubutu da karatu
sosai ba. Hausawa dai sun ce aka taru aka zama ɗaya ba dan
haka wasu masana musamman ƴan Afrika
irin su Mbiti (1980)da Gyeke (1995) da Onyeweenyi (1993-1995 duk sun mayar da
martani ga waɗannan Turawa
cewa lallai Afrikawan suna da falsafa suka ƙara da cewa
shirgici-bagiji ne ma a ce wai don kawai al'ummar Afrika ba ta daɗe da fara
rubuta harshen ta ba don haka a ce ba ta da falsafa. waɗannan masana
sun ce a nazarci adabin baka na al'ummar Afrika idan bana ga falsafa ba. Don
haka ne ma gyeka ya ce la shakka da za a nazarci karin magana da guntattakin
zantukan hikima da tatsuniyoyi da hikayoyi da tarihi na mutanan Afrika to kuwa
da za a iske falsafa maƙale cikinsu, ya ƙara
da cewa " ba a raba ɗaya biyu idan aka nazarci waɗannan ɓangarori na
adabin baka lallai za a iske falsafar al'ummar Afrika gameda ma'anar da ita.
Haka kuma a daɗa naƙaltar
ɗan Adam da
inda ya sa gaba , kai har ma da makoma bayan fakuwa duk da za a same su a waɗannan ɓangarori na
adbin baka na mutanen afrika.
Dangane da bunƙasar falsafa
kuwa, Gusau, (2022) ya bayyana cewa duk lokacin da ake son gane yadda ilimin
falsafa ya faro yana da muhimmanci a faro bincike tun daga lokacin da ɗan Adam ya
fara tunani da kansa, wato ilimin sanin mutum kansa. Shi kuma sunan falsafa
suna ne da ya samo daga yonanawa da girkawa mutane ne da masu son bincike , da
gwaje-gwaje da zurfafa tunani, wajen tabbatar da duk abin da suka sa gaba tun
farkonsu zuwa yau (Muhammad, 19-15 7).
Bincike
ya nuna cewa sun fara tunani shin mene ne a cikin wannan duniya kafin samuwarta
da kuma abinda ya samar da ita, yin bincike akan "samuwa", Haƙiƙa
sun zurfafa bincike akai don haka suka sanyawa kansu wasu tambayoyi guda uku ,
wanda suka shafi kowanne mutum ko ya kan tambayi kansa:
=
Daga ina ?--...nake.
=
Ina zuwa ?--...ina za ni
=
Domin me?
Da waɗannan tambayoyi ne
aka ɗora nazarin
fannin falsafa tun asali, daga al'ummar yonanawa . Haƙiƙa
mutum an samar da shi da wasu ɗabi'u wanda suka bambanta shi da
waninsa, kamar dabbobi da tsirrai, da duwatsu. Babban abinda ya bambanta su shi
ne :
v
Tunani : Nazari da bincike da neman dalili
v
Hankali : ƙwaƙwalwa
v
Harshe : furucin magana
Domin haka sai mutum tun farko ya
fara tunanin ya aka yi ya sami kansa a wannan fili, kuma me ya samar da shi ?
kuma don me, ta yaya ake yin rayuwa?, masana suka haƙiƙance
cewa masomin tunani a fannin falsafa. da wannan dalilin wasu masana suke ganin
cewa ba yunanawa ko faransawa ne asalin ilimin falsafa ba. Suna ganin cewa
wannan tunani ne da kowa daga cikin ɗan Adam zai iya yi, don haka matuƙar
akwai tunani a wani ɓangaren to akwai falsafa a wurin. Amma idan
ana magana akan wanzuwar ilimin da taskance shi to babu ja su ne sama da kowa
Saffar, (1982) (sh 1), Faruwar tunani ga mutum
daɗaɗɗe ne kamar
yadda mutum ya daɗe , kuma ya
zama abin da ba a ce ga daga wurin da tunani ya soma, shi tunani baiwace ta
Allah ta jikin ko ta yin amfani da tunani shi ya bambanta, shi tunani nishaɗi ne na ƙwaƙwalwa
". ya ƙara da cewa idan kuma muka koma izuwa bunƙasar
falsafa to muna iya cewa wannan ilimi ya ƙunshi wasu
matakai guda huɗu a farkonsa
kamar haka :
Alhawani,(1962)
ya yi bayanin yadda falsafa take a tsarin addinin musulunci cikin littafinsa
mai suna " Falsafa al-islamyya" an bayyana faruwar tunani ga mutum daɗaɗɗe ne kamar
yadda mutum ya daɗe , kuma ya
zama abinda ba za a ce ga daga wurin da tunani ya soma ba, shi tunani baiwa ce
daga Allah ta jikin kowanne ɗan Adam yin amfani da tunani ne ya
bambanta su, shi tunani nishaɗi ne na ƙwaƙwalwa".
A
ɓangaren
rabe-raben falsafa kuwa Gusau, (2021) ya kasa falsafa zuwa gida uku muhimmai,
wanda suka haɗa da falsafar
Harshe, falsafar kwatance, da kuma falsafar Rayuwa.
Guya,(2001).ya
fito da tunanin Bahaushe a littafin gasa ta farko (1993) ya fito da tunanin
Bahaushe dangane da kyawawan ɗabi'u da halaye waɗanda Hausawa
ke kira ayi koyi da su, kamar jarumta,haƙuri da tunani
da gaskiya da kara da kunya.
Edger,(2010).
wanda ya yi managarcin sharhi akan tunani , inda yace , kalmar tunani na da alaƙa
ta ƙut-da-ƙut da ƙoƙarin
yin imani ko yarda musamman akan abin da ba a da tabbaci akan sa . Har ila yau
ya ƙara da cewa tunani nasa hankalta akan wani
abu musamman wanda ya ke kusa da mutum. Edger bai tsaya a nan ba sai da ya kawo
alaƙar da ke tsakanin ilimi da tunani da fagen
ilimin mutuntaka. Haka zalika masanin ya bayyana cewa masana ilimin ɗabi'a irin su
Skinner (1971 sun bayyana cewa mutane na tunani ne da dukkannin jikinsu ba da
kwakwalwa kaɗai bax wato
tunani ɗabi'a ce a
maganance ba a aiwace. Bugaje,(2014) yana da ra'ayin cewa tunani hanya ce ta
warware matsala a wajen lissafi ko ƙirƙira
ko a wasanni musamman irin na dara.
Bunza,(2015).
ya ce kowanne al'amari falsafa na kallon mafari ko sanadinsa da dalilin
samuwarsa tare da hujjoji da za su tabbatar da hasashen. A fagen nazari falsafa
kimiyyar kanta ce, Hangen falsafar Bahaushe bai saɓa da ta
Bature da Balarabe da Bagirke da Balatine ba, tattare da sanin cewa ƙamusoshin
Hausa ba su kula da kalmar ba a hangensu, za mu iya cewa:
A
wajen Bahaushe falsafa ita ce ƙololuwar
basirar ƙyallaro dalilan faruwar abubuwa da hasashen
fassarorinsu na kusa da nesa, bisa ga dalilan hankalin tuwo domin su yi
cancaras da al'adun mutanensu. Falsafar kimiyyar hasashe ce, mai tafiya da
al'adun mai hasashe da al'adar rayuwa da aka saba da ita. Falsafa kuratun
mutanen jiya ne, da ya gagari mutanen yau saukewa, ya zama maganaɗisun rayuwar
mutanen gobe. Ya ƙara da cewa: Idan za a yi hasashen falsafar
Bahaushe, dole a dubi adabinsa na baka, da nau'o'in bautarsa, da warkarwarsa,
da tattalin arziƙinsa,bda tsarin siyasar zamantakewarsa. Sanin
cewa rayuwarsa ta gargajiya gaba ɗaya akan falsafarsa yake tafiyar da
su, na ga ya dace in yi garkuwa da falsafa ɗaya in
tunkari muradina, gundun ka da a yi kwasan karan mahaukaciya.
Gusau,(2022).
ya yi bayani dalla-dalla game da asali da kuma shi kansa ilimin falsafar,har
ila yau kuma an yi ƙoƙari
matuƙa wajen bayyana tarihin masu ruwa da tsaki a ɓangaren
binciken falsafa tare da zayyano manyan mafalsafan duniya kama daga ƙasashen
ƙetare da ma duk wani sauran fannonin rayuwar ɗan Adam.
Marubucin
bai tsaya iya nan ba, domin kuwa ya fito da yanayin falsafa a zamantakewar
Hausawa ta farko a ƙasar Hausa, da kuma
ayyana tsarin rubutun boko a matsayin tsari na gabatar da wasu ayyukan falsafa
a rayuwar Hausawa. Tabbas ko ba a ce komai ba wannan muhimmin littafi na da
makusanciyar alaƙa da wannan binciken, domin kuwa ya taɓo fannin
falsafa ne tun daga samuwarta har yadda Hausawa suka riƙa ta'ammali
da ita cikin lamuransu, duk da kuwa wasu na ganin cewa Hausawa dama suna da
falsafarsu tuntuni, sai dai du da haka ba zai hana gudanar da wannan binciken
ba domin kuwa ba a ware wani ɓangare na daban an fito da falsafar
Bahaushe cikinta ba, kamar yadda wannan binciken zai fito da falsafar Bahaushe
cikin wasannin gargajiya.
Yakasai,(1988
). ya yi nazari a kan rayuwa da falsafa cikin al'ummar sinawa, inda ya fito da
keɓaɓɓun kalmomin
fannu da kuma maganganun azanci da hikima, waɗanda suka yi
tasiri a rayuwar falsafa cikin al'ummar sinawa, sa'annan ya zaɓo tare da
fassara irin kalmomi da wasu manyan masana suka yi bayani a kansu.
Marubucin
ya yi ƙoƙari matuƙar
gaske domin kuwa aikin zai bunƙasa ilimi
dangane da falsafar al'ummar sinawa da tarihi da kuma aikin fassara da fahimtar
falsafar sinawan game da rayuwarsu.
Muhammad,(1977).ya
yi amfani da wani baitin waƙa na siyasar
jam'iyyar NEFU mai suna ƴar fulani ya
kawo misalin zalunci da ake yi ta hanyar ƙarya da
makirci da yake cewa:
"waƙa na fulani
yimre,
mun ji ƙara sun ce
masa yombe
ƙarfi sun ka ƙira
shi da samba,
kai kasabubu abokin camba,
ƴar ƙarya
da yawan makirci.
Ya
yi amfani da wannan baiti ne domin nuna tunanin Bahaushe akan ƙarya
da zalunci da kuma nuna cewa dukkan waɗannan abubuwa ne da
bai kamata ana yinsu ba.
Maryam,
(1998). ta bayyana mawaƙi a matsayin
mafalsafi, a inda ta kawo matsayin mawaƙi a idon
jama'a da kuma matsayinsa a addini da kuma matsayin mafalsafi da yadda falsafa
take a ƙasar Hausa. Har wa yau ta kawo falsafa na
marubuta waƙoƙi da yawa
kamar "falsafar waƙar malam Muhammadu na
Birnin gwari" ta kawo wasu baitoci masu nuni da halin duniya in da malamin
ke cewa:
Komi na duniya mai ƙarewa,
Ni ban ga wanda zai shi ɗore ba,
Na dubi duniyar har babinta,
Ni ban ga tattali ya ibada ba,
Da ku da duniya kwa ƙare
duk,
Da dukiyarku har da sarautarku.
Haƙiƙa
wannan zancen na Muhammadu Birnin gwari ya yi gaskiya domin ya yi wannan waƙa
ne da daɗewa, amma ga
shi yanzu kamar yau ne ya yi ta, saboda a wannan lokacin mafi yawan jama'ar
duniya suka sa a gaba sun mance da lahira. Haka ma idan muka dubi waƙar
sa'adu zungur ta AREWA JAMHURIYA KO MULUKIYYA ya nuna falsafa sosai a waƙar
inda yake cewa.
In kun dage kun shantako,
Bisa al'adu na mazan jiya,
Za ku rera faɗar
da-na-sani,
Da na bi jawabin gaskiya.
Saboda haka shima wannan bincike na da alaƙa
da wannan aikin, domin kuwa duk suna magana ne akan falsafa.
Shi
kuwa sankalawa,(1994).ya nazarci rayuwar Sani Sabulu da falsafar waƙoƙinsa
a inda ya fito da yanaye-yanayen waƙoƙinsa
ta fuskar jigo da zubi da tsari da salon sarrafa harshe a waƙoƙin.
Bello,(1993).
ya yi bajakolin tunanin Bahaushe a harshen Hausa, inda ya zurfafa tunani wajen
zaƙulo hikimomin Bahaushe game da Harshensa da
kuma rayuwarsa a da da yanzu.
Adamu,(1994).
ya gudanar da nazari akan tunanin Bahaushe game da duniya inda ya yi bayanin
yadda Bahaushe ke kallon duniya da kuma hikimominsa game da zamantakewar
rayuwar duniya, da ma yadda ya riƙa kwatanta
duniya da sanyata cikin adabinsa ta ko ina da suka haɗa da
zantukansa na hikima, karurrukan maganganunsa, azanci, da dai duk wani abu da
ya shafi adabinsa da kuma zamantakewarsa.
Amin,(2004).ya
binciko falsafar Bahaushe game da rayuwar ɗan Adam in da
ya fito da irin tunane-tunanen Malam Bahaushe da hikimarsa har ma da dabarun
rayuwarsa ta yau da kullum, ba ma iya tasa rayuwar ba har ma da yadda ya riƙa
sanya daburu cikun zamantakewarsa da bakin al'ummomi da suka yi tarayya da su.
Don haka shima wannan binciken na da alaƙa da wannan
domin duka dai falsafar Bahaushen za su gano sai dai kuma kowa da inda ya
karkata binciken nasa, wato shi ya yi game da rayuwar ɗan Adam
wannan kuma akan wasannin gargajiya. Yayin da Amin, (2010) shi kuma ya fito da
gudunmawar Mamman shata katsina wajen bunƙasar falsafar
Bahaushe, ya bayyana irin ƙoƙarinsa
wajan sanya hikimomin Bahaushe cikin waƙoƙinsa
masu alaƙa da fannonin rayuwa iri daban-daban harma da
harshensa. Shi kuwa Gobir 2012), ya fito da falsafar Bahaushe ne game da
cututtukan iskoki ya yinda ya fayyace yadda Bahaushe ke kallon iskoki da kuma
tunaninsa game da cututtukan da ɗan Adam ke samu a sanadiyyarsu da kuma
yadda suke ta'ammali da iskoki cikin harkokinsu na yau da kullum.
Shi
kuwa Musa,(2013). ya fito da falsafar Bahaushe a kan waƙar tsuntsaye
ta malam Amadu ɗan matawallen
Haɗeja,
marubucin ya kawo irin hikimomin da ke tsuntsaye ke da shi inda mawaƙin
ya yi bajakolinsu cikin waƙar tasa, haka
kuma ya bayyana falsafofin ne ta hanyar zaƙulo nau' o'in
falsafa da aka gina a waƙar
dalla-dalla tare da tabbatar da wuraren da suka zo cikin waƙar
ta hanyar kyakkyawan bayani, har ma da yanayin falsafar. Don haka nake ganin
wannan binciken ma na da makusanciyar alaƙa da wannan,
domin kuwa shi ma dai ɗungurungum falsafar ya binciko ta tsuntsaye,
sai dai shi ya dubi waƙa ne, wannan kuma ya
shafi wasanni ne. don haka ba zai hana a cigaba da wannan binciken ba.
Bunza,(2017).
ya yi na zari game da falsafar al'ada a makamin democraɗiyya, ya yi
namijin ƙoƙari ƙwarai
da gaske wajen fito da yadda Bahaushe ya tsara hikimominsa a cikin al'adar
shugabacinsa, wadda ƙarara suka bambanta
da sabon tsarin da muke ciki. Shi kuwa Sani (2012 ) ya nazarci yadda ƙabilu
suke a tunanin Bahaushe, aikin ya fito da irin ƙabilun da
Hausawa suka riƙa tarayya da su da kuma irin fitattun labarai
game da waɗannan ƙabilu
da kuma ɗora su bisa
tunanin Bahaushe na " da wayo ake faɗawa wawa gaskiya
" tare da amfani da faɗakarwa da nishaɗantarwa".
Abubakar
(2018), ya yi nazari game da bigire a tunanin Bahaushe, aikin na abubakar ya
fitoda duk wani abu da ya danganci bigre (muhalli) na Bahaushe, da suka hada da
gida, kasuwa, da dai sauran wurare daban-daban da suka shafi bigeren da kuma
irin muhimmancinsa a wurinsu.
Dumfawa,(1988
). ya fito da tnanin Bahaushe ne cikin littafin ruwan bagaja inda ya hasko irin
tunanin Bahaushe na rayuwar yau da kullum wadda ta danganci ɗan Adam, ya
yi bayanin tunin Bahaushe da ya danganci neman abu ga masu shi, da matsayin
sarki ga Bahaushe, da imani da aljanu, da muhimmancin naciya ga mai nema, har
ma da muhallin tsofaffi a cikin al'umma waɗannan su ne
abinda marubucin ya karkata wajen fito da ma'anar da suke ɗauka a
tunanin Bahaushe game da rayuwa.
Yusuf,
(1988 ).ya gudanar da bincikensa kan falsafar malanta cikin littafin ruwan
bagaja, shi ma wannan aikin ya taɓo falsafa ne ta Bahaushe game da
al'amarin malanta (koyarwa) a inda aka fito da hikimomin da ke cikin koyarwar
malam Bahaushe da kuma irn dabarun da yake da shi a fannin har ma da binciko
irin matsalolin da ake samu a tsakanin malamai na hassada, da kushen juna da
son ɗaukaka wanda
wasu lokutan kan haifar da fito-na-fito .
Haƙiƙa
wannan binciken ba zai hana cigaba da gudanar da wannan bincikenba,domin kuwa,
shi ya karkata ne ga abinda ya shafi falsafar malanta.
Alala,
(2021).ya nazari game da waƙoƙin
Haruna Uji a inda ya fito da tunanin Bahaushe cikinsu, wato irin hikimomin
malam Bahaushe da ya riƙa sanyo wa cikin waƙoƙin,
Shi kuwa Ibrahim, (2021) ya yi nazarin falsafane cikin waƙoƙin
sadi sidi sharifai, aikin ya yi matuƙar ƙoƙari,
domin kuwa ya fito da irin falsafofi ko hikimomin mawaƙin da ya ke
sawa cikin waƙoƙinsa.
Duka
waɗannan
nazarce-nazarce da aka bibiya game da falsafa, daga ayyukan magabata ba za su
dagatar da wannan aikin ba, domin kuwa dukansu akalarsu ta karkata zuawa ɓangarori
daban-daban da ake binciken falsafar a kansu, kamar waƙoƙi,
bigire, malanta da saurnsu. Ko ba komai dai aikin falsafa ma ba baƙo
ba ne a wurin masu nazarin, domin kuwa mun ga irin yadda masana suka gudanar da
aikace-aikace na falsafa a fannoni daban-daban.
2.4
WASANNI
Kalmar
wasanni jam'i ne na wasa a Harshen Hausa, wadda a yaren Ingilishi aka fi
saninsa da (play/plays). Wasa wani motsi ne da gaɓoɓin jiki tare
da magana ko ishara don washewa da nuna nishaɗi ko dan a
kau da baƙin ciki ko a nuna gwanintaka, ko bajinta ko ƙwazo
ko kuma akan yi wasa domin a kwaikwayi wani abu na musamman.
Ɗangambo,
(1984). an bayyana kalmar wasa da duk wani abu da ya shafi raha ko nishaɗi da akan
aiwatar da su ta mabambanta hanyoyi da kuma sigogi daban-daban.
Yahaya,
(1981) ya ce Wasa abu ne da yake nufin ba'a ko raha, ko wani abu da ake yinsa
amma ba dagaske ba. shi kuwa Umar (2000) ya bayyana da Wasa hanya ce ta bayyana
halaye ko ɗabi'u da buƙatu
ta hanyarmotsa jiki da fasahar baka da hannu da hannu wadda ke ɗauke da hoton
rayuwar al'umma.
Ƙamusun Hausa
CNHN, (2006), aka bayyana ma'anar wasa da abu wani abu da aka yi cikin raha da
nishaɗi.
Tukur, (1994/1999).ya fassara wasa da abu ne
da yake nufin ba'a ko raha ko wani abin da aka yi shi amma ba da gaske
ba". yayin da Gusau (2013) shi kuma ya kawo ma'anar wasannin yara da wasu
hanyoyi ne da dabaru waɗanda yara maza da mata suke amfani da su na
tsinka jininsu da motsa jki tare da cinye lokaci da samun walwala da naƙaltar
dabarun zaman rayuwa cikin nishaɗi.
Idris, (2019).ya kawo muhimmancin wasa da dama
da suka haɗa da ƙulla
dangantaka da zumunta tsakanin yara ko samari saboda ta sanadiyyar wasa yara
kan taso tamkar ƴan Uwa., da kuma yadda yake da tasiri wajan
hana yawace-yawacen yara ko kuma ƙar musu ƙaimi
cikin duk wasu ayyuka da za su tunkare shi.
Duba da yadda masana suka bada ma'anonin wasa
za mu iya fahimtar cewa, "Wasa wani motsi ne da gaɓoɓin jiki tare
da magana ko ishara don washewa da nuna nishaɗi ko dan a
kau da baƙin ciki ko a nuna gwanintaka, ko bajinta ko ƙwazo
ko kuma akan yi wasa domin a kwaikwayi wani abu na musamman.
Yahaya, (1972), ya kawo ire-iren wasannin
gargajiya da dama da kuma yadda ake aiwatar dasu cikin tsari da kuma abin
burgewa.shi kuwa Umar, (1977), ya kawo ire-iren wasannin tashe ne da dama wadda
ake da su a ƙasar hausa,da suka haɗa da tashen
mai magani, mairama da Daudu, da dai sauran wasannin tashe da kan aiwatar a ƙasar
Hausa musamman a lokutan azumi. Shi ma Lawan, (1977) ya yi bayanin wasannin
yara na gargjiya da yadda ake yinsu , ya kuma bayyana amfaninin wasannin na
yara a rayuwasu, sa'annan kuma ya yi bayanai sosai akan dandali.
Wannan binciken na Umar ba zai hana gudanar da
wannan binciken ba, domin kuwa shi ya kalli wasannin tashe ne kurum wannan kuma
zai yi nazari ne game da falsafar da ke cikin wasannin gargajiya ta Bahaushe.
Dembo, (2007), ya yi bayanin wasu wasannin
gargajiya na yara sosai da suka haɗa da wasan langa, wasan ƴar
kurciya, wasan kangal-kangal da sauransu.Wannan marubucin ya yi matuƙar
ƙoƙari da
burgewa, domin kuwa ya gudanar da aikin ne a sigar wasan kwaikwayo, amma cikin
hikima ya riƙa sanyo wasannin yara daban-daban, tare da
bayaninsu a taƙaice ta yadda wanda bai san wasannin ba kai
tsaye ba lallai ya iya fahimtar yadda ake gudanar da shi ba akan bayaninsa. Don
haka wannan binciken ya ƙudiri aniyar
fito da duk wata falsafa ta Bahaushe a cikin wasanninsu tare da kuma faɗaɗa bayanai
sosai domin fito da yadda tunaninsa ya cika wasannin nasa.
Daura,
(1982). ya yi bayani game da wasu daga cikin wasannin gargajiya,sai dai a iya
cewa su wasannin da ya yi magana akan su sun ta'allaƙa ne da
wasannin manya kurum,irin su kokuwa,dambe, bori,ƴan hoto da
sauransu. Marubucin ya yi ƙoƙari
sosai sai dai bai zo da wani bayani game da wasannin gargajiya ba musamman yara
da kuma matasa,don haka nke ganin ya dace a fito da hikimarsu a sarari domin ƙarin
haske.
Sani
da Gobir, (2020) sun fasalta wasanin ƙasar Hausa
bakin gwargwado ta fuskar jinsi da shekaru da kuma yanayin aiwatarwa har ma da
lokutan aiwatar da wasannin, hakan kuwa tabbas ya nuna jajircewa da kuma nuna
bambanci da sauran takwarorin littattafan wasannin da suka shafi ƙasar
Hausa, domin kuwa littafin na kammale da nau'ikan wasannin gargajiya da ma
sauran wasanni har guda ɗari biyu da goma sha huɗu 214 waje
guda.
Muhammadd,
(1984) ya kawo fa'idoji da illoli da kuma matsayin ma'abota sana'o'i a idon jama'a,
ƙarƙashin haka ya
kawo wasannin masu yawa da yadda ake gudanar dasu awasu sana'o'in gargajiyar
Bahaushe . A cikin wasannin ya ɗan taɓo wasu daga
cikin wasannin yara . wannan aikin ma na da alaƙa da wannan
binciken domin kuwa ya taɓo abinda ya shafi wasanni.
Ado,R.
(1987) sun fito da irin alaƙar da ke
tsakanin wasannin kwaikwayo da rayuwar al'ummar Hausawa musamman na yanzu, d
kuma wasannn kwaikwayon da ake aiwatarwab yanzu, inda ya fito da irin halaye da
kuma ɗabi'u da suka
mamaye rayuwar Hausawa wadda kuma akan tsinto su ne daga daga cikin nau'ikan
wasannin kwaikwayon da ake aiwatarwa.Saboda haka nake ganin ko kaɗan wannan
kundi ba zai hana gudanar da wannan aiki ba.
Bunza
da koko, (1988) sun bayyana yadda ake aiwatar da wasannin yara a ƙasar
gwandu wanda suka ƙunshi wasannn maza da
mata na gargajiya. wannan bincikenma ba zai hana aiwatar da wannan binciken ba.
su kuwa Safiyanu,Hassan da Hassana(2017) sun gudanar da bincikensu game da
dusashewar wasannin gargajiya a ƙasar yabo
yayin da suka bayyana ire-iren wasannin da ake aiwatarwa a ƙasar
yabo da kuma bayyana tsirinsusa annan suka bayyana yadda wasannin suka ɓace/dusashe a
ƙasar yabo , har ma da dalilan da suka jawo
dusashewarsu. yayin da Kaduna, (1988) ya binciko irin tasirin da zamani ya yi
akan wasannin yara ƙasar Hausa da kuma
hanyoyin da za a bi wajan farfaɗo da su. Aikin nasa na da dangantaka
kwarai da gaske da wannan binciken, dalil kuwa shi ne dukkannisu biyu za su yi
tsokaci ne game da wasanni, sai dai kuma aikin na Kaduna ba zai tsayar da
wannan binciken ba saboda shi hikimomin cikinsu zai dubo.
Sakkwato,
(1982) ya binciko ire-iren wasannin yara masu ɗauke da
wake-waƙe sa'annan kuma ya karkata akalar bincinken
nasa ne ga garin sakkwato. ya yin da aikin Mai rukubta,(1994) ta fayyace tawai
a matsayin dabarun reno a ƙasar Hausa, a
wannan binciken ta fito da waƙoƙi
kala-kala waɗanda mata
musamman ƴanmata ke yi wa yara lokacin raino.Irin waɗannan waƙoƙi
na ɗauke da
zambo, habaici, da ba'a da kuma kurarawa da gwarzantawa.
Dangantakar wannan binciken da wannan shi ne
kasancewar wasannin Hausa da dama suna ɗauke da waƙoƙi
sannan yayin rainon kansu waƙa ake musu.
Abdu,yahaya
bichi, (2002) ya yi bayanin tsofaffin Wasannin Hausawa da tsare-tsarensu da
kuma yanayinsu. Yayin da Shehu (2002) shi kuma yayi nazari game da tashe
dabire-irensa a garin kano, bayannan ya zayyano wasannin tashen da suka ƙunshi
na mata da na maza.
Hadiza,S.
(2009) ta yi nazari game da haƙuri a tunanin
Bahaushe ainda ta yi duba cikin wasannin jatau na kyallu da wasan tabarmar
kunya da wasan matar mutum kabarinsa da uwar gulma, a inda ita kuwa Garba.R
(2009) ya yi nazari akan mace cikin rubutattun wasannin kwaikwayo, misali cikin
Uwar gulma da kulɓa na ɓarna.
Badamasi,
(2013) ya fito da yadda wasannin Hausawa suke wajan bunƙasa lafiyar
al'umma , ya kawo wasu daga cikin wasannin yara tare da nuna yadda suke
gudanarwa cikin ƙiriniya da doke-doke da sauransu. aikin nasa
na da alaƙa matuƙa da wannan
binciken amma duk da haka ba zai hana gudanar da shi ba.
Autatuwa
,(2021) ya yi bincike game da taɓarɓarewar
wasannin gaɗa a garin haɗeja, a inda
manazarcin ya fito da tasirinsu da kuma dalilan ɓacewarsu har
ma da ci bayan da aka samu game da ɓacewar tasu.
Shi
kuwa Malumfashi, (1984) ya yi bayanin akan bori addini ne ko kuma wasan
kwaikwayo, binciken ya ƙunshi dukkanin
bayanai game da yadda Hausawa ke kallon tare da gudanar da al'adar bori.ya kuma
fayyace matsayinsa a rayuwar Hausawa. aikin ya na da alaƙa da na
Malumfashi, domin kuwa shi ya fayyace Bori a matsayin wasan kwaikwayon kansa.
2.3 TATSUNIYA
kalmar tatsuniyar nan tana ɗauke da
sunaye mabambanta, ta la'akari da muhalli ko yankin ƙasar Hausa.
Kamar yadda Bergery (1934/51:37) da kuma Gusau, (2013:1) suka bayyana,
Tatsuniya ana kiranta da sunan “Gatana” a yankunan Sakkwato (da ya haɗa Kebbi da
Zamfara a yau) da Katsina wanda suka yi hasashen samuwarta daga tsarin kalmomin
da ake fara buɗe tatsuniyar
dasu na “gata nan gata nan ku”. Sa'annan suka ci gaba da bayyana yadda ake
kiranta a sauran yankunan Kano da Zariya da suke kiranta da suna tatsuniya
masana da manazarta da dama irin su Bergery
(1934/15: 1005) sun bayyana tatsuniya ko gatana a matsayin “Labari ko Almara”.
Shi ko Skinner (1965:62) ya fassara kalmar
“Fable” da “tatsuniya ko almara ko labari”. Shi ma Newman (1997:93/102) ya
bayyana ta da kalmomi masu dangantaka da tatsuniya wato fable a matsayin hikaya
da kuma folktale a matsayin tatsuniya wacce ta shafi tauraro Gizo”.
Idan muka yi nazarin ma'anonin da suka gabata,
dukkaninsu suna magana kan tatsuniya inda suka siffanta ta da labarun da suka
dangance ta wato almara da hikaya da kuma ita kanta tatsuniya. Sai dai kuma
dukkanin ma'anonin an bayar da su a dunƙule, ba tare
da bayyana tatsuniyar ta yadda wanda bai santa ba zai iya gane ta.
Ta fuskar ma'anar tatsuniya a sarari kuwa,
masana da dama sun samu tofa albarkacin bakinsu kamar: Umar (1980:11) ya
bayyana tatsuniya a matsayin:
“ƙagaggen
labari ne wanda magabata kan shirya don bayar da tarbiyya kan tafarki na
gargajiya”.
Shi kuwa Zarruk da wasu (1987:7) suna kallonta
a matsayin “Labarin da aka shirya domin gizo da waninsa, mai tattare da hikima
da fasaha”. Sai Yahya da wasu (1992:7) Sun kuma bayyana ma'anar ta tatsuniya a
matsayin: “Tsararren labari na hikima mai an tsawo da nuna ƙwarewa
wanda ya ƙunshi shiryawa kan nuni zuiwa ga kyawawan
halaye da koyar da ilimin zaman duniya, tare da saka nishaɗi da kuma
cinye lokaci”.
Su
ma Junaidu da ƴar'aduwa (2007:75) sun daɗa zancen ta
bayyana cewa “ƙagaggen labari ne na ƙarya marar ƙamshin
gaskiya a cikinsa, wanda Hausawa kan shirya don sanya annashuwa da raha”. Ɗangambo
(2008:30) shi ma ya bayar da tasa gudummuwa da cewa: “Tatsuniyoyi da labarai su
ne makarantar farko ta ƴaƴan
Hausawa, a zamanin da, lokacin da ba a samu ilimin karatu da rubutu ba, inda
ake koyar da su tarbiyya da hani da horo da dabarun fafutukar tafiyar da
rayuwa. Sai Koko, (2009:2) ita ma ta ce: “Tatsuniya labari ne da mutane ke ƙirƙirawa
cikin azanci don tarbiyantar da ƴaƴansu
da kuma cimma wasu buƙatoci dangane da al‟umma”.
Gusau,
(2013:5) ya bayar da nasa agaji wajen samar da ma'anar tatsuniya da cewa: Tatsuniya
wani tsararren labari ne shiryayye wanda ake shiryawa cikin hikima da nuna ƙwarewa
da naƙaltar harshe domin koyar dabarun zaman duniya
daban-daban.
Rabi'u (2018:65) a nasa kundi ya ƙara
da cewa : Aiki ne da mai ba da labari ke tsarawa domin ya saita tunanin yara
masu sauraro ta amfani da taurarinsa a lokacin da yake warware zaren
tatsuniyarsa‟.
Idan muka yi la'akari da ra'ayoyin masana da
suka gabata dangane da ma'anar tatsuniya, za mu ga cewa dukkaninsu sun tafi kan
abubuwan da yawa da su ne suka haɗu suka bayar da tatsuniya kamar “ƙagaggen
labari ne da ake tsarawa” kenan bayan
an ƙaga, sai kuma an tsara don ya dace da manufar
da ake so a isar, da kuma tunanin masu sauraro. Sa'annan kuma dole ne ya
kasance yana “koyar da gyaran hali ta fuskar cusa tarbiyya da hani daga abubuwa
marar kyau.” Sa'annan ya samar da nishaɗi. Idan har labarin
ya kasance ya tsallake waɗannan dokoki to ya tashi daga zama
tatsuniya, sai dai labari ko hikaya ko almara da sauransu
Labarun tatsuniya an tsara su ne ta yadda suka
dace da al‟adun Hausawa
da tunanin yaro. Sa‟annan suna da matuƙar
muhimmanci, domin ana koyar da halayya mai kyau da tarbiya a cikinsu. Labaran
suna da daɗin sauraro,
kuma ba su saurin gundurar da waɗanda ake baiwa labarin, musamman waɗanda ake
tsara labarin domin su, wato ƙananan yara.
Kasancewar salon ba da labari da ake amfani da
shi tare da riƙa jefa gajerun baituka na waƙa
akai-akai wadda take jawo hankalin mai sauraro. Tatsuniya tana ɗauke da wasu
muhimman abubuwa da suke ɗauke dabarun koyar da iya zaman
duniya, da taskace al'adun al'umma da koyar da tarbiyya da saka nishaɗi. Duk da
cewa wasu rukuni namalaman addinin musulunci suna kallonta a matsayin hululu,
saboda kasancewarta ƙirƙira,
amma tana da tasiri a zukatan masu saurare da saurin isar da saƙo
da daidaita tunanin ƙananan yara masu
tasowa.
Dangane da tatsuniya a idon ƴan
kallo, Su kuwa masu bayar da tatsuniya suna ganin tatsuniya a matsayin labari
mai armashi wanda yake tarbiyantar da ƙananan yara
da cusa musu wani zance tunani cikin sauƙi, su fahimta
ba tare da ɓata lokaci
ba.
Kasancewar yaran yanzu ba su sauraren
tatsuniya, amma an samu zantawa da wasu magidanta masu shekaru 50-55, inda suka
bayyana cewa tatsuniya abu ce mai matukar amfani ga rayuwar Bahaushe wacce take
ɗauke tsantsar
al'adunmu na gargajiya da suke koyar da ɗa'a da zamantakewar
rayuwa. Sun ƙara bayyana cewa rashin tatsuniya ya taimaka
wajen samar da baƙin al'adu a cikin ƴaƴan
Hausawa. (Hira da Malam Sama'ila ).
A ƙarƙashin
wannan rukuni na labarun Hausa, wanda aka fi sani da tatsuniya, masana sun
karkasa shi ta la'akari da kayan cikin tatsuniya kamar Ruth (1970) da Skinner
(1969) da Yahaya (1992) da Koko (2009). Sai dai za a bi fasalin Koko (2009)
domin samun gabatar da su a bisa faifan nazari tare da yin sharhin ra'ayoyin
masana kan yadda suka fahimci kashe-kashen tatsuniyar.
Tatsuniya
sha kundum ce, domin ta ƙunshi labaru
da suka haɗa da na
mutane (na zamanin da ake ciki da tarihin abin da ya gabata) da labarun dabbobi
(na nau'o'in dabbobin da ake samu a cikin muhallin Bahaushe na gida da na daji)
da labarin aljannu (domin kuwa imanin Bahaushe bai kammala sai an samar ma
aljannu matsugunni) da labarin gamin-gambiza (labari ne ya haɗa taurari na
jinsi daban-daban) da Labarin tsuntsaye da kwari da tsiraruwa da labarin tarihi
(Ahmad da malumfashi, 2019).
Dangane da asalin samuwar tatsuniya kuwa
masana irin su Gusau (2017), Yahaya (1987), Ɗangambo
(1996), sun bayyana cewa Tatsuniya na ɗaya daga cikin ƙananan
rukunnan adabin baka daɗaɗɗu da ba a iya cewa ga lokacin da aka
faro su, ko kuma ga yadda suka samu, saboda tsawon lokaci da suka ɗauka cikin
al'umma. Hasali ma ka ana iya cewa tana daga cikin hikimomin harshe na farko da
Bahaushe ya samu bayan ya samu wurin zamansa na dindindin. A wajen neman asali
ko samuwa ana duban tushe ko salsala don sanin lokacin abin ya faro da yadda ya
faro, wannan ya sa a cikin fannin ilimi daban-daban ake neman sanin faruwar
abubuwa da dama da suka wanzu lokaci mai nisa. Ma'ana a nan shi ne ana ƙoƙarin
danganta wasu abubuwa ko al'amurra da samuwarsu, wanda lokacin da abin nan ya
faro babu hanyar karatu da rubutu na taskace shi, Waɗanda suka
faro shi ba su raye, waanda suke da labarin su ma sun kau. Ya kasance lokaci ya
yi nisa da za a iya samun bayanan abin da ake nema
Yahaya da wasu (1992:7) sun bayyana cewa
tatsuniya tana daga cikin labarun Hausawa na farko waɗanda su suka ƙirƙiro
su da kansu domin saka nishaɗi da koyar da yara tarbiyya. Sun yi riƙo
da wannan hanya ta gado da suka gada daga kakanni da daɗewa kafin su
samu cuɗanya da baƙin
al'ummu. Tsintsar al'adun Hausawa, su ne harsashen ginin tatsuniya.
Wannan ra'ayi na Yahaya da wasu (1992:7) ya ƙara
tabbatar da bayanan da suka gabata na cewa Hausawa su da kansu suka ƙirƙira
labarunsu ta hanyar amfani da fasaha da ƙwarewa da
harshe don tsara labarunsu da za su taimaka wajen cusa tarbiyya a cikin zuƙatan
ƙananan yara tare da koyar da su tsari da
dokokin da ke yi wa al'ummarsu jagorancin rayuwa. Idan muka yi nazarin
tatsuniya da idon basira za mu ga cewa babu wani ɓangare na
rayuwar Bahaushe da ba ta taɓo ba, wanda ya shafi horo da hani a
kan rayuwar yau da kullum.
Haka ma Gusau, (2013:5) ya bayyana cewa tun
asali Hausawa suna da daɗaɗɗun labaransu
da suka tashi da su tun kafin cu]anya da wasu al'ummu wanda tatsuniya na ɗaya cikin waɗannan
labarun. Waɗannan labarin
da jimawa suka ƙirƙirarsu ta
hanyar amfani da azancin da suke da shi a matsayinsu na al‟umma.
A cewar Harward (1910:vii) ya bayyana cewa
dukkanin yara suna sha'awar labarai. Duk da cewa akwai labarun da ake samu a
cikin kowace al'umma da ke kowace nahiya ko yanki. Akwai wanda sun shafi keɓantacciyar
al'umma wanda kowane yaro yana tashi da nau'in labarin ya shafi al'umma da muhallin
da yake rayuwa a cikinsa. Shi ma Herskovits, (1961:169) ya bayyana cewa a cikin
tatsuniyoyi da yanayin tsarin gabatar da su wata hanya ce ta gano abin da
al'umma ke aiwatarwa da yanayin imaninsu, da tsarin zamantakewarsu, wanda shi
zai bayar da haske kan yanayin al'adarsu.
Haka ma Koko (2009:5-6) ta ƙara
da cewa tatsuniya na daga cikin fannonin adabin baka da suka game duniya baki ɗaya. Domin
kuwa a kowane harshe da ke cikin faɗin duniyar nan ana samun tatsuniya,
kome ƙanƙantarsa, kome
ƙarancin mutanen da ke amfani da shi, kenan
tatsuniyar ta zama ruwan dare. Sa‟annan ta ƙara da cewa
jigogin tatsuniyoyi na harsuna daban-daban suna nuna cewa akwai dangantaka ta ƙut-da-ƙut
tsakanin harsunan tsawon shekaru da dama daga wani yanki zuwa wani. Wannan ya
sanya suke kamance ta fuskar salo da manufa da yanayin da ake amfani da shi.
Shi ma Usman (2018: 44) a nasa bayani ya bayyana cewa a kowace al'umma ta birni
da ƙauye suna da labarun gargajiya da suka gada
daga magabata. Waɗannan labarun
ko da ace suna raye har yanzu a cikin al'umma ko sun mutu, amma dai rubutaccen
adabin da ke rayuwa a yanzu, dole ya samu asali ne da daga tsohon adabin baka
na gargajiya na kowace al'umma.
A
cikin al'ummar Hausawa kuwa babu inda ba a san da zaman tatsuniya ba. Idan muka
duba yanayin ƙasar Hausa akwai ɓangaren
mutanen Arewacin Nijeriya da suka haɗa da yankin Bauchi da jigawa da
Zariya, Kano. Inda ake kiranta da suna tatsuniya Sai kuma Yammacin Arewacin Nijeriya
da suka haɗa da Katsina
da Sokoto da Kebbi da Zamfara har zuwa cikin garuruwan ƙasar Nijar
suna kiranta dad a suna Gatana, ta la'akari da ra'ayin Bergery (1934/51:37)
Wannan ya tabbatar da cewa dukkanin waɗannan yankuna suna riƙo
da tatsuniyar. Sai dai nisan da ke tsakanin waɗannan
garuruwa na ƙasar Hausa, yana sanya a samu ƴan
bambance-bambance na karin harshen mazauna wurare daban-daban ta fuskar sautuka
kalmomi da kuma musanyar kalmomi da suka dangance kowane yanki. Wannan ya sanya
wasu yankuna ake kiranta a matsayin "tatsuniya", inda a wasu yankuna
kuma "gatana" suke kiranta.
Har
wayau Alidou (2002) ta ci gaba da bayyana cewa a cikin adabin baka ana la'akari
wasu dokoki wajen bayar da labari da suka danganci jinsi da shekaru na masu
sauraren labari. Inda ta bayyana cewa tatsuniya mafi yawa mata ne, musamman tsoffafi
aka fi sani da aiwatar da ita a al'adance. A al'ummar Hausawa Dattijuwa (daga
cikin Kakanni) a cikin gida ko a maƙwabta ke da
alhakin tara yara tana ba su labarun tatsuniya, domin ita ce take da ilimin
zamantakewa, kuma ta ga jiya ta ga yau, ta iya tsara labari da adana shi, da
kuma sadar da shi ga masu saurare.
Koko
(2009: 16-17) ta bayyana cewa, bayan an tsara tatsuniya akan sami mutane da
suka shahara wajen bayar da labaru da hikayoyi da almara su riƙa
bayar da tatsuniya a cikin al'umma. Wasunsu ma sukan yi tafiya daga wannan guri
zuwa wani, musamman a tsakanin ƙauyuka, wanda
wasunsu ma na ɗaukan shi a
matsayin sana'a don samun wani ihsani. Ta bayyana ana samun waɗannan mutanen
tsakanin ƙabilu irin na Hausa da Tamne da Yaroba da Yao
da wasu ƙabilu masu yawa na Afirika. Hakama ta ƙara
da cewa ko bayan manya da aka sani da bayar da labarun akwai ƙananan
yara da suke bayar da labarun tsakanin junansu irin na kacici-kacici don wasa ƙwaƙwalwa.
Hakama samari ko matasa a wajen hirarsu suka haɗu ko bukukuwa
sukan ɗan taɓa labarun
tatsuniya.
Shi
kuwa Bichi (2014:1) ya tabbatar da cewa maza magidanta da matasa na daga cikin
masu bayar da tatsuniya a ƙauyuka. Mafi
yawa a lokutansu na aiki irin na gona da sauransu. Ya ƙara da cewa
daga cikin waɗanda suka ba shi
labaran tatsuniya akwai namiji ɗan shakara talatin da huɗu (34).
Wannan ya nuna cewa masu tsara tatsuniya mutane ne masu zurfin tunani da azanci
a cikin al'ummar Hausawa. Sai dai har wayau Bichi, (2014) ya ambato tsofaffin
mata da sababbin amare a matsayin waɗanda suka fi bayar da labarun
tatsuniya a cikin al'ummar Hausawa.
Shi
ma Gusau, (2013:8-18) ya kalli masu bayar da tatsuniya ta fuskar zamunna da
suka shuɗe, inda ya
bayyana cewa, kafin zuwan musulunci a wuraren ƙarni na sha ɗaya (11).
Manyan mutane maza da mata su neke aiwatar da tatsuniya, a bisa tunanin cewa
tatsuniya wata hanya ce ta koyar da matakan zaman rayuwa a rukunonin jama'a.
Wataƙila hakan ya sa aka bunƙasata don ta
dace da wasu sassa na ɓangarorin zamantakewar rayuwar. Bayan zuwan
musulunci, sai malamai suka ɗauki tatsuniya a matsayin ƙarya
da hukunci wanda ya yi ƙarya, ya aikata
zunubi. Wannan ya sanya ta ɗauki fasaha daban idan an gama gabatar
da ita, inda ake cewa, “ƙurungus kan ɓera, ba don
gizo ba da na yi ƙarya…..”. Sa'annan kuma aka barwa mata da ƙananan yara
jan ragamar tafiyar da tatsuniya.
Dukkannin
masana da suka yi rubuce-rubuce kan tatsuniya da suka haɗa da Bichi
(2014) da Koko (2009) da Yahaya (1996) da Umar (1980) da Gusau (2013), sun
tabbatar da ƙananan yara ne suka fi saurare tatsuniya,
domin kuwa ko yanayin labarin an tsara shi ne ta yadda zai dace da tunaninsu.
A
cewar Alidou (2002) masu sauraren tatsuniya sun haɗa da yara
maza da mata a gaban tsohuwa wadda itace za ta yi ta koyar da su darussa har
lokacin da za su girma, inda tarbiyyar yara maza za ta koma hannun iyayensu
maza, su riƙa yin labarunsu na maza, mata kuwa su ɗore da nasu
labarai na mata.
Masana
irin su Yahaya (1992:8) sun bayyana cewa, yawanci an fi yin tatsuniya da dare,
bayan an ƙare cin abincin dare, kafin yara su shiga
bacci. Ita ma Giwa (2012: 25) ta goyi bayan Yahaya (1992) a cikin kudin
bincikenta inda ta ƙara da cewa, kamar
yadda aka ruwaito a gabani, al'ummar Hausawa suna aiwatar da tatsuniya da rana,
wanda da rana ɗin nan na iya
yiwuwa da sanyin safiya ko kuma idan rana ta yi, idan har an tabbatar da cewa
za a aiwatar da dokar da al'ada ta tanada kafin gabatar da tatsuniya. Sa'annan
kuma da dare wanda a wannan lokacin aka fi aiwatar da ita.
Ana
aiwatar da tatsuniya da dare saboda dalilai na rage tsawon lokaci kafin a yi
bacci da hana yara yawon dare. Da kuma nishaɗantar da su
cikin hikima, tare da koyar da su nau'ukkan ilimi da ake so su tashi da shi tun
suna cikin ƙuruciya. Crowley da wasu (1954:3) sun ƙara
jaddada cewa a zamanin da ya gabata ana bayar da labarun tatsuniya da dare a
cikin babban gida na taro ko kuma idan aka taru a wata lalura ta abokai ko aka
kai ziyara a wani gida da rana . Da farko, ƙananan yara
za su fara gabatar da tatsuniyoyin, sai manya matasa su shigo ciki, wanda ana
cikin yi, yara za su yi bacci, matasan su ci gaba da baje-kolin tunaninsu,
wanda ya fi ƙarfin fahimtar ƙananan yaran.
Umar (1980: 11) ya bayyana cewa ita dai
tatsuniya galibi an fi aiwatar da ita da dare, idan kuwa har za a yi ta da
rana, dole ne a gabatar da wata al'ada ta ɗaure gizo,
maganin yin makuwa. Shi kuwa Ahmad (1997:8) ya nuna cewa ana aiwatar da
tatsuniya da yamma a wasu yankunan ƙasar Hausa
bayan an gama hadar-hadar yini, inda a wasu yankuna suna aiwatar da ita da
dare, bayan an ci abinci kafin a yi bacci.
Bichi
(2014:1-2)ya bayyana muna cewa a al'ummar Hausawa waɗanda suke
sauraron tatsuniya su ne ƙananan yara.
Zaman yana kasancewa da rana ko da dare, kuma mafi yawa a gidajen kakanni da maƙwabta
idan akwai wata dattijuwa a nan. Su suke nishaɗantar da
yaran da labarai a ɗaya ɓangaren suna ƙura
zare da saƙa da ɓarar gyaɗa da
sauransu. Idan akwai sabuwar amarya a gida, yaran suukan taru a wajenta da dare
don su yi wasa, sa‟annan su saurari labaru.
Su ma Yahaya da wasu (1992:7) su ma sun
bayyana labarun tatsuniya kamar yadda al'ada ta bayyana, hirar yara ce. Ashe
kenan abar yara ce, sai dai mata tsofaffi da amare sukan yi ruwa da tsaki wajen
gudanar da ita, wajen yi wa yaran ita, inda su kuma za su riƙa
sauraro. Wannan haka yake, domin kuwa Gusau (2013:11), ya goyi bayan wannan
zance, inda ya tabbatar har wayau yara ne jagororin tafiya na tatsuniya,
tsofaffi da amare suna yada musu hanya ne kawai.
Daga
cikin masana da suka yi ayyuka kan tatsuniya sun bayyana irin muhimmancin da
take da shi da suka haɗa da Umar, (1980:12) inda ya bayyana cewa
tatsuniya tana da matuƙar amfani wajen gina
kyawawan ɗabi‟u tare da
rusa munana, haka zalika tana taimakawa wajen koyar da yara harshensu na uwa,
tana ɗauke kyawawan
al'adunmu tare da bai wa yara nishaɗi.
Shi ma Yahaya, (1974:1) ya ƙara
da cewa duk da cewa gaskiya ne labarun tatsuniya ba su taɓa aukuwa ba,
amma idan aka yi nazarinsu abin da ke ƙunshe
cikinsu, za mu ga cewa suna nuni ga halayen zaman duniya ne. Sa‟annan tana da
kama da wasan kwaikwayo inda ake amfani da mutane da dabbobi da tsuntsaye da ma
wasu ƙirƙirarrun
halittu irin su gizo wajen nuna halayen kirki da kuma sakayya ga wanda ya
munana daga ƙarshe. A cikinta ne ake cin karo da kyawawan
al'adun Bahaushe irin sana'o'i da kunya da zumunta da tarbiyya da sauransu. A
wata faɗa ta
Yahaya,(1992:8) ya }ara fito muna da wani amfani da tatsuniya take dashi na
katange yara a wuri ɗaya a hana su yawace-yawacen banza, sa'annan
suna taya sabuwar amarya hira ta manta da kewar da take da ita na barin gidansu
zuwa sabon wuri, su ma su kasance cikin nishaɗi. Sa'annan
ga irin darussa daban-daban da suke ƙaruwa da su
ta hanyar sauraren labarun na tatsuniya. Ita ma Koko, (2009:31-36), ta bayyana
cewa muhimmancin tatsuniya ya fi gaban a bayyana shi duka sai dai a tsakura,
domin ilmantar da take da koyar da zamantakewa da koyar da tarihin abubuwa,
sadar da rayuwar al'umma daga wani zamani zuwa wani da kasancewarta ma'adanin
al'adu, da koyar da matakan tsaro da madubin rayuwa na sanin sirrin al'umma da
sauransu.
Rabi'u,
(2018) ya gudanar da nazari mai taken habarcen tatsuniya a, nazarin ya bayyana
cewa, Al’ummar Hausawa suna da nau’o’in habarcen tatsuniyoyi da dama, waɗanda suka haɗa da labari
da tarihih da hikaya da almara da sauransu. Nazarin ya yi amfani da ra’in
kwatantan adabi wanda ake amfani da shi wajen kwatanta adabin al’ummomi waɗanda ake
ganin suna da wata dangantaka ko kuma wasu kamanni a wasu ɓangarori na
adabi ko al’adu domin a tabbatar da alaƙarsu. An
kwatanta tatsuniyoyin al’ummomin Hausa a ɓangaren arewacin
Nijeriya da kuma Jumhuriyar Nijer. Bincike ya kwatanta yanayin tatsuniyoyin da
jigo da salo da kuma adon harshen ta hanya kwatanci. Nazarin ya gano abubuwa
masu kama da juna da kuma waɗanda suka bambanta da juna a duka
tatsuniyoyin al’ummomin biyu. Misali kamar jigo a tsarin sarautar gargajiya,
musamman dangantakar sarki da talaka inda suka bambanta.
Shi
kuwa ahmad, (2017) ya yi nazari ne kan kwatancin taurarin waniƙiƙi
a tatsuniyoyin Hausa da fulatanci, nazarin ya fayyaci irin abubuwan da suke da
alaƙa ta kusa cikin tatsuniyoyin waɗannan
al'ummomi biyu, wato Hausa da fulani, tare da ƙawata nazarin
da misalai dgga kowanne ɓangare.
2.5
NAƊEWA
Ko ba a ce komai ba an ga yadda babi na biyu
ya bibiyi ayyukan magabata waɗanda su ka yi kusanci da wannan
binciken kamar yadda aka labarta a shinfiɗar babin. Haƙiƙa
wannan babin ya waiwayi ayyuka daban-daban da aka yi akan Bahaushe da Hausawa,
a inda aka kutsa cikin littattafai da aka wallafa masu magana kan Hausa da
Hausawa har ma da Harshensu da ƙasarsu, haka
ma kundaye da muƙalu da mujallu da sauran fannonin ilimi. Idan
an koma kan falsafa ma haka abin yake domin kuwa an bibiyi ayyuka da dama da
aka yi kan falsafar Bahaushe, wanda shi ma aka bincika littattafai da muƙalu
da mujallu. A ɓangaren
wasanni da tatsuniyoyi ma haka abin ya kasance domin manazarta da dama sun yi
nazarce-nazarce haɗe da wallafa littattafai game da wasannin
gargajiya, wasu kuma sun gudanar da nazarin ne a kundayensu na kammala karatu,
haka ma cikin mujallu duk dai kowa da inda ya kalla a ɓangaren.
A ƙarshe kuma an
tabbatar da cewa dukkannin ayyukan da aka bibiya babu wanda zai hana gudanar da
wannan binciken domin kuwa kowa da inda ya karkata akalar binciken nasa.
BABI NA UKU
HANYOYIN
TATTARO BAYANAI
3.1 SHINFIƊA
Kamar yadda sunan babin ya nuna wannan ɓangare ne na
musamman da ake bayyana irin hanyoyin da aka da aka yi amfani da su wajan samo
dukkanin bayanan da aka kawo a cikin bincike a inda wannan binciken ya bibiya
hanyoyi da dama yayin gudanar da wannan binciken da aka bibiye su domin tattaro
duk wani Sbayani da aka gabatar ko za a gabatar a cikin binciken tun daga
farkonsa har zuwa ƙarshensa, don haka a
wannan babin za a bayyanawa yadda aka yi ƙoƙarin
bibiyar muhimman hanyoyi da za su taimaka wajan cimma nasaran fito da abinda
ake ƙulafacin ganowa, a ƙarshen babin
kuwa a nannaɗe ko tattare
duk wani abin da aka tattauna a cikinsa domin ƙara fito da
abin fili yadda ya kamata.
3.2 HANYOYIN
TATTARO BAYANAI
Binciken sanin rayuwar al’umma yana gudana ta
hanyoyi daban-daban, wannan ya sanya Osuala (2013) ya ce "dole ne
ma’abocin sanin rayuwar al’umma ya tattaro ingantattun bayanai da aka
adana". Ana kuma so bayanan su dace da aukuwar al’amuran da ake bukatar
ganowa. Ana bukatar mai gudanar da irin wannan bincike ya san gwarazan mutane
da suka wanzu a wannan zamani da yake ƙoƙarin
tattaro bayanai a kansa. Idan ya yi haka, zai sanya ya sami sauƙin
ƙulla bayani a lokacin da yake ƙwanƙwance
bayanai da ya tattaro. Masanin ya ce, yana da kyau ma’abucin sanin rayuwar al’umma ya lura da yanayin yadda
al’amura suke, domin lurar za ta sanya ya san tambayoyin da ya kamata ya yi
idan ya fita fagen bincike. Ana so mai gudanar da irin wannan bincike ya san
yadda zai ɓullo wa
al’amura daban-daban da suka shafi al’ummar da yake yin nazari a kanta.
(Abubakar, 2019)
Wannan binciken ya tattaro bayanai ta hanya biyu;
Babbar hanya da kuma sauran hanyoyi. Lura da yanayin littafin tatsuniyoyi da
kuma wasanni su ne ginshiƙin hanyar da
wannan bincike ya dogara a kansu ya sa tun a ranar 30/3/2022 wannan bincike ya
fara tattaro bayanai a kan tunanin Bahaushe game da su. Binciken ya kai ziyara
wasu sassan jami'o' da nufin ya samo bayanai game da yanayin tatsuniyoyi da
wasannin Bahaushe da tunane-tunanen Bahaushen a kan wasannin da kuma
tatsuniyoyin da suke ƙirƙira
a zamantakewar rayuwarsu . Binciken ya nemi sanin tarihin wasu al’amura game da faruwar tatsuniyoyi da wasanni a ƙasar
Hausa ta hanyar tattaunawa da mutane daban-daban. Haka kuma binciken ya zagaya
wurare daban-daban domin ya yi hira da mutane, kamar yadda ya ƙudurta
a ransa yana so ya fahimci falsafar Bahaushe game da tatsuniyoyi da wasanni.
Bincike kuma ya nemi izini daga Sashen
Harsunan najeriya na Jami’ar Sule lamiɗo da ke kafin Hausa.
Yayin da bincike ya samu takardar gabatarwa zuwa wurare da ya ziyarta daga
sashe, mai bincike ya tuntuɓi wasu mutane mazauna garuruwan da ya
ziyarta. Wasu garuruwan kuma kai tsaye mai binciken ya tafi, ya gana da masu
ruwa da tsaki a ɓangaren da
sauran wurare da bincike ya ziyarta.
3.3 BABBAR
HANYAR TATTARA BAYANAI
Babbar hanyar da aka yi amfani da ita wajan
tattaro wannan bayanai ita ce nazartar littafin tatsuniyoyi da wasanni.
Litttafin tatsuniyoyi da wasanni, littafi ne da ya yi ficea a duka zagiyar
Arewacin ƙasar Hausa wannan bincike ya nazarci wannan
tun daga na ɗaya zuwa na
shida a tsakanin ranar 03/12/2022 zuwa 11/01/2023, domin kuwa an tattaaro duka
littattafan daga na ɗaya zuwa na shida wadda ke ɗauke da
wasanni guda 31 , a inda aka fara nazartar littafi na farko wadda yake ɗauke da
darrusa guda uku, kuwa wasa ne na karya harshe wadda malami ke koyawa yara
yadda ake kakkarya harshe cikin hikima, darasi na ukun kuwa shi ma tatsuniya ce
aka kawo ta gizo da budurwar danƙo duka waɗannan wasanni
an kawo su ne cikin shafuka daban-daban. A haka dai aka cigaba da nazartar
littattafan ɗaya bayan ɗaya har zuwa
na shida, wato na ƙarshe.
Hikimar Bahaushe shi ne dalilin da ya sanya
bincike ya tsayar da ƙafa a waɗannan sashe.
Waɗannan
tatsuniyoyi da wasanni da aka nazarta samfuri ne wajen nazarin tunanin
Bahaushe. Wannan ya sa bincike ya tsaya ya lura da irin hikimomi da Bahaushe ya
riƙa sanya su cikin wasanninsu da kuma
tatsuniyoyinsu, waɗannan tatsuniyoyi da wasanni suna taimakawa
matuƙa wajen adana al’adu da suka ƙunshi
zamantakewar Hausawa, inda duk suka zama abu guda wajan isar da saƙonninsu
a wannan lokacin, sai dai ‘yan
bambance-bambance kurum. Bincike ya lura akwai hikimomi a cikin wasannin
Hausawan da tatsuniyoyinsu.
Wannan nazari na waɗannan
littattafai, ya ba binciken damar gano wasu bayanai game hikimomin Bahaushen,
kuma binciken ya ga wasu wurare daban-daban da Bahaushen ya riƙa
sanya tunaninsa cikin wasannin da kuma tatsuniyoyin, musamman wajen zaɓar taurarin
da yanayin gudanarwa da tsare-tsarensu da sauransu. Bincike ya riƙa
lura da yanayin kowacce hikima da aka sa, ya kuma lura da tsarin gininsu, da
yadda suke da tasiri a rayuwa. Bincike ya lura da amfanin sanya waɗannan
hikimomi cikin rassan na adabi musamman waɗannan ɓangarori.
3.3 ƘARAMAR
HANYAR TATTARO BAYANAI
Daga
cikin ƙana nan hanyoyin da aka bi wajan tattaro wannan
bayanai akwai:
3.3.1 TATTAUNAWA
Wannan Bincike ya gana da manya masana ilmi a
fannin adabi. Haka cikin rukunin masanan da aka tttauna da su akwai manyan
malamai masu digirin ƙoli da kuma shehunnan
malamai; da ma sauran malmai maza da mata. Wasu daga cikin mutanen da aka yi
hira da su ɗalibai ne
masu neman digirin farko a sashen harsunan najeriya da ke da ke jami'ar Sule
Lamiɗo ta K/Hausa.
Wasu daga cikin ɗaliban sun
sada wannan bincike da mutane daban-daban, musamman tsofaffi, kuma sun yi wa bincike
jagora zuwa wurin waɗannan mutane. Wasu malamai na ciki da wajen
Jami’ar Jami'ar Sule Lamiɗo ta Kafin Hausa sun yi ƙoƙarin
bada gudunmawa a wajen binciken, yayin da aka yi magana da su baka-da-baka a
kan abin da bincike yake bukata. Waɗannan malamai sun bayar da shawarwari
kuma sun sanar da mai bincike wasu littafai da ya kamata ya tuntuɓa domin a kai
gaci. Binciken ya kai ga wasu mutane saboda sanayyar da take tsakaninsu da mai
bincike, kuma bincike ya yi iyakar ƙoƙarin
adana sunan mutane da aka gana da su da wurin da aka yi hira da su, da kuma
matsayin kusan duk wanda aka tattauna da shi. Rataye yana ɗauke da
jadawalin sunan akasarin mutanen da aka yi hira da su da ranar da aka yi hirar
da kuma wurin da hirar ta gudana. Bincike ya sami adadin shekarun wasu daga
cikin mutanen da aka yi hira da su, wasu kuma ba a samu ba saboda dalilai da
suka sha ƙarfin bincike.
3.3.2 ZIYARAR ƊAKUNAN
KARATU
Ɗakin karatu
yana cikin muhimmin wuri da wannan bincike ya taro wasu bayanai daga cikinsa,
wato, mai bincike ya shiga ɗakin karatu a Jami’ar Sule Lamiɗo ta Kafin
Hausa da Jami’ar Bayero ta Kano da kuma kwalejin ilimi ta garin Gumel. Binciken
ya samo littafai da kundayen digiri da maƙalu a waɗannan ɗakunan
karatu. Yayin da binciken ya sami kundaye da littafai da maƙalu
a waɗannan ɗakunan
karatu, ya nazarce su, kuma ya amfana da su. ɗakin karatun
ya ba da gudunmawa sosai ga wannnan bincike, musamman a fagen adabin baka ɓangaren
wasanni da tasuniyoyi da kuma falsafar da ma shi kansa Bahaushen da kuma abinda
ya shafi ƙasarsa da harshensa da sauransu.
Wata hanyar da ta ƙara taimakawa
wannan bincike ita ce Intanet, wannan kafa ta taimaka wa binciken ya samu
bayanai ko ƙarin haske a fagagen da suka shafi falsafa da
wasannin gargajiya da tatsuniya da sauransu. Binciken ya karɓi saƙuna
daban-daban ta intanet (email) da dandalin sada zumunta, musamman wazof daga
mutane na kusa da nesa. Binciken ya yi hira da mutane ta waɗannan kafafe,
inda yawanci suka aiko da gudunmawarsu a rubuce. An yi musayar saƙonni
tsakanin mutane da mai bincike ta wannan kafa, kuma binciken ya adana wasu saƙonnin
a waya domin tabbatarwa masu nazari bayanai game da inda aka bincika da kuma waɗanda aka
bincika . tare da taƙataccen bayani da zai
taimakawa wannan binciken.
3.4 NAƊEWA
Wannan babin dai ya bayyana yadda aka gudanar
da aikin ne, ta hanyar kawo wurare da abubuwan da aka bibya ko aka tattaro da
suka taimaka wajen tsayuwar wannan binciken, waɗanda suka haɗa manyan
hanyoyi da kuma ƙanana , manyan hanyoyin sun ƙunshi
nazartar littafin da aka yi tsokaci akansa gabaki ɗaya, sa'annan
kuma an bibiyi ɗakunan karatu
a mabambanta makarantun ilimi na cikin gida, bugu da ƙarin ƙoƙarin
nemo ƙarshen zaren ikin ya haddasa tattaunawa da
jama'a iri-iri , kama daga malamai mazauna makarantar da ake gudanar da aikin ƙarƙashinta,
da kuma sauran manyan malamai fitattu a wuurare daban-daban, al'amarin bai
tsaya iya nan ba, domin kuwa tattaunawar ta kasance harda wasu daga cikin ƴan
uwa abokan karatu, dama makusanta abokai da dai sauransu. ba ma iya nan abin ya
tsaya ba domin kuwa an binciko bayanai da dama ta hanyar kafar sadarwa ta
internet, wasu kai tsaye aka riƙa binciko su,
wasu kuwa an same su ne ta hanyar neman shawara daga gurin wasu inda suka bada
bayanan ta kafar sadarwar wazof, da sauransu.waɗannan duk su
ne ƙananan hayoyin da aka tattaro bayanan.
BABI NA HUƊU
FALSAFAR
BAHAUSHE CIKIN LITTAFIN TATSUNIYOYI DA WASANNI
4.1 SHINFIƊA
Babi na huɗu a kowanne bincike shi ne
ƙashin
bayan aikin, ma'ana a shi ne gundarin aikin yake, kasancewar aikin ya shafi
binciko falsafar Bahaushe ne cikin tatsuniyoyi da wasanni, don haka wannan
babin zai yi bayani dalla-dalla tare da fiddo da falsafar da ke cikin wasannin
da tatsuniyoyin da farfajiyar binciken ta iyakance ɗaya
bayan ɗaya , da suka haɗa da
tatsuniyar gizo da ɓaure, ɗan
sarki ya zama miciji, tatsuniyar na-goma, da kuma wasannin ka-cici-ka-cici,
wasannin ɓata da sauransu, haka kuma a babin ne za a bayyana yadda fannin falsafa
yake da mukusanciyar alaƙa
da da fannin adabi ta ɓangarori da dama da suka
jiɓancesu, kamar ma'anarsu, ire-irensu, bunƙasarsu, da ma sauran ɓangarori
duk babin zai fayyace irin dangantakarsu ta waɗannan
fuskoki, a ƙarshe
kuma a tattauna duk wasu muhimman abubuwa da suka zo a cikin babin.
4.2 DANGANTAKAR FALSAFA DA ADABIN BAKA
Wannan ɓangare
zai dubi dangantakar dake tsakanin falsafa da adabin baka ne na Hausa, saboda
haka kafin a je ga dangantakar ta su kai tsaye ya dace a yi waiwaye baya a dubi
irin wanzuwarta tare da ma'anar falsafar da adabin da kuma rabe-rabensu, daga
nan ne za a ga irin dangantakar da ke tsakanin adabin da kuma falsafar.
Kamar yadda bayanai suka gabata dangane da
ma'anar falsafa, kai tsaye ana iya taƙaicewa
a ce :
" Ita falsafa wani ƙasaitaccen tunani ce mai koyar da hikima da kujiba -kujibar rayuwa",
ko mu ce amfani hikima da kuma iya sarrafa mu'amala." (Gusau 2022).
Ta fuskar bunƙasa kuwa muna iya cewa : falsafa ta samo asali ne tun daga zaman
farko na al'ummar duniya haka ta yi ta samun cigaba har izuwa yau, kuma duk
hikimomin da ake isarwa a falsafa duk da harshe ake isar da shi, abubuwa ne da
suka shafi rayuwa kai tsaye ba tare da wahalarwa ba , haka kuma idan muka kalli
irin rabe-raben falsafa kamar yadda masana suka bayyana ta kasu kashi uku,
wadda ya haɗa da, falsafar harshe, falsafar kintace/kwatance,falsafar rayuwa.
(Gusau, 2022).
A ɓangaren
adabi kuwa shi dai adabi kamar yadda masana suka bayyana wani sarrafaffen
harshe ne mai ɗauke da fasaha ta musamman mai ayyana basirori da hikimomin
al'ummar Hausawa. Sannan kuma kai tsaye ana iya kallon adabi ta fuskoki guda
uku, wato Waƙa, zube
da kuma wasan kwaikwayo.
To a wannan gaɓar
farko abinda za mu fara dubawa shi ne dangantakar falsafa da adabin baka ta
fuskar ma'anoninsu. da farko ita falsafar kanta tunani ce game da abin da ya
shafi rayuwa yayinda adabi kuma yake bayyana mana hotunan rayuwar al'ummar masu
ɗauke da hikimominsu . to anan ita falsafa dai ita ce
tunane-tunanen da suke sanya wa cikin al'amuransu, waɗannan
al'amuran da suke aiwatarwa masu ɗauke da
tunanin kuma su ne adabin.
Don haka wannan wata dangantaka ce mai ƙarfi game da falsafa da adabi.
DANGANTAKAR FALSAFA DA ADABI TA FUSKAR
RABE-RABENSU:
v Falsafa
na amfani da kwatance haka kuma ana amfani da kwatance a fannin adabi.
v Falsafa
na amfani da harshe a wani muhimmin kaso daga cikin kashe-kashenta, harshe shi
ne abin da ya bambanta mutum da dabbobi, kuma shi harshe yana mazaunin linzami
na tunani a hannun ɗan Adam, ta hanyar
linzamin nasa ne zai iya karkata tunaninsa duk yadda yake so.
v haka
kuma abin ya ke ta fannin adabi , domin shi ma adabi ƙashin bayansa shi ne harshe. domin kuwa mutum kan yi amfani da
harshe a matsayin kyautatwa ko yabo ko zuga, sai kaga wadda ya zuga yana tsuma
har ya tuɓe rigarsa ya bashi ko matarsa ko duk wani abu da ya mallaka. Kuma
mutum ne kawai ke gwada fasaharsa da nishaɗi
ta hanyar harshe misali irin, karin magana, waƙa, Azanci, habaici, zambo, sakaya zance, taƙaitaa zance da sauransu.
v Adabi
na bincike ko tattaunawa game da rayuwa da zamantakewar al'umma, haka kuma
falsafar rayuwa na ɗaya daga cikin jiga-jigan
falsafa.
v Falsafa kan nuna tsarin mulki da waɗanda
za a mulka haka shima adabi kan fito mana da irin tsare-tsaren da ake tafiyar
da mulki a rayuwa.
DANGANTAKAR
FALSAFA DA ADABI TA FUSKAR ILIMI
* Adabi a harshen Hausa ya samu shigar zamani
a cikinsa kuma ya kai matuƙa
wajen ɓaci har al'umma na yin alawadarai da irin abin da yake faruwa
musamman in mun dubi wasannin kwaikwayo na Hausa na zamanin yau.
haka abin yake in mun dubi falsafa domin ita
ma ta samu canje-canje na musayar tunani, inda aka sami irin su (Kalmus) a
falsafance suna ganin addinin mutane da al'adunsu masu kyau, sa'annan kuma ana
faɗin ra'ayin falsafar ga ɗalibai da
baka ba a rubuce ba.
DANGANTAKAR
FALSAFA DA ADABI TA FUSKAR WANZUWA DA BUNƘASARSU:
v Adabi
ya bunƙasa ne
kamar yadda tarihi ya nuna bunkasar falsafa ta hanyar samun wasu gwaraza da
suka shafe lokutansu da yin tunani don samar da wani abu mai amfani.
v Adabi
Adabi ya biyo wasu matakai kafin fara rubuta shi, har ya zama rubutacce haka
sha'anin yake a bunkasar falsafa.
v Falsafa
ta bunƙasa ne
har ta kai ga an samu falsafar musulunci, kamar yadda Adabi ya samu bunƙasa zuwa adabin bayan zuwan musulunci, da
kuma na gargajiya shi ne adabin da Hausawa suke tun kaka da kakanni, kuma ana
kiransu da adabin baka, domin asalinsa ba a zube yake ba kuma shi ne adabin da
ya ƙunshi
makaɗa da kayan kiɗansu, da
tatsuniyoyi da labarai da almara da sauransu.
DANGANTAKAR
FALSAFA DA ADABI TA FUSKAR FARUWARSU:
v Shi
adabi babu wani takamaimai lokaci da za a ce ga ranar da aka fara shi, haka ita
ma falsafa babu wanda zai ce ga ranar da ɗan adam
ya fara tunani akan kaza ba.
v Adabin
Hausa ya fara da adabin baka kamar yadda falsafa ta samo asali daga tunani da
ka.
DANGANTAKAR
ADABI DA FALSAFA TA FUSKAR BA DA GUDUMMAWA GA RAYUWA:
v
Keɓe
tarihin Bahaushe adabi da falsafa za su taimaka wajen taskance tarihi domin
sanin jiya da yau, da kuma yadda za a fuskanci gobe.
v Adabi
da falsafa suna tabbatar tare da nuna martabar Bahaushe, kuma suna cusa
alfahari da kai da kuma sanin ciwon kai, da kishin zuci, da kuma kishin ƙasa, da girmama abubuwan da aka gada tun daga
kakanni.
v Falsafa
da adabi suna bunƙasa ilimi
da wayar da kai.
v Sa'annan
falsafa da adabi suna koya dabarun zaman duniya.
v Adabi
da falsafa na wasa ƙwaƙwalwa, ta bayyana abubuwan fasaha da lugga da
sauransu.
Duk waɗannan
abubuwa ne da suka haɗu wajen dangantakar
falsafa da adabi.
Wani babban abin sha'awa shi ne dukkanin
masana falsafa a ƙarnukan
da suka gabata za ka same su masana ne ƙwararru
a fagen ilimn manɗiƙ, dan
haka sai dangantakarsu da masana adabi ta yi ƙarfi, kuma da wuya ka sami masanin adabi da yake da jahilcin
falsafa, domin ita ce matakin da ake takawa wajen sarƙafa tunani har a furta abinda zai zama adabi ga al'umma.
Idan muka ɗauki
ilimin (manɗik) shi ilimi ne da ke bin diddigin sirrikan harsuna, da kuma gano
ma'ana mai zurfi cikin maganganun jama'a har ma da masu adabin. Masan adabi
suna zurfafa tunani wajen yin hange dan su kwatanta abubuwa domin kyautata
adabi, kamar yadda masana falsafa kan zurfafa tunani don gano wata matsala,
kuma mafi yawa matsalolin sun yi tarayya da malaman adabi, wajen yin wani abu
da zai taimakawa rayuwar al'umma.
Kuma mafi yawan taƙaitattun jawaban da masana falsafa kan yi su na da dangantaka da
wani abu mai kama da karin magana da salon magana ko kuma ɗan
waƙa mai ƙunshe da wani saƙo mai muhimmanci misalima maganganun su (BROTAJOROS) da sauransu.
Misali:
= Mutum magwaji ne na duk wani abu.
= Abinda ya yi kyau na wajen ka to muni na ga
wani.da suransu.
Haka kuma
idan muka kalli ɓangaren adabin gargajiyar Hausawa akwai jigo mai nauyi ta fuskar
magungunan gargajiya, wanda in mun waiga baya masana falsafa su ne likitoci da
binciken cuta da maganinta misali: Irin su IBN SINA da IBN NAFIS da can ma baya
irin su "ALATO" in da ya bada gagarumar gudunmawa wajen fannin lafiya
da riga-kafi wanda Hausawa kan ce " ya fi magani" a wani littafi mai
suna Tafhatul- Arus shafi na 129, ya kamo irin gudunmawar "Plato" ta
fuskar wasu abubuwa biyar da su kan iya kawo matsala akan lafiya:
1. Tsoron talauci
2. Rabuwa da masoya
3. Tunanin abubuwa na ɓacin rai
4.Ƙin karɓar
nasiha
5. Biyan da damuwa game da dariyar jahili.
Don haka in muka dubi adabi ta fuskar magani to akwai falsafa
cikin harkokin lafiya da magani,
Akwai dangantaka ta amfani da harshe ne ake koyar da yara tun suna
ƙanana,
domin su, bunƙasa tunaninsu
da kyau, in mun dubi misalan kacici-kacici da maganganun karya harshe, da wasa ƙwaƙwalwa,
ta yadda za su rike sunayen abubuwa da siffofinsu. dukkannin waɗannan
hanyoyin suna da dangantaka da falsafa.
Kuma akwai dangantaka ta fuskar manufar adabin Hausa, ya sa a gaba
da kuma masana falsafa suka sanya a gaba idn muka koma baya irin ƙoarin da platon ya yi wajen sabunta tunanin
al'umma ta fuskar zamantakewarsu. Haka abin yake a adabi Gusau (2002), SALIHU
JAN KIƊI a shafi
na 68 a sakin layi na ƙarshe
malam ya ce" Makadi mai falsafa wato masanin tsari kan hanyoyin zaman
jama'a ya kan yi ƙoƙari wajen bayyana halayyar wanda yake yi wa
waƙa da kuma
tsarin da ya ɗauka yake tafiyar da rayuwarsa a kansa. Irin wannan makaɗi
za a tarar da shi mai hangen nesa ne mai gargaɗi,
mai faɗakarwa mai wayewa, kuma mai ilimantarwa kuma kullum yake ƙoarin ya ga al'ummar da ya ke a cikinta ta
zama tagari".
Anan ana ganin cewa akwai dangantaka mai ƙarfi tsakanin falsafa da masanin adabi ko mai aiwatar da adabi
makaranci mai karin magana" Mai fashin baƙi , da sauransu. A wani ɓangare za
ka samu adabin Hausa na taɓo
harkokin ilimi mai zurfi na hisabi wanda asalinsa daga falsafa yake , in mun
dubi mawaƙi na
rubutacciyar waƙa kan yi
amfani da ramzi wajen rubuta shekarar waƙarsu
ko kwanan watan da suka yi waƙa.
4.3 TUNANIN BAHAUSHE CIKIN TATSUNIYOYI DA WASANNI:
Kowace al'umma tana da nata tunanin na rayuwa, sa'annan kuma duk
wani tunani da za ta yi dole ya dace da tata rayuwar. shi yasa Hausawa kan ce “ƙafar wani ba ta yi wa wani tafiya”. Sai dai
duk da bambance-bambancen tunani da ake samu tsakanin al‟ummomi
daban-daban akwai wasu keɓantattun
abubuwa da suka zama gama-gari ne, ana samunsu a cikin kowace al'umma.
Haƙiƙa Bahaushe na sanya tunaninsa da falsafarsa
cikin abinda ya shafi adabinsa, wanda ya jiɓanci
rayuwarsa da zamantakewarsa ta yau da kullum, don haka ana iya kallon wannan
falsafar cikin rabe-raben falsafa da falsafar rayuwa kasancewar al'amuran da
yake gina tatsuniyar da kuma wasan duka kan gyaran tarbiyya ne da fatan samun
kyakkyawar mu'amala.
Irin wannan falsafa ta ƙunshi ciki da wajen waɗannan ɓangarori,
domin kuwa abubuwa da dama ke wakana a wasu keɓantattun
wurare da aka tsara bisa ga tunanin Bahaushe wanda ba haka lamarin yake a cikin
rayuwarmu ta yau da kullum ba, domin kuwa magabata sun ɓata
lokaci wajen yin tunani da yin ƙirƙirar abubuwan da suke son tsarawa a cikin
al'ummarsu wanda zai dace da tsarin addininsu da al'adarsu da tunanin
al'ummarsu da yanayin wurin zamansu da duk wani abu da ya jiɓinci
rayuwarsu ta yau da kullum.
Akwai abubuwa da dama da ake samu a cikin
tatsuniyoyin kowace al'umma da kuma wasanninsu, sai ɗan
bambance-bambancen da ba a rasa ba, wanda ya shafi yadda kowace al'umma ke
gudanar da rayuwarta.
A wajen al'ummar Hausawa, suna da nasu keɓantaccen
tunani da suka tanadarwa tatsuniyoyi da wasanni a matsayin bayyana yanda
al'amuranta ke wakana, ta hanyar amfani da wasu hikimomi da ake sanya wa wadda
suka dace da su, kama daga taurarin da ke rayuwa a cikinta, da irin bidirin da
ake aiwatarwa ba tare da takura ko rashin walawa ba. irin waɗannan
wurare da ake riskar hikimar Bahaushe sun haɗa
da muhallin da ake aiwatarwa, abubuwan da ake tsarawa, da kuma taurarin
cikinsu.
4.3.1 MUHALLI
Ba kowanne al'amari ne yake gaskiya ba a al'amuran tatsuniya da
kuma wasanni kamar yadda yake zahiri bisa sararin duniyar da muke rayuwa. Ba a
iya cewa ga wani wuri takamaimai da wani al'amari daga cikin al'amurran
tatsuniya ke gudana. To idan hakan ne, haƙiƙa an yi haka ne da ta hanyar amfani da ɗumbin
tunani, domin kuwa a karon farko idan aka fara kallon duniyar da aka jingina
tatsuniyar da ita, duniya ce da ta samu wahalawa ta yi yabanya take cin karenta
ba babbaka, ba tare da tsangwama ba, haka kuma babu ita a zahiri sai dai mutum
ya riƙa ƙiyasta ta a birnin zuciyarsa tare da tunani
da imani ko kuma yarda. Wasu duniyoyin da ake gina tatsuniya a cikinsu a saman
iska suke rayuwa, ko kuma a cikin tunani da imani wanda suna rayuwa a cikin
duniyarmu ta yau da kullum, suna cin kasuwarsu daidai gwargwado. Kuma
tatsuniyar ta yi tsawon lokaci na wani zango ba tare da tsangwama ba, kuma ta
samu karɓuwa a zukatan al'umma manya da ƙanana.
Haƙiƙa wannan ɓangaren
na ɗauke da muhimmin tunani, wajen zaɓar
muhallin gina tatsuniyar na musamman wanda babu shi a duniyarmu ta gaskiya, sai
dai keɓantacciyar duniyar ta ƙunshi
wurare mabambanta kama daga waɗanda muke
dasu a cikin duniyar mu da suka haɗa da
kogon itace, da kogon dutse, da ƙunƙuwa ko suri, da ruƙuƙin daji,
da sararin samaniya, da gona, da fadar sarki, da cikin ruwa da faɗo,
gidan azurfa ko zinare da sauransu. Haka ma da wasu da muke riya akwaisu a
tunanin tunaninmu, amma ba mu ganinsu, waɗanda da
yawansu ƙirƙarsu aka yi, aka cusa su a cikin tunanin mai
sauraro don ya riƙa riyawa
a ransa akwaisu, alhali kuwa babu su a cikin rayuwarmu ta yau da kullum, kamar
kasuwar sama, da birnin aljannu, da wani gari da ake yawan ambatowa (ba a
bayyana inda yake), da duk wasu wurare na musamman (Koko 2009:4).
Idan aka yi nazarin abin da masanan suka
bayyana da kuma amfani da ilimin da muke da shi, na mun wayi gari cikin
al'ummarmu mun tarar da cewa ana aiwatar da wannan tatsuniyar. Mun san da cewa
duk waɗannan abubuwa da aka ambata a sama ana riya cewa akwai su ko kuma
suna wakana ne a wata duniya ta daban, a inda mu kuma muna karanta labarin
wannan duniya ne kai tsaye, tare da imanin cewa ko shakka babu hakan abin ke
faruwa. Sai daga baya idan hankali ya shiga ake rarrabewa tsakanin aya da
tsakuwa, wato tsakanin zahirin gaskiya da kuma tatsuniya.wannan wata babbar
hikima ce ta bahaushe.
4.3.2 AL'AMURAN RAYUWA
Haka kuwa akwai abubuwa da dama da ke a cikin
tatsuniya. Kamar yadda aka sani ne, a cikin rayuwarmu ta yau da kullum akwai
ayyuka da aka al'adanta aiwatar da su, waɗanda su
ne rayuwar. Duk wanda yake kan wannan turbar a cikin al'umma ana yi masa kallon
yana kwantanta rayuwarsa bisa tsarin da al'umma ta aminta da shi. Wannan ma
haka yake a cikin rayuwar tatsuniya, domin kuwa akwai tunane-tunane da dama da
aka tsara game da al'amuran da suke aukuwa a cikin duniyar nan. Kuma waɗannan
al'amurran ana tsara su bisa tsani na tunanin al'umma da tarbiyya da yanayin
zamantakewar rayuwa. Misali, a tatsuniyar Maraya da saniya mai magana,
tatsuniya ce da ke ɗauke kishi da ƙiyayya tsakanin
ɗa da kuma
matar ubansa, ta fifita soyayyar ƴaƴanta
da ta haifa a kansa, saboda shi mahaifiyarsa ta rasu, amma kuma duk irin
muguntar da take shirya masa sai saniyar da mahaifiyarsa ta bar masa gado ta ke
sanar da shi tare da faɗa masa hanyar da zai bi ya kare kansa, har
dai Allah ya kuɓutar da shi
ita kuma ya nuna ishara a kanta, misali inda ta ke rera waƙa ta ke cewa:
Janniya janniya jannati
kishiyar uwa,
jannaiya jannati,
Ba uwa ba ce
janniya jannati
za ta baka
tuwo janniya jannati
Tuwo da magani
janniya jannati
Idan ta baka
janniya jannati
Ka zo nan
guna janniya jannati
Ka haƙa
ka rufe janniya jannati.
A cikin tatsuniyar Mutuwa da Sa kuwa ana iya
tsintar wayo tsakanin Gizo da Mutuwa, inda ta yi kiyon Santa sai da ya girma ta
riƙa yawo da shi, tana neman wanda za ta baiwa
ya ci soye bayan shekara ɗaya za ta zagayo ya taɓo kololuwar
kanta, kowa yaƙi karɓa sai Gizo. Sai da
shekara ta zagayo ta zo da niyyar a taɓo saman kanta. Sai ya
yi mata dabara ya haye saman jimƙar ɗakinsa, da ta
zo ta umurci ya fito, sai ya ce ta dakance shi yana ɗinke ginin ɗakinsa da ya
tsage, sai ta yi nufin ta leƙa don ta ga
yadda ake wannan ɗinkin. Sai
kuwa ya yi sauri ya taɓo ƙololuwar
kanta, alhali mutane suna biye da su da su ga yadda za su warware. Shi kenan
sai ya tsira da rayuwarsa ta hanyar yi mata dabara. (Hira da Mama Amarya, mai
shekara 59).
Akwai kuma tatsuniyoyi irin su, Ɗan
sarkin agadas, Musa ɗan Sarki, Fifi dallo, da sauransu, duka
ire-iren waɗannan
al'amura ne da suka shafi zamantakewar al'umma ta yau da kullum a mabanbanta
abubuwa da Bahaushe ke hikimar amfani da da su cikin tatsuniyoyi domin fito da
illar wani abu ko muninsa, wadda kusan kowacce tatsuniya ko wasa sai ka samu
wani muhimmnin al'amari cikinta ko da babu a fili kuwa to matuƙar
an zurfafa tunani sai an riske shi, kamar irinsu, wasannin ka-cici-ka-cici, ɗan ƙashin
gwiwa, daskin da riɗi, da dai sauransu..
Bugu da ƙari Bahaushe
kan yi amfani da hikima wajen zaɓar yanayin cima a cikin wasa ko
tatsuniya, misali a ɓangaren abinda yake mai muni ko fito da
illarsa da rashin kyautuwarsa ana amfani da nau'ikan abinci munana waɗanda suka saɓa da cimar da
al'ada ta yarda da su, kamar ɓera, kwaɗi dusa, dss.
misali a tatsuniyar na-goma, an nuna irin abincin da dodanniya ke ci su ne, ɓeraye, ƙudaje
dss. Ga ɓangaren
abinda yake mi kyau kuwa ko mai muhimmanci za ka iske cewa an bayyana irin
abincin da nama, ko zuma fura da nono alkaki da dai duk wsu dangogin abinci
masu daraja da alfarma a ƙasar Hausa.
Su kuwa Wasanni galibi akan gina su ne ɗauke da
al'adun Hausawa iri-iri da ke zayyana hotonsu da suka haɗa da abinda
ya shafi harkokin Aure, kama daga yadda ake neman auren har zuwa yadda ake
gudanar da zamantakewar auren, da duk wasu abubuwa da suka jiɓance shi, ta
wannan hanya ce al'ummar Hausawa kan riski abubuwa da dama da kuma samun haɓakar
al'adunsu, da nusar da yaransu musamman ƴanmata ga
fahimtarsa sosai ba tare da shan wahalar zaunawa a koyar da su ba. haka kuma
nishaɗi, Sana'a ,
ilimi, da sauransu.
Bugu da ƙari wasu
wasannin akan gina su da hikimar shimfiɗa tsarin mulki lko
shugabanci ga al'umma wadda yau da gobe wannan abin zai zauna a zuciyar yaran
ko matasan, su san daidai da kuma abinda ba daidai ba, su kuma horu da bin doka
ko zartar da ita, kasancewar wata rana su ne a fagen. kusan babu wani wasa a
cikin wasannin malam Bahaushe da ba ya ɗauke da wata hikima
makamanciyar waɗannan .
4.3.3 TAURARIN
TATSUNIYA
Bahaushe kan gina tunaninsa matuka wajen zaben
taurarin Tatsuniya, Galibi za a ga cewa abubuwa da yawa na dangin abubuwa masu
rai da marasa rai da kuma ƙirƙirarrun
abubuwa ne ke karaɗe cikin tatsuniyar Bahaushe, daga cikin
ire-iren taurarin akwai mutane da Aljanu, Imanin da Bahaushe yake da shi game
da aljannu da tunaninshi dangane da siffarsu, halayyarsu da ayyukan ban mamaki
da suke da shi ake fitowa da su a zahiri. Haka kuma ga abinda ya shafi
Dabbobi,da tsuntsaye da kwari, Wasu daga cikin taurarin tatsuniyar ma kuwa babu
su, ƙirƙira su aka
yi, irin su Gizo da ƙoƙi
da Botorami da Dodo da sauran Daga cikinsu akwai waɗanda su aka
fi ambato, akwai waɗanda sukan fito jefi-jefi. Misali ta ɓangaren
mutane ana yawan ambaton sarakuna; da jarumai; da mata da miji; da kishiyoyi da
yanayin zamantakewarsu ta yadda za a fito da darussan da ke aukuwa a cikin
yanayin zamantakewarsu ta aure. Misalin wannan kuwa shi ya fi yawa a cikin
tatsuniya. Sa'annan dukkanin dabbobin da tsuntsaye da ƙwarin da ke
fitowa a cikin tatsuniya ana mutunta su a ba su halayyar mutane ta yadda suna
iya magana. Kamar Sa a cikin tatsuniyar Maɗori, mai bai
wa ubangidansa labarin yadda aka yi kiwonsa don mai shi ya san yadda zai yi ɗori. Waɗannan duka
wani kasaitaccen tunani ne da Bahaushe yake gina wa wadda kuma sai an zurfafa
tunani ake iya gano su.
Tunanin Bahaushe ya karaɗe taurarin
cikin tatsuniya, kamar yadda yake yawan ambato su, tare da ba su matsayi ko
aiki a cikin tatsuniyoyin, wasu taurarin an kirkire si su ne domin su tare wani
giɓi da su kaɗai suka dace
da shi. Domin kuwa dukkanin rayuwar da ake laƙabawa
taurarin, rayuwar mutanenmu ake so a yi gyara. Don haka akwai halayyar da dole
a nemo wasu taurari da ba waɗannan ba don su dace da saƙon
da ake son a isar. Misalin halayyar tsoro da ake so a cusa a cikin zuƙatan
ƴaƴan Hausawa,
sai aka nemo Dodo aka ba shi wannan ragamar. Dabara da iya yi da yaudara da
sauran halaye aka jingina su ga Gizo, sa'annan aka samar masa a murya ta
musamman da ta yi daidai da tunanin yara, aka mutunta shi ta hanyar samar masa
matarsa ƙoƙi, wacce take
da haƙuri da shi kuma halayyarsa ya sha bamban da
nata. Shi kuwa gizo-gizo ƙwaro da muke
da shi a nan ƙasar Hausa, bai taɓa fitowa a
cikin kowane labari na tatsuniya ko da sau ɗaya kamar
yadda sauran dabbobi suke fitowa ba (Labura 2008:263). Gizo da muke da shi a
cikin tatsuniya ya bambanta da gizo-gizo, haka ma matarsa ƙoƙi
ba ita ce ƙoƙi-ƙoƙi
ba. Gizo fitaccen tauraro wanda aka fi sani da mijin ƙoƙi
yana da wasu keɓantattun
halaye da babu tauraron da yake da su kamar wayo da haɗama da
yaudara da ƙarya da wuce iyaka da sauransu. Dalilin da ya
sa mutane suke ɗaukar Gizo a
matsayin gizo-gizo, shi ne wasu daga cikin marubutan littattafan tatsuniya
kamar Yahaya (1971) da Gusau (2013) idan aka zo wajen zana gizo sai a zana shi
da surar gizo-gizon da aka sani, (Rabi'u, 2018).
Dukkanin
waɗannan wasu
abubuwa ne da Bahaushe yake shimfiɗa tunaninsa wajen zaɓarsu, da su
ke haɗuwa wuri ɗaya don samar
da gangar jikin tatsuniya. Haka kuma rashin ɗaya daga
cikin waɗannan ababen,
yana hana kammalar tatsuniya na kasancewarta mai inganci.
Ga
ƙwari da tsuntsaye kuwa tunanin Bhaushe ya fi
karkata ga Tsuntsuwa da maciji, haƙiƙa
tsuntsuwa sha kundum ce a a tatsuniyar Bahaushe duba da cewa waɗanda
tatsuniyar da shafa yara ne, shi kuwa miciji a har kullum ɗabi'arsa ita
ce mugunta don haka dole ya zama abin tsoro ga al'umma.
Sa'annan
kuma haka abin yake ga ɓangaren wasanni ma, sai dai shi wannan fannin
ya ɗan sha bamban
da tatsuniya domin kuwa shi wasa akan tsinkayi tunanin da ya gina ne cikin
gundarin wasan, haka kuma wasu wasannin sun bambanta da jinsin masu aiwatarwa,
ma'ana akwai waɗanda ake
tarayya maza da mata, da kuma wadda maza ne kawai zalla ko mata zalla. ma'ana
dai babu wata ƙirƙirarriyar
halitta ko wani sauyi game da al'amarin kayan cikin wasa ko masu aiwatarwa.
misali akan tsara wasa musamman a shiryashi ta hanyar zayyano ko lissafo duk
wasu kyawawan ɗabi'u da ake
son matashi ya siffantu da shi, ko kuma a ambato halaye abin ƙyama
ga samari, amma sai ka iske cewa wasannin ƴammata ne
masu aiwatar da shi ba su samarin ba. Ko a tsara wasan ta hanyar kwatance da
siffanta yadda mata suke zaman aure da kula da miji da abinda ya shafi reno da
tarbiyyar ƴaƴa, kuma duka ƴammata
ne kawai masu aiwatar da irin waɗannan wasannin. Su kuwa Maza galibi
wasanninsu sun fi karkata ne ga abinda ya shafi faɗa, ko yaƙi,
a ciki za ka iske yadda shugaba ke aiwatar da doka ga mabiyansa da kuma da ƙoƙarin
nuna jarumta don kada a ga gazawar mutum, kamar irinsu wasannin ɗan Akuya na
da sauransu.
Akwai
kuma wasannin da ake haɗuwa maza da mata wajen aiwatar da su, kamar
irin su wasannin ɓuya, ko
wasannin tattaɓa gwiwa, ko
wasannin tambayoyi da amsoshi daban-daban. waɗannan
wasannin duka jinsi biyun maza da mata sukan haɗu wajen
aiwatar da shi. Babban abin lura anan shi ne Bahaushe ya zuba falsafa a wannan
muhallin, domin kuwa duka nau'ikan waɗannan wasannin ana
yinsu ne domin nishaɗi kawai, ko kuma akwai ilimi da ya jiɓanci harshen
nasu, babban abin birgewa anan shi ne yaran duka babu matasa ko kuma ƴammata
sai dai a iske ƙananan yara ne kawai.
Don
haka kuwa kenan ba ma iya cikin wasannin ba hatta da da tsarinsu ma akwai
hikima da tunani.
4.3.4
WAƘA
Waƙa sha kundum
ce a fagen hikimar Bahaushe cikin tatsuniyoyi da wasanni, domin kuwa mafi yawan
kaso na tunanin Bahaushe cikin waɗannan rassa guda biyu waƙa
ke taka rarwar gani wajen bayyanarsu.
Bahaushe
na amfani da hikimar sanya waƙa cikin waɗannan ɓangarori da
nufin jawo hankalin masu sauraro, kasancewar kuma mafiya sauraron ko aiwatarwar
yara ne wannan zai yi tasiri matuƙa wajen
saurin ɗaukar abin ta
hanyar bibyar waƙar, ya yin da suka haddace ta a hankali saƙon
zai riƙa shiga ƙwaƙwalwarsu,
ba sai an maimaita kullum ba wannan ya sa galibi wasannin Bahaushe na gargajiya
ake aiwatar da shi da waƙa, sa'annan
kuma tatsuniyoyi ma kaɗan ne babu waƙa cikinsu
kuma waƙoƙin su ke ɗauki da wani
muhimmin kaso na saƙon da ke ciki misali
tatsuniyar musa ɗan sarki a
baitin da budurwar ke rerawa kamar haka:
Kai wane, Kai wane wannen gayya,
wane ɗan makaranta,
wane ɗan sarakai,
ka ƙaunaci Allh
wane bani zane na,
ka ƙaunaci Allah
wane ban riga ta,
ka ƙaunaci Allah
wane ban bantena.
Wasu waƙoƙin
kuma cikinsu ne ake warware wata matsala da ta faru a cikin tatsuniyar .alal
misali idan aka ɗauki waƙar
cikin tatsuniyar Gizo da ɓaure inda tsuntsuwa ke cewa:
Kai Gizo, kai Gizo,
a can ka ci ɓaurenka,
har ka kuskure bakinka,
har ka manto jallonka.
Haka
kuma idan aka kalli waƙoƙin
wasanni ma inda anan kuma gaba ɗaya cikin waƙen ne ma ake
aiwatar da wasan, ma'ana a cikin waƙar manufar
wasan ta ke misali, wasannin gaɗa:
jagora: Ina da ƴata da ba za
na bai wa fulani ba,
ƴ/amshi: maye
dalilin da ba za ki bai wa fulani ba,
jagora: yini a daji kwana a daji kamar
kura
ƴan/Amshi:sai
tumoro ala bamu kairin masoya.
jagora : ina da ƴata da ba za
na baiwa barebari ba
ƴ/amshi: maye
dalilin da ba za ki bai wa barebari ba
jagora: ƴa da tsagu
uba da tsagu kamar ƙwaya
ƴ/amshi: sai
tumoro ala bamu kairin masoya
A wata waƙar
da ake cewa:
jagora: Tama yaro tama galadima wasa
ba faɗa ba
ƴ/amshi:
Arerere
jagora: Ni nawa ɗan maharbi
ƴ/amshi: ya
harbe ki, kuci harbi ku kwana harbi
gadon gidanku ne, bulala ɗari da hamsin
ta shafeki, gaba tsudum, baya tsundum
a aljanna,
jagora : wasa ba faɗa ba
ƴ/amshi:
arerere.
kai
tsaye mai sauraron wannan waƙar zai
fuskanci cewa ana so ne a bayyana nau'ikan al'adun wasu al'ummomi daban, wato
yadda suke gudanar da al'adunsu da kuma al'amuran rayuwarsu. sa'annan kuma ɗaya waƙar
na nuna irin saurayin da al'adar Bahaushe ta yarda da aurensa, wato mai sana'a,
wannan aka tsara wasan ta wannan sigar.
Wani
babban abin lura game da wannan gaɓa shi ne ba ma iya al'amuran da suka
shafi wasannin yara kurum ba, hatta da wasannin da manya ke aiwatarwa akan yi
su cikin sigar waƙa, yau da kullum kan sa ya riƙa
tasiri a zuƙata, don haka wannan ma wani muhimmin tunani
ne na Bahaushe a wannan ɓangare.
Bugu
da ƙari duka waɗannan abubawa
da Bahaushe kan yi game da wannan ɓangare na adabi (Tatsuniyoyi da
wasanni) masu ɗauke da
hikimomi iri daban-daban yana aiwatar da su ne bisa tunanin fito da wani
muhimman al'amari da zai kyautata rayuwarsa da kuma zamantakewarsa ta yau da
kullum.
Dan
haka yasa aka zaɓo wasu
fitattun misalai daga waɗannan rassa domin binciko ire-iren falsafar,
wato tunanin, domin ganinsu a zahiri dan a nazarce su tare da gano dalilan
sanya su da irin muhimmancinsu a rayuwa. kamar yadda za mu gani a ƙasa.
4.4 TATSUNIYAR
GIZO DA ƁAURE
Tatsuniyar gizo da ɓaure
tatsuniya ce ta farko cikin littafi na ɗaya a jerin
littattafan guda shida, sa'annan kuma ƙirƙirarriyar
tatsuniya ce wadda ta ƙunshi rayuwa da
zamantakewar al'umma guri ɗaya, da kuma abinda ya shafi shugabanci
a tsakanin al'ummar, haka kuma tana ƙunshe da al'adu
daban -daban.
Babban maƙasudin zaɓar wannan
tatsuniya a wannan binciken shi ne a gano irin hikmomi da tunani da Bahaushe ya
gina a cikinta wadda a taƙaice akan iya
kiranta da falsafa.
Da farko dai Bahaushe ya gina tunaninsa a
wurare daban-daban cikin wannan tatsuniyar wadda kai tsaye ba za a iya gano su
ba sai ta hanyar zurfaffan nazari, ire-iren wuraren kuwa sun haɗa da zaɓen taurari da
sauran abubuwan cikin tatsuniyar misali:
Idan aka yi duba na tsanaki game da tatsuniyar
za a ga cewa tun a farko Bahaushe ya gina tunaninsa wajen zaɓar sarki a
matsayin wanda ya mallaki gonar ɓauren. A kowacce al'umma sarki mutum
ne mai girma da matsayi har ma kuwa al'ummar Hausawa, baya da haka a bisa
al'adar Bahaushe duk wani shugaba akan same shi mutum ne da ba a ƙetare
umarninsa ko a yi watsi da hukuncinsa. ba kuma hakan yana nufin isa ba, sai dan
ɗaukaka da
daraji al'amarin gabaci, dake taka muhimmiyar rawa a al'adunsa.
Tabbas Bahaushe ya zuba hikimarsa a nan domin
bai zaɓo wani mutum
daban daga cikin gari ya sanya shi matsayin mamallakin gonar ba, sai ya zaɓi sarki ya
sanya domin girman al'amarin da yake son fiddowa.
Haka kuma idan aka koma aka yi duba ga bishiyar
ɓauren ma akwai
babbar hikima wajen zaɓarta da Bahaushe ya yi, dalili kuwa shi ne
bishiyar ɓaure dai
bishiya ce mai daraja sa'annan kuma ba kowa ne zai ga bishiyar ɓaure ya kau
da kansa ba, ko da kuwa ace ba aikin tsinkarta zai yi ba, saboda ɓaure abu ne
mai zaƙi da ƙamshi da kuma
garɗi, kamar
yadda aka bayyana a tatsuniayar. Saboda haka wannan ma tunani ne na Bahaushe me
kyau, domin kamar yadda tarihi ya nuna ƙasar hausa ƙasa
ce mai tarin bishiyoyi da za a iya lissafa nau'ikansu ba, sa'annan akwai
kayayyakiin amfanin gona kamar hatsi da sauransu, duka kowanne ana iya gina
tatsuniyar a kansa, amma duka bai yi amfani da waɗannan ba sai ya
ɗauko bishiyar
ɓaure, saboda
zaƙinta da ƙamshi, da
kuma darajarta a idon al'umma Musamman yara.
A
ɗaya ɓangaren kuma
idan aka duba alƙawarin da sarki ya yi ga wanda ya amince da
buƙatarsa da ya zo da ita , tabbas a nan ma ya
yi amfani da tunani da hikima, domin kuwa idan aka duba a tarihin rayuwa da
zamntakewar Bahaushe da yadda ya ƙarfafi
al'amuransa za mu ga cewa a koyaushe sarki mai iya bada umarni ne ga kownne
irin abu ba tare da ya biya lada ba , kai tsaye yana iya sawa a yi wannan aikin
tare da gindaya irin wannan sharaɗin (babu wanda zai sha har ya gama)
saboda girman shugabancinsa da kuma matsayinsa a wurin waɗanda yake
mulka. kenan wannan gaɓar ma Bahaushe ya yi amfani da tunanin yin alƙawarin
lada game da aikin da za a gabatar .
Haka
kuma a wajen da sarki ya tara mutanen gari domin isar ga buƙatarsa,
babu wanda ya amshi wannan buƙatar sai
Gizo, kuma kaf cikin mutanen garin Gizo ne kaɗai wanda za a
iya iya siffanta shi da wanda ba mutum ba, kamar yadda aka gani a hoton da aka
zana ƙirƙirarriyar
halitta ce . A nan tunanin Bahaushe ya fito kan cewa al'ummar Hausawa mutane ne
masu tsananin tsoron amana, domin al'ada ce mai ƙarfi cikin
kyawawan halayen Bahaushe, wannan ya sa kowa ya ƙi karɓa sai shi
gizon a yayin da muka ga gizo dai ba za a kirashi da mutum kai tsaye ba. Don
haka wannan ma wata hikima ce da Bahaushe ya yi amfani da ita cikin tatsuniyar.
Da
gizo ya gama tsinke ɓauren aka kwashe, sa'annan aka cika masa alƙawarinsa
(Bashi amarya da gararta) kafin a kai ga tafiya tsuntsuwa ta zo ta fallasa
asirin gizo tahanyar bayyana abinda ya yi da waƙa.
To
a wannan gaɓar kowa ya
san cewa dai babu wani tsuntsu a duniya da yake magana bare har ya fahimci wani
abu ya rera shi cikin waƙa ya kuma
furta, kamar yadda masana suka bayyana ɗaya daga cikin
abubuwan da suka bambanta ɗan Adam da dabbobi shi ne hankali da
tunani, kuma abinda tsuntsuwa ta yi a wannan muhalli aiki ne na mai hankali da
kuma tunani.
Bahaushe
ya gina tunaninsa mai kyau a nan, wajen tabbatar da cewa duk abinda mutum ke
aikatawa a ɓoye ko a fili
ko da babu kowa to Allah mahalicci yana kallonka, kuma duk abinda aka aikata
cikin rashin gaskiya abu ne da ba ya tasiri domin komai daren daɗewa sai
gaskiya ta yi halinta ( kamar yadda sarki ya janye alƙawarin da ya
yi wa gizo ya tashi a biyu babu , gashi dai ya sha wahalar tsinkewa ɓauren amma
kuma buƙatarsa bata biya ba sakamaomakon cin amanar
da ya yi ). Wannan ne ya sa Bahaushe yayi amfani da tsuntsuwa a wannan gaɓar domin
nusarwa da tarbiyyayntarwa zuwa ga tsarkake zuciya da yin gaskiya tare da yarda
da kasantuwar mahalicci tattre da bawa a duk inda ya kasance.
Haka
kuma ya yi hikimar zaɓar tsuntsuwa a wannan muhallin ne saboda
galibi waɗanda ake bawa
labarin tatsuniya yara ne maso tasowa kuma mafi akasarin yara suna da wata ɗabi'a ta son
tsuntsaye da ƙaunar su, sa'annan kuma tsuntsu halitta ce da
masana suka siffanta shi da ɗabi'ar wayo. Don haka kai tsaye wannan
abun zai fi yin tasiri a ƙwaƙwalwarsu.
Baya
da waɗannan
hikimomi na Bahaushe da aka fito da su a wasu wurare na cikin wannan
tatsuniyar, akan iya gano wani wani muhimmin tunanin wadda ya gauraye tun daga
farko har ƙarshen tatsuniyar. Tunanin kuwa shi ne ya yi
hikimar ƙirƙirar
tatsuniyar ne domin nuna illar CIN AMANA, Hakan kuma hikima ce ta koyar da ƴaƴansa
ta irin waɗannan hanyoyi
kamar yadda aka bayyana a baya cewa "Tatsuniya ita ce makarantar farko da
Bahaushe ya ke ilimantar da ƴaƴansa
".
Don
haka kai tsaye ana iya cewa babban tunani/hikima da Bahaushe ya gina cikin
wannan tatsuniyar shi ne nusar da yara su guji CIN AMANA , a falsafance wadda
idan kuma aka koma a fannin adabi, manazarta da masana adabi a fagen nazari za
su kira wannan tunani da Jigo/manufa, wato saƙon da
tatsuniyar ke ɗauke shi.
4.5 TATSUNIYAR
ƊAN SARKI YA ZAMA MACIJI
Wannan tatsuniyar na ƙunshe da
abubuwa daban-daban na zamantakewar rayuwa, domin kuwa an gina tatsuniyar ne
akan zuri'ar wani mutum da yake neman haihuwa saboda ba shida ɗa ko ɗaya, sa'annan
kuma matansa guda uku ne, wadda kuma kowacce a cikinsu tana buƙatar
haihuwar.
Haƙiƙa
wannan tatsuniyar akwai hikimomi a wurare da dama da Bahaushe ya gina, wadda
idan ba a zurfafa tunani ba za a kalle su a matsayin tunani ne mai kyau a
wannan gaɓar ba,
misali:
An nuna cewa mutumin na da mata har guda uku,
sai dai kaf cikinsu akwai guda ɗaya wadda ita ba ya sonta, hasali ma
da ya karɓo maganin
haihuwar iya matan da yake so ya bawa, amma banda ita.
Ba za a fahimci cewa hikima ce mai kyau a
wannan gaɓar ba, sai an
waiwaya zuwa ga ire-iren waɗannan tatsuniyoyi, wadda ƙarara
ake bayyana fifikon soyayyar mace ɗaya ita kuma ɗayar a nuna ƙiyayya
a kanta ƙarara. Kamar tarsuniyar Ruwan bagaja, Daskin-
da- riɗi, da sauransu.
Bahaushe na da tunnnin yin amfani wannan gaɓar domin nuna
illar wani abu, ko kuma muhimmancinsa, domin idan aka duba al'ada ce mai ƙarfi
da ya riƙe, akan sami Bahaushe mai matuƙar
kula da iyalansa yadda ya dace ko dan gudun yin abin kunya da zubar da murunci,
ko rage martaba a idon mutanen gari. Wannan yasa ko a tarihi ba a fiya samun
ire-iren waɗannan halaye
ba bisa ga rayuwar Bahaushe ta zahiri, sai dai ya ƙirƙire
su cikin adabinsa, da nufiin fito da wani abu fili ko kuma nusarwa zuwa ga wani
abu muhimmi ,misali; Tatsuniyar Daskin- da- riɗi, da ta ɗan sarkin
agadas, da kuma tatsuniyar ruwan bagaja da sauransu.
Haka kuma an bayyana cewa bayan da aka samo
magani dukkansu suka sha suka samu ciki suka haihu, har da wadda ba a so wato
(bora) sanadiyyar ɗiban ɗan guntun da aka
zubar ta sha har aka haifi ƴaƴa
duka mata, lokacin aurar da su ya yi, dukansu ya bada su ga waɗanda yake so,
ita kuma gwi-da-yara (ɗiyar bora) ya kaita jeji saboda ƙiayayyar
da yake wa mahaifiyarta ta shafe ta, ya haɗa da maciji a
matsayin wadda za ta yi rayuwa da shi, haka kuma tayi biyayya, daga ƙarshe
miciji da mutum ne kuma ɗan sarki, da aka bayyana cewa sai ya
zama maciji da ya samu matar aure.
Awannan gaɓar kai tsaye
za a iya kallon wannan a matsayin hikima ce mai kyau, domin kuwa ɗan sarki
mutum ne mai ƙima wadda kuma ya kasance abin so ga kowacce
yarinya, amma sai aka nuna cewa ya rasa matar aure . An yi hikimar amfani da ɗan sarki a
wannan gaɓar domin
tatsuniyar ta karɓu sosai,
ma'ana abinda ake son bayyanawa ya karɓu a wurin masu
sauraron tatsuniyar, wannan ya sa ba a zaɓo wani saurayin daban
cikin tatsuniyar ya zama matsayin wanda ya nemi aure bai samu ba, sai aka ce ɗan sarki,
kowa zai ji abin da mamaki, domin kuwa duk kalar matar da ɗan sarki yake
son aura , kai tsaye zai samu ba tare da shan wahala ba ko da kuwa ba ta so,
saboda girman matsayinsa.
Bugu
da ƙari hikimar sanya ɗan sarki ya
zama miciji shi ne, kusan dabbobin da aka san su a zahiri. Maciji na ɗaya daga
cikin muhimman dabbobi da ake tsoransu, saboda hatsrinsu, wannan yasa Bahaushe
ya yi tunanin zaɓar miciji, ta
haka ne za a fito da jarumtar yarinyar fili, aka sanya shi matsayin wadda za ta
zauna da shi duk da kuwa ire-iren abubuwan tsoratarwa da aka nuna micijin ya
yiwa yarinyar ba ta nuna ta tsorata ba.
A
ɗaya ɓangaren kuma
wata hikimar Bahuashe ta sanya miciji a wannan gaɓar za ta yi
tasiri matuƙa ga masu sauraron tatsuniyar, musamman yara
da galibi su ake yiwa tatsuniyar, sanya miciji (abin tsoro da firgici) a wannan
muhallin zai taimaka wajen kiyaye abinda yake son nusarwa da saurin yin tasiri
a zuciyoyinsu.
Bayan da uban yaran ya shirya kai ziyara
gidajen ƴaƴansa domin
gano irin halin da kowacce ke ciki, an nuna cewa gidan ta farko da ya je ya
samu abinci da miyar ɓera, a nan Bahaushe ya yi amfani da ɓera a
matsayin abinci bisa tunanin fasalta irin munin abincin da kuma ƙasƙancinsa,
domin kuwa ɓera ba abin
arziƙi ba ne, kuma al'ada ba ta ɗauki ɓera a
matsayin abu mai daraja da za a ci ba, hasali ma a rayuwar Bahaushe ɓera abu ne da
ake ƙyama saboda mummanar ɗabi'arsa ta ɓarna. Haka ɗaya gidan ƴar
da ya je ya tarar da tuwon dusa miyar ɗata, duk dai hikimr ɗaya ce a nan
da muhallin da aka sanya ɓera, domin ita ma dusa kowa ya san ba
cimar mutane ba ce sai dabbobi, amma sai aka gina tunani da yin amfani da dusa
a muhallin da kai tsaye zai fito da ƙasƙancin
abin da ɗumbin
muninsa.
Bayan
da uban ya samu labarin gidan gwida- yara a wurin ƴan matan har
ta bada umarnin a kai shi jikin tagar gidan, ta wullo masa kaya masu kyau ya
saka. A wannan gaɓar an yi
amfani da tunani domin an nuna cewa wullo kayan da tayi maimakon ta ba shi a
gidan, amma saboda kar mahaifinta ya ƙasƙanta
sai ba a nuna ya shiga gidan ba sakamon yanayin matsayin gidan da kuma irin
shigar da ke jikinsa.
Haka
kuma bayan ya koma gida ya ba wa kowacce tsarabar ƴarta ta bayar
an nuna da aka aikawa ƴaƴan
su zo an sake nuna ɗaya daga ciki ta kawo babbakakkun ɓeraye duka waɗannan abubuwa
ne da Bahaushe ya sanya tunanisa wajen saka su a cikin wannan tatsuniyar. A ɗaya ɓangaren kuma
idan aka kalli tatsuniyar gaba ɗaya a tsanaki, akwai manyan hikimomi
da suka game tatsuniyar ta fuskar saƙon da take ɗauke da shi ;
kamar muahallin da ake ƙuntatawa uwar
gwi-da-yara, har ta kai da an raba ta da ƴarta,
Bahaushe ya kan yi amfani da irin wannan gaɓar domin
nusarwa zuwa ga yin haƙuri a duka al'amuran
rayuwa, da kuma biyayya ga aure, kuma haƙurin ya kan
zama riba nan gaba (kamar yadda gwi-da-yara da mahaifiyarta suka ci nasara kan
haƙurin da suka yi). Har ila yau ya yi amfani da
tunani wajen nusarwa ga yiwa iyaye biyayya, wannaan ya sa aka yi amfani da
gwi-da -yara, ba ta wulaƙanta
mahaifinta ba lokacin da ya iske muhallinta da ta ke ciki. Sannan akwai hikimar
nusarwa ga cewa babu wani abu da zaka nun ka fi ƙarfinsa
(girman kai) a duniya komai matsayinka musamman game da manyan al'adun Bahaushe
kamar Aure, wadda kuma al'amari ne da babu mai iya yin san rai game da shi sai
wanda ya halicce shi, wannan ne yasa Bahaushe ya yi hikimar sanya ɗansarki a
wannan tatsuniyar a matsayin wanda ya rasa matar aure, saboda al'umma na kallon
jinin sarauta ya fi ƙarfin komai saboda
matsayin mahaifinsa.
Waɗannan hikimomi su ne suka haɗu suka samar
da muhimmin saƙon da ake nufin isarwa, su ake kira falsafa
wato tunani, ta hanyar amfani da falsafa ne saƙon ya ke
fitowa sosai da sosai, su kuma manazarta adabi a fagen nazari suke nazarin saƙon
tatsuniyar kai tsaye , kamar yadda sauka kira shi da jigo, misali, a ɓangaren adabi
wannan tatsuniyar za a bayyana cewa tana ɗauke da jigon Haƙuri
ne, kamar yadda Bahaushe ke cewa "mai hauri yana tare da riba" akwai
kuma ƙananan jigogi da suka haɗa da wahala, ƙiyayya,
da na sani da sauransu.
4.6 TATSUNIYAR
NA-GOMA
Tatsuniyar na-goma tatsuniya ce da aka gina ta
game da wani maharbi da ƴaƴansa
guda goma, wadda kuma tunanin Bahaushe ya game ciki da wajen tatsuniyar.
Idan aka lura da kyau za a ga cewa, an faɗi wani
maharbi da kuma ƴaƴansa goma duk
maza, kullum ya je farauta ya samo tsuntsu sai ya neme shi ya rasa, ashe ɗansa ne na ƙarshe
ke ɗauke tsuntsun
ya gasa ya cinye ba a sani ba , har ta kai ga uban ya gajiya ya yanke hukuncin
a tafi kogin rantsuwa domin a gano wanda yake cinye tsuntsun.
A wannan gaɓar tatsuniyar
ana iya hango hikimar Bahaushe, dalili kuwa shi ne an nuna cewa ƴaƴan
wannan maharbi duka maza ne ba mata kuma sannan kaf cikin ƴaƴan
nan babu wanda yake aikata wannan laifin sai ɗan karaminsa
(Ɗan auta), to a nan za a iya cewa me yasa ƙaramin
ciki ne ya kasance mai laifin?, Amsar anan ita ce Bahaushe ya yi ƙoƙarin
bayyana wata al'ada tasa, a bisa tsarin zamantakewarsa, soyayyar ƴaƴa
ba ta ɗaya daga
cikin abinda yake fifitawa a rayuwarsa musmman ƴaƴan
fari (manyan ƴaƴa) duk wata
walwala da iyaye ke yi da ƴaƴansu
sai dai ka tarar ƴaƴan nan ba na
fari ba ne, haka kuma duk abinda yaro ya aikata ba daidai ba a fasa yi masa
hukunci komai ƙanƙntarsa domin
gyaran gaba, kuma komai ƙanƙantar
laifin (kamar laifin na goma na cinye tsuntsu a wannan tatsuniyar bai kai ga
yin wannan hukuncin ba, domin kowa yasan in kogi ya cinye mutum zai yi wahala ya
yi rai) amma Bahaushe ya yi amfani da wannan gaɓar domin
cimma manufar saƙon da yake son isarwa, sa'annan kuma a wannan
muhalin Bahaushe ya yi la'akari da cewa masu sauraron tatsuniyar duk yara ne ƙana
ba manya ba, wannan yasa ya tsara hikimar sanya ɗan ƙaramin
ciki ya kasance mai aikata laifi, domin ya kasance labarni tatsuniyar ya yi
daidai da tunani da kuma matsayin masu sauraronta
Haka kuma akwai wani muhimmin tunani na
Bahaushe da ya yi wajen fito da tasirin wasu abubuwan halitta da suke alaƙanta
su ko danganta su da da wata buƙata ta
musamman zuwa gare su, (kamar rantsuwar da aka yi wa kogi). Sa'annan ya nuna
cewa bakin kogi dai wuri ne na iskoki ke zaune (muhallin iskoki ne) kamar yadda
ya nuna cewa da ruwa ya tafi da na -goma har ya kai shi bakin kogi anan ya haɗu da
dodanniya ta nemi cinye shi bayan ya bayyana mata duk abinda ya yi sanadiyar
zuwansa wannan wurin da a baya bai faɗa ba.
A tsakanin zaman dodanniya da na-goma akwai
hikima saboda a tarihi babu wata halitta wai ita dodo, Bunza (1986), ga waɗanda kuwa
suka yarda da akwai shi suna nuna cewa dodo da mutum ba sa zama inuwa ɗaya, dan kuwa
mutum abincin dodo ne, haka kuma duk wasu dangogin abincin mutane ba sa ci sai
dai na su na daban, amma a tatsuniyar nan sai dodo bai cinye na-goma ba har ma
ta kan fita gari domin nema masa na sa abincin ta kuma cigaba da yi masa abin
siyarwa (ƙosai) yana shiga gari yana siyar mata amma
bai taɓa neman
gidansu domin ya gudu ba, har Allah ya sa ya haɗu da ƴan'uwansa,
suka kuma yiwa dodanniya goma ta arziƙi suka fanshi
ɗan uwansu.
Wannan ya nuna cewa ana samun kyakkyawar alaƙa da fahimtar
juna tsakanin waɗansu jinsin
halittu da mutane, musamman ma iskokai kamar yadda zamantakewarsu ta maguzanci
har bautarsu suke yi. wannan yasa Bahaushe ya yi hikimar tsara wannan, domin
kuwa da ruwan ya tafi da na goma ya cinye shi za a iya iske shi a bakin kogi in
dodanni suka gani su cinye shi. A ɗaya ɓangaren kuma
an yi amfani da dodo ne domin tsoratarwa da nusarwa ga barin halin da bai dace
ba ga yaro, wannan yasa ake horar da su tun da fari.
4.7 WASANNIN
KA-CICI-KA-CICI
A Ƙamusun Hausa
Na Jami'ar Bayero, Kano (2006), an bayyana kacici-kacici da: “Zaɓi ko kintata”
Amma dangane da asalin Kalmar ka -cici-ka-cici kuwa, Yahaya (1991: 27) ya
bayyana cewa:
“Kalmar ka-cici-ka-cici tana da ma'ana kashi
biyu masu alaƙa da juna. Da fari ya nuna an samo asalinta
ne daga kalmar 'cinta', wato kintaci faɗi. Ya fito da haka ta
nuna yadda yara sukan yi wasa a inda ɗaya zai rufe wani abu
a hannunsa ya buƙaci ɗayan ya cinta, wato
ya yi kintaci-faɗin abun da
yake a hannunsa. A kan haka, Almajir, (2013: 4) ya bayyana cewa, wannan wasa da
yara suke yi tsakanin junansu shi ne ya gina wannan wasa ta kacici-kacici wanda
ake yi da tunani da siffanta wasu abubuwa. Sannan akan yi ta ga yara cikin wata
irin Hausa mai zuzzurfar ma'ana
Wasan ka-cici-ka-cici wani ɓangare ne na
adabin baka, wasa ne da ya shafi yara da Hausawa suka ƙirƙire
shi wanda yake tafiyar da cigaban rayuwarsu da kuma inganta zamantakewarsu.
Wasanni ne masu ɗauke da ɗumbin hikima
da kuma tunani na malam Bahaushe, irin waɗannan tambayoyi sun ƙunshi
siffantawa ne na wani abu, da za a juya kamanninsa na yadda aka san shi, ta
yadda mutum zai gano shi ne ta hanyar ɗan gajeren tunani,
kafin gano abinda ake nufi.misali:
v
Makaranta a dokar daji (gidan tururuwa)
v
Shanu na dubu maɗaurinsu ɗaya
(Tsintsiya)
v
Fai-fai na ɗinkin marido
(Zuma)
v
Ƴar baƙa
jakar mata (kujera)
v
Samarin gidanmu masu fararen kawuna (Taɓare)
Waɗannan misalan idan aka lura dukkansu
an gina su ne ta hanyar siffanta kamanninsu ko abubuwan da suke yi, wato a nan
Bahaushe ya yi tunanin sarrafa tambayar ta hanyar siffantawa dan a samar da
amsar abin daidai yadda yake. Irin wannan ta kan zo ne kamar sauran zantuka ko
bayanai waɗanda idan
mutum ya yi zai iya gane ma'anarsu, amma maimakon a bar su haka a fili, sai a
kan yi dabara a ɗan ɓoye su don ruɗa mutum. ko
kuma a yin tunanin amfani da sauti ko aikin da abun yake wajen tambayar domin
gano kaifin basirarsu wajen ba da amsar, misali:
v
Daga nesa na jiyo muryar ƙawata
(Ganga)
v
Rub-rub kushewar bayi (ƙaiƙayi)
A ƙasar Hausa an
rungumi kacici-kacici a matsayin wata hanya ta sanya shaƙuwa tsakanin
al'umma. Kacici-kacici na sanya kaifin basira da kuma iya fahimtar maganganun
na gaba da shi. Sannan yana zama wani rumbu da ke adana kalmomin al'umma. Yana
kuma sanya raha da annushuwa ga waɗanda suke yin sa.
Haƙiƙa
wannan nau'in wasan cike yake da ɗumbin hikima da tunani kan irin
abubuwan da ake gina wasan, da su ka ƙunshi abubuwa
na rayuwa iri daban-daban, Hausawa na cewa "idan yau kai ne, gobe ba kai
ba ne sai wani" idan yau ka san duk wasu abubuwan rayuwa, sunayensu da
siffofinsu gaba ba lallai masu tasowa su sansu ba, wannan ya sa Bahaushe ya yi
tunanin sarrafa wannan hikima ta hanyar sassauya abubuwan rayuwarsu ta yau da
kullum, ta sigar wasa, domin na baya su taso da ilimin saninsu, duk wanda ya
san amsar sai ya faɗa wanda kuma bai sani ba ya kan ce ya ba da
gari. Wannan kansa yana nuni ne zuwa ga babban abu na rayuwar ɗan Adam,
wanda mutanen duniya gabaki ɗaya suka yi amanna da shi, shi ko
wannan abu ba wani abu ba ne da ya wuce horo, shi mai gabatar da
ka-cici-ka-cicin na yin horo ne, ta hanyar biɗar a bashi
gari, wannan wani horo ne da tun mutum yana yaro yake amanna da shi.
A ɓangaren Kalmomin da ake amfani da su
airin waɗannan wasan,
wata babbar hikima ce, domin ma'adana ce ta ajiye kalmomi waɗanda sai dai
tatsuniyoyin kaɗai ko
wasannin za a iske su, misali:
v
Ƙulun ƙulufita.
v
Shirin ba ci ba.
v
Ta ƙanda ba ƙashi
ba.
v
Kurkucif kucif. Dss
Duka waɗannan kalmomi
ne da ba a riskar su cikin zantuka yau da kullum, domin ba kalmomi ne da
ma'anarsu ta ke a fili ba galibi sai dai cikin tatsuniyoyin da kumma ire-iren
waɗannan ake
samun su domin ƙarawa harshe daraja da ƙaimi,
sa'annan waɗannan kalmomi
da ake yi wata hikima ce ta gyaran zance ya yi daɗi da kuma
saurin fahimta da daɗaɗa zancen.
Akwai kuma tunanin fito da hikima da baiwar
ubangiji ga halittunsa masu ɗauke da abubuwan mamaki game da su.
Bahaushe tun kafin ya karɓi musulunci ya yi imani da yarda da
abubuwan da ya tarar a duniya kamar Rana, Wata,Taurari,Duwatsu, Itatuwa,
Tsirrai, da kuma ƙwari, wannan dalili ya ba shi damar ɗaukarsu a
matsayin ababen bautarsa domin neman biyan buƙatunsa na yau
da kullum. A irin waɗannan abubuwa Bahaushe ya yi tunanin nusar da
ƴaƴansa su san
waɗannan abubuwa
da kuma nuna irin hikimomin dake tattare da su, komai ƙanƙantarsu,
kuma komai girmansu, da yadda suka kasance ababen amfani ga rayuwarsu. misali:
v
Gaya ɗaya dama duniya/
Farin wuri dama kogi (Farin wata)
v
Abu siriri abu sarara abu tufkar Allah.
(Gashi)
v
Kututture uku gagara ɗauri (ƙwai)
v
Mace da miji sun haifi ƴaƴansu
iyaka
A nan ana nufin Rana da wata da kuma
taurari, waɗannan abubuwa
ne da ubangiji ya halitta, masu ban mamaki da muhimmanci ga rayuwar ɗan Adam. Idan
aka kalli yadda farin wata ya ke,. ga shi dai abu ne ga yadda muke kallona a
zahiri ɗan ƙarami,
amma ya yin da dare ya yi shi kaɗai ya isa haska ko'ina a duniya baki ɗaya, wannan
wani babban abin al'ajabi ne da hikima tattare da halittar wata, haka ma gashi,
shi ma dai dubi yadda yake kusan babu wani bawa da ya isa ƙirga adadin
zirin gashin da ke jikinsa, amma dubi yadda Allah ya halicce shi, siriri abin
ban mamaki, haka sauran abubuwan da ba za ƙirgu ba cikin
halittun ubangiji irin su ƙwai duk cike
suke da abubuwan ban mamaki .
Bugu
da ƙari wani tunanin na Bahaushe da yake cikin
wannan wasan shi ne yadda ya riƙa gina
muhimman al'adunsa da ya gada tun kaka da kakanni, da kuma kwatanta wasu manyan
al'adun nasa da irin kusanci da kayakkawar alaƙa da suke da
shi da addini, misali:
“Abu uku ya yi kama
da abu uku, abu uku ya zo ya hana"
Amsar wannan gaɓa ta
ka-cici-ka-cici ita ce, na ɗaya -Aure ya yi kama da bauta, ƴanci
ya zo ya hana. Na biyu barci ya yi kama da mutuwa, numfashi ya zo ya hana. Na
uku zabuwa ta yi kama da saƙi amma tozo
ya zo ya hana. Aure muhimmin abu ne da ɗan Adam ke aiwatarwa,
bauta kuwa kowa ƙinta yake, ƴanci kuma abu
ne da kowa ya ke son sa , shi kuwa barci abu ne da yai yi kama mutuwa amma kuma
shi numfashi kan sanya ran mutum ya dawo yadda ya ke.
Wani babban misalin a nan shi ne gaɓar da ake
cewa:
* Yadda ɗillin ta kan
yi ɗillin haka ma
ɗillin ta kan
yi ɗillin"
A nan kai tsaye an saka mai bada amsa cikin ruɗu, domin zai
kutsa ne tunanin gano wane abu ne wannan, yakan samar da abu sannan abun ya
samar da shi, sai kuma ka gano cewa a ga kaza ai ita take yin ƙwai,
haka kuma kwai ne yake zama kaza, to da zarar wannan tunnnin ya zo maka amsar
ta hau daidai da tambayar, wadda bayan ita ma akan iya samun wasu abubuwan masu
kama da hakan.
Irin waɗannan dabarun da
hikimomin su suka gauraye wannan wasan suna da yawan gaske
4.8 WASANNIN ƁATA
Wasannin ɓata wasu
nau'ikan wasanni ne da yara ke aiwatarwa alokuta daban-daban domin motsa
jikinsu da kuma samar da nishaɗi. Irin waɗannan
wasannin yara maza zalla ke yinsa, wasanni ne da ake da tsalle-tsalle da kuma
guje-guje a tsakanin yaran ta hanyar rera waƙoƙi
iri-iri.
Haƙiƙa
wasannin ɓata cike suke
da hikimomi da tunanin Bahaushe, domin kuwa ba haka kurum suke rera waƙoƙinba
akwai abubuwa da yakan tsara cikinsu bisa wani keɓantaccen
tunani na musamman, haka kuma waje tsarin wasan nan ma wasu tarin hikimomi ne
da da cusa domin fito da wata manufa ta musamman da ke da nufin fiddowa alal misali,
idan aka ɗauki wasan Ɗan
akuyana.
Da farko idan aka yiwa wasan kallo na tsanaki
za a ga cewa, wasa ne da ya ƙunshi doka da
kuma hukunci game da wata ɓarna, Bahaushe na da tunanin nuna wa ƴaƴansa
muni da kuma illar ɗaukar abin wani da kuma yadda al'adarsa ta yi
tir da Allah wadai da irin wannan ɗabi'a, wannan yasa wasan ɗan akuya na
ya siffanta duk yanayi da halin da mai irin wannan halin ke tsintar kansa a
yayin da ya aikata irin ɓarnar, sai ya yi hikimar tsara wasan
da tunanin juya al'amarin kan wata halittar da ba mutum ba wato dabba (Ɗan
Akuya) kasancewar al'amarin ba abin so ba ne, Sa'annan kuma gurin da ya shiga
rumbu ne, sai aka siffanta shi da haɗa hannaye da yaran suka yi wato ƙawanya,
domin kowa ya san abincin dabba dai ba ya wace hatsi, kuma sannan duk abinda
aka sanya shi bisa rumbu abu ne da aka killace shi wuri guda, don haka kai
tsaye an san ba gurin ajiyar abincin dabbobi ba ne.
A
ɗaya ɓangaren kuma
cikin waƙar sai aka bayyana cewa waɗanda suka
ritsa mai lefin dukkaninsu suna ɗauke da munanan makamai na illata shi,
ya yinda shi kuwa yake ƙoƙarin
samun wata ƴar hanya da zai gudu domin ya tseratar da
kansa daga azabar da suke shirin yi masa.
wannan wasa ne kai tsaye da aka yi hikimar
tsara shi domin gujewa aikata ɓarna ta ɗaukar hakkin
wani da kuma ƙyamatar wannan ɗabi'ar.
4.10 NAƊEWA
Tabbas
in ka ga wane ba banza ba, haƙiƙa
al'ummar Hausawa ba kanwar lasa ba ne a fagen tunani game da al'amuransu, domin
tun kafin a haifi uwar mai sabulu balbela take da farin gashinta" tun
kafin cuɗanyar
Bahaushe da baƙin al'ummu yake da wayewarsa ta fuskar
kyautata zamantakewa da amfani da kaifin tunani da basira ga duka lamuransa. haƙiƙa
ko ba a ce komai ba wannan babin ya fayyace tsaki da tsakuwa, gama kuwa an
binciko tare da zaƙulo wannan baiwa ta
bahaushe wato falsafa, a cikin waɗannan muhimman ɓangarori, in
da aka zayyane duk wani tunani da hikima da ke cikin littafin tatsuniyoyi da
wasanni guda shida da aka ambata a farfajiyar binciken, tunanin bahaushe ya
fito da abubuwa da dama da kusan za a iya cewa babu su a a yau , kamar wajen zaɓen taurari
al'amuran da ke cikinsu,wurare da muhallin da ake gina su, har ma da irin
dangantakar da ke a tsakanin adabi da kuma falsafa ta fuskoki daban-daban.
BABI NA BIYAR
NAƊEWA
5.1 SHIMFIƊA
A kowanne irin al'amari dole a samu farko da
kuma ƙarshe, wannan babin a kodayaushe shi ke
tattare duk wasu bayanai da binciken ya ƙunsa waje
guda, domin ya samu kammaluwa ta hanyar taƙaitawa da
kuma irin muhimman shawarwari daga bakin mai gudanar da aikin da ma irin
sakamakon tambayoyin da binciken ya ɗauko bashin amsasu tun a farkon babin,
ko kuma gano gaskiyar hasashen da bincken yake ɗauke da
dakonsa, a taaice dai a wannan babi ake tattare tsaki da tsakuwa tare da nannaɗe tabarmar
nazarin wuri guda domin a kaucewa wuce gona da iri a aikin binciken, wannan
dalili ya sa ake yiwa babin laƙabi da kammalwa
ko naɗewa.
5.2 TAƘAITAWA
Wannan bincike an gina shi bisa tsarin babi-babi
har guda biyar. Babi na ɗaya ya yi ƙoƙarin
fito da manufofi da kuma dalilan wannan bincike a kan tunanin Bahaushe game da
tatsuniyoyi da wasannani, haka kuma ya amsa hasashen binciken ta hanyar lura da
yadda binciken ya iyakance farfajiyarsa, sannan kuma a babin ne aka zayyano
irin muhimmancin da binciken yake da shi, ya zo duk a babi na ɗaya.
Babi na biyu kuwa ya ƙunshi
waiwayen ne kan ayyukan da suka gabata, kuma babin ya kasu gida-gida. Yayin da
binciken ya zo yin bitar ayyukan da suka gabata, ya yi la’akari da muhimman
kalmomi da suka shafi aikin baki ɗaya. Waiwayen ayyukan da suka gabata
ya taɓo jiga-jigan
kalmomin da suka haɗu suka samar da batun. Wato babin na biyu ya
waiwayi wasu ayyuka da suka yi magana a kan Hausa da Hausawa da kuma ƙasar
Hausa, baya da haka babin ya yi waiwayen ayyukan da aka gudanar akan falsafa da
kuma tunani, babin na biyu ya yi bitar wasu ayyuka a kan Wasanni da
Tatsuniyoyi. Bita a kan falsafa ta taɓo wasu batutuwa a kan
adabi a Hausa, yayin da wasu ayyukan suka yi maganar falsafar a Musulunci.
Waiwaye ya yi tsokaci a kan falsafar Afirka da na mafalsafa a Yammacin duniya.
Shi kuwa babi na uku ya yi tsokaci a kan
hanyoyin tattara bayanai, inda bayanai suka samu ta hanyar manya da kuma ƙananan
hanyoyi. Babin ya yi tsokaci a kan ginshiƙin hanayar
tattara bayani (babbar hanya) da kuma sauran hanyoyi tattara bayanai.
Binciken
ya yi hira da mutane daban-daban a wurare da dama. Mutanen da binciken ya gana
da su malamai na jami’a da na addini da maza da mata da matasa da tsofaffi.
Bugaggun littafai da kundaye da maƙalu da
intanet sun taimaka wajen samun bayanai.
Babi na huɗu ya nazarci
falsafar Bahaushe ne a littafin tatsuniyoyi da wasanni wato muhimman rassan
adabin baka na Hausa. Babin ya gwama tunanin da yake cikin ɓangarorin na adabin
baka na Hausa da wasu bayanai da bincike ya samo a wuraren da ya ziyarta. Lura
da yanayin tunanin/falsafar da abin da wasu bayanai a rubuce suka ce sun
taimaka wajen warware bayanai a babi na huɗu. Inda aka
gano tunanin Bahaushe a cikin tatsuniyoyi da wasanni ya gauraye gurare da dama,
amma hikimomi game da al'amuran rayuwa da zamantakewa shi ne abu na kusa-kusa
da ya fi zuwa ran jama’a idan aka yi zancen tunanin nasu. Muhalli da lokaci da
kuma taurari suna da alaƙa da irin
abubuwan da ake gina tunani kansu cikin waɗannan ɓangarori.
Wasu daga cikin rukunin Hausawa da aka yi hira da su sun ce, tunanin Bahaushe a
wannan gaɓar yana
tafiiya ne da fata da kuma burin zamantowar ƴaƴansa
mutumen kirki masu tarbiyya.
Babi
na huɗu ya ƙarfafa
nazari cikin wasu tatsuniyoyi da wasannin na cikin littattafan, kuma ya kawo
ingantattun bayanai masu ɗauke da misalai game da tunanin da
yake cikinsu kama daga kan muhallin, taurarin da kuma sauran al'amuran da aka
gina su akai.
Binciken
ya yi nazari akan tunanin Bahaushe kamar yadda al’ummomi da yawa na Afirka da
sauran sassan duniya suke da irin wannan tunani. Bahaushe yana harkokinsa na
yau da kullum, kuma adabin baka na Hausa ya nuna tatsuniya tana da tasirin
gaske ga al’amuran da suke gudana yau da kullum. Babi na huɗu ya yi
tsokaci a kan yadda adabin baka na Hausa yake da dangantaka da tunani/falsafa.
Babin
ya yi tsokaci a kan dangantakarsu ta fuskar ma'anarsu, rabe-rabensu, samuwarsu,
har ma da bunƙasarsu, musamman yadda suke da muhimmanci a
rayuwar Hausawa. Duk da haka babin bai tsaya nan ba sai da ya taɓo
dangantakarsu da fuskar ilimi.
5.3
SAKAMAKON BINCIKE
Wannan bincike an gudanar da shi ne a kan adabin
baka, ɓangaren ƙagaggun labaran
zube da kuma wasanni, a inda aka nazarci falsafar Bahaushe da ke cikin waɗannan ɓangarori a littafin Tatsuniyoyi da Wasanni... na Ibrahim Yaro Yahaya.
Tunani na da matuƙar tasiri ga
rayuwar al’umma
musamman saboda sauƙin aiwatar da kyakkyawar rayuwa. Bahaushe na amfani da tunani a duka
al'amuransa kama daga maganganu na yau da kullum da waƙa da ƙagaggen labari na
zube da kuma wasanninsa, ta yadda za a iya sarrafa harshe a zaɓi kalmomi masu ma’ana da suka dace da saƙon da ake son a isar ga al’umma.
Binciken ya tallafi kansa da wasu misalai daga
wasu tatsunitoyi domin dukkansu wasu ginshiƙai ne a wajen
samun falsafar rayuwa, musamman dokoki da rayuwar iyali da ilmi da kuma
zamantakewa baki ɗaya
(Kirk-Greene, 1973:3). Waƙa ta agaza wa
binciken da wasu misalai, kasancewar tana adana falsafar al’umma baya ga
kasancewarta makarantar da ke koya nagarta da hikimomin rayuwa ga al’umma a
gargajiyance (Ahmad, S.B. 1997:13). Dalilan da suka sa aka kawo misalai daga
wasu tatsuniyoyin a wasu wurare cikin wannan bincike sun haɗa da: dukan
su dai abu ɗaya ne dake ƙunshe
da wasu saƙonni da Bahaushe ke da manufar isarwa ga
al’umma kamar yadda (ƙaraye, 1995:184) ya
tsakuro amfanin adabin baka daga (Malinowski, 1971:19) inda yake adana tunani
da al’adu da kuma faɗakar da mutum game da rayuwa.
Wannan binciken ya tabbatar da akwai tunani da falsafa
a cikin littafin Tatsuniyoyi da wasanni--domin kuwa an fito da irin hikimomin
da Bahaushen ya yi amfani da shi, wato tunanin da ya sanya a wurare daba-daban.
Binciken ya
gano cewa an yi amfani da hikimar zaɓar taurari
wajen gina labarin kowacce irin tatsuniya daidai yadda saƙon zai fito fili a fahimce shi. Wannan dalilin yasa tatsuniyar Bahaushe
ko da yaushe ke gauraye da nau'ikan halittu daban-daban tun daga mutane,
dabbobi a wajen abinda ya shafi tsoratarwa kamar micizai, dodanni, kura. Ko kuma
ƙwari, har ma da
halittun da ƙirƙirarsu yake bisa kyakkyawan tunani, don ya zama mai
armashi da kuma sauƙin ganewa. Su kuwa wasanni na ɗauke da
hikimar aiwatarwa ta hanyar amfani da jinsin da abin ya shafa, ko kuma adadin ƙimar shekarun masu aiwatarwa, wato dai a ɓangaren wasanni Bahaushe kan yi amfani da wannan karin maganar da ke cewa
"kowacce ƙwarya da abokin
burminta".
Binciken ya
gano cewa hikimar ba ta tsaya kan iya taurari ba, domin kuwa duk wasu al'amura
da suka shafi rayuwarsa ya kan tsara hikima ta musamman ya juya ta ko ya gina
ta hanyar amfani da yadda yake a zahiri da kuma amfani da muhallin da ya dace
da tsarin tatsuniyar ko wasan, domin cimma manufar da burin da ya sa shi yin
ta, kamar abinda ya shafi rayuwar aure, maƙwabtaka, amana, gaskiya, cima ta abinci da sutura da sauransu.
Wani babban al'amari da binciken ya gano shi ne
Bahaushe na amfani da sanya waƙa cikin dukka waɗannan ɓangarori domin saurin karɓuwar abin,
kasancewar masu sauraron tatsuniyar galibi yara ne, waƙa za ta yin tasiri wajen saurin jawo hankulansu zuwa ga fahimtar
muhimmancin abin, haka kuma wasanninsa kaf na ɗauke da waƙe-waƙe da ke taimakawa masu aiwatarwa wajen sanya su
nishaɗi a junansu da ƙara musu ƙaimi wajen ɗarsuwar saƙonnin da waƙar ke ɗauke da shi
cikin zuƙatansu, idan an
dubi duka tatsuniyoyin da wasannin da aka nazarta babu wadda babu waƙa a cikinta, wannan ita ma wata hikima ce cikin ɗumbin hikimomin malam Bahaushe a wannan ɓangaren.
Wani babban al'amari da binciken ya ƙara gano wa shi ne, Bahaushe na sanya waɗannan hikimomin ne da tunani domin inganta tarbiyyar yara da kyautata
rayuwarsu, ta hanyar nusar da su abubwa masu kyau da kuma marasa kyau, wannan
yasa ake kiran waɗannan ɓangarori da makararanta ce ta farko a gurin ƴaƴan Hausawa, domin
duka suna aukuwa ne ta irin hanyar da ake aiwatar da makarantu a yanzu. Don
haka tun kafin haɗuwarsa da baƙin al'ummu ya ke da tsarin karantarwarsa.
Wannan bincike ya kai ga fahimtar ko gano cewa
Wasannin gargajiya da tatsuniyoyi suna da matuƙar amfani musamman ta ɓangaren
motsa jiki da kuma kaifafa tunani, wannan yasa galibi ƴaƴan Hausawa ke
tasowa da hazaƙa da kaifin basira,
sannan kuma ga ƙarfafa danƙon zumunci a tsakanin yaran ta yadda akan samu shaƙuwa mai ƙarfi har akai ga matakin tsufa, wata shaƙuwar ma mutuwa kaɗai ke iya raba ta.
Binciken ya fahimci cewa falsafar da Bahaushe ya riƙa cusawa cikin adabinsa ta yi tasiri matuƙa da kuma kasancewa abar al'fahari ka duk wani
Bahaushe, domin kuwa duk irin abubuwan da yake fata game da ƴaƴansa ya samu, a iya cewa kusan duk inda ake ambaton tarbiyya da
kyakkaywar mu'amala da zamntakewar rayuwa to al'ummar Hausawa ce kan gaba, don
haka wannan nasara ce babba.
Babban abinda binciken ya fahimta game wannan
al'amari shi ne, Bahaushe na so da kuma fatan ganin ƴaƴansa sun zama na
gari,Alhaji Ɗahiru Musa Jahun
yana cewa:
"Yaro kamar makaho ne,
Shi babba ai majayi ne,
Don haka neyasa shi ƙirƙirar irin waɗannan muhimman hanyoyin domin fatan ganin al'ummarsa ta kasance ta gari.
5.4 SHAWARWARI
A fage na shawarwari lallai ko shakka babu
wannan binciken an samar da wasu muhimman bayanai da za su taimaka wa al’umma.
Wannan
bincike na ƙalubalantar al’umma musamman a irin wannan
zamani da ilimi ya yawaita, a da lokacin da ilimin bai yawaita ba, al’umma sun
riƙa amfani da tatsuniya musamman ta kallon wasu
halayen taurari, suka riƙa koyar da ‘ya’yansu kuma
aka sami nagartaciyar al’umma, saɓanin yanzu.
Saboda haka ya kamata waɗannan halaye na taurari a tatsuniya su
zama darasi ga al’umma.
Manazarta sun gudanar da bincike-bincike a
Hausa a fagage daban-daban, an wallafa littafai da ƙamusoshi da
kundayen digiri masu yawan gaske da Hausa ko a kan Hausa. Yawancin manazarta
sun bibiyi Hausa ta fuskar nazarin harshe da adabi da kuma al’adu. A iya cewa
har yanzu manazarta ba su yi barci ba, duk da yake wasu suna ƙorafin
kamar an bar Hausa a baya. Domin an gudanar da bincike-bincike na falsafa da
sauran sassan ilmi a wasu harsunan Nijeriya da Afirka, amma ba a gudanar da
irinsu a Hausa ba. Wannan ba zai sanya a ce nazarin Hausa yana baya-baya ba,
sai daɗa bunƙasa
da yake yi a ƙarni na ashirin da ɗaya. Hausa
tana gogayya da manyan harsunan duniya a fagage daban-daban, tana gaba a
harsunan Afirka, tana sahun gaba idan ana batun harsuna da ake yaɗa labaru da
rubutu a ciki da wajen Afirka. Hausawa da masu sha’awar Hausa suna ƙoƙarin
ganin Hausa ta ci gaba da gwagwarmaya kamar yadda ta saba.
Tabbas wannan bincike yana ba manazarta Hausa
shawara su daɗa zage dantse
wajen cigaba da nazartar rassan adabi, domin tantance ɗimbin basirar
Hausawa. Idan ɗalibai da
manazarta Hausa suka ƙara ƙaimi
a wannan ƙarni, babu shakka za su daɗa faɗaɗa bincike a
kan falsafa ta fuskoki daban-daban. Nan gaba kaɗan za su ƙara
tabbatar da dangantakar da take tsakanin adabi da harshe da ta harshe da adabi
ko ta adabi da duniya da ta duniya da adabi, ko dangantakar adabi da fasihi da
ta fasihi da adabi, da ta adabi da makaranci da ta makaranci da adabi da kuma
dangantakar adabi da sauran matanoni da ta sauran matanoni da adabi. Idan
manazarta adabin Hausa za su ƙara jurewa a
irin wannan bincike, babu makawa Ilmi zai ƙara inganta,
basira za ta ƙara bunƙasa, kuma ana
fata rayuwa za ta ƙara inganci.
Irin waɗannan bincike-bincike
da makamantansu za su ƙara ƙarfafa
gwiwar ɗalibai da
mahukunta, su ƙara kutsawa fagen tunanin al’umma domin su gano yanayin harshe da adabi da kuma
dangantakarsu da falsafa. Zuzzurfan tunani ruhin duk wani nazari ne ko rayuwa
baki ɗaya, musamman
idan aka ƙara lura da dangantakar falsafar da adabin da
komai na rayuwa, baya ga martabar Hausa a Afirka ta Yamma da duniya baki ɗaya.Idan
manazarta za su ƙara zage damtse a fagen tunani, da yadda yake
da tasiri a cikin adabin Bahaushe. Ɗalibai da
masu sha’awar Hausa za su ƙara gane al’adun Hausawa fiye da yadda aka fahimci Hausa a jiya da
shekaranjiya. Idan manazarta suka karkato da nazari ta wannan fuska, za a ci
gaba da sake sabunta fahimtar yadda za a nazarci adabin al’umma domin tafiya da wannan zamani.
Akwai buƙatar Idan
jami’o’i da sassan nazarin harsuna da al’adu za su ci gaba da ƙalubalantar ɗalibai su riƙa
ɗaukar waɗansu
kwasa-kwasai da suka shafi tunanin Bahaushe, wannan wata hanya ce da za ta ƙara
ƙarfafa gwiwar ɗalibai da
tunaninsu a kan rayuwar, da yadda za su kwatanta adabin (yin bincike) za su
dubi tunanin ta fuskoki daban-daban. Wannan bincike yana ba masu sha’awar faɗaɗa bincike a
kan falsafa shawara, suna iya yin nazarin falsafa dangane da rayuwar Bahaushe, ba
tare da sun danganta aikinsu da adabin baka na Hausa ba ko rubutaccen adabin
Hausa ba. Nazarin falsafar Bahaushe zai iya taƙaita kansa a
al’adunsu ko kuma a yi nazarin tunanin ta
la’akari da Harshensu na yau da kullum.
Idan kuma ana da bukata za a iya ƙara yin
nazarin daga wani ɓangare na adabi kamar yadda wannan bincike ya
gudana.
Haka kuma wannan bincike yana bayar da shawara
ga manazarta da su yi nazari a kan tunanin Bahaushe game da rassan na adabi.
Bincike yana bayar da shawara ga masu bincike na gaba su ɗora daga inda
wannan ya tsaya, musamman abin da ya shafi sauran dangogin tatsunya, kamar su
hikaya almara da sauransu. Bugu da ƙari masu
bincike za su iya nazartar sauye-sauyen da tunanin Bahaushe ya samu a yau, game
da tatsuniyoyi da kuma wasannin da ake ƙirira a
aiwatar a wannan zamani.
5.5 KAMMALAWA
Wannan
bincike ya yi ƙoƙarin amsa hasashen
da binciken ya yi, kuma ya tabbatar da manufa da kuma dalilan bincike, inda
adabi da al’ada suka yi wa binciken tasirin gaske. Saboda da yawan mutane suna
ganin Hausawa ba su yi fice a falsafa irin yadda wasu al’ummomi suka sanu ba a
duniya, sai dai hikimarsu da adabinsu na baka ya adana akwai falsafa mai yawa a
ciki tun daga al’amuransu na gargajiya da kuma sauyin da baƙin
al’adu suka haifar wa rayuwarsu. Adabin baka na Hausa ya zama tsanin hango
tunanin Bahaushe a wannan bincike, kuma tatsuniya da sauran nau’o’in adabin
baka na Hausa sun cancanci a kafa hujja da su yayin da aka nazarci tunanin
al’umma. Dalilin da ya sanya haka kuwa shi ne, salon da adabi ya ƙunsa
shi ne yake warware jigon adabi, jigo kuma tunani ne da fasihi ya yi game da
yanayin kusan komai na al’ummarsa; a zamantakewarsa, ko wani abu da yake aukuwa
a cikinta, Tunani na da yalwatattun ɓangarori a Hausa, wadda kan iya zama
kan rayuwarsu da muhallinsu da kuma harshensu kamar yadda misali ya bayyana a
babi na huɗu. Don haka
wannan binciken ya zaƙulo ire-iren waɗannan
hikimomi na Bahaush cikin waɗannan muhimman ɓangarori na
adabin baka (Tatsuniyoyi da wasanni).
MANAZARTA
Abraham, R.C. (1977). Dictionary of the Hausa Language.
London: Hodder and Stoughton.
Abdurrahman,
M.S. (1983). Nazari a kan Tatsuniyoyin
Hausa da na Nupanci. Kundin Neman Digiri na Farko. Sakkwato: Sashen Koyar Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Abdurrahman, M. (2006). Nazari a kan Sababbin ƙagaggun
Labarun Almara na Hausa.Kundin Neman Digiri Na Farko. Zariya: Sashen
Harsunan Nijeriya Da na Afirika, Jami’ar Ahmadu Bello.
Adamu, J.S. (2010). Hikayar Mafari da Ire-irenta a
Al’ummar Hausawa. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Ahmad,
R. (2010). Kwatancin Tatsuniyar Hausawa da ta Fulani. Kundin Neman
Digiri Na Farko. Zariya: Sashen Harsuna Da Al’adun Afirka, Jami’ar Ahmadu
Bello.
Ahmad, Sakina Adamu, (2016) Tunanin Bahaushe a wajen zaɓen ƙwari
a matsayin Magani a cikin The Hausa people Language and History: past,
present and future. Kaduna: DNLL, Kaduna State University and Garkuwa
publishing.
Ahmad, S.B. (1997).
Narrator as Interpreter: Stability and Variation in Hausa Tales.Rudiger
Koppe Verlag Koln.
Ahura, T. (2008). Egalitarian Ethos in Tiv Folktales.
In G.G. Darah (ed.), Radical Essays on Nigerian Literatures. Abraka: Department
of English and Literary Studies, Delta State University, MalthousePress
Limited.
Alhassan, H. da wasu (1982). Zaman Hausawa (Bugu na
biyu). Lagos: Islamic Publication Bureau.
Aliyu A. H. (1978). Abokin Hira 1. Zaria: Northern
Nigerian Publishing Company.
Al-Ghazzali,(1095M) Tahfati al-falsafa. Baghdad .
Alhawani,(1962) Falsafatu al-islamiyya.
Ajayi, J.F A&Crowder, M.(1974&1976) History of
west africa. Volume two.
Londo: longman Group limited.
Amin, N. (2010). Littattafan Tatsuniyoyi Na Hausa Na
Frank Edg. Muhimmancinsa Wajen Adana Al’adun Hausawa. A cikin Dundaye No,
3, Vol 1. Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu Xanfodiyo.
Aminu, M. (1977). Tatsuniyoyi Dominku. Kano:
Mainasara Publisher.
Amin,M.L (2007) Gudunmawar Dr. Mamman Shata katsina.
Amin,M.L (2004) Falsafar Bahaushe a kan rayuwar Ɗan'adam
cikin Algaita king Journal of Hausa Studies; No: 3 Vol. I Kano:
Department of Nigerian Languages, Bayero University.
Ayuba, A. (2018) Bigire a tuananin Bahaushe.
Kundin digiri na uku a jami'ar Ahmadu Bello, Zaria.
Balarabe, H. (2001). The Relevance of Teaching Folk-Narrative
(Tatsuniya) In Modern Hausa Society. In Faki, A.U. (ed.), Huda-Huda, No. 1,
Vol. I Kano: Federal College of Education.
Baro, T.J. (2003). Nazarin Tatsuniya, Kundin Neman
Digiri na Farko, Sashen Harsunan Nijeriya Da na Afirika, Jami’ar Ahmadu Bello.
Bello, M. (2004). Jigogin Gargaɗi a Cikin
Tatsuniyoyin Hausa. Kundin Neman Digiri na Farko. Sakkwato: Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Xanfodiyo.
Bargery, G.P. (1934). A Hausa-English Dictionary and
English-Hausa. and is Vocalary. London: Oxford University Press.
Bichi, A.Y. (1995). Hausa Folkgenres. In Rufa’I, et
al (ed.), Harsunan Nijeriya, vol xvii, CSNL. Kano: Bayero University.
Bichi, A.Y. (1979). Cultural Reflection in Hausa
Folklore. In Yahaya, I.Y. (ed.), Harsunan Nijeriya, Vol. ix, CSNL. Kano:
Bayero University.
Dembo,U.(1971) Wasannin yara. zaria: Northan
publishing company.
Dumfawa, (1986), Falsafar Malanta.
Ɗangambo, A. (2008) Rabe-raben
Adabin Hausa da muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. kano: Amana publishers.
Bichi, A.Y. (2002/2003). A Brief History of Hausa Folklore
Scholarship. In Bchi, A.Y.(ed.), Harsunan Nijeriya, Vol. xx, CSNL. Kano: Bayer University.
Bichi, A.Y. (2008). The Type and Motif-Index of Hausa
Folktale. In Bichi, A.Y. (ed.), Harsunan Nijeriya, Vol xxi, CSNL. Kano: Bayero
University. Narrative A Case Study of Hausa Tatsuniya. Unpublished M.A. Thesis.
Kano: Bayero University.
Chamo, Y.I. (2008). Mataki da Hanyoyin Nazarin
Tatsuniya. A cikin Gusau, S.M. (ed.), Algaita No.5 vol. i. Journal of
Current Research in Hausa Studies. Kano: Jami’ar Bayero.
CNHN (2006). Ƙamusun Hausa
Jami’ar Bayero. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya.
Xangambo, A. (1978). Dangantakar Labarun Gargajiya da
Al’umma, First International Conference on Hausa Language, Literature and
Culture. Kano: Bayero University.
Xangambo, A. (1984). Rabe-raben Adabin Hausa da
Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph Publication Company.
Xangambo, A. (2008). Rabe-Raben Adabin Hausa (Sabon
Tasri). Zaria: Amana Publishers Limited.
Edgar, F. (1911). Littafin Tatsuniyoyin Hausa Littafi
na Biyu. London: Frank Cass.
Fatima, Y. (2002). Tatsuniya: The Art of Story Telling
in the Hausa Society. B.A in Literature. Zaria: Department of English,
A.B.U.
Finnegan, R. (1970). Oral Literature in Africa.
London: Oxford University.
Furniss, G. (1996). Prose, Poetry and Popular Culture
in Hausa. London:Edingburg University Press
Garba, S.A. (2013). Media and Folklore: Hausa Folktale
on the Radio. Kano: Bayero University. (Paper Presented at International
Conference Kano).
Galadanci, M.K.M. da Wasu (1993). Hausa Don ƙananan
Makarantun Sakandare, littafi Na 3. Lagos: Animo Press.
Gusau, S.M. (1986). Tatsuniya: Sigoginta da
Muhimmancinta a Adabin Baka na Hausa. Sakkwato: Kwalejin Ilimi, Maru. (Muƙala
wadda ba a buga ba).
Gusau, S.M. (2000). Tatsuniya a Rubuce: Nazarin Sigogi da
Hikimomi da Tasirin Tatsuniya, Kano: Gidan Dabino.
Gusau, S.M. (2006). Tatsuniya (Gatana): Sigoginta da
Hikimominta. A cikin Gusau, S.M. (ed.), Algaita No.4, vol. 1. Kano: Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Hassan, S. (2014). Trickster in Folktale: a
Comparative Analysis between Hausa Bura/Babur. Kano: Bayero University,
(Paper Presented at Kano).
Hayward, W. F. (n.d). Folklore: Trickster Stories
Across Time-From African Ancestors to African American Rappers.
Junaidu, I. da ‘Yar’aduwa, T.M. (2007). Harshe Da Adabin
Hausa A Kammale. Ibadan: Spectrum Book Limited.
Ƙaraye, M. (1979). Structural
Characteristic of the Gizo in Hausa Folktales, Unpublished M.A. Thesis. University
of Khartoum.
Ƙaraye, M. (1982). The
Structural Study of African Oral Narrative: Evidence from Hausa. In Yahaya,
I.Y. (ed.), Harsunan Nijeriya, xii, CSNL. Kano, Bayero University
Ƙaraye, M. (1997). Trends
and Issues in Development Theories and the Place of Folklore in National Development.
In Rufa’i, A. (ed.), Harsuna Nijeriya xviii CSNL. Kano: Bayero University.
Ƙaraye, M. (2001). Gizo:
A Structural Approach to the Interpretation of the Trickster in Hausa Folktales.
In Bichi, A.Y. (ed.), Harsunan Nijeriya, xix, CSNL. Kano: Bayero University.
Ƙaraye, M. (n.d). The
Trickster in Folklore and Folklore Scholarship. Kano: Bayero University
(Paper Presented at Kano).
Labaran, S.M. (2005). Waƙoƙin
Cikin Tatsuniya: Nazari Kan Muhallan Da Masu Rera su, Kundin Nemasn Digiri
Na Farko. Sakkwato: Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Mukhtar, I. (2002). Jagoran Nazarin ƙagaggun
Labarai (Tsari na Biyu). Kano: Benchmark Publisher Ltd.
Muhammad, M.S.C. (2008.) Hauka A Idon Bahaushe Unpublished
M.AThesis. Sakkwato: Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usman
Xanfodiyo.
N.I.N.L, (2011). Basic Linguistics for Nigerian
Languages, Ore, Yusuf (ed.).
Aba: Shebiotimo Publications.
Nasir, I. (2009). Gabatar Da Katun Na Hausa a Kan
Tatsuniyar Gizo da ɓaure, Unpublished
M.A. Thesis. Kano: Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
NNPC (1968). Labaru Na Da Da Na Yanzu. Zariya:
Northern Nigerian Publishing Company.Pinto, C.F. (n.d). The Animal Trickster-An
Essential Character in African Tales. Portugal: School of Education Polytechnic
Institute.
Rattray, R.S. (1969). Hausa Folk-lore, Customs,
Proverbs, etc. Vol.1, & II London: Oxford University Press.
Rufa’i, A. (1982). Huce Haushin Talaka Kan Basarake
Misalai Daga Wasu Tatsuniyoyi. A cikin Yahaya, I.Y. (ed.), Harsunan
Nijeriya, xii, CSNL. Kano: Bayero University.
Serekoane, B.B. (1996). Trick, Trickster Characters
and Trickster Tales in Tswana Folktales, Unpublished M.A. Degree Rand
Afrikaans University.
S.N.E.R.D.C and H.S.A.N, (1990). Hausa Metalanguage D.
Muhammed (ed.), vol. i. Ibadan: University Press.
Shimizu, K. and Agabi, B.A (1975). Jukun Oral
Literature: An Introduction and a Tale.In Yahaya, I.Y. (ed.), Harsunan
Nijeriya VoL.v, CSNL. Kano: Bayero Unive College.
Skinner, A.N. (1980). An Anthology of Hausa Literature.
Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.
Smith, J. (2005). African and Native American
Trickster Folktale. Yahoo
Umar, M.B. (1987). Dangantakar Adabin Baka da Al’adun
Gargajiya. Kano: Triumph, Tofa Commercial Press.
Usman A K. (2014). Symbol of Entertainment and
Education: Appraising the Binary Function of Gizo, the Trickster in
Selected Hausa Folktales Kano: Bayero University. (Paper Presented at Kano).
Usman, A.S. (2000). Women in Hausa Folktales. In
Bunza A.M. (ed.), Hausa Studies vol. II No. 2. Sokoto: Usman Danfodiyo University.
Usman, B. (2005). Taskar Tatsuniyoyi, Littafi Na (1-6). Kano: Gidan Dabino Publisher.
Usman, H. (2002). Tatsuniya a Matsayin Tubalin Wasan
Kwaikwayo: Nazari Kan Wasannin Kwaikwayon Hausawa, Kundin Neman Digiri Na Farko.
Zariya: Sashen Harsunan Nijeriya Da na Afirika, Jami’ar Ahmadu Bello.
Uthman, A. N. (1996). Representation of the Status and
Role of Women in Hausa Folktales, Unpublished M.A. Thesis. Zaria:
Department of English, A.B.U.
Wushishi, B.J. (1998). Adabin Baka: Sigoginsa Da
Hikimominsa,
Unpublished M.A Thesis. Kano: Sashen Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero.
Yahaya, I.Y. (1971). Tatsuniyoyi da Wasanni Na (1-6).
Zariya: Oxford University, Press.
Yahaya, I.Y. (1972). The Style and Content of a Hausa
Tale. In Muhd (ed.), HarsunanNijeriya, Vol. ii, CSNL. Kano: Abdullahi
Bayero College, Ahmadu Bello University.
Yahaya, I.Y. (1974). Labaru Gargajiya Na (1-2). Ibadan:
University Press.
Yahaya, I.Y (1979). Hausa Folklore as an Educational
Tool. In Yahaya I.Y. (ed.),Harsunan Nijeriya No. ix, CSNL. Kano: Jami’ar
Bayero.
Yahaya, I.Y. (1979). Oral Art and the Sociolization
Process: A Socio-Folklore Perspective of Initiation from Childhood to Adult
Hausa Community Life Ph.D Thesis, Vol. 1. Zaria: Ahmadu Bello University.
Yahaya, I.Y. (1991). Nazarin Tsari Da Hikimomin
Kacici-kacicin Hausa. A cikin Harsunan Nijeriya Vol. xv, CSNL. Kano: Bayero
University.
Yahaya, I.Y. da Wasu (2001). Darusan Hausa 1. Ibadan:
University Pres.
Yahaya, I.Y. da Xangambo, A. (1986). Jagoran Nazarin
Hausa. Zariya: Northern Nigerian Publishing Company.
RATAYE (1)
JERIN WAƊANDA AKA
TATTAUNA DA SU
Farfesa
S'idu Muhammad Gusau |
Gidansa na rijiyar zaki da kano |
15/06/2022 23/06/2022 29/08/2022 12/02/2023 |
Da dare |
Farfesa
Bashir Aliyu Sallau |
A cikin jami'ar Sule Lamiɗo K/Hausa |
03/04/2023 |
11:45 Am |
Farfesa
Abduladir Ɗangambo |
Gidansa da
ke rijiyar zaki kano |
17/06/2022 |
7:30pm |
Farfesa
Aliyu Umar B/kudu |
A Gidansa |
20/05/2023 |
8:00pm |
Farfesa
Ahmad Yusuf |
|
09/12/2022 |
3:48pm |
Dr. Mu'azu
Sa'adu kudan |
A Jami'ar Sule Lamiɗo,
ofishinsa |
06/02/2023 |
1:13pm |
Dr. Salisu
Garba Karki |
Tattaunawa
ta yanar gizo |
02/03/2023 |
4:37pm |
Dr. Sani
(Abu ubaida), BUK |
Tattaunawa
ta yanar gizo |
23/01/2023 05/04/2023 |
7:00pm 10:19pm |
Farfesa I.G
Satatima |
A ofishin
H.O.D languages jami'ar Sule lamiɗo |
08/03/2023 |
12:00pm |
Hajiya
Uwani |
Tsangayar
Damau B/kudu |
07/05/2023 |
02:56pm |
Mama Amarya |
A Gidanta |
22/04/2023 |
4:00pm |
Yusuf
Mukhtar |
A Jami'ar
Sule Lamiɗo K/Hausa |
04/01/2022 25/6/2022 11/01/2023 03/04/2023 |
9:15Am 12:17pm 3:00pm 5:40pm |
Rabi'u Arma |
A Jami'ar
Sule Lamiɗo K/Hausa |
03/ 03/2023 17/04/2023 |
10:30Am 2:35pm |
Malam Shehu |
A gidansa
Masaya |
14/05/2023 |
6:04pm |
Hauwa'u
Asheer |
gidansu
B/kudu |
04/05/2023 |
9:08Am |
RATAYE (2)
JERIN TATSUNIYOYI DA WASANNIN DA AKA NAZARTA
TATSUNIYAR
GIZO DA ƁAURE
Ga ta nan ga ta nan
ku.
Wata rana ne dai wani sarki yana zance a zuci,
yana cewa, ‘Gonata ta ɓaure ta yi kyau. ɓauren yanzu
duk ya nuna. Gara in sami wani ya je ya tsinke mini duk ɓauren, kar in
bar shi ya ruɓe a banza.
Amma fa wanda zai tsinke ɓauren ba zai sha ba ko da ɗaya ma. Idan
ya gama bai sha ba, zan ba shi.’yata tare da gararta baki ɗaya’.Shi ke
nan. Kashegari sai sarki ya sa duk a yi shela a gaya wa mutanen gari sarki yana
kiransu a ƙofar fada. Mutane suka taru a qofar gidan
sarki. Sai sarki ya ce, dama ba wani abu ya sa na yi kiran ku ba. Gonar ɓaurena ce
nake so a tsinke min, amma ba za a sha ko ɓaure ɗaya ba. Sai
dai zan ba wanda ya tsinke xin ladan tsinkewar. Watau zan ba shi ‘yata da
gararta baki ɗaya’. Sai
kowa ya ce ba zai iya ba, domin ɓauren ya cika kyau, ga kuma ƙanshi
da zaqi.Ba wanda zai iya ba tare da ya sha ba. Can, sai Gizo ya zo ya ce wa
sarki ‘Zan iya’. Shi ken an, sai sarki ya ce, ‘To. gobe ka yi shiri ka tafi’.
Da gari ya waye, sai Gizo ya ɗura ruwa a
jallo, ya ɗauki madubi
da kuma tsinkensa na sakace. Ya je gonar sarki ya kama tsinkar ɓaure.In yana
cikin yi mutane suka zo suka ce, ‘Gizo barka da aiki’; sai ya tsiri tofar da
yau, yana cewa, ‘Tuf! Kai wannan vaure! Ko warinsa ba na so’.Idan sun wuce, sai
ya ci gaba da tsinkar ɓauren, yana sha yana zubo wani a ƙasa.
Shi ke nan, ashe bai sani ba, wata ‘yar tsuntsuwa tana kallon sa.
Da ya gama tsinkar vauren tas. Ya sauko zai
tafi gida, sai ya ɗauko jallon ruwansa ya kurkure bakinsa, ya ɗauko madubin
nan da tsinken sakace, duk ya ciccire ɓauren da ya maƙale
masa a haqorinsa. Bakinsa ya yi tas, kamar bai ci kome ba. Sai sarki ya aiko
mutane don su debi ɓauren da Gizo ya tsinke. Suka zo suka sami
Gizo suka ce, ‘Sannu da aiki Gizo’.Ya ce, ‘Yauwa’ Suka ce, ‘Har ka gama?’Sai ya
ce, ’I. Amma da ƙyar na gama. Kamar na yi amai, saboda warin
vauren nan. Warin duk ya cika mini ciki’.Sai suka zuzzuba ɓauren a
buhunhuna suka tafi suka kai wa sarki.Da suka je gida, sarki ya tambaye su
labarin Gizo da tsinkar ɓaure.Suka ce, ‘Ai, yallavai, Gizo bai
sha ɓauren ba,
domin mun ga muna zobawa a buhu yana tofad da yau. Kuma da muka ce da shi, ‘Me
ya sa kake zubad da yau?’ Sai ya ce warin ɓauren ne ya
cika masa ciki.’ Sun gama faɗin haka ke nan, sai ga Gizo ya zo
gidan sarki.Sarki ya ce da shi, ‘To, Gizo Ka yi aiki mai kyau, Sai kuma ka je
gida ka gyaggyara, za a kawo amarya da gararta’. Shi ke nan Gizo ya je gida ya
gyaggyara sarai.
Aka ɗauko amarya da gara
aka zo da ita gidan Gizo.Kafin ‘yan ɗaukar amarya su tafi gida, sai suka ji
tsuntsuwa tana waqa tana cewa:
‘Kai Gizo,
kai Gizo,
A can ka ci ɓaurenka,
Har ka
kurkure bakinka,
Har ka manto
jallonka…’
Tana ta faɗar haka har
sai da mutanen suka ce, ‘kai, ku tsaya mu ji abin da tsuntsuwar can take faɗa.’Sai Gizo
ya ce da su, ‘kai, ku rabu da ita don Allah, shirmenta take yi.’ Sai mutanen
suka ce, ‘Wane irin a rabu da ita? Kai! Mu tsaya mu ji.’Shi ke nan, sai ‘yan
kawo gara da amarya suka ji tana cewa:
‘Kai Gizo,
kai Gizo,
A can ka ci ɓaurenka,
Har ka
kurkure bakinka,
Har ka manto
jallonka…’
Sai suka ce ‘La’ila!
Ashe dama ka ci ɓaurenka ce ba
ka ci ba?’ Sai suka yi ta surutu da hayaniya. Shi ke nan. Sai suka mayar da
amarya da gararta gida suka gaya wa sarki abin da ya faru. Kurunƙus.
An ciro wannan tatsuniya daga littafin
Tatsuniyoyi Da Wasanni na ɗaya (Yahaya 1971:1).
TATSUNIYAR ƊAN SARKI YA
ZAMA MACIJI
GA TA NAN GA TA NAN
wani
mutum ne dai yana da matans uku, ya fi son biyu daga cikinsu, ɗaya
ba ya son ta sosai, sai ta zamo bora a gidan.
To shi dai wannan mutumin ba shi da da ɗa
ko ɗaya, ya damu saboda rashin ƴaƴa. Ana nan ana nan, ran nan sai ya sayo wa
matansa guda biyu maganin haihuwa. Sai bai sayo wa bora ba.sai bora ta bari sai
da suka jiƙa suka
sha suka bar saura har ya sane sannan suka kai juji suka zubar, sannan ta bi ta
ɗebo ta wanke da ruwa ta jiƙa
sannan ta sha. Allah da ikonsa sai matan mutuminnan sua samu ciki baki ɗaya
har da borar.
A kwana a tashi sai ran nan suka haihu rana ɗaya
kuma duk matan suka haihu rana ɗaya kuma
duk mata suka haifa, da aka kwana bakwai, watau ranar suna, sai mijinsu ya yi
wa ƴaƴan matan da yake so suna amma ya ƙi yiwa ƴar
bora suna. sai bora ta ɗinga bin sa a gindi a
gindi don ya yi wa ƴarta
suna amma ya ƙi, da ya
fusata sai yasakawayarinyar suna gwi-da -yara.
Shikenan yara suna nan suna girma tare, duk
lokacin da ya tshi yiwa ƴaƴan ɗinki sai
ya yi ban da ƴar bora,
ga tsangwamar matan gida da suke yi mata ita da mahaifiyarta.
A kwana a tashi yara suka girma har suka isa
aure gaba ɗaya, da babansu ya ya tashi yi musu aure sai ya zaɓarwa
ƴaƴan nana biyu mazaje kyawawa ya aura musu, ita
kuwa gwi-da-yara ya tafi da ita jeji cikin surƙuƙin dokar
daji ya haɗa tada wani miciji ya ce da ita "kinbi wannan micijin, in ki
ka ƙi , Allah
ya tsine miki". sai ta ce, "to ba zan ƙi binsa ba baba".
Sai mutumin nan ya tafi gida yan cike da farin
ciki, haka suka yi ta murna shi da matan nan guda biyu, ita kuwa bora ba ta ce
komai ba ta kuma kula da abinda suke yi ba.
A can daji kuwa yarinyar nan sai ta bi micijin
nan duk inda ya shiga sai ta bishida macijin nan ya ga ta bi umarnin babanta
sai ya ce " ba za ki ji tsorona ba" sa ta ce "A 'a ba zan ji
tsoronka ba".
Daga nan sai ya hau jikin yarinyar ya ƙadandane a jikinta , ya sauƙa ya kanannaɗe
a ƙasa ya
fasa kansa, amma duk abinda yake ba ta tsorata ba, da micijin nan ya ga haka,
sai ya ɗauke ta ya haɗiye ta,
ya mai da ita fara , ya fito da ita ya dube ta ya ce "kai ba haka nake son
ki ba" sai ya ƙara
haɗiyeta ya ƙara
haɗiyeta, y mai da ta ja zur, kyakkyawa, ga kyan gashi, ta zama ta
kai haka. " ita kuma yarinyar duk haɗiyar da
micijin nan ya yi mata ba ta ji tsoransa ba ko kaɗan.
Amma kuma al'amarin can gidan su yarinyar ya ɓaci.
kishiyoyin uawarta suna ta tsangwamarta , ita kuwa ba ta cewa komai. ashe dai
macijin nan ba mutum ba ne wani ɗan sarki
ne wanda taɓa neman aure a garinsu ya rasa shine wani malami yace sai ya zama
maciji ya shiga daji za haɗu da
matar aure, shi dalilin da yasa ya dawo daji ya zama maciji.
Bayan da macijin ya mai da yarinyar yadda yake
so sai ya zama mutum , ta ba shi duk labarin abinda ya faru har aka kawota
daji, da irin iyayyar da ake musu ita da uwarta a gidan," sai ya ce to ba
komai rufe idonki" da ta rufe idon bayan ta buɗe
sai gata a wata babbar alƙarya
suna tafiya mtane na ta kallonsu suna cewa " la kunga ɗan
sarki da wata kyakkyawar yarinya, wa ye kuma ya bashi ita?"
Da suka je gida dgga isarsu wurin babansu
yanyi murna sosai , ya kwashe duk labarin a ya faru ya bashi, sarke ya ce
"to Allah ya bada zaman lafiya' daa nan ya sa aka gina gidan zinariya da
benaye ɗan sarki ya zauna tare da matarsa bayan anyi ƙasaitaccen biki.
A can gidan iyayenta kuwa ran nana mijinsu a
shiraya domin kai wa ƴaƴansa ziyara gidajensu, da ya tashi sai ya
fara zuaea gidan ɗaya daga cikinsu ya tarar tayi miya da ɓera
a gidan aka zuba masa ya ci ya rage guntu ya ce ya kai gida aga irn abinda ta
ke ci, haka ita ma gian ɗayar ya
tarar ta girka tuwon dusa miyar ɗata nana
ma ya ci ya rage guntu domin kai wa uwarta irin abincin da take ci.
Bayan ya bar gidan ɗayan
ya kama hanya ,yana cikin tafiya sai ya tarar da wata rijiya wasu ƴan mata na ɗiban
ruwa sai ya ce musu sannunku ɗan mata suka
cenyawwa sannu sai ya ce don Allah ƴam
mata ba kwa sam min ruwan nan na sha ba, sai suka ce tab a kwanan gwi-da -yaran
zamu baka ruwa ka sha dk bakinka gaje-gaje da shi, sai mutumin ya yi shitu, can
kuma sai ya ce "ƴammata
don Allah wa ce ce kuma gwi-da -yara", sai suka harare shi suka rabu da
shi, ashe gwi-da yara na jin duk gardamar da suke yi sai gta leƙo ta taga sai ta gani ashe babanta ne, sai ta
kirawo wata daga cikin yaran ta ta ce a kawo tshohon gindin tagar gidan. sai a
ka kawo shi, garin kallon ginin gidan yau har jiƙa rigarsa ya yi bai sani ba. Da ta ga haka sai ta ji bai kamata ya
shiga gidan surukansa a haka ba sai ta jefa masa malun-malun da babbar riga ta
taga. da ganin rigar sai ya kama ta da kokawa kici-kici, sai ta ce da shi
" baba gidan surukanka ne fa" danya sa kayan sai ta s aka shigar da
shi gidan suka fashe da kuka baki ɗaya, ta
kwashe duka labarin da ya faru tsakaninsa da macijinnan ta bashi, sai ya yi
mamaki sosai, tasa aka shirya masa shifiɗa a soro
aka kawo masa abinci ya ci, can sai mai mijin nata ya dawo ya wuce bai san
wanene ba , sai da gwi-da-yara tanyi masa bayani ya sake komawa har ƙasa ya gaida shi,sai da ya kwana uku a
gidanta kana aka haɗa masa tara taarziƙi ya taho gida akan doki.
D isarsa
gida matansa suka taryeshi da murna ya ɗauko
tsarabar kowacce da ya samo daga gidan arta ya basu, sa'annan ya sa aka kirawo
bora itama aka bata tsarabar da ƴarta
ta byar, mamaki duka ya rufe su, daga nana sai boranta fashe da kuka, su kuma
sauran suka yi yaji.
D a aka dawo da su sai suka ce su basu yarda
ba, sai an aikawa ƴaƴansu sun zo dukansu. dukkannin ƴaƴan
kowa ya zo har da gwi-da-yara da ka rakota akan dawakai, aka shiga da tsarabra
da ta zo da ita gidan,sauranma duka suka zo da tsarabarsu, aka rarraba
kayayyakin da suka kawo harda na gwi-da -yara. sai suka saki baki galala suna
kallonta.
Daga ƙarshe
gabaki ɗaya suka shiga jeji saboda baƙin ciki, su kuwa suka cigaba da zamansu lafiya.
Ƙurunƙus.
TATSUNIYAR NA-GOMA
GA TA NAN GA TA NAN KU!
To !
Wani mutum ne dai da ya ‘ya ‘yansa guda goma,
kowane lokaci yana zuwa daji yana yin harbi yana kama tsuntsuye. Shi ke nan
kullum ya je kamun tsuntsaye daji sai ya kama tsuntsu ɗaya, shi ke
nan duk lokacin da ya dawo daga daji wajen harbi, idan ya ajiye tsuntsun sai a
sami wani daga cikin yaran nan na mutumin sai ya ɗauke
tsuntsunwar nan da babansu ya kamo daga harbi ya je yacinye shi ka]ai.
Shi ke nan sai mutumin nan ya zo yana neman
tsutsun sai ya tarar babu, shi ke snan sai mutumin ya zo yana neman tsutsuwar
yana ta fa]a, babu wanda ya kula shi a cikin yaran, shi ke nan sai mutumin ya
ce to shi ke nan ai na san maganin wanda ya cinye mini tsuntsu, idan gobe ta yi
za mu je kogi kowa sai ya shiga ciki ya yi ranstuwa ba shi ne ya cinye
tsuntsuwa ba.
Shi ke nan sai ya kwashi ‘ya’yansa gaba ɗaya suka tafi
bakin kogi, don ana so a gane wanda yake ɗauke tsuntsuwar
baban. Shi ke nan suna zuwa bakin kogi sai aka ce na farko ya fara shiga, da ya
shiga sai ya fara waƙa da cewa:
Ni na fari, ni na fari,
ni na ci tsuntsun Babaye,
Ruwa tafi da
ni,
Kar ka dawo
da ni.
Shi ke nan sai ruwa ya kawo mishi zuwa tafin-ƙafa,
shi ke nan sai aka ce ya fito ba shi ba ne. Shi ke nan sai aka ce na biyu shi
kuma ya shiga, shi ma sai ya shiga ya fara waƙa :
Ni na biyu, ni na biyu,
In ni na ci tsuntsun Babaye,
Ruwa tafi da ni,
Kar ka dawo da ni.
Shi ke nan sai ruwa ya kawo mishi iya
idon-sawu , shi ma sai ka ce ya fito ba shi ba ne. shi ke nan sai aka ce na uku
shi kuma ya shiga, sai shi ma ya shiga, sai ya fara waƙa :
Ni na uku, ni na uku,
In ni na ci tsuntsun Babaye,
Ruwa tafi da ni,
Kar ka dawo da ni.
Shi ke nan sai ruwa ya kawo mishi daidai iya ƙwabri
, shi ma sai ka ce ya fito ba shi ba ne. shi ke nan sai aka ce na huɗu shi kuma ya
shiga, sai shi ma ya shiga, sai ya fara waƙa :
Ni na huɗu, ni na huɗu,
In ni na ci tsuntsun Babaye,
Ruwa tafi da ni,
Kar ka dawo da ni.
Shi
ke nan sai ruwa ya kawo mishi daidai iya gwiwa , shi ma sai aka ce ya fito ba
shi ba ne. Shi ke nan sai aka ce na biyar shi kuma ya shiga, sai shi ma ya
shiga, sai ya fara waka,
Ni na biyar, ni na biyar,
In ni na ci tsuntsun Babaye,
Ruwa tafi da ni,
Kar ka dawo da ni.
Shi
ke nan sai kogi ya kawo mishi daidai iya cinya , shi ma sai aka ce ya fito ba
shi ba ne. Shi ke nan sai aka ce na shida shi kuma ya shiga, sai shi ma ya
shiga, sai ya fara waƙa :
Ni na shida, ni na shida,
In ni na ci tsuntsun Babaye,
Ruwa tafi da ni,
Kar ka dawo da ni.
Shi ke nan sai ruwa ya kawo mishi daidai iya
kwankwaso , shi ma sai aka ce ya fito ba shi ba ne. Shi ke nan har aka zo kan
na goma sai aka ce shi kuma ya shiga, sai shi ma ya shiga, sai ya fara waƙa
:
Ni Na-goma, ni Na-goma,
In ni na ci tsuntsun Babaye,
Ruwa tafi da ni,
Kar ka dawo da ni.
Shi ke nan sai ruwa ya haɗiye shi ya
tafi da shi ‘yan uwan na kallo, sai suna ta kukan rashin an’uwansu ruwa ya tafi
da shi.
Shi ke nan ana cikin haka har sai Na-goma ya
kawo gidan wata dodanniya a cikin ruwa, sai dodanniyar nan ta ɗauki Na-goma
ta kai shi gidanta, shi ke nan ana nan ana nan sai bayan ya kwana biyu sai
dodanniya ta ce to ba zan cinye ka ba, amma zan mai da kai ka zama yarona, shi
ke nan sai Na-goma ya ce to shi ke nan kowace ranar kasuwa sai dodanniya ta riƙa
ɗora ma
Na-goma tallar ƙosai yana kai mata kasuwa yana talla.Shi ke
nan rannan Na-goma ya kawo tallar ƙosai kasuwa
sai kawai ‘yan ‘uwansa suka gamu, suna ganin Na-goma sai suka ce kana ina, shi
ke nan sai ya ce ai yanzu dodanniya ce mamanshi, ita ce ma ta ɗora masa
talla yanzu, ku zo mu je gidannmu, shi ke nan sai suka kama hanya har gidan
dodanniya, shi ke nan sai dodanniya ta ce idan za ku tafi da Na-goma sai kun
kawo mini abinci iri-iri. Shi ke nan sai suka koma gida suka kawo mata buhu na
hatsi iri-irisai dodanniya ta ce haka cikin waƙa :
Kai ! Na-goma
Kai ! Na-goma
Ba ci na ba !
Ba ci na ba !
Na goma
Ba ci na ba !
Shi ke nan sai suka koma gida suka sake shi,
to a wannan karo sai suka ]auko kayan abinci irin wanda suka dace da dodanniya,
sai suka taho da buhu-buhu na }udaje da kyankyasai da tsutsotsi da kwa]i da
sauran duk wani abncin }azanta, sai da aka kawo ma dodanniya. Shi ke nan suna
kawo mata kayan abincin sai ta mi}e ta na wa}a :
Ga ci na nan !
Na-goma,
Ga ci na nan
!
Ga sha na nan
!
Na-goma,
Ga sha na nan
!
Madalla dai !
Na-goma,
Madalla dai !
ɗau wandonka !
Na-goma,
ɗau wandonka !
Sa rigarka !
Na-goma !
Sa rigarka !
Na-goma.
Sai wata rana
Na-goma
Sai wata rana.
Shi ke nan sai
Na-goma ya biyo ‘yan uwansa suka dawo gida, daga ranna bai ƙara
ƙaukar wani abu wanda ba nashi ba.
ƙurungus.
WASANNIN KA-CICI-KA-CICI
Wasan ne da yara kan taru da yawa, ɗaya yana sako
tambaya sauran kuma na amsawa ɗaya bayan ɗaya, misali:
Kande: Ƙulunƙulufita?
Garba: Gauta.
Kande: Shirin ba ci
ba?
Sima: Baba.
Kande: Faifaina ɗinkin marido?
Dudu: zuma.
Kande: Kuntukurun ɓarin ɓas?
Garba: Gidan
tururuwa.
Kande: Tshohuwar
gidanmu kullum za su fita sai sun raba mana
goro?
Dudu: Kashin awaki.
Kande: Kututture uku
gagara ɗauri?
Garba: Ƙwai.
Kande: Shanuna
dubu-dubu maɗaurinsu ɗaya?
Ziza: Tsintsiya.
Kande: Iya ta zaga,
Baba ya zaga, ba su haɗu ba?
Ilu: Kunne.
Kande: Gya ɗaya dama
duniya.
Sima: Farin wata.
Kande: Kogina ya kai
ya kawo sai a gefe na ke wanka?
Garba: Fate-fate.
Kande: Kogina ya kai
ya kawo babu maai tsallake shi sai
Bello mai ɗan warki?
Dudu: Kwaɗo.
Kande: Na je jeji,
jeji na yi mini dariya?
Ilu: Auduga.
Kande: Rub-rub kushewar
bayi?
Ziza: Ƙaiƙayi.
Kande: Na wanke ƙwaryata
tas tas na je maka da madina na
dawo ba ta bushe ba ?
Sima: Hancin kare.
Kande: Ɗan
baka a bayan suri?
Garba: Farce.
Kande: Abu ɗil ya sa mai
gari kuka?
Dudu: Abu ɗil sauko da
sarki daga kan doki?
Ziza: Fitsari.
Kande: Ke wannan
shegiyar da kika tsefe kanki wa zai yi miki kitso?
Ilu: Bishiya.
Kande: Daga nesa na
jiwo muryar ƙawata?
Sima: Ganga.
Kande: Abu siriri,
abu zarara, abu tubkar Allah?
Garba: Gashi.
Kande: Tsumagiyar kan
hanya fyaɗe yaro fyaɗe babba?
Ziza: Yunwa.
Kande: Ɗillin
bar ɗillin, ɗillin , ɗillin na
kallon ki?
Ilu: Kaza bari tono,
shaho na kallon ki.
Kande: Yadda ɗillin ta kan
yi ɗillin haka ma
ɗillinbya kan
yi
ya kan yi ɗillin.
Sima: Yadda ta kan yi
ƙwan nan, haka ma ƙwan nan ya
kan yi
kaza.
Kande: Ƴar
baƙa jakar mata?
Garba: Kujera.
Kande: Samarin
gidanmu masu fararen kawuna?
Ziza: Taɓare.
Kande: Kurkucif
kucif?
Ilu: Kwanciyar kare.
Kande: Gwanda lili da
liyo?
Sima: Gwanda noma da
awo.
WASANNIN ƁATA