Kundin neman digiri na farko (b.a. Hausa) a ƙarƙashin sashen nazarin harsuna da al’adu, jimi’ar tarayya gusau, jihar zamfara, nigeria, 2023
Nazarin Rayuwar Malam Aliyu Ɗanbaba (Aliyu Sha'iri) Da Waƙoƙinsa
NA
SAMIR AMINU MUSA
08109474995
AMINCEWA
An amince da wannan kundin binciken na Samir Aminu Musa (1710104013) a kan cewa, ya cika duk ƙa‘idojin kammalawa da aka shimfiɗa dangane da neman takardar kammala digiri na farko (B.A. HAUSA) a sahen Nazarin Harsuna da Al‘adu, Jami‘ar Gwamnatin Tarayya Gusau.
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan aiki zuwa ga kakata
Malama Rahamatu Abdullahi, da kakana Malam Musa Langaye. Ina roƙon
Allah jiƙan sa da rahma, ita kuma ya sa ta gama da
duniya lafiya. Amin.
TSAKURE
Wannan bincike da aka
gabatar ya ƙunshi wani ƙwarya-ƙwaryar
nazari kan rayuwar Malam Aliyu Ɗanbaba (Aliyu
Sha'iri) da waƙoƙinsa tun daga
haihuwarsa da tasowarsa da neman iliminsa da kuma rasuwarsa, shirya waƙoƙinsa,
da kuma sharhin wasu daga cikin waƙoƙinsa.
GODIYA
Haƙiƙa
dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda bai haifa ba, kuma ba a haife
sa ba. Tsira da aminci su ƙara tabbata
zuwa ga mafificin halittu cika makin Annabawa Annabi Muhammad (S.A.W), da
iyalan gidansa da Sahabbansa da waɗanda suka bi su da kyautatawa har zuwa
ranar sakamako.
Ina miƙa
godiya ta musamman ga jagoran wannan aiki Dr. Musa Fadama Gummi, bisa irin ƙoƙari
da jajircewa da ya yi a kan ganin cewar wannan aiki ya sami kammaluwa. Ba
kammaluwa kaɗai ba ya
tsaya tsayin daka domin aikin ya sami inganci da ake buƙata. Allah
saka masa da mafificin alkairi.
Bayan haka, ina miƙa
godiya ta musamman ga ɗaukacin malaman jami'ar tarayya Gusau
musamman waɗanda suke a
sashen koyar da harsuna da al'adu. Ina jinjina da ban girma gare su bisa irin
namijin ƙoƙari da suka
yi na ganin mu ɗalibansu mun
samu ilimi haɗe da tarbiyya
wadda take sahihiya. Malaman sashen koyar da harsuna da al'adu waɗanda na zuƙo
daga mashayar iliminsu su ne: Dr. Adamu Rabi'u Bakura wanda yake shi ne
shugaban sashe, Dr. Musa Fadama Gummi, Malam Aliyu Rabi'u Ɗangulbi,
Malam Isah S Fada, Malam Musa Abdullahi Zariya, Malam Bashir Abdullahi, Malam
Abu-Ubaida Sani, Malama Halima Kurawa, Malam, Muhammad Arabi Umar. Allah saka
masu da mafificin alkairi.
Haka kuma, ina miƙa
godiya ga manyan jigajigan malamammu da suke ziyartar mu daga manyan jami'o'i
waɗanda su ma
suna da kaso mai yawa da alhaki a kan mu malaman su ne: Farfesa Aliyu Muhammad
Bunza wanda yake shi ne shugaban sashe na biyu bayan shugaba na farko Farfesa
Ahmed Haliru Amfani, Farfesa Ahmad Atiku Dumfawa, Farfesa Muhammed Abdulhameed Ɗantumɓushi, Farfesa
Salisu Ahmed Yakasai, Dr. Nazir Abbas. Daga jami'ar Usumanu ɗan Fadiyo.
Sai kuma malamammu daga jami'ar Ahmadu Bello Zariya su ne: Farfesa Magaji Tsoho
Yakawada, Farfesa Muhammad Lawal Amin, Farfesa Balarabe Abdullahi, Dr.Muhammad
Tahir, Allah saka masu da mafificin alkairi.
Ina kuma miƙa
godiya ga mahaifana (Alhaji Aminu Musa Yasuf da Hajiya Faɗimatu Musa)
bisa ɗawainiyoyinsu
da suka yi a kai na tun daga haihuwata har zuwa yau. Ba su kasa ba wajen ba ni
gudunmuwa da abin hannunsu da addu'o'i dare da rana ina roƙon Allah saka
masu da mafificin alkairi.
Ina miƙa
godiya zuwa ga kakannina Alhaji Musa, Hajiya A'ishatu Allah gafarta mata, da
Hajiya Amina. Haka kuma ina miƙa godiya ga
yayyena Mukhashinu Aminu Musa, Marwanatu Aminu Musa, ƙannena Samira
Aminu Musa, Musa Aminu Musa, Abubakar Aminu Musa Hafizu Aminu Musa, Muhammad
Aminu Musa A'isha Aminu Musa. Fauziyya Aminu Musa.
Ina miƙa
godiya ga abokaina kamar Aminu Rabi'u, Sirajo Umar, Abdullahi Abdullahi (Ɗan
Samu). Haka kuma ina godiya ga malamaina na gida Malam Umar Abbas, Malam, Malam
Hamza Abubakar Dr. Sirajo Musa, Liman Saluhu Imam, Malam Jamilu Bello, da sauransu.
Har wa yau ina godiya
ga abokanan karatuna da muka sha gwagwarmayar karatu tare irin su:
Alhaji Biliya
Abubakar shugaban aji kuma mantor nawa, Sani Adamu (Dr.) Sabitu Sani (kwaleji)
Babangida Ahmad Barau (Kagara), Ibrahim Muhammad (Gummi) Muhammad Yahaya
(Darawa), Mustapha Ibrahim (Ɗan malam),
Isma'il Aminu Adam (Abuja) Hajiya Ruƙayya Yusuf S
Fada, Zainab (Maman Prof). Allah saka wa kowa da mafificin alkairi ya sa mana
albarka amin.
KUNSIYA
Take -- --i
Amincewa-- ii
Godiya-- iii
Sadaukarwa-- --iv
Tsakure-- v
Kumshiya-- vi
Babi Na Ɗaya
Gabatarwa
1.0 Shimfiɗa -- 1
1.1 Manufar Bincike --
--1
1.2 Hasashen Bincike-- --2
1.3 Farfajiyar
Bincike -- --2
1.4 Matsalolin
Bincike-- --3
1.5 Muhimmacin
Bincike-- -3
1.6 Hanyoyin Gudanar
Da Bincike-- 4
1.7 Naɗewa-- 5
Babi Na Biyu
Bitar Ayyukan da Suka Gabata
2.0 Shimfiɗa-- 6
2.1 Bitar ayyukan da
Suka Gabata-- 6
2.2 Hujjar Cigaba Da
Bincike-- -10
2.3 Naɗewa-- 11
Babi Na
Uku
Fashin Baƙi A kan Ma’anonin
Da Suka Shafi Tubalan Bincike
3.0 Shimfiɗa-- 12
3.1 Ma’anar Waƙa-- --12
3.2 Ire-Iren Waƙa-- --13
3.3 Rubutacciyar Waƙa
-- -14
3.4 Tsarin
Rubutacciyar Waƙa -- 18
3.5.0 Hanyoyin
Nazarin Rubutacciyar Waƙa ---25
3.5.1 Tarihin Marubuci: -- -25
3.5.2 Ma’aunin Waƙa -- --25
3.5.3 Mabuɗin Waƙa:
-- --26
3.5.4 Jigo: -- -28
3.5.5 Warwarar Jigo: -- --30
3.5.6 Salo da Sarrafa -- --30
3.5.6 Zubi da Tsari: -- --30
3.5.7.1 Salon Karin
Magana-- -33
3.5.7.2 Salon Hoto
Cikin Bayani-- 34
3.5.7.3.1 Kamancen Fifiko-- -35
3.5.7.3.2 Kamancen
Daidaito-- -35
3.5.7.3.3 Salon
Kamance-- -35
3.5.7.3.4 Kamancen Kashi Ko Kasuwa----36
3.5.7.4 Salon Jinsantarwa-- 37
3.5.7.4.1 Mutuntawa -- --37
3.5.7.4.2 Dabbantarwa -- --37
3.5.7.4.3 Abuntarwa-- --38
3.5.7.5 Salon Kambamawa-- -39
3.6 Naɗewa-- 39
Babi Na Huɗu
Nazarin Rayuwar Malam Aliyu (Ɗanbaba Aliyu Sha’iri) Da Waƙoƙinsa
4.01 Shimfiɗa-- 40
4.1 Taƙaitaccen Tarihin
Malam Aliyu Ɗanbaba---40
4.1.1 Haihuwarsa-- -42
4.1.2 Ƙurciyarsa da
Tasowarsa da Neman Iliminsa--42
4.1.3 Yaransa -- 43
4.1.4 Yawace-yawacensa-- 44
4.1.5 Shirya Waƙoƙinsa-- -44
4.1.6. Rasuwarsa-- --47
4.1.7
Matsayin Aliyu Ɗanbaba A
Tsakanin Marubuta Waƙoƙin Da da na
Yanzu--
--48
4.2.1 Koyon Waƙarsa --
--48
4.2.2 Nau’o’in Waƙoƙinsa -- -48
4.2.3 Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa-- 52
4.2.4 Zubi Da Tsarin Waƙoƙinsa-- 53
4.2.5 Jigon Waƙoƙinsa-- --58
4.2.6 Warwarar Jigon Waƙoƙinsa-- 58
4.2.7 Salon Sarrafa Harshe-- -61
4.3.1 Nazarin Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa ---62
4.3.2 Waƙar Yabon
Islahuddini--
63
4.3.3 Nazarin Waƙar Yabon Liman Aliyu---70
4.3.4 Nazarin Waƙar Bulaliya -- 74
4.3.5. Naɗewa-- 79
Babi
Na Biyar
Sakamakon Bincike
5.0. Shimfiɗa --
--66
5.1
Sakamakon Bincike -- 66
5.2
Shawarwari -- --68
5.3.Naɗewa-- --69
Manazarta-- -71
Babi Na Ɗaya
Gabatarwa
2.0 Shimfiɗa
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Maɗaukakin
sarki, wanda a cikin ikonsa ne da iyawarsa da baiwarsa ya halicci ɗan Adam har
ya ba shi hankali, da harshe da hazaƙa. Tsira da
aminci su ƙara tabbata ga mafificin halitta da hikima
Annabi Muhammad (S.A.W). A wannan babin za a kawo manufar bincike da hasashen
bincike da matsalolinsa. Haka za a bayyana muhimmancinsa da hanyoyin da za a bi
wajen aiwatar da binciken daga ƙarshe a zo da
naɗewa.
1.1 Manufar
Bincike
Manufar wannan bincike ita ce samar da wani
kundi da zai ƙunshi nazari a kan rayuwar malam Aliyu Ɗanbaba
(Aliyu sha’iri) da waƙoƙinsa
tare da fito da jigogin waƙoƙin
da salailansu domin a haɓaka adabin Hausa.
Nazari a kan marubuta
waƙoƙin Hausa abu
ne da aka daɗe ana yin sa
ko kafin a yi wannan nazarin amma an ce “kowane bakin wuta da nasa hayaƙi”
kasancewar wannan marubuci ba a samu wani aiki da aka yi a kansa ba wannan ya ƙara
ba mu ƙwarin guiwa wajen yin nazarin rayuwar malam
Aliyu sha’iri da kuma waƙoƙinsa
gwargwadon abin da Allah ya ba da ikon yi. Bayan haka tabbas manufar wannan
bincike ita ce taimakawa wajen raya adabin Hausa, da kuma bar wa na baya tarihi
da abin koyi da ƙara ƙarfafa su don
su tashi tsaye tsayin daka domin ganin an ci gaba da raya wannan adabi na
Hausa.
1.2 Hasashen
Bincike
An yi hasashen cewa, idan wannan aiki ya samu
kammaluwa zai taimaka wajen raya harshen Hausa don haka ya sa muka zaɓi rubuta
kundinmu game da nazarin malam Aliyu sha’iri da waƙoƙinsa.
Domin waƙoƙin Hausa na
da muhimmanci ƙwarai ga rayuwar Hausawa. Waƙa
ta baka ko rubutatta, kamar yadda aka sani tun ba yau ba, ita ce hanya mafi sauƙi
da ake bi wajen isar da saƙo ga jama’a.
A ƙarshe, muna
hasashen bincikenmu zai ba mu damar cika ƙa’idojin
da aka shimfiɗa na neman
takardar shaidar digiri (B.A. Hausa) a sashen nazarin harsunan Najeriya a
Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau.
1.3 Farfajiyar
Bincike
Aikin binciken da za a gudanar ya shafi waƙoƙi
rubutacci ne na Hausa. Saboda haka za a yi nazari ne a kan malam Aliyu Ɗanbaba
(Aliyu sha’iri) da waƙoƙinsa
daga farko har zuwa ƙarshen aikin.
Haka kuma, aikin zai
tsaya a farfajiyar jigogi da salailai na waƙoƙinsa.
Haka kuma binciken zai zaƙulo yanayin
rayuwar malam Aliyu Sha’iri musamman yadda ya koyi waƙa da ire-iren
waƙoƙinsa.
1.4 Matsalolin
Bincike
Kamar yadda aka sani cewa babu wani aiki da za
a gudanar ba tare da an yi karo da matsaloli ba nan da can, musamman a kan
aikin bincike. Malam Aliyu Sha’iri ya yi fice a kan kawo cigaban addini da kuma
harshen Hausa ta fannin adabi rubutacce. Amma manazarta da masu bincike ko
nazari a kan harshen Hausa ba su mayar da hankali ba wajen bincike ko nazari a
kan malam Aliyu Sha’iri da waƙoƙinsa.
Kuma koda an yi ba su yi yawa ba. Wannan ya sa na ci karo da matsaloli
daban-daban a kan wannan binciken.
Ganin irin matsalolin da na fuskanta wajen
wannan bincike, ya ƙara ba ni ƙarfin
guiwa ganin cewa manazarta ba su yi yawa ba a wannan fagen bincike. Don haka
wannan aikin zai taimaka ma na tafe masu sha’awar nazari a akan malam Aliyu
Sha’iri da waƙoƙinsa.
1.5 Muhimmacin
Bincike
Muhimmancin bincike shi ne bayyana matsayi da
fasahar da ke akwai a cikin waƙoƙin
malam Aliyu Sha’iri, dangane da haka, waƙoƙin
malam Aliyu Sha’iri wani babban madubi ne na kallon
rayuwar Hausawa ta fuskar addini da rayuwa, sannan kuma idan Allah ya so waɗannan waƙoƙi
za su zama dalili na haɓakar adabin Hausa, da kuma taskace shi. Haka
kuma muhimmancin wannan bincike ya haɗa da yin sharhi game
da ma’ana a kan waƙoƙin
malam Aliyu Sha’iri a ƙasar Hausa.
1.6 Hanyoyin Gudanar Da Bincike
Hanyoyin da aka bi don gudanar da wannan
bincike su ne:-
Ganawar da aka yi da
iyalansa ido- da-ido kamar mai ɗakinsa malama Maimuna da ɗansa malam
Lawwali a garin Talata Mafara 10- 02- 2023 a gidan shi marigayi malam Aliyu
Sha’iri da ke garin Talata Mafara.
Sannan kuma an gana da wasu abokanan karatunsa
kamar Liman Sani a gidansa da ke garin Talata Mafara 22-02-2023. Alhaji Maidaga
a gidansa da ke garin Talata Mafara 15-02-2023. Haka zalika an gana da malam Naziru
a gidansa da ke garin Talata Mafara 15-3-2023. Da kuma malama Rabi'atu a gidan
malam Ibrahim mai Li'irabi da ke garin Talata Mafara 21-3-2023
1.7 Naɗewa
Wannnan babi wanda shi ne na farko a cikin
tsarin wannan aiki an kawo abubuwa da dama wanda suke su ne muhimman bayanai na
shimfiɗa. Da farko
an kawo gabatarwa da shimfiɗa, Manufar Bincike, Hasashen Bincike,
Farfajiyar Bincike, Matsalolin Bincike, Muhimmancin Bincike, Hanyoyin Gudanar
da Bincike da kuma Naɗewa.
Babi Na Biyu
Bitar Ayyukan da Suka Gabata
2.0
Shimfiɗa
Wannan babi wanda shi ne na biyu a cikin
tsarin wannan aiki za mu kawo abubuwa waɗanda suke su ne
muhimman bayanai kamar haka: shimfiɗa, bitar ayyukan da suka gabata, hujjar
cigaba da bincike, da kuma naɗewa.
2.1 Bitar ayyukan da Suka Gabata
Hausawa na cewa “waiwaye adon tafiya” duk
aikin za a yi, ya kamata a yi bitar ayyukan masana da manazarta da suke da alaƙa
da wannan aiki ko suka yi kama da shi, da nuna hanyar da suka bambanta da
wannan aiki. An nazarci kundaye, da litattafai. Ayyukan da aka nazarta waɗanda ke da
nasaba da wannan aiki su ne:
Kabiru (1982), a cikin kundin digirinsa na
farko, ya yi tsokaci ne a kan yadda ake nazarin rubutattun waƙoƙi,
a inda ya fara da kawo tarihin marubucin waƙa, da yadda
ake tsara waƙa har wa yau, ya ƙara da
bayyana irin salon sarrafa harshe da ake amfani da shi.
Kadage (1982), a cikin kundinsa na farko ya yi
tsokaci ne a kan bambancin da ke tsakanin waƙar baka da
rubutacciyar waƙa inda yake cewa “Waƙar
baka duk da yake waƙa duka waƙa
ce, amma duk da haka akwai waɗansu hanyoyi da akan bi domin a gane
wannan waƙa ta baka ce ko rubutacciya ce, waƙar
baka ita ce waƙar da ake rerawa da baka, kuma ba a fuskar
takarda take ba, ba a rubuce ba. Waƙar baka
tsohuwa ce domin kuwa tattare take da daɗaɗɗen tarihi na
halitta, wato ke nan tun da ɗan Adam ya fara furuci ya fara rera waƙa
da baki, amma ita kuwa rubutacciyar waƙa ta kasance
ita kanwa uwar gami a wajen waƙar baka. Saboda
haka ɗan Adam ya daɗe yana tsara
waƙa da ka, yana kuma rera ta da baki. Wannan
tarihi ya nuna cewa rubutaciyyar waƙa a Hausa ba
ta fi ƙarni biyu zuwa huɗu da samuwa
ba.”
Ikara (1983), a cikin kundin bincikensa ya
bayyana tarihin waƙa da jigo da zubi da
salon sarrafa harshe.
Yakawada (1987), ya yi bayanin salon sarrafa harshe a waƙoƙin Aliyu Namangi, haka kuma ya yi amfani da salon saɓi zarce ko kuma ɗinkin baiti, wato shi ne zarcewar jumla daga wani layi ko ɗango zuwa mai bi masa, ba tare da katsewar tunani ba. Misali a waƙar Infiraji ya bayyana yadda yake ɗinkin baiti kamar haka:
“Na taho Manzon ina gaishe ka,
Zaɓaɓɓen isasshe,
Kar ka bar sheiɗan ya ɓasshe ni don
Haka ko da yaushe,
Na tuna ka ba nai baƙin ciki ba.”
Haka kuma ya kalli
jigo da warwarar jigo da salon tsari da kuma salon sarrafa harshe tare da yin
amfani da adabin baka kamar su: karin magana, kirari, sannan ya ƙara
da adon harshe irinsu, mutuntawa, siffantawa, tamka, kwalliya da kuma ƙarangiya.
Hauwa (2011) a kundin bincikenta na digiri na
biyu ta yi aikinta ne a kan marubuta waƙoƙin
mata amma a kan wa’azi da kuma
irin gudunmuwar da mata suke bayarwa a rubutattun waƙoƙi.
Suleiman (2011), a kundin bincikensa na digiri
na biyu, ya kawo kwatancin rubutattun waƙoƙi
ne guda biyu na waɗansu mashahuran malamai waɗanda suka yi
rayuwa a lokuta mabambanta, malam Shi’itu Ɗan Abdurra’uf
ya yi rayuwarsa ne a ƙarni na sha tara (19
century) ya rubuta waƙa mai suna “Ajizi
Azimi” a in da ya bayyana ma’anarta
da cewa (Ƙwazon gajiyayye), sa’annan
Aliyu Namangi wanda ya rayu a cikin ƙarni na
Ashirin (20), ya kuma yi wata waƙa mai suna “Kanzil
Azimi” wadda ya ba ma’ana da cewa (Babbar
Taska). Wannan marubuci ya yi ƙoƙarin
kwatanta waɗannan waƙoƙi
guda biyu ta hanyar nuna, ko kuma fito da manufar kowanensu.
A’isha (2016) a cikin kundin bincikenta na
digiri na farko ta yi aikinta ne a kan shahararren marubucin waƙoƙin
nan Malam Ahmad Maƙari Da Waƙoƙinsa,
inda ta bayyana taƙaitaccen tarihinsa,
tun daga haihuwarsa
har zuwa tsufansa, an bayyana yadda yake tsara waƙoƙinsa
da jigogin waƙoƙinsa ta
fuskar sarrafa harshe.
Nura (2016) a kundin digirinsa na farko ya yi
aikinsa ne a kan Malam Ibrahim Bin Ahmad Kabara (Natsugunne) Da Waƙoƙinsa,
a nan ma an bayyana tarihin marubucin tun daga haihuwarsa har zuwa tsufansa,
kuma an bayyana yadda yake tsara waƙoƙinsa
da jigogin waƙoƙinsa da salon
waƙoƙinsa ta
fuskar sarrafa harshe daga ƙarshe aka yi
nazarin wasu daga cikin waƙoƙinsa.
Ibrahim (2019) a kundin bincikensa na digiri
na farko ya yi nazari ne a kan Malam Nasiru Kabara Da Waƙoƙinsa,
ya bayyana rayuwar Malam Nasiru Kabara tun daga haihuwarsa har zuwa tsufansa da
kuma irin gwagwarmayarsa, tare da bayyana yadda tsarin waƙoƙinsa
yake da kuma yin nazarin wasu daga cikin waƙoƙinsa
ta fuskar jigogin waƙoƙin
da salailansu.
Hussaini (2021), a cikin kundin bincikensa na
digiri na farko, ya yi aikin bincikensa ne a kan fasihin makaɗin nan ne
Alhaji Ɗan Balade Morai. An bayyana tarihinsa tun
daga haihuwarsa har zuwa mutuwarsa, da kuma yadda yake tsara waƙoƙinsa
da salon waƙoƙinsa, a ƙarshe
aka yi nazari a kan wasu daga cikin waƙoƙinsa.
Yahya (2001) a cikin littafinsa mai suna “Salo
Asirin Waƙa” a ciki ya yi
bayanin ma’anar salo a cikin waƙa.
Sannan kuma ya bayyana muhimmancin salo, bayan wannan kuma ya yi bayani a kan
sauran dabarun sarrafa harshe kamar jinsarwa, kamance, kinaya, zayyana da
makamantansu.
Bisa la’akari da ayyukan da suka gabata, na
kundaye har zuwa litattafai, za a samu cewa ba wani aiki da ya yi daidai da
nawa, saboda an yi wasu ayukka a akan wasu marubuta waƙoƙi
daban-daban. Don haka a nan za a yi nazari ne a kan rayuwar Malam Aliyu Sha’iri
da waƙoƙinsa.
Daga ƙarshe an dubi
waɗannan ayukka
ne domin a ga yadda magabata suka gudanar da bincike, da kuma abin da bincike
ya ƙunsa da irin hanyoyin da ya kamata mai
bincike ya bi da kuma kariyar harshe daga salwanta.
2.2 Hujjar
Cigaba Da Bincike
Za a cigaba
da wannan bincike ne sakamakon ba wani aiki da aka taɓa samu wanda
aka aiwatar a kan wannan marubuci Malam Aliyu Sha’iri. Bayan bitar ayyukan da
aka aiwatar masu alaƙa da irin wannan aiki
nawa.
Saboda haka idan
Allah ya so za a shiga cikin wannan aiki a aiwatar da shi gwargwardon abin da
Allah ya sawwaƙe.
2.3 Naɗewa
Wannan babi a cikinsa ne aka kawo bitar
ayyukan da suka gabata, a inda aka fara shi da shimfiɗa aka yi
tsokaci a kan wasu kundayen kammala karatu da litattafai na magabata, duk a
cikinsa ne aka kawo hujjar cigaba da wannan bincike, da kuma naɗewa.
Babi Na Uku
Fashin Baƙi A kan Ma’anonin Da Suka Shafi Tubalan Bincike
3.0
Shimfiɗa
A wannan babi za a kawo ma’anonin da suka
shafi taken bincike, waƙoƙin
da Malam Aliyu Sha’iri ya rubuta
na Hausa dukkaninsu rubutattu ne, don haka wannan babin zai garzaya wajen
masana don nemo ma’anar waƙa
ire-irenta haka kuma a fito da tsarin rubutacciyar waƙa, da kuma
hanyoyin da ake nazarin ta.
3.1 Ma’anar Waƙa
Waƙa ɗaya ce daga
cikin manyan rassan adabi, kuma fage ne da ya fi kowane fage farin jini a wajen
masana da manazarta. Wannan ya sa masana da manazarta kowa yake ƙoƙarin
tofa albarkacin bakinsa dangane da ma’anar waƙa. Ma’anar
waƙa daga bakin masana da manazarta a iya rubuta
manya-manyan litattafai masu tarin yawa ba tare da ƙure fagen ba,
don haka za mu taƙaita daga bakin masana kamar su:
A.B. Yahya {1991,sh.3} ya ce " Waƙa
tsararriyar maganar hikima ce da ake rerawa ba faɗa kurum ba,
wadda ke ƙunshe da wani saƙo a cikin zaɓaɓɓun kalmomi waɗanda aka auna
domin furucinsu ya yiwu ba tare da tuntuɓe ba."
M.B Umar a cikin Muhammad {2019,sh.1) ya ce
"Waƙa Bahaushiya ita ce, nau'in sarrafaffen
harshe da ake gabatarwa da shi ta sigar gunduwoyin zantuka da ake kira baitoci
ko ɗiyoyi waɗanda ake
ginawa a kan kari ƙayyadadde, kuma ake
rerawa da wani irin sautin murya na musamman."
Ɗangambo
{2008, sh.6} cewa ya yi “Waƙa wani saƙo
ne da ake gina shi kan tsararriyar ƙa’ida
ta baiti da ɗango da kari
{bahari} da amsa-amo {ƙafiya} da sauran ƙa’idojin
da suka shafi daidaita kalmomi da zaɓensu da amfani da su cikin sigogin da
ba lalle hakan suke a maganar baka ba.”
Sa'id, {2016, sh.xi} ya ce "Waƙar
Hausa wani fanni ne na hikimar tsara kalmomi masu rauji bisa ƙa'ida,
wanda yake kuma baiwa ce daga Allah."
3.2 Ire-Iren
Waƙa
Dangane da ire-iren waƙa kuwa,
masana sun kasa waƙa gida biyu wato waƙar
baka, da kuma waƙa rubutacciya. Daga cikin masanan da suka
karkasa ko kawo ire-iren waƙa akwai:-
Ɗangambo,{2007,
sh.5} ya ce "Ya kamata mu tuna cewa akwai waƙoƙi
iri biyu wato: Rubutacciyar waƙa da waƙar
baka wato waƙar makaɗa."
Sa'id, {2016, sh.xi} ya ce "Waƙar
Hausa iri biyu ce: akwai waƙar baka,
akwai kuma waƙa rubutacciya. Waƙar baka ba a
san ta da wasu tsayayyun ƙa'idoji ba,
amma ita rubutacciyar waƙa ana tsara
ta ne a bisa wasu shifiɗaɗɗun ƙa'idoji.
3.3 Rubutacciyar
Waƙa
Rubutacciyar waƙa ta Hausa ta
samo asali ne sakamakon cuɗanya ko zuwan Larabawa ƙasar
Hausa domin saye da sayarwa da kuma yaɗa addini. Dangane da
ma’anar rubutacciyar waƙa kuwa, wasu daga
cikin masana sun ba da ma’anoni da dama
daga cikin su akwai:
Mukhtar {2005,sh.2} ya ce "Rubutacciyar
waƙa wata hanya ce ta gabatar da wani saƙo
a cikin ƙayyadaddun kalmomi da aka zaɓa, waɗanda ake
rerawa a kan kari da ƙafiya a cikin
baitoci."
Sarɓi {2008,sh.1}, ya bayyana ma’anar
rubutacciyar waƙa da cewa “
Wani saƙo ne da aka gina shi cikin tsararriyar ƙa’ida
na baiti da ɗango da kari
da amsa-amo da sauran ƙa’idojin
da suka danganci daidaitattun kalmomi da zaɓarsu tare da
yin amfani da su a rubuce sannan a rera su lokacin da ake buƙata.”
Hiskett {1975}, da Sa'id {1978}
"Rubutacciyar waƙar Hausa ta samo
tsari ne na kai-tsaye daga waƙoƙin
Larabci, domin malaman Musulunci na Daular Usmaniyya su ne suka fara rubuta waƙoƙin
Hausa a bisa tsarin waƙoƙin
Larabci yadda za su ilmantar da al'umma addinin Musulunci cikin sauƙi,
su kuma sami damar karkatar da nunaninsu daga sha'awar waƙoƙin
hululu, su koma wa rera waƙoƙin
addini da wa'azi da faɗakarwa. Da ma kuma Hausa harshe ne da za a
iya auna kalmominsa a waƙe, kamar
yadda ake auna waƙoƙin
Larabci." Sa'id {2016, sh.xi}
Rubutacciyar waƙa hanya ce ta
isar da saƙo ga al’umma wadda
ake amfani da zaɓaɓɓun kalmomi
tare da amsa-amo {ƙafiya} da kuma amfani
da kari {bahari} don jan hankalin mai sauraro ko karantawa.
Dangane da tarihin samuwar rubutacciyar waƙa
a ƙasar Hausa kuwa, Ruƙayya {2008}
ta ruwaito Sa’adatu {2005}, ta ce “Tarihi
ya nuna an fara samun rubutattun waƙoƙin
Hausa tun a ƙarni na sha bakwai {17} A national archives
Kaduna, an samu waɗansu waƙoƙi
waɗanda ake
kyautata zaton a wannan ƙarnin na sha
bakwai {17} aka yi su cikin rubutun ajami, bayan zuwan Musulunci, daga cikin waƙoƙin
da aka samu akwai: Shi’ir Hausa, Jumiyyah waɗanda Shaikh
Ahmad Abdul Ƙadir Tofa ya yi su, sannan kuma akwai wata waƙa
mai suna ‘Sartse’
ta Malam Ali Abubakar Ƙutun Kura. Sannan
kuma akwai wasu waƙoƙi
guda uku waɗanda aka haɗe su aka ba
su suna ɗaya waƙar
Hausa.”
A cikin wannan ƙarni na sha
bakwai {17} ne aka samu wasu shahararrun malamai guda biyu waɗanda su ma
sun rubuta waƙoƙi na Hausa a
wannan ƙarni su ne: Wali Ɗan Marina,
Wali Ɗan Masani daga cikin ayukkan da Wali Ɗan
Marina ya yi akwai ‘Daliyya’ da
Nuriyya da waƙar Sharrin taba; haka kuma shi ma Wali Ɗan
Masani ya rubuta ‘Nafhatul-ambariyya’
da Sharhin Ishiriniyya alfazazi da sauransu.
A cikin ƙarni na sha
takwas {18} an sami cigaba da rubuta waƙoƙin
Hausa domin a wannan ƙarni ne aka sami
aikin su Malam Muhammad Alkatsinawi, da Malam Muhammad Birnin Gwari, da Malam
Shi’itu Ɗan Abdurra’uf,
wanda waɗannan malamai
sun rubuta waƙoƙin Hausa
cikin ajami, shi ma Malam Shi’itu ya rubuta
waƙoƙin Hausa daga
cikin waɗanda suka
shahara misalin su shi ne: Wadar tuba, da waƙar Wawiyya,
Jiddul azizu, da sauransu.
Ƙarni na sha
tara {19} nan ne aka sami bunƙasar
rubutattun waƙoƙi na Hausa,
sakamakon aikin da masu jihadi suka yi, waƙoƙin
sun sami tasiri da karɓuwa sosai a wannan lokaci, yawancin waƙoƙin
masu jihadi ne suka yi su ƙarƙashin
jagorancin Shehu Usman ɗan Fodiyo wannan ya sa ake kiran waƙoƙin
wannan ƙarnin da waƙoƙin
masu jihadi domin waƙoƙin
da aka rubuta a wannan ƙarni an yi su ne a
kan jigon addini saboda Musulunci a wannan lokaci ya yi ƙarfi shi ya
sa ba a sami wata waƙa ba wadda jigonta ba
na Musulunci ba, kuma duk waƙar da aka
samu an rubuta wadda ba ta addini ba ana kiran ta da suna ‘fululu’
wato waƙa maras amfani wannan ya sa waƙoƙin
ƙarni na sha tara {19} duk suna da jigon
addinin Musulunci ne, Yahya {1988, sh. 36-60}.
Muhammad {2019,
sh.8-10} ya nuna cewar a ƙarni na sha
tara {19} ne aka tabbatar da yawaitar samuwar rubuttun waƙoƙi
a ƙasar Hausa. Bayan da Shehu Usumanu ɗanfodiyo shi
da jama'arsa suka yi jahadi a ƙasar Hausa, a
wannan lokaci an samu marubuta da suke rubuta waƙoƙi
domin isar da saƙo da wa'azi daga cikin irin waɗannan
marubuta akwai irinsu: Shehu ɗanfodiyo, da ƙanansa
Abdullahin Gwandu, da 'ya'yansa kamar Isan Kware, da Nana Asma'u, da dai
sauransu.
Shehu Usmanu da mabiyansa duka waɗannan
rubuce-rubuce da suka yi a cikin harshen Larabci, da ajamin Fulatanci da kuma
ajamin Hausa suka yi su. Misalin waƙoƙin
da aka rubuta, kamar waƙar Shehu Usumanu
" Tabban Haƙiƙan"
wadda 'yarsa Nana Asma'u ta fassara zuwa Hausa, ɗansa Isan
Kware ya yi tahamisinta. Manufar waɗannan waƙoƙi
na {Ƙ.19} shi ne yaɗa addinin
Musulunci.
A ƙarni na {Ƙ.20}
an samu sauye-sauye domin kowane zamani yana nuna hoton mutanen wannan zamani
ne. Shigowar baƙin al'adu, to a duk lokacin da wata al'ada ta
kutso kai a cikin wata takan haifar da mutane su ma su canja ko kuma su rungumi
wani sashe na baƙuwar al'dar da ta riske su. Wannan ya faru da
Hausawa bayan shigowar Turawa a ƙasar Hausa.
Wannan ya sa aka samu canji cikin rubuce-rubuce ta fuskar haruffan da ake
rubutu a ƙarni na {19} duk rubuce-rubucen da aka yi a
cikin harshen Larabci ne da Hausa ajami, amma a ƙarni {20} sai
aka sauya saboda samun ilimin boko.
Saboda haka an samu marubuta waƙoƙi
a wannan ƙarni na {20} da suka haɗa da Sarkin
Zazzau Aliyu ɗan Sidi, da
Malam Aliyu Namangi Zariya, da Malam Sa'adu Zungur, da Alhaji Billo Giɗaɗawa Sakkwato,
da Malam Garba Gwandu da Alhaji Sambo Wali Sakkwato, da Malam Nasiru Kabara, da
Mudi Sipikin, da Na'ibi Sulaiman Wali da Alhaji Abubakar Ladan Zariya, da Malam
Ɗahiru Musa Juhun, da Haruna Aliyu Ningi da
sauransu. Haka zalika jigogin waɗannan waƙoƙi
na ƙarni {20} sai ya cuɗanya ana
samun jigon addini, sannan kuma ana sumun abin da ba addini ba kamar soyayya
siyasar duniya da dai sauransu. An duba Sulaiman {2019, sh.9-10}.
3.4 Tsarin Rubutacciyar Waƙa
Kamar yadda
muka sani kowane abu yana da tsari ko siga, ko kuma matakin da ake bi wajen
samar da wannan abu to ita ma waƙa rubutacciya
tana da tsari wanda kuma shi ne ya bambanta ta da waƙar baka, idan
muka ɗauki ma’anar
da Sarɓi {2007,
sh.1} ya bayar ta rubutacciyar waƙa da ya ce “Wani
saƙo ne da ka gina shi a kan tsararriyar ƙa’ida
na baiti da ɗango da kari
da amsa-amo da sauran ƙa’idojin
da suka danganci daidaitattun kalmomi da zaɓarsu tare da
yin amfani da su a rubuce sannan a rera lokacin da ake baƙata.”
Sarɓi {2007, sh.
50-66} ya kawo tsarin rubutacciyar waƙa kamar haka:
v Mabuɗin Waƙa
v Farawa da
Bisimilla {sunan Allah}
v Farawa da
Godiya ga Allah ko Annabinsa
v Farawa da
yabo ko salati ga Annaabi {S. A. W}
v Farawa da
Addu'a
v Jinkirta Mabuɗi
Bari a bayar da
misalin abin da ake nufi da jinkirta mabuɗi saboda su biyar na
sama akwai misalansu zuwa gaba a cikin Hanyoyin nazarin rubutacciyar waƙa
da aka kawo. Misalin jinkirta Mabuɗi shi ne:
A waƙar
Aƙilu Aliyu mai suna Saƙo a Hannun
Mumini
1. Saƙo a hannun
mumini,
Zai kai shi ba wani bimbini.
2. Ni na kira sarki gwani,
Wannan da ya samar da ni.
A nan an samu
jinkirta mabuɗi maimakon a
fara da baiti na biyu a matsayin na farko sai aka jinkirta shi zuwa baiti na
biyu da marubucin ya ce " Ni na kira sarki gwani". Kamar yadda aka
gani wannan shi ake kira jinkirta mabuɗi.
7- Rashin Mabuɗi
Misali A waƙar
Aliyu ɗan Sidi ya
fara da faɗar
Aboka
zo nan mu bata,
Ka
dubi ɗan ɗai ga wata,
Wada
daban da batta,
Haske
na rana da wata,
Ba za su zamo daidai ba.
A nan idan an lura
kai tsaye aka shiga waƙar babu mabuɗi kamar
addu'a ko yabon Allah ko salati ga Annabi {S. W. A}, to irin wannan shi ake
kira rashin mabuɗi a cikin waƙa
rabutacciya.
8- Makullin waƙa
Misali a waƙar Na'ibi
Sulaiman Wali ta Gargaɗi Don Falkawa
36. Na gode Allah nai yabo,
A gare shi a nan zan dakata.
37. Tsira da aminci rabbana,
Ga rasulu da ya hana yin fuce.
40. Tamat yau waƙa ta cika,
Allah sa mu mu bar son yin fuce.
Wannan shi ake kira
mukullin waƙa a yi yabo ga Allah, ko kuma a ce 'tamat'
kamar yadda aka ga wannan marubucin waƙa ya yi.
9- Rashin Makullin Waƙa
Misali
a waƙar Aƙilu Aliyu ta
"Daddaɗan daɗi
Saniya"
67.
Jama'a daga nan zan dakata,
In sanya alama in tsaya.
68.
Ni naku Aƙilu Aliyu ne
amsa a wajen mai tambaya.
10- Sunan Marubuci a
Cikin Waƙa
Misali a cikin waƙar Mu'azu Haɗeja ta
"Yabon Ubangiji"
79. Ni ne Mu'azu Haɗeja ni na yi
wallafar
Haza a ƙallu minal ƙalili
yabon shi.
Wannan shi ne abin da
wannan masani ya kawo dangane da tsari ko sigogin rubutacciyar waƙa.
Bayan wannan akwai ilimin karin waƙa
wanda ake iya rubuta waƙa da shi, wannan ma
an aro shi daga harshen Larabci ne.
Bello {2013,
sh.10-36} ya kawo karuruwan da ake da su tare da ƙafafun da
suke samar da wannan karuruwan kamar haka:
1- Dawil.
2- Madid.
3- Basid.
4- Wafir.
5- Kamil.
6- Hajaz.
7- Rajaz.
8- Ramal.
9- Sari’i.
10- Munsari.
11- Hafif.
12- Mulari’i.
13- Muƙtalib.
14- Mujtas.
15- Mutaƙarab.
16- Mutadarak.
Ya cigaba da cewa daga waɗannan
karuruwa guda goma sha shida {16} da suka samo asali daga waƙoƙin
Larabawa guda goma sha huɗu {14} ne aka samu a waƙoƙin
Hausa a yanzu, kamar yadda ya jero su ya nuna cewa SARA’I ne da MULARI’I
Hausawa ba su amfani da su, sai kuma ƙafafuwa da
ake amfani da su wajen samar da karuruwan kamar haka:
Fa’ulun
Mafa’ilun
Mafa’alatun
Fa’ilatun
Fa’ilun
Mustaf’ilun
Fa’ilatun
Mutafa‘ilun
Maf’ulatun
Mustaf’ilun
Dangane da yadda Hausawa suke tsara layukan waƙoƙinsu
kuwa, nan ma abin lura ne, domin yana cikin tsarin rubutacciyar waƙa,
ya zamana ana iya rarrabe adadin layuka da waƙa take ɗauke da shi,
da kuma yadda tsarin layukan suke a cikin baitukan waƙa.
Sa'id, {2016, sh.38-44} ya ce: "Bincike
ya tabbatar da cewa, akwai ire-iren waƙar Hausa guda
takwas. Don haka ana jin cewa rubutacciyar waƙar Hausa ba
za ta fita daga da'irar waɗannan ire-iren ba. Amma kuma wani
lokaci a bisa wasu dalilai, akan sami wasu mawaƙa su saɓa wa wannan
tsarin." Ya kawo su kamar haka:
Gwauruwa.
Ƙwar Biyu.
Ƙwar Uku.
Ƙwar Huɗu.
Ƙwar Biyar.
Tarbi’i.
Tahmisi.
Tashɗiri
Waɗannan su ne yadda tsarin rubutacciyar
waƙa yake, kuma shi ne ya bambanta ta da duk
wata waƙa wadda ba rubutacciya ba.
3.5.0 Hanyoyin Nazarin Rubutacciyar Waƙa
Dangane da
yadda ake nazarin rubutacciyar waƙa kuwa, masana
sun fitar ko sun bayar da yadda mai nazari zai nazarci waƙa cikin sauƙi
don fito da wani abu na ilimi a ciki.
Sarɓi {2007,
sh.31-180} ya bayyana hanyoyi kamar haka:
3.5.1 Tarihin Marubuci: yana daga
cikin abin da ake lura da shi wajen nazarin waƙa a san inda
aka haifi mawaƙi, da lokacin da aka haife shi da kuma
tarihin asalinsa da nasabarsa, bayan nan sai ƙurciyarsa da
matakan karatunsa da kuma fito ko gano harsunan da yake ji da sunayensa ko
cikakken sunansa, yana da kyau a san matansa nawa ne, da kuma adadin ‘ya’yansa,
in ya rasu ya yi masa addu’a.
A ƙarshe sai a
bayyana tarihin fara rubuta waƙarsa, da abin
da ya jawo ra’ayinsa ya fara rubutawa da sunayen waƙoƙinsa.
3.5.2 Ma’aunin Waƙa: wannan fage ne da ake iya gane
rubutacciyar waƙa masana sun tabbatar da cewa dole waƙa
rubutacciya ta kasance tana da ma’auni da za a
iya gane karinta da shi, da kuma nau’in gaɓoɓinta da aka
tsara waƙar da su, ta haka ne za a iya gane waƙar
ta tsaru, ko kuma ba ta tsaru ba, kuma a iya fito da illolin da ke cikinta.
Misali a waƙar Aƙilu Aliyu ta
Kadaura Babbar Inuwa.
Na gaida Manzo Alu su da abokai,
Mata da 'ya'yaye nake tarawa.
Na gai da man/ zo Alu su/ da abokai/
Mata da 'ya/ 'yaye nake/Tarawa/.
Idan aka lura ƙafa ta ɗaya da ta biyu
a layi na ɗaya da na
biyu, sun daidaita a kan gaɓoɓi hurhuɗu ko wacce.
Amma ƙafa ta uku a layi na ɗaya ta saɓa wa ƙafa
ta uku a layi na biyu, kamar haka:
1 2 3 4 1 2 3 4 1 2 3 4
Na gai da man/ zo Alu su | da abokai
1 2 3 4 1 2 3 4 1 2 3
Mata da 'ya | 'ya ye nake| tarawa|.
Wannan misalai ke nan
na ma'aunin waƙa, idan aka yi la'akari da yawan gaɓoɓi, za a iya
cewa, layi na ɗaya ya fi na
biyu tsayi ko yawan gaɓoɓi.
3.5.3 Mabuɗin Waƙa: kasancewar
rubutattun waƙoƙin da aka
fara yi na addini ne da ya nuna fara yin komai da sunan Allah ko salati ga
Annabi Muhammad {S. A. W} wannan ya jawo duk waƙar da za a
rubuta sai an yi ɗayan abu huɗu kamar haka:
Basmala.
Godiya ga Allah {S.W.A}.
Salati ga Annabi
Muhammad da Alayensa da Sahabbansa.
Addu’a. Misali
Farawa da basmala
A waƙar
Aƙilu Aliyu ta Kadaura Babbar Inuwa
1. Bisimillahi da shi nake farawa,
Kome nake niyyar nufin shiryawa.
2. Na gaida manzo, Alu su da abokai,
Mata da 'ya'yaye nake tarawa.
Farawa da godiya ga
Allah
A waƙar
Lalura ta Shehu Usuman ɗan fodiyo
Gode Allah bisa ga samun bushara,
Ahma ash shugabanmu mi ad da saura,
Wanda an nashi nan da can shi ka tsira,
Na fa gode ma wanda yab ban basira,
Nasa addin saninsa dukkan lalura.
Farawa da yabo ko yin
salati ga Annabi {S.A.W}
A waƙar
“Mu yi yaƙi da Jahilci”
Ina
yin nan salati zuwa
ga manzon duk halittu.
Farawa da Addu'a
A waƙar
Giya ta Ma’azu Haɗeje
1. Allah na nemi buɗi gare ka,
Zan waƙar mashaya
giya.
2. Allah ka daɗan basira
gama
Ko da ba ka ban ba zan godiya.
Sannan idan an sami waƙa ba ta da
mabuɗi, mai
nazarin waƙa zai bayyana hakan yayin da yake nazarin.
3.5.4 Jigo: jigo na nufin
gundarin saƙon da marubucin waƙa yake son
isarwa ga al’umma, dole ne mai nazari ya yi ƙoƙarin
fito da jigon waƙar a fili tare da kafa ƙwararan
hujjoji daga cikin waƙar sannan a nuna wasu
baitukan da jigon ya fito ɓaro-ɓaro a ciki.
Misali a cikin waƙar Usmanu Ɗanfodiyo
"Tabban haƙiƙan wadda Nana
Asma'u ta fassara zuwa Hausa kuma Isan Kware ya yi mata tahamisi, an fara da
gabatar da furucin jigo har wurare huɗu, wato baiti na 34
da na 41, da na 45, da na 49 kamar haka:
34 Wa'azu an yo shi 'yan'uwa don ku farka,
Kui ta tsoron Ubangiji kui ta kuka,
Kun jiya gaskiya fa babu shakka,
Hakimai masu yin faɗa can ga
zakka,
Gobe a ta zakkace su tabban haƙiƙan.
41. Wa'azu na anka yo daɗa don ku
falka,
Don ka shirya ma gobe can inda za ka,
Bari zuwa yanzu-yanzu roƙo a ba ka,
Mai fa roƙon da yaf
faye gobe huska,
Tai ana ƙarƙare
ta tabban haƙiƙan.
Watau idan aka duba
waɗannan wurare
da aka nuna a sama za a ga duk ana ambaton wa'azi, wanda shi ne babban jigon waƙar.
3.5.5 Warwarar Jigo: a nan ana so ne mai
nazarin ya kawo jigon waƙar tare da
kawo ƙananan jigogin da marubucin ya yi amfani da
su wajen ƙulla waƙarsa, don
ganin saƙon ya fito yadda ake buƙata, sannan
ya bi ta da sharhin baitukan da ya kawo don ƙarfafa
hujjarsa.
3.5.6 Zubi da Tsari: wannan ɓangare ne da
mai nazari zai kawo waƙar gaba ɗayanta ya
kuma nuna yadda mawaƙi ya zuba tunaninsa a
cikin waƙar, da yadda ya tsara ta, ana so ne ya dinga
tattaro tunanin mawaƙin, misali ya ɗauka tun daga
baiti na ɗaya {1} zuwa
na biyar {1-5} mawaƙin ya fara ne da
yabon ubangiji daga baiti na (5-15) a nan ya fito da jigon waƙarsa
{15-30} sake bayyana manufarsa ya yi, tare da {30-39} sake bayyana manufarsa ya
yi, {39- 45} ya faɗi sunansa da shekarar da ya rubuta waƙar,
{45-53} ya yi addu’a ya kuma
rufe waƙar tasa. Haka ake so a ga mai nazari ya fito
da zubi da tsari waƙa wannan shi zai sa a
san ya karanta waƙar sosai daga farko har ƙarshe.
Amsa-amo: wannan wata gwaninta ce da mawaƙa
ke yi a cikin waƙa, amsa amo {ƙafiya} yana
zuwa ne a ƙarshen baitin waƙa, wani
lokacin yana zuwa ne da wasali ko baƙi, wani
lokacin kuma kalma. Dangane da ire-irenta masana sun raba ta biyu kamar haka:
Amsa-amon ciki/ Ƙaramin
amsa-amo,
Amsa-amon waje/ Babban amsa-amo. Misali
Ƙaramin
amsa-amo: Kamar yadda Dumfawa a laccar aji {2022} ya ce mana "Ƙaramin
amsa-amo shi ne gaɓar sautin da kowane layi da ke cikin baitin
waƙa ke ƙarewa da ita.
Ana samun ƙaramin amsa-amo a waƙoƙi
'yan ƙwar uku ko huɗu ko biyar.
Ba a cika samun ƙaramin amsa-amo a waƙa ƙwar
biyu ba face idan amsa amonta mai zaman kansa ne". Misalin ƙaramin
amsa-amo:
Ya
wanda sh ne tun azal,
Kuma tun azal yake lam yazal,
She ne Ganiyu bila misal,
Shi yay yi komai ga shi fal
Yai lahira yai duniya.
Shi yai dare kuma yai wuni,
Yai mai gani da marar gani,
Yai jahili yai mai sani,
Yai babba yai ɗan ƙanƙani,
Kowansu yai masa kishiya.
A waɗannan baitoci
an ga cewar kowane layi da ke cikin baitin waƙar na ƙarewa
da irin sauti ɗaya, wannan
shi ake kira ƙaramin amsa-amo.
Babban
Amsa-Amo shi ma Dumfawa a laccar aji {2022} ya ce "Babban amsa-amo shi ne
gaɓar sautin da
kowane baiti na waƙa ke ƙarewa
da ita. Misali:
Bisimillahi
na nufi za ni waƙa,
Bisa maƙiya Muhammadu
Annasara.
Muna
roƙo ga sarki mai sarauta,
Mu sami fita mu bar jama'ar Nasara.
Mutane sun ɗime wansu sun
makafta,
Yawanci sun zamo jama'an Nasara.
A nan wannan gaɓar sauti ta
"Annasara" ita ce babban amsa-amo da ake bayani.
Waɗannan su ne
nau’o’in amsa-amo {ƙafiya} da ake samu a
rubutattun waƙoƙi na Hausa,
kuma yana da kyau ga mai nazarin waƙa ya fito da
irin amsa-amon da waƙar ke da shi.
3.5.7 Salo da Sarrafa Harshe:
wannan ma wata dabara ce da mai nazari ake so ya lura da shi, yana da kyau ya
fito da irin salon da marubucin ya yi amfani da shi sannan ya bayyana salon
wane iri ne, wato salon miƙaƙƙe
ne, ko rago ne, yana da armashi ko ba ya da shi.
Sarrafa harshe kuma, ana so ne mai nazari ya
yi bayani gaba ɗaya na yadda
marubuci ya yi amfani da kalamansa wajen rubuta waƙa, kamar su
adon harshe, wato {karin magana}, da hoto cikin bayani, da kamanci, da
jinsantarwa, da abuntarwa, da dabbantarwa, da kambamawa, da sauransu, sannan
mai nazari ya bayyana karin harhen mawaƙi Kananci ne,
ko Sakkwatanci, ko Katsinanci, da sauransu. Bari a bayar da misalin irin waɗannan salalai
da ake samu a cikin rubutattun waƙoƙin
Hausa.
3.5.7.1 Salon Karin Magana
Karin Magana gajeriyar jimla ce wadda ta ƙunshi
ma'ana mai faɗi. Hikima ce
da ta shafi fasahar dunƙule magana mai yawa
wuri ɗaya.
Aikin mai nazari shi ne ya gano baitin da aka
yi amfani da karin magana watau haƙi ne ga mai
nazari ya yi la'akari da irin yadda marubuci ya sarƙa karin
magana a cikin waƙarsa. Misali a cikin waƙar yabon
Sojojin Nijeriya ta Aƙilu Aliyu.
Baiti na 54 yana
cewa:
1. Duk abin da shukawarka,
2. Za ka girbe kayanka.
(Abin da ka shuka shi za ka girba)
3.5.7.2 Salon Hoto Cikin Bayani
Hanya ce ta bayyana wani yanayi mai kama da na
wasan kwaikwayo. Dabara ce ta jawo hankali ta hanyar saka wasu mutane ko
dabbobi ko wasu abubuwa a wani hali ko bisa wani matsayi waɗanda idan an
karanta ko an saurara, za a ga wato yanayin a zuci. Wato a ga kamar ga abin a
fili yana faruwa. Misali a cikin waƙar Aliyu ɗan Sidi ta
Tabarƙoƙo a baiti na
22
Ga wani wai shi ya iya
Ya je ya jawo igiya
Ta nannaɗe mai ga wuya
Yana kira da waiwaya
Ba za a ɗebe mai ba.
Idan aka lura da
wannan misali a cikin wannan baiti za a ga cewa marubucin yana ba da hoton
yanayi ko halin wanda yake magana a kansa.
3.5.7.3 Salon Kamance
Kamantawa
hanya ce ta kwatanta abubuwa biyu don fayyace irin dangantakar da ke
tsakaninsu. Kamance ya kasu kashi uku akwai na daidaito da na fifiko da kuma
kasuwa ko kashi.
3.5.7.3.1 Kamancen Daidaito
Kamancen daidaito shi ne inda marubucin waƙa
kan kwatanta wani abu da wani ya ce daidai suke ba wanda ya fi wani. Yana yin
wannan ta amfani da kalmomin daidai, ko sai ka ce, ko kamar ko tamkar. Misali
Waƙar Karuwa ta
Ma’azu Haɗeja
Dube ta idan tana tafiya, sifarta kamar sifar
gafiya.
A wannan misali an yi amafani da salon
kamancen daidaito shi ne "kamar" watau marubucin yana so a dubi sifar
karuwa kamar yadda aka san gafiya.
3.5.7.3.2
Kamancen Fifiko
Kamancen fifiko shi ne wajen da
marubucin waƙa zai kwatanta abubuwa guda biyu amma ya nuna
cewa ɗayan ya fi ɗayan. Ana yin
wannan ne ta hanyar amfani da wasu kalmomi na nuna fifiko irin ya fi, ya ɗara, ya
zarce. Misali a waƙar Aƙilu
Aliyu ta Kadaura Babbar Inuwa ya ce:
Ilimi ga mai shi ya fi babban rumbu,
Domin hatsin rumbu suna ƙarewa.
A nan marubucin ya kwatanta abubuwa
biyu, ilimi da kuma babban rumbu, amma ya nuna ilimi "ya fi" rumbun
hatsi ba ma rumbu ba kawai babban rumbu gaba ɗaya.
3.5.7.3.3
Kamancen Kashi Ko Kasuwa
Kamancen Kasawa shi ne yadda marubucin
waƙa zai kwatanta abubuwa biyu amma ya ce ɗayan bai kai
kamar ɗayan ba. Ana
amfani da kalmomi kamar su bai kai ba, wane, wa kaza, da sauransu. Misali waƙar
”Me zan faɗa ne”
13. Zancen ɗabi'a ko a
birnin Sakkwato,
Aka reni 'ya halinta bai kai naki.
A wannan baitin marubuci ya yi amfani
da salon kamancen kasawa ya nuna cewa mace ko a birin Sakkwato da aka sani can
ne asalin cibiyar Musulmi to, ko a can aka reni 'ya halinta bai kai na wadda
yake yabo watau ya kasar da wadda ba ta kai gare ta ba, ta hanyar amfani da
kalmar "bai kai".
3.5.7.4
Salon Jinsantarwa
Salon jinsantarwa wani salo ne da
marubuta waƙa ke amfani da shi ta hanyar saka wa wani abu
musamman mutum halayya ta wani wanda ba mutum ba. Ana yin haka ne domin fito da
wata kama wadda marubucin waƙar ke saka wa
abin da yake magana game da shi. Salon jinsantarwa kashi uku ne mutuntawa da
dabbantarwa da kuma abuntarwa.
3.5.7.4.1
Mutuntawa
Mutuntawa salo ne da marubuta waƙa
ke amfani da shi ta hanyar saka wa dabba ko wani abu wata halayya ta mutum da
nufin a dubi wannan dabba ko abun kamar mutum saboda irin halin da mutum da aka
ce tana da shi. Misal a waƙar Aƙilu
Aliyu ta Duniya Rawar 'Yammata ya ce:
4. In shari a tai kira Je ka amsa ka jiya.
A wannan baiti marubucin ya mutunta shari'a ya
ba ta halayya irin ta mutum da aka sani da yin magana da ya ce "in shari'a
tai kira."
3.5.7.4.2
Dabbantarwa
Dabbantarwa ita ma wani nau'i ne na
jinsantarwa, wanda a nan ne marubucin waƙa ke saka wa
mutum halayya ta dabba domin a dube shi kamar irin dabbar da aka saka masa
halayyarta. Misali a waƙar "Son Maso
wani Cuta ne"
5. In na yo carar zakara,
Kyarkyarata gun ki take.
A wannan misali marubucin waƙar
ya dabbantar da kansa da ya ce "in ya yo carar zakara", mutum ba a
san shi da yin cara ba zakara aka sani da wannan sifa haka da ya ce "kyarkyarata
gun ki take" kaza aka sani da kyarkyara ba mutum ba wannan shi ake cewa
dabbantarwa.
3.5.7.4.3
Abuntarwa
Abuntarwa shi ma wani nau'i ne na
salon jinsantarwa. A wannan salo marubucin waƙa na ɗaukar wata
halayya ta wani abu wanda ba mutum ba ba kuma dabba ba ya saka wa mutum ko
dabba. Misali a waƙar Aliyu ɗan Sidi ta
"Tabarƙoƙo" ya
ce:
Na ga shi duk ya kwaɓe,
Ya yi taɓo ya taɓe,
Ya yi baƙo ya raɓe,
Neman jini ga babe,
Ba za a sa mu nai ba.
A ɗangon farko
na baitin, marubucin waƙar yana bayyana yadda
ya ga wani mutum ya ce ya kwaɓe. Mutum ba ya kwaɓewa, tuwo ko
wani abu mai kama da tuwo shi ke kwaɓewa, saboda haka cewa mutum ya kwaɓe to shi ake
kira abuntarwa.
3.5.7.5
Salon Kambamawa
Kambamawa shi ne salon da marubucin waƙa
zai ƙara gishiri wajen bayyana wani abu ga mai
sauraro ko karatu ta hanyar bayyana abin fiye da yadda yake. Misali a waƙar
"Allah da kansa ya ƙera 'yar nan
Dije"
23. Ke Dije ni fa ina da tarihinki,
Mata na Hurul'aini ne asalinki.
A wannan misali a ɗango na biyu
nan ne marubucin waƙar ya kambama
masoyiyar tasa Dije ya faɗi abin da hankali bai ɗauka cewa
Dije matan Hurul'aini ne asalinta. Irin wannan shi ake kira kambamar zulaƙe
a cikin nazarin rubutacciyar waƙar Hausa.
Sarɓi
{2007,sh.140-150}.
3.6 Naɗewa
A cikin wannan babi mun fara gabatar da shi ne
da taken fashin baƙi a kan ma’anonin
da suka shafi taken bincike an ji ra’ayoyin masana
dangane da waƙa, sannan an kawo ire-irenta daga wajen
masana, sannan kuma an kalli rubutacciyar waƙa a ƙeɓance, tare da
yadda tsarinta yake da kuma yadda masana suke ganin za a bi wajen nazarin
rubutacciyar waƙa. Wannan babi na uku abin da ya yi ƙoƙarin
kawowa ke nan.
Babi Na Huɗu
Nazarin Rayuwar Malam Aliyu (Ɗanbaba Aliyu Sha’iri) Da Waƙoƙinsa
4.01 Shimfiɗa
A babi na
huɗu kuma za a kawo bayanai game da gundarin taken bincike. Wato bayanai
a kan malam Aliyu Shi’iri da waƙoƙinsa, a inda muka
fara da shimfiɗa game da tarihin malam Aliyu Sha’iri wato haihuwarsa, ƙurciyarsa, da tasowarsa, da kuma neman iliminsa.
Haka an zo da bayanai dangane da koyo da fara waƙoƙinsa, da
yaransa, da kuma yawace-yawacensa, da yadda yake shirya waƙoƙinsa, da rasuwarsa,
da matsayin malam Aliyu Sha’iri a tsakanin mawaƙan da da na yanzu, da nau’o’in waƙoƙinsa. Babin bai kammala ba sai da aka nazarci wasu daga cikin waƙoƙinsa, inda aka fayyace jigon waƙoƙin tare da
warwarar jigo, haka kuma an bayyana salon sarrafa harshe a cikin waƙoƙinsa, sannan kuma aka yi bayanai game da zubi da tsarin waƙoƙinsa daga ƙarshe kuma aka zo da naɗewa.
4.1 Taƙaitaccen Tarihin
Malam Aliyu Ɗanbaba
An haifi Malam
Aliyu Ɗanbaba wanda aka
fi sani da Aliyu Sha’iri a garin Talata Mafara. Ya fara karatun allo a wajen mahaifinsa
sannan ya wuce garin Gusau domin ci gaba da karatun allo a wajen malam Isa na
malam Ango. Ya yi karatun litattafai a wajen malam Ibrahim Mai Li’irabi.
Malam Aliyu Ɗanbaba mutum ne da aka shaide shi da son addini
da kuma nuna ƙiyayya ga maƙiya addini. A wata fira da wasu daga cikin
abokanansa na karatun ilimi kamar Liman Sani Talata Mafara ya bayyana mana cewa
“shi malam Aliyu duk wanda ka ga yana hulɗa da shi, ko kuma yana kai masa ziyara to ka tabbata malami ne ko kuma
almajiri. Kuma malam Aliyu ta ɓangaren ƙungiya yana tare da ƙungiyar Islahuddini kuma mabiyin ɗariƙar Tijjaniyya.
Haka kuma malam Aliyu Sha’iri Allah ya azurta shi da ‘ya’ya maza
da mata da jikoki.
‘ya’yansa maza su ne:
Malam Lawwali
Malam Rabu’u
Malam Jamilu
‘ya’yansa mata kuwa su ne
Malama Zabba’u
Malama Nana
Malama Suwaiba
Haka kuma malam Aliyu sha’iri ya auri mata uku su ne:
Malama Maimuna
Malama Zara’u
Malama A’ishatu
Malam Aliyu a fagen sana’a
manomi ne, kuma yana taɓa wa’azi
musamman a ƙauyuka. Haka
kuma shi kafinta ne, kuma ya taɓa aikin
Bakalori daga shekara ta (1977-1979). A fannin waƙa ta rubutu Malam Aliyu ya shahara, ya yi waƙoƙi masu yawa waɗanda suka haɗa da:
Waƙar Bakalori, Waƙar Alfarma da dai sauransu.
4.1.1 Haihuwarsa
An haifi
malam Aliyu Sha’iri a garin Talata Mafara ƙaramar hukuma da ke cikin jahar Zamfara a cikin wata unguwa da ake
kira Gwadara, a shekara ta alif da ɗari tara
da arba’in da biyu (1942). An samu waɗannan bayanai daga shi kansa malam Aliyu kafin Allah ya yi masa cikawa
a lokacin da ake ganawa da shi yayin da ake rubutun littafin Talata Mafara Jiya
da Yau.
4.1.2 Ƙurciyarsa da
Tasowarsa da Neman Iliminsa
Kamar
yadda muka yi fira da malam Lawwali wanda yake shi ne babban ɗa magaji a wajen malam Aliyu, ya bayyana mana cewa “kamar yadda
al’adar Bahaushe take idan ya haifi ɗa idan ya
tasa ya kai lokacin ƙuruciya babansa yana kai shi makarantar allo domin ya koyi ilimin
Addinin Musulunci saboda haka, malam Aliyu Sha’iri ya fara karatun Alƙur’ani mai girma a hannun mahaifinsa mai suna malam Muhammad ana yi masa
laƙabi da (Ɗanbaba). Bayan nan mahaifin nasa ya yanke
shawarar ya kai malam Aliyu zuwa Gusau wajen malaminsa wanda shi kuma gare sa
ya yi karatu, wannan malami shi ne malam Isa na malam Ango, a wajen sa ya sauke
Alƙur’ani mai girma. Bayan ya sauka mahaifinsa ya ji
cewa malam Ibrahim mai Li’irabi zai wuce da ‘ya’yansa
zuwa Zariya sai ya haɗa shi da ɗansa watau malam Aliyu Sha’iri a can ne ya fara karatun ilimi.”
4.1.3 Yaransa
Kamar
yadda muka sami nusarwa daga malam Lawwali ɗanɗan malam Aliyu Sha’iri cewa akwai wata yayar malam Aliyu tana nan da
ranta za mu iya samun wasu bayanai waɗanda shi ba shi da su, wannan datijiya ita ce malama Rabi wadda take
mata ce ga malam Ibrahim mai Li’irabi malamin da malam Aliyu ya yi karatun
ilimi a wajensa, mun samu ƙarin bayani daga wajen ta cewa “malam Aliyu Sha’iri yana da yara da yake rera waƙa tare da su, suna yi masa amshi daga cikin yaran akwai: Yakubu, da
Saluhu, waɗannan yara nasa suna taimaka masa yayin da yake rera waƙar tasa, suna yawace-yawace tare da shi a wasu
lokuta har ana ba su sadaƙa.”
4.1.4
Yawace-yawacensa
Kamar
yadda aka faɗa a can baya cewa malam Aliyu almajiri ne duka yawace-yawacensa ba su
wuce a kan neman ilimi ne da karantar da ilimi ba. Malam Aliyu Sha’iri ya zauna
a Bilbil har ma ana yi masa laƙabi ana ce da shi Nabilbil. Haka kuma ya yi yawace-yawace zuwa ƙauyuka domin yin wa’azi da faɗakarwa, sannan ya yi zuwa Ƙauran Namoda musamman a wajen abokanansa da suke tare a kan tafiya ɗaya da fahimta ɗaya a
cikin Addini.
Malam Aliyu Sha’iri ya yi yawon
wa’azi a cikin wasu ƙauyuka da ke cikin Talata Mafara kamar irin Take-tsaba, Mirkidi da dai
sauransu. Bugu da ƙari malam Aliyu bai koma ga Mahaliccinsa ba, sai da ya sami damar
sauke farali na aikin hajji, saboda haka malam Aliyu Sha’iri ya je ƙasa mai tsalki domin gudanar da iba’dar aikin
hajji.
4.1.5 Shirya Waƙoƙinsa
Kamar yadda muka sani cewa mawaƙa suna da wani tsayayyen tsari na musamman da
suke amfani da shi wajen rubuta waƙoƙinsu, to shi ma
malam Aliyu Sha'iri yana amfani da irin wannan tsari wajen rubuta waƙoƙinsa misali
a) Mabuɗi (basmala): A nan ana dubawa ne a ga wane irin mabuɗi mawaƙi ya yi amfani
da shi wajen buɗe waƙarsa, ko kuma ba
a tsara waƙar da mabuɗi ba ma. Mafiya yawan waƙoƙin malam Aliyu
suna da buɗi misali
Ya ku musulmi za ni yin fakarwa,
Ga ɗalibai almajirai duka kowa.
Bulaliya ce mai shirin tsalarku,
Ba ta bugawa zahiri na jikinku.
Cikin zukata ne take tsalarku ,
Tana horo don ku gyara halinku.
Dangane da marufi kuwa, waƙoƙin malam Aliyu
wasu suna ƙarewa da marufi
wasu kuma ba su ƙarewa da marufi.
b) Amsa-amo (ƙafiya): Dangane da amsa amo kuwa (ƙafiya), waƙoƙin malam Aliyu
Sha'iri suna tafiya tare da kula da amsa-amo na ciki da na waje (babba da ƙarami).
c) Tsarin Baitocin Waƙoƙinsa: Malam
Aliyu Sha'iri waƙoƙinsa mafiya yawa 'yan tagwai ne, amma ana samun
mai ƙwar biyar misali
i) Ƙwar biyu ('yar
tagwai)
Duba na sakko babban jigo,
Allah ya ƙara mai imani.
Ina nufin haji Garba Ɗanɗa,
Ya munfiƙu fi hazaddini.
Ya yi ruwa kuma ya yi
tsaka-tsiki,
Ga taimakon Islahuddini.
Ya Allah ka tsare muna wannan,
Ga dukkanin sharrin shaiɗani.
Misalin wata 'yar tagwai
Liman Aliyu na ban sha'awa,
Don bai guruf-guruf na siyasa.
Bakin shi ba ka jin wata kalma,
Mugunya da ba a so ta siyasa.
Bai nuna wai ka zo ka yi fati,
Da ya zan yana cikin ra'ayinsa.
ii)'Yar Ƙwar Biyar
Na gode Rabbana mai baiwa,
Sarkinmu jalla shi adda baiwa,
Ya rarraba waɗansu da baiwa,
Ya ba mu malami mai baiwa,
Dalili na sayyadi mai asali.
Malam Muhammadu Majtaba,
Ibnu mu'allimu Isah,
Allah jiƙan mu'allimu Isah,
Domin rasulu manzon Isah,
Don Ɗaha sayyadi mai asali.
Wannan shi ne mafi yawan tsarin da malam Aliyu yake
bi wajen shirya waƙoƙinsa.
4.1.6. Rasuwarsa
Kamar
yadda bayanai suka gabata dangane da malam Aliyu Sha’iri, tun daga haihuwarsa
har zuwa ƙurciyarsa da
yadda ya gudanar da rayuwarsa. Abin da aka sani shi ne cewa kowace rayuwa za ta
ɗanɗani mutuwa, haka malam Aliyu ya rasu ranar Alhamis (17) ga watan
Rabi’ul Awwal wanda ya yi daidai da 13-10-2021. Kuma yana da shekara (79) a
duniya, ya bar mata biyu da ‘ya’ya kamar malam Lawwali malam Jamilu.
4.1.7 Matsayin
Aliyu Ɗanbaba A
Tsakanin Marubuta Waƙoƙin Da da na
Yanzu
Kamar
yadda aka yi bincike a ka cewar ko malam Aliyu Sha’iri yana da wasu abokanai da
suke hulɗa da su kan rubuce-rubucen waƙoƙi, amma abin da
aka samu na bayanai cewa malam Aliyu galibi a kan abin da ya shafi addini ne
yake rubuce-rubucensa saboda haka, idan Allah ya sa ya rubuta wata waƙa yana aikawa zuwa ga abokanansa malamai da
almajirai domin su karanta. Haka kuma malam Aliyu ba shi da wata alaƙa da marubuta waƙoƙin wannan zamani
domin shi duka waƙoƙinsa a cikin Hausa ajami ya yi su.
4.2.1 Koyon Waƙarsa
Kamar
yadda aka tambayi Malama Rabi’atu matar malam Ibrahim mai Li’irabi malamin
malam Aliyu, cewa shin ko malam Ibrahim ya koya wa malam Aliyu rubuta waƙa? Sai ta ce “A’a ko alama baiwa ce kawai Allah ya ba shi, malam Ibrahim ya gan sa da
baiwarsa ne kawai saboda haka, babu wanda ya zaunar da malam Aliyu ya koya masa
rubuta waƙa.”
4.2.2 Nau’o’in Waƙoƙinsa
Kamar
yadda bayanai suka gabata cewa malam Aliyu Sha’iri ya yi rubuce-rubucen waƙoƙi musamman a kan abin da ya shafi addini, haka kuma, ya yi a kan abin
da ya shafi rayuwa daga cikin nau’ukan waƙoƙinsa akwai:-
Waƙar Yabon Ƙungiyar Islahuddini ya ce:
Duba na sakko babban jigo,
Allah ƙara mai Imani.
Ina nufin haji Garba Ɗanɗa,
Ya munfiƙu fi hazad dini.
Ya yi ruwa kuma ya yi tsaka tsaki,
Ga taimakon Islahuddini.
Ya Allah ka tsare mana wannan,
Ga dukkanin sharrin Shaiɗani.
Sai babban jigo a gare mu,
Kun ji turakun ƙauye da birni.
Ai shugaban Islahu na Ƙaura,
Bai kunyar maƙiyin addini.
Ka sha kabsawa da mutane,
Kan salla rukunin addini.
Alhaji Sidi abansu Rumaisa,
Mashin suke maras Imani.
Ka ba su nassi ka ba su shafi,
Ya jikan kakansu Husaini.
Ya babansu Umar da Sumayya,
Ya hadimi wurin jelani.
Sai Sufi mai tsoron Allah,
Ya fitila hasken zamani.
“Waƙar Yabo Ga Liman Ali” ya ce:
Liman Aliyu na ban sha’awa,
Don bai gurub gurub na siyasa.
Bakinshi ba ka jin wata kalma,
Mugunya da ba a so ta siyasa.
Bai nuna wai ka zo ka yi fati,
Da ya zan yana cikin ra’ayinsa.
Limamman ku zo ku kun yi,
Da liman Aliyu ɗabi’a tasa.
Kowar riƙa shina nan
nashi,
Har wanda bai riƙa bai ƙin sa.
To ƙaddara hukuncin
Allah,
Shi ke izo ma bayi nasa.
Don ɗai ya zan yana jarabawa,
Domin a gane mai tsoron sa.
Malamai waɗansu sun ƙarnanta,
Karatunsu sun gama da siyasa.
Sai ɗai a ɗauki ayar Allah,
Ana fassara ta nan ga siyasa.
“Waƙar Ta’aziyyar ‘Yanuwa” ya ce:
Na gode Allah da Annabi manzo,
Fiyayyan halitta mannzo
ma’aiki.
Kafi da ya’i da su za ni roƙo,
Du’a’in da zan yi wurin
marigaya.
Allah jiƙan su Inna da
baba,
Da yannansu ƙannansu domin ma’aiki.
Malam Muhammadu Nasiru Bilbil,
Allah jiƙan shi domin ma’aiki.
Malam Muhammadu Majimu ba shi,
Allah jiƙan shi domin ma’aiki.
Malamai waɗanga an yi
hasara,
Allah jiƙan su domin ma’aiki.
Malam Musa Tullu Ɗanrini ke nan,
Allah jiƙan shi domin ma’aiki.
4.2.3 Wasu Daga
Cikin Waƙoƙinsa
Kamar
yadda bayanai suka cewa malam Aliyu sha’iri ya rubuta waƙoƙi da dama, daga
cikin wasu waƙoƙin nasa akwai:-
1. Waƙar ‘yan yau
2. Waƙar ɗalibai da malam sunna
3. Waƙar marsiyya ta
malam Ibrahim
4. Waƙar sharuɗɗan salla
5. Waƙar sheɗan
4.2.4 Zubi Da Tsarin Waƙoƙinsa
Dumfawa (2022) a laccar aji ya ce "Zubi da tsari shi ne wanda ake
duba yadda mawaƙi ya zuba ya
kuma tsara baitocin waƙarsa. Wannan shi ya sa wasu suke ce masa salon zubi da tsari. Salon
zubi da tsari ya ƙunshi zubin
baitoci kamar yawansu da yawan layuka a cikin baitoci da yadda cikon ma'ana ko
kalmar wani layi ko baiti ke shiga cikin wani baiti da kuma amsa-amo."
Malam Aliyu yana zuba waƙoƙinsa ne wasu
'yan ƙwar biyu wasu
biyar amma ya fi yin zubin 'yar tagwai wato (ƙwar biyu) misali
Liman Aliyu na ban sha'awa,
Don bai gurub-gurub na siyasa.
Bakinshi ba ka jin wata kalma,
Mugunya da ba a so ta siyasa.
Saɓi zarce
Wannan wani salo ne da cikon ma'anar layin waƙa kan kasa cika sai a cikin layi da ke biye. Kowane layin waƙa kamata ya yi ya zama cikakkar jumla, to idan
jumla ba ta cika ba sai a cikin layi mai zuwa shi ake kira salon saɓi zarce a cikin rubutattar waƙa. Dumfawa, (2022)
Irin wannan salo malam Aliyu ya yi amfani da shi a cikin waƙarsa misali
Bakinshi ba ka jin wata kalma,
Mugunya da ba a so ta siyasa.
Bai nuna wai ka zo ka yi fati,
Da ya zan yana cikin ra'ayinsa.
Salon Ɗinkin Baiti ko
Raɓa danni
Ɗinkin baiti ko raɓa dannin
baiti shi ne baitin da ma'anar da ke ƙunshe a cikinsa ba ta cika sai an tsallaka cikin baiti da ke bin sa.
Dumfawa (2022).
Irin wannan salo malam Aliyu yana amfani da shi wani lokaci a cikin waƙoƙinsa misali
32 A rijiyar zaki zan koma
Akwai Mahir masanin Ƙur'ani.
33. Ina nufin Shaikhu na
musamman
Bello abin faharin addini.
Babban amsa-amo
Shi ne gaɓar sautuka da
kowane baitin waƙa ke ƙarewa da ita.
Malam Aliyu yakan tsara waƙarsa bisa tsari na amfani da babban amsa-amo a wani lokaci. Misali
10. Tsarin Yahudu wagga siyasa,
Mai hankali ka gane dasisa.
11. Kana malami bafaden Allah,
To mi za ya sa ka zaɓi siyasa.
12. Wasu kam Yahudu sun halaka
su,
Ƙiyayyarsu yau tana ga siyasa.
Amsa-amo Mai Zaman Kansa
Amsa-amo mai zaman kansa shi ne amsa-amon da ya
kasance kowane baitin waƙa yana da nasa amsa-amo na daban.
Malam Aliyu ya ɗora
harsashin ginin waƙarsa a kan irin wannan tsari na amsa-amo. Misali
Gida na malam ba a son a bas
shi,
Wurin karatu kawai ɗiyanai su yi shi.
A zan ka sauraren karatu nasu,
Ban da fa girman kai fa ko an
fi su.
A zan nufin Allah da Manzon Allah,
A samu yarda nan ta sarki
Allah.
Mabuɗi
A tsarin waƙoƙin malam Aliyu
Sha'iri wasu suna farawa da mabuɗi, wasu
kuma ba su ba su farawa da shi. Misalin waƙarsa da ya fara ta da mabuɗi kamar
waƙar yabon
Islahuddini da ya ce
1. Bisimillahi da sunan Allah
Sarki jalla gwani mai baiwa.
A wannan baitin ya buɗe ne da
basmala, amma kuma a wata waƙar sai ya buɗe da godiya ga
Allah da Annabi misali
1. Na gode Allah da Annabi,
Fiyayyen halitta Manzo ma'aiki.
2. Kafi da ya'i da su za ni roƙo,
Du'a'in da zan yi wurin
marigyaya.
Marar Mabuɗi misali
1. Liman Aliyu na ban sha'awa,
Don bai gurub-gurub na siyasa.
2. Bakinshi ba ka jin wata
kalma.
Mugunya da ba a so ta siyasa.
Marufi
Wasu waƙoƙinsa suna da marufi wasu kuma ba su da marufi.
Misalin mai marufi
70. Don Islahu ta haɗa kowa,
Dukkan mai kishin addini.
Tamat bihadillahi wa husni
aunihi.
Maras Marufi misali
13. Dut wanda ba ya fati nasu,
Kamar kafiri suke hangensa.
30. Sai wanda ya zan nakasa ta
kama,
Ba shi da mai ɗaukan lalura taima.
31. Shi zan bara nai ban da yin
ƙarya ko,
Shi na ta yi nai ban da cin
zarafi ko.
Wannan shi ne misalin yadda malam Aliyu yake zuba ko tsara waƙoƙinsa a taƙaice.
4.2.5 Jigon Waƙoƙinsa
Jigo shi ne saƙo ko manufar da marubuci yake son isarwa ga mai karatu ko nazarinsa.
A nan za a duba jigogin waƙoƙin malam Aliyu
Sha'iri. Kamar yadda aka gani bayan nazarin wasu daga cikin waƙoƙinsa an ga cewa waƙoƙin duka
jigoginsu suna da alaƙa da addini ne kaitsaye ko a fakaice. Misali kamar waƙar yabon ƙungiyar Islahuddini an ga yadda wannan marubuci ya ɗauki manufarsa ta waƙe wasu manyan mutane da suka bayar da gudunmuwa ga wannan ƙungiya ta Islahuddini.
Haka kuma idan aka ɗauki waƙar yabo da ya yi wa Liman Aliyu, za a ga jigonta
na yabo ne kan wasu nagartattun halaye nasa. Haka kuma, idan aka ɗauki waƙar Bulaliya da
aka kawo za a ga tana ɗauke da jigon faɗakarwa ko gargaɗi
musamman ga ɗalibai da almajirai kan su guji wasu munanen halaye, sannan su yi riƙo da wasu kyawawan halaye. Saboda haka waƙoƙin malam Aliyu Sha'iri galibi suna ɗauke da jigogi ne da suka shafi addini kaitsaye ko a fakaice.
4.2.6 Warwarar Jigon Waƙoƙinsa
Kamar yadda aka gani waƙar da aka fara nazari an yi warwarar jigonta ita da sauran waƙoƙin da aka kawo. Kamar dai yadda aka faɗa mafi yawan jigogin waƙoƙin malam Aliyu
Sha'iri sun shafi addini ne.
Waƙar yabon ƙungiyar Islahuddini tana ɗauke da jigon yabo ne kuma wanda ke da alaƙa da addini. Haka zalika, waƙar yabon Liman Aliyu ita ma waƙar yabo ce, domin ya nuna yabawa ga wasu nagartattun halaye na Liman
Aliyu misali da ya ce
Liman Aliyu na ban sha'awa,
Don bai gurub-gurub na siyasa.
Bakinshi ba ka jin wata kalma,
Mugunya da ba a so ta siyasa.
Bai nuna wai ka zo ka yi fati,
Da ya zan yana cikin ra'ayinsa.
Kamar haka dai ya ci gaba da yabon sa da kyakkyawan harshe.
Sai kuma waƙar da ke ɗauke da jigon faɗakarwa ko gargaɗi watau
waƙar Bulaliya.
Wannan waƙa ya yi ta ne
domin ya faɗakar da masu neman ilimi wasu halaye maras kyau da ya kamata su guje
su, da kuma kyawawan halaye da ya dace su yi riƙo da su. Misali
1. Ya ku musulmi za ni yin faɗakarwa,
Ga ɗalibai almajirai duka kowa.
2. Bulaliya ce mai shirin tsalarku,
Ba ta
bugawa zahiri na jikin ku.
3. Cikin zukata ne take tsalar
ku,
Tana horo
don ku gyara halinku.
4. Dut wanda almajiri ga su malam,
Shi daina
jayayya da 'ya'yan malam.
5. In malamin nan naku ya yi wafati,
Sai ku riƙe kulan dubu na salati.
Haka dai marubucin ya ci gaba da nusar da ɗalibai da almajirai har ya kai ga cewa
13. A zan ka sauraren karatu
nasu,
Ban da girman kai fa ko an fi
su.
14. A zan nufin Allah da Manzan
Allah,
A samu yarda nan ta sarki
Allah.
To duka idan aka lura jigogin waɗannan waƙoƙi ke nan da suke ɗauke da darasi da abin a yi koyi.
4.2.7 Salon Sarrafa Harshe
Salo yana nufin dabara ko
hikima da aka yi amfani da ita domin isar da saƙo.
Dumfawa (2022) a laccar aji ya ce "Salon kwalliya ko sarrafa
harshe a cikin rubutacciyar waƙa shi ne amfani da wasu zaɓaɓɓun kalmomi masu ratsa zuciya da marubucin waƙa ke amfani da su cikin hikima da basira domin saka wa mai sauraron sa
ko karatunsa ko nazari raha tare da jawo hankalinsa ta yadda zai fahimci saƙon waƙar ba tare da ƙosawa ba."
Masu nazarin waƙa sun saka wa waɗannan
salailai sunaye domin bambance kowane nau'i na salo daga wani. Daga cikin
fitattun nau'o'in akwai salon kinaya, da kamance, da jinsantarwa, da alamtarwa,
da kambamawa, da hira, da dai sauransu.
Idan aka dubi waƙoƙin malam Aliyu Sha'iri suna ɗauke da wasu daga cikin waɗannan
nau'o'in na salo misali
Salon Kambamawa
Salon kambamawa shi ne a faɗi abin da hankali bai iya ɗauka,
marubuta waƙa suna yin hakan
ne domin su nuna gwarzantawa ga wanda suke yi wa waƙa.
A cikin waƙar yabon Islahuddini malam Aliyu ya yi amfani da irin wannan salo na
kambamawa da ya ce:
24 Ya baharun fi kulli
fununi,
Ya ƙa'ilun riauli irfani.
25. Ina nufin Shaikhu Bilalu
Kano
Ma'adinun lifumiddini.
37. Ya kogin ilimi tarbiyya,
Anta Mudarrisus sibiyani.
Kamancen Daidaito
12. Dut wanda ba ya fati nasu.
Kamar kafiri suke hangen sa.
4.3.1 Nazarin
Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa
Wannan
nazari na waƙoƙin malam Aliyu Sha’iri zai kasance ƙwarya-ƙwaryar nazari ne
na jigo da zubi da tsari da salon sarrafa harshe, a cikin waƙoƙin malam Aliyu za a nazarci waƙoƙin ne kamar
yadda masana suka bayyana a babi na uku. Da farko za a yi nazari a kan waƙar malam Aliyu da ya yi ta Yabon Islahuddini.
4.3.2 Waƙar Yabon
Islahuddini
Kamar yadda bayani ya gabata a
cikin bayanin tarihin malam Aliyu Sha’iri
cewa shi mabiyi ne ga wannan ƙungiya ta Islahuddini. Marubucin ya rubuta wannan waƙa ne domin yabo ga ƙungiyar da kuma manyan jagororinta. Haka zalika domin ya nuna manufar
wannan ƙungiyar da ci
gaban da take kawo ga addinin Musulunci.
1. Zubi Da
Tsarin Waƙar: an tsara wannan waƙa ne a cikin baitoci masu layuka biyu -biyu wato ‘yar tagwai ko ƙwar biyu. Haka kuma waƙar tana da baitoci {70}, dangane da ɗangwaye kuwa tana ɗauke da ɗangwaye {140}. Haka kuma, waƙar tana ɗauke da babban amsa-amo na “ni”. Haka zalika, waƙar tana da mabuɗi ta fara
da basmala da yabon Ubangiji da godiya ga Allah, da neman daɗin tsira ga Annabi Muhammad {S.A.W}. Misali
1. Bisimillahi da sunan Allah,
Sarki jalla gwani Rahamani.
2. Sai shukarammu ga sarki
Allah
Ya ƙara samu ruƙon addini.
3. Allah ka yi tsira da aminci,
Ala Muhammadu ɗan Adinani.
2. Jigon Waƙar: Dangane da jigon wannan waƙa za a iya cewa wannan waƙa tana ɗauke da jigon “Yabon ƙungiyar Islahuddini da jagororinta”.
Marubucin ya bayyana hakan tun a baiti na 4 inda ya ce:
4. Na yi nufin in tsara ƙasida,
Ta yin yabon Islahuddini.
3. Warwarar
jigo: Marubucin bayan ya bayyana manufarsa tun farko
sai ya ci gaba da yabon malamai jagororin wannan tafiya ta Islahuddini kamar
daga baiti na 10- da ya ce:
10. Shaikhu Yusufu Ibnu Yahuza,
Ka yi gadon kishin addini.
11. Sai jarumi mai halin girma,
Jagoran Islahuddini.
12. Zaki ja da ƙarfin Allah,
Kar ka ji tsoron bawa fani.
Bayan marubucin ya cika abin da ya amabata a matsayin manufa da ya
gina waƙarsa a kansa
watau yabo ga jagororin ƙungiyar Islahu da ya ce a baiti na 53
53. Bayan yabo ga malammaina
Zan yi nasiha gun ikhwanni.
A baiti na 65-66 sai marubucin ya nemar wa wannan ƙungiya tsari daga sharrin shaiɗan da ya ce:
65. Ya Allah domi Shurafa’u,
Don kakan su Hassan da Husaini.
66. Ya Allah ka tsare Islahu,
Ga dukkanin sharrin Shaiɗani.
A ƙarshe sai
marubucin ya kammale da nuna cewa ƙungiyar Islahu ta haɗa kowa
idan har mutum mai kishin addini ne yana cikin ta. Ya ce:
68. In an ce ma wayyi ƙasida
La tabahal a’ada’addini.
69. Ce Ibrahim ɗan Abbdullahi,
Ce mariƙin wuridin Tijjani.
70. Don Islahu ta haɗa kowa,
Dukkan mai kishin addini.
4 Salon Waƙar: Salo dabara ce da marubuta waƙoƙi suke amfani da
ita domin su jawo hankalin mai karatu ko mai nazarin waƙoƙinsu. Marubucin
ya yi amfani da miƙaƙƙen salo, domin
an fahimce saƙon da waƙar take ɗauke da shi babu kwan-gaba-kwan-baya a ciki. Bugu da ƙari ya yi amfani da salo mai armashi kuma sassauƙa. Haka kuma, an yi amfani da salailai na jawo
hankalin mai sauraro ko mai nazari ga su kamar haka:
5. Salon aron
kalmomi: wannan wata dabara ce da marubuta waƙoƙin Hausa ke amfani da ita, ta hanyar tsalma wasu kalmomi da aka aro
daga wani harshe misali harshen Larabci ko Ingilishi. kalmomin aro da aka yi
amfani da su
Larabci
v Bisimillahi Da sunan Allah
v Allah Ubangiji
v Shukur Godiya
v Ƙasida Abin da aka rubuta a waƙe
v Hizbu Runduna
v WujubanAbin da yake tilas
v Addini Hanyar bauta
v Shaikh Dattijo ko babban malami
v ZamanWani lokaci
v Ƙur’an Littafin Allah mai tsalki
11 Baharun Teku
12 Funun Ilmoma
13 Ƙa’ilunMai
abin cewa
14 Lisanun Harshe
15 KulliGaba ɗaya
16 MaƙalAbun magana
17 MakanBigire
18 Amana Yarjejeniya
19 Faharun Ƙware
20 IslahGyara
21 Jaza’u Sakamako
22 Ihsan Kyautatawa
23 Da’awa Kira zuwa ga Ubangiji
24 IlimiSani
25 AntaKai
26 Mudarris Mai koyarwa
27 SibiyanYara
28 MunfiƙuMai ciyarwa
29 Fi Ciki
30 Haza Wannan
31 Sharri Mugun abu
32 Ikhwan‘Yan uwa
33 Majanun Marar hankali
34 Alƙadir Mai iko
35 La tabahal Kar ka yi rowa
36 A’ada’a Maƙiyi
37 Fani Mai ƙarewa
Kalmomin Ingilishi da aka yi amfani da su
1 Sakatare Maga takarda
2 Fi’ar’o Mai sanarwa
6. Salon
Siffantawa Gajeruwa
Marubucin ya yi amfani da salon siffantawa gajeruwa a baiti na 12-13
inda ya ce:
v Zaki ja da da ƙarfin Allah
Kar ka ji
tsoron bawa fani.
v Malam Abdul Basir Ishaƙa
Ya Allah ya daɗa maka auni.
7. Salon
Kambamawa
Marubucin ya yi amfani da salon kambamawa domin gwarzantawa da kaiwa
maƙura wajen yabon
jagororin ƙungiyar
Islahuddini. Misali da ya ce:
24 Ya baharun fi kulli
fununi
Ya ƙa’ilun ri’auli ir’fani.
25 Ina nufin Shaikhu Bilalu
Kano
Ma’adinun lifumiddini.
Haka kuma, marubucin ya sake yin amfani da wannan salo na kambamawa
misali a baiti na
30 Ya lisanun fi kulli maƙali
Ya faɗinun fi kulli makan.
37 Ya kogin ilimi tarbiyya,
Anta mudarrisussibiyani.
4.3.3 Nazarin Waƙar Yabon Liman
Aliyu
Wannan waƙa malam Aliyu ya yi ta ne domin ya nuna hali na dattako da ke ga Liman
Aliyu, saboda rashin shigar sa cikin lamarin siyasa.
1. Zubi Da
Tsarin Waƙar
Dangane da yadda marubucin ya
zuba waƙar tasa, wannan
waƙa tana ɗauke da baitoci (13), ɗangwaye
(26). Haka kuma, tana ɗauke da babban
amsa amo na “sa.” Haka kuma a tsarin waƙar ba ta da mabuɗi ba ta
da marufi.
2. Jigon Waƙar
Wannan waƙa jigonta shi ne “yabo ne zuwa ga Liman Aliyu”
3. Warwarar Jigon
Waƙar
Tun a baiti na 1-3 marubucin ya
bayyana manufarsa inda ya ce:
v Liman Aliyu na ban sha’awa
Don bai gurub-gurub na siyasa.
v Bakin shi ba ka jin wata kalma,
Mugunya da ba a so ta siyasa.
v Bai nuna wai ka zo ka yi fati,
Da ya zan yana cikin ra’ayinsa.
A baiti na ɗaya marubucin ya
nuna cewa Liman Aliyu yana ba sa sha’awa domin ya tsare ƙimarsa da mutuncinsa bai shigar da kansa cikin siyasa ba saboda
kasancewar sa jagora na addini. A baiti na biyu kuma sai marubucin ya sake
yabon Liman Aliyu amma sai ya nuna ba siyasar ce Liman Ali ba ya yi ba a’a ba
ya yin wani zance na Allah waddai a kan siyasa.
Sai kuma a baiti na uku sai ya marubucin ya sake nuna wasu halayen
Liman Aliyu ko da yana yin siyasa a matsayin sa na jagoran addini bai nuna wa
mutane ga inda yake muradin a zaɓa. Wannan
marubuci yana so ya nuna ko da malami yana yin siyasa to bai kamata ya nuna a
zahiri ba.
Sai kuma marubucin bayan ya yabi Liman Ali sai ya waiwaya domin ya
bayyana waɗansu malamai da ba su yi koyi da irin halin Liman Ali ba, domin su sun
gwama karatunsu da siyasa. Sannan kuma marubucin ya nuna abin da ya fi wannan
muni shi ne yadda suke ɗaukar ayar Ƙur’ani suna ba ta warin zama a cikin siyasa domin son zuciya da neman
abin duniya.
8. Malamai waɗansu sun ƙarnanta,
Karatunsu sun gama da siyasa.
9. Sai ɗai a ɗauki ayar Allah,
Ana fassara ta nan ga siyasa.
4. Salon Waƙar
Wannan waƙa tana ɗauke da salo mai armashi kuma ba ta ɗauke da kalmomi masu wuyar fahimta, kaitsaye ana fahimtar saƙon da ke ciki. Akwai wasu nau’ukan salailai da aka yi amfani da su domin jawo
hankalin mai karatu ko nazari, daga cikinsu akwai:
5. Salon Aron
Kalmomi: Wannan wata dabara ce da marubuta waƙoƙin Hausa ke amfani da ita ta hanyar cusa wasu kalmomi waɗanda ba na harshen da aka rubuta waƙar a kansa ba. Misali harshen Larabci ko ingilishi. A cikin wannan waƙa mawaƙin ya tsalma kalmomin Larabci da Ingilishi misali
Larabci
1.Ƙarnantawa Haɗawa ko Gwamawa
2. Allah Ubangiji
3. Aya Alama
4. Yahud Masu biyar addinin Yahudanci
5. Imam Liman ko Jagora
6. Ɗabi’a Abin da aka saba
7. Kalimat Kalma
8. KufurKafirci
Kalmomin Turanci
v Gurub Taro ko Ƙungiya
v Fati Jam’iyya
6. Salon
Habaici: Magana ce za a yi ta gugar zana, domin yin hannun
ka mai sanda ga wani mutum ko wasu ɗaiɗaikun mutane. Malam Aliyu ya yi amfani da irin wannan salo misali da
ya ce
8. Malamai waɗansu sun ƙarnanta
Karatunsu sun haɗa da siyasa.
Mawaƙin yana yin
habaici ne ko zuzar zana ga wasu malamai da suka gwama karatunsu da siyasa.
Amma wannan ba wai don ya tozarta su ba, ya yi haka ne domin ya isar da saƙo ga irin malaman da ke yin irin wannan domin su
gyara.
Salon kamancen daidaito: marubucin ya yi amfani da salon kamance amma
na daidaito da ya ce:
12 Dut wanda ba ya fati nasu,
Kamar kafiri suke hangensa.
Salon amfani da karin harshe: mawaƙin ya yi amfani da karin harshen Sakkwatanci a cikin waƙar a baiti na 10 da ya ce
10 Tsarin Yahudu wagga
siyasa,
Mai hankali ka gane dasisa.
Kalmar wagga Sakkwatanci ne. Daidaitacciyar Hausa kuwa (wannan).
2 Bakinshi ba ka jin wata
kalma,
Shi ma wannan “bakinshi” Sakkwatanci ne. Daidaitacciyar Hausa kuwa shi
ne (bakinsa)
4.3.4 Nazarin Waƙar Bulaliya
Wannan waƙa ta bulaliya ya yi ta ne domin yin faɗakarwa da gargaɗi ga ɗaliban ilimi da almajirai domin su guje wa ɗabi’u waɗanda suke abin zargi, haka kuma su yi riƙo da ɗabi’u masu nagarta.
1. Zubi Da
Tsarin Waƙar: marubucin ya zuba baitoci (31) dangane da yawan ɗangwaye kuwa, wannan waƙa tana ɗauke da ɗango (62). Tsarin waƙar ba ta da mabuɗi, haka
kuma ba ta da marufi. Dangane da amsa-amo wannan waƙar tana da amsa-amo wanda ya kasance kowane baitin waƙa yana da nasa na daban.
2. Jigon Waƙar
Wannan waƙa tana ɗauke da jigon faɗakarwa ko
gargarɗi.
3. Warwarar Jigon
Waƙar
Marubucin ya bayyana manufarsa tun a baiti na ɗaya da ya ce:
1. Ya ku musulmi za ni yin faɗakarwa,
Ga ɗalibai
almajirai duka kowa.
Wato mawaƙin yana so ne ya faɗakar da
masu neman ilimi kan wasu ɗabi’u da
bai kamata a ce suna aikatawa ba, sannan kuma da nusar da su kan abin ya dace
su yi.
Daga cikin faɗakarwar da ya ce
zai yi ga ɗalibai da almajirai shi ne, su bar jayayya da ‘ya’yan malamansu. Inda
ya ce
4 Dut wanda almajiri ga malam,
Shi daina jayayya da ‘ya’yan
malam.
Bayan mawaƙin ya faɗakar da almajirai da ɗalibai
kan wannan ɗabi’a marar kyau. Sai kuma ya ci gaba da faɗakarwarsa ya ce
v A zan ka saurarin karatu nasu,
Ban da girman kai fa ko an fi su.
Malam Aliyu da ya ke ya san halin waɗanda yake gargaɗi sai ya
nuna su guji yin girman kai ga ‘ya’yan malamansu ko da kuwa sun fi su domin su
sami albarkar ilimi.
A baiti na 18-19 sai mawaƙin ya nuna dalilin da ya sa ya faɗakar da ɗalibai da almajirai a fakaice da ya ce
18 Waɗansu manyan ɗalibai na zaure,
Da babu malam yanzu dut sun
ware.
19 Sun yi ta jayayya karatu
nashi,
Sun yi nufin gade gida nashi.
Marubucin yana bayar da labari ne kan waɗansu ɗalibai da irin wannan abin da yake faɗakarwa a kansa, ya faru da su, saboda Hausawa sun ce “Gani ga wane ya
ishi wane tsoron Allah.
4. Salon Waƙar
Salo wata dabara ce ta ko
hikima ta isar da saƙo da marubuta waƙoƙin Hausa ke
amfani da ita domin su jawo hankalin mai karatu ko mai nazarin waƙoƙinsu. Wannan waƙa tana ɗauke da salo mai armashi kuma wanda yake sassauƙa sannan marubucin ya yi amfani da wasu salailai domin jawo hankalin
mai nazari ko karatu, daga cikin salailan da ya yi amfani da su akwai:
5. Salon aron
kalmomi: a cikin wannan waƙa mawaƙin ya yi amfani
da salon aron kalmomi misali
Larabci
1.Muslim Musulmi
2. Zahir. Abin da yake a fili
3. Hali yanayi
4. Salati Ambaton Ubangiji
5. Wafati Rasuwa
6. Aibi. Mummuna
7. Ɗalibi. Mai neman
ilimi
8. Halifa. Mai maye gurbi
9. Ilimi. Sani
10. Kulli. Baki ɗaya
11. Fanni. Wani yanki
12. Waliyi. Masoyin Ubangiji
13. Allah. Ubangiji
14. Wa'azi. Faɗakarwa
15. Waƙati. Lokaci
16. Maktubi Sanannen lokaci
6. Salon kinaya: Marubucin ya yi amfani da irin wannan salo a baiti na ɗaya da ya ce
1. Ya ku musulmi za ni yin faɗakarwa,
Ga ɗalibai almajirai duka kowa.
Marubucin ya ambaci ɗalibai
yana nufin ɗalibai 'yan matsakaita. Haka kuma, da ya ce almajirai yana nufin waɗanda ana iya kiran su malamai.
7. Salon Mutuntawa
Mawaƙin ya yi amfani
da salon mutuntawa inda ya yi ƙoƙarin mutuntar da
Bulaliya da ya ce
2. Balaliya ce mai shirin
tsalar ku,
Ba ta bugawa zahiri na
jikinku.
3. Cikin zukata ne take
tsalar ku,
Tana horo don ku gyara
halinku.
6. Salon Amfani
da Karin Harshe
Marubucin ya yi amfani da karin harshen sakkwatanci a cikin waƙarsa da ya ce
31 Shi zan bara nai ban da cin
zarafi ko,
Shina ta yi nai ban da cin
zarafi ko.
Sakkwatanci Daidaitacciyar Hausa
Shi zan Ya zan
Bara nai Baransa
Shina ta yi nai Yana ta yin sa
4.3.5. Naɗewa
A cikin wannan babi an fara da gabatar da shi ne, inda aka kawo
bayanai game da gundarin taken bincike. Wato fashin baƙi a kan malam Aliyu Sha'iri da waƙoƙinsa, a inda aka
fara da Shimfiɗa, sai kuma Tarihin Malam Aliyu Sha'ir i, Haihuwarsa, Ƙuruciyarsa, da Tasowarsa, da Neman Iliminsa,
Koyon waƙoƙinsa, Yaransa, Yawace-Yawacensa, Shirya Waƙoƙinsa, Rasuwarsa, Matsayin malam Aliyu Sha'iri a Tsakanin Mawaƙan Da da na Yanzu, sannan sai Zubi da Tsarin Waƙoƙinsa, Jigon Waƙoƙinsa, Warwarar
Jigon waƙoƙinsa, Salon Sarrafa Harshe, daga ƙarshe sai Nazarin Wasu daga cikin Waƙoƙinsa da Naɗewa.
Babi Na Biyar
Sakamakon Bincike
5.0. Shimfiɗa
Kamar yadda za a gani a cikin wannan babi na
biyar sh ne babin ƙarshe a cikin wannan
bincike da aka gabatar. A cikin wannan babin za a gabatar da Shimfiɗa, Sakamakon
Bincike Shawarwari, Naɗewa, da kuma Manazarta.
5.1. Sakamakon Bincike
Sakamakon wannan bincike ya dace da hasashen
wannan bincike da aka yi tun farko cewa wannan zai taimaka wajen raya harshen
Hausa.
Bayan
kammala wannan nazari, binciken ya gano wasu abubuwa musamman ta la'akari da
jigogi da salailai da ke cikin waƙoƙin
malam Aliyu Sha'iri. Daga cikin abubuwan da wannan bincike ya gano su ne kamar
haka:
1)
Wannan bincike ya gano cewa waƙoƙin
malam Aliyu idan da a ce al'ummar musulmi za su riƙa komawa
cikinsu suna nazari to ana sa ran samun gyaruwar halaye da ɗabi'un
al'ummar musulmi tun daga mu'amalar mutum tsakaninsa da mahaliccinsa, da kuma
mu'amala tsakanin Shugabanni da talakawansu, da malamai da almajiransu.
2)
Haka kuma wannan bincike ya gano cewa malam Aliyu Sha'iri yana da ƙungiya
domin shi mabiyi ne ga ƙungiyar Islahuddini
waɗanda ake cewa
('yan sai mun gani). Har wa yau kuma shi malam Aliyu ɗan ɗariƙar
Tijjaniyya ne kamar yadda ya nuna a cikin rubuce-rubucensa.
3)
Har wa yau wannan bincike ya sake la'akari da cewa, malam Aliyu duk da cewa
malami ne kuma Sha'iri amma wannan bai hana sa neman na kansa bai miƙe
ƙafafuwa yana bara ba. Wannan ne ya sa a cikin
waƙoƙinsa yake yi
wa wasu malamai zuzar zana da suka mayar da wa'azi hanya ta samun abin duniya.
Watau a taƙaice an gano cewa malam Aliyu mutum ne mai
tsantseni da gudun duniya.
4)
Bugu da ƙari wannan bincike ya gano cewa ashe malam
Aliyu har a cikin abin da ya shafi harkokin duniya, ba addini kaɗai ba yana ƙoƙari
wajen baza hajar baiwar da Allah ya yi masa. Malam Aliyu ya nuna ƙyamar
abin da waɗansu limamai
da malamai ke yi kan sha'anin siyasa, su daina nuna inda suke so ko kuma
tallata 'yan siyasa a kan mumbari domin wannan aikinsu ba ne. Idan aka lura
wannan abun yana faruwa har yau a wannan ƙasa ta mu
Najeriya.
5)
Har wa yau an gano cewa waƙoƙin
malam Aliyu Sha'iri cike suke da hanyoyin warware matsaloli da suka shafi
al'ummar musulmi amma saboda ba a sami yin nazari a kan rayuwarsa da waƙoƙinsa
ba shi ya sa ba a ci gajiyar wannan baiwa Allah ya yi masa ba.
Wannan
abu kuwa ana iya cewa ya faru ne saboda dalilai kamar haka:
i)
Kasancewar malam Aliyu yana rubutunsa ne da Hausa ajami, ga shi kuma yanzu an
sami ilimin boko Turawa sun zo da wasu haruffa saɓanin Larabci
wannan ya sa rubutun ajami ya yi ƙoƙarin
ɓacewa baki ɗaya zamani ya
kau da shi.
ii)
Aka yi rashin sa'a malam Aliyu bai sami wasu magadansa da za su ci gaba daga
inda ya tsaya ba musamman su da suka shiga wannan zamani suka yi karatun boko ƙyila
da an samu da waƙoƙinsa sun yaɗu sosai ga
al'ummar Hausawa.
5.2 Shawarwari
A ƙarƙashin
5.1 an bayyana sakamakon wannan bincike. An zayyano sakamakon da aka tattara. A
wannan bagire kuma 5.2 za a mayar da hankali wajen ba da shawarwari, dangane da
abin da ya kamata a yi kan wannan marubuci da kuma waƙoƙinsa.
Daga cikin abin da ya kamata a yi shi ne:
1)
Ya kamata a sake samun wani mai nazari da bincike ya yi nazari a kan wasu daga
cikin waƙoƙin wannan
bawan Allah domin akwai alfanu a cikin yin hakan daga cikin amfanin sake yin
nazarin wasu daga cikin waƙoƙinsa
sh ne:
i)
Domin ƙara raya adabin Hausa da kuma taskace shi.
ii)
Domin ƙara fito da wani ilimi wanda ba a gano ba a
karon farko.
iii)
Domin samun abubuwan da za a iya yin nazari nan gaba idan an sami taskace su.
2)
Ya kamata a riƙa binciko irin waɗannan
marubuta da ba su bayyana ba sosai, ana yin nazari a kan rubuce-rubucensu domin
hakan zai taimaka wajen ƙara raya
harshen Hausa.
3)
Ko yanzu ƙofa a buɗe ta ke ana
iya samun wani mai bincike ya sake faɗaɗa wasu
abubuwa da suka tsuke a cikin wannan bincike.
4)
Ya kamata marubuta waƙoƙin
Hausa su daina mayar da hankali ko da yaushe kan abin da ya shafi duniya kawai
a cikin waƙoƙinsu,
maimakon haka su riƙa gwamawa da jigogi
na tauhidi da wa'azi, gargaɗi, sallah, kamar yadda malam Aliyu
yake yi.
5.3.Naɗewa
Kamar yadda sunan wannan aiki ya gabata watau
"Nazarin rayuwar malam Aliyu sha'iri da waƙoƙinsa."
Wannan babin shi ne babin da aka kawo magaryar taƙewa na wannan
bincike watau wannan shi ne babin ƙarshe na
wannan bincike da aka gabatar.A cikin wannan babin an zayyana wasu abubuwa da
wannan bincike ya yi ƙoƙarin
ganowa a matsayin sakamakon bincike. Har wa yau an kuma bayar da shawarwari a
kan abin da zai ƙara taimakawa wajen raya wannan harshe na
Hausa da kuma ci gaban al'umma.
A babi na ɗaya a cikin
wannan bincike an kawo abubuwa muhimmai kamar haka farko an kawo Gabatarwa,
Shimfiɗa, Manufar
Bincike Hasashen Bincike, Farfajiyar Bincike, Matsalolin Bincike, Hanyoyin
Gudanar da Bincike da kuma Naɗewa.
Babi na biyu kuwa, wanda shi ne na biyu a
cikin tsarin wannan bincike an kawo abubuwa muhimmai kamar haka: Shimfiɗa Bitar
Ayykan da Suka Gabata, Hujjar Ci gaba da Bincike, da kuma Naɗewa.
A babi na uku kuwa, shi ne babi wanda ya ƙunshi
fashin baƙi a kan ma'anonin suka shafi taken bincike a
inda aka fara da Shimfiɗa, Ma'anar Waƙa, Ire-iren
Waƙa, Rubutacciyar Waƙa, Tsarin
Rubutacciyar Waƙa, Hanyar Nazarin Rubutacciyar Waƙa
sai kuma Naɗewa.
Babi na huɗu kuwa, wanda
shi ne ƙashin baya ko kuma ruhin wannan bincike,
kamar yadda aka gani wannan babi shi ne babin da ya ƙunshi fashin
baƙi a kan Rayuwar malam Aliyu Sha'iri da Waƙoƙinsa.
Inda aka fara da Shimfiɗa, Taƙaitaccen
tarihin malam Aliyu Sha'iri har zuwa ƙarshen wannan
babin.
A ƙarshen wannan
bincike kuwa, watau babi na biyar ya ƙunshi Shimfiɗa, da bayani
a kan Sakamakon Bincike, sai kuma Shawarwari. Sai kuma Naɗewa da kuma
Manazarta.
Manazarta
Adam,
S.N. (2016). "Malam Ibrahim Bin Ahmad Kabara da Waƙoƙinsa."
Kundin digiri na farko Wanda aka gabatar a Sashen harsuna da a'adun Afrika. Jami'ar
Ahmadu Bello Zariya.
A'isha,
A.S. (2016). "Malam Ahmad Maƙari Sa'id da
Waƙoƙinsa."
Kundin digiri wanda aka gabatar A Sashen harsuna da al'adun Afrika. Jami'ar
Ahmadu Bello Zariya.
Bello,
A. da Sheshe, I. N. (2013). Arulin Hausa
A Sauƙaƙe. Kano: S M
Graphics Printers & Publishers.
S M Graphics Printers & Publishers Kano.
C.B.T.T.M.
(2008). Talata Mafara Jiya Da Yau.
Dumfawa,
A. A. (2022). A ajin ALH 407 Contemporary Poetry in Hausa.
Ɗangambo, A. (2008). Ɗaurayar Gadon Feɗe
Waƙa. Zariya: Amana Publishers.
Husaini,
Y. (2O21) “Ɗanbalade Morai Da Waƙoƙinsa.”
Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Nazarin harsuna da Al’adu
Jami’ar tarayya Gusau.
Ibrahim,
(2019) "Malam Nasiru Kabara Da Waƙoƙinsa."
Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen harsuna da al'adun Afrika
Jami'ar Ahmadu Bello Zariya.
Mukhtar,
I. (2OO5) Bayanin Rubutacciyar Waƙar Hausa. Abuja:
Countryside
Publishers.
Muhammad,
S. S. (2019) Matakan Nazarin Rubutacciyar
Waƙar Hausa.
Zariya:
Jami’ar A B U.
Sarɓi, S. A.
(2007). Nazarin Waƙen Hausa. Kano: Samarib
Publishers
Sa’id,
B. (2016) Rubutacciyar Waƙa Hausa Ma’auninta da Amsa-amonta da
ire-irenta. Kano:
Jami’ar B U K.
Yahaya,
A. B. (2001). Salo Asirin Waƙa. Sokoto: Guaranty Printers Sokoto.
Yahaya,
I. Y. (2002). Hausa A Rubuce. Zariya:
NNPC.
Waɗanda Aka Yi
Fira da Su
Suna Tsokaci |
Malam Lawwali Babban
ɗan Malam
Aliyu Sha'iri |
Malam Naziru Aminin
Malam Aliyu Sha'iri |
Alhaji Maidaga Aminin
Malam Aliyu Sha'iri |
Liman Sani Abokin
Karatun Malam Aliyu Sha'iri |
Malama Maimuna Matar
Malam Aliyu |
Malama Rabai'atu
Yayar Malam Aliyu |
Rataye
Waƙar Yabon
Islahuddini da jogororinta.
1.
Bisimillahi da sunan Allah,
Sarki jalla gwani Rahmani.
2.
Sai shukurammu ga sarki Allah,
Ya ƙara sa mu ruƙon
addini.
3.
Allah ka yi tsira da aminci,
Ala Muhammadi ɗan adinani.
4.
Na yi nufin in tsara ƙasida,
Ta yin yabon Islahuddini.
5.
Ba ƙafiya babu aruli,
Sai ƙaunar hizbur
Rahmani.
6.
Ya Allahu ka ƙarfafa tsarin,
Ɗan baiwarka
mutum mai rauni.
7.
Yin jinjina a gare ka wujuban,
Ga dukkanin mai son addini.
8.
Ya Allah ka tsare Shaikh Yasuf,
Da ya riƙa muna wannan
tsani
9.
Ya ce ban shakkar sa ku taka,
Allah tare da ikhwani.
10.
Shaikhu Yasufu ibnu Yahuza,
Ka yi gadon kishin addini.
11.
Sai jarumi mai halin girma,
Jagoran Islahuddini.
12.
Zaki ja da ƙarfin Allah,
Kar ka ji tsoron bawa fani.
13.
Malam Abdul Basir Ishaƙa,
Ya Allah ya daɗa maka auni.
14.
Dole na sa babansu Husaina,
Sarkin tsauri na bin addini.
15.
Allah ɗai da ya yo
shi ya san shi,
Sakataren Islahuddini.
16.
Bai tsoro kuma ba ya rauni.
Wurin karo da mutan zamani.
17.
In sun yi gungu don su tare shi,
A hankali yaka sa masu rauni.
18.
A ba shi hujja ko ko ya ba da,
Kun ji nufin rayat addini.
19.
Ina nufin Shaikh Nasiru nawa,
Mai kanwa ne ismus sani.
20.
Naku ma'auni bayan namu.
Fira da kwaɗɗi ya ikhwani.
21.
Ina nufin malam na marere,
Sufina mai yin Tijjani.
22.
Masu kira a bi hanyar Allah,
Da damana bazararsu da rani.
23.
Ya shiga ƙauye lugu-lugu,
Don tabbatar da biyar Ƙur'ani.
24.
Ya baharun fi kulli fununi,
Ya ƙa'ilun
ri'auli irfani.
25.
Ina nufin Shaikhu Bilalu Kano,
Ma'adinun lifumiddini.
26.
Wallahi malam sai Allah saka,
Ya yi rawa ta ƙane ikhwani.
27.
Sai Alhaji Mukhtaru Balarabe,
Allah ya ƙara ma imani.
28.
Su sa jikinsu su sa kuɗinsu,
Kun ji mujahiddan addini.
29.
Sai ma'ajin wannan jam'iyya.
Ina nufin malam Zayyani.
30.
Ya lisanun fi kulli maƙali,
Ya faɗinun fi kulli makani.
31.
Halin ƙwarai a wurin Zayyanu,
Riƙon amana ba
nuƙusani.
32.
A rijiyar sarki zan koma,
Akwai Mahir masanin Ƙur'ani.
33.
Ina nufin Shaikhu na musamman,
Bello abin faharin addini.
34.
Akwai fi'ar'o gun Islahu,
Mai himma mai son addini.
35.
Malam Hasan Allah ya biya
Jaza'ul Ihsani Ihsani.
36.
Sai malamin da'awa Ya'aƙubu,
Tunatarwa yaka yi ba rauni.
37.
Ya kogin ilimi tarbiyya,
Anta mudarrisussibiyani.
38.
Dole na sakko babban jigo,
Allah ya ƙara mai
imani.
39.
Ina nufin haji Garba Ɗanɗa,
Ya munfiƙun fi hazad
dini.
40.
Ya yi ruwa kuma ya yi tsaki-tsiki,
Ga taimakon Islahuddini.
41.
Ya Allah ka tsare muna wannan,
Ga dukkanin sharrin shaiɗani.
42.
Sai babban jigo a gare mu,
Kun ji turakun ƙauye da
birni.
43.
Ai shugaban Islahu na Ƙaura,
Bai kunyar maƙiyin addini.
44.
Ka sha kabsawa da mutane,
Kan salla rukunin addini.
45.
Alhaji Sidi aban su Rumaisa,
Mashin soke maras imani.
46.
Ka ba nassi ka ba su shafi,
Ya jikan kakansu Husaini.
47.
Ya baban su Umar da Sumayya,
Ya hadimi wurin Jelani.
48.
Sai Sufi mai tsoron Allah,
Ya fitila hasken zamani.
49. A nan manufata Shaihu Yahaya,
Manyan gwagwarmayar addini.
50.
Baban Abdullahi da Aliyu,
Baban Zainab mai imani.
51.
Ya sha kakaniyar munkirai,
Masu musun hanyar addini.
52.
Ya Allah ka daɗa ma baiwa,
Ta lafiya da yawan imani.
53.
Bayan yabo ga malammaina,
Zan yi nasiha ya ikhwani.
54.
Mui biɗar ilimin
Isalamu,
Don shi ne tushen addini.
55.
Mai gaskiya bai jan fitina don
Kar gaskiyarsa ta zan baɗalani.
56.
Mu kauda zargi cikin tafiyarmu,
Da jita-jita cikin addini.
57.
Mugun zato kuma ba shi da kyawo,
Domin kay ya saka muna rauni.
58.
An yi kira an ce muna gyara,
Dole mu amsa ya ikhwani.
59.
Mun tafi mun shiga don mu ga gyaran,
In ko an gyara ikhwani.
60.
Ba mu da zaɓi kan
manufarmu,
Sai bin addinir Rahmani.
61.
Amma kau in anka ƙi gyaran,
Ba a hana mu biyar addini.
62.
A kan bakarmu ga wannan hanya,
Ba ma bin dukkanin majanuni.
63.
Ga wanga ƙarni babu jununa
Kamar hana mu biyar Ƙur'ani.
64.
Ya Allahu gwani mai ƙarfi,
Ya Ƙadirun fi
kulli zamani.
65.
Ya Allah domin Shurafa'u,
Don kakan su Hasan da Husaini.
66.
Ya Allah ka tsare Islahu,
Dukkanin sharrin Shaiɗani.
67.
Dubun tsira Allah da aminci,
Ga Musɗafa sirrir rahmani.
68.
In an ce ma wayyi ƙasida,
La tabahal a'a da addini.
69.
Ce Ibrahim ɗan Abdullahi,
Ce mariƙin wuridin
Tijjani.
70.
Don Islahu ta haɗa kowa,
Dukkan mai kishin addini.
Tamat bi hamdillhi wa husni aunihi.
Waƙar
Bulaliya
1.
Ya ku musulmi za ni yin faɗakarwa,
Ga ɗalibai almajirai duka kowa,
2.
Bulaliya ce mai shirin tsalar ku,
Ba ta bugawa
zahiri na jikin ku.
3.
Cikin zukata ne take tsalar ku,
Tana horo don ku gyara halinku.
4
Dut wanda almajiri ga malam,
Shi daina jayayya da 'ya'yan malam.
5.
In malamin nan naku ya yi wafati,
Sai ku ruƙe
kulan dubu na salati.
6.
Fi kulli yaumi waƙati maktubi,
Riƙe hakanga sai
ka tsalke aibi.
7.
In malamin nan naku ba shi da manya,
Cikin ɗiya sai ƙanƙana
ba manya.
8.
To ɗalibai nan za
ku taru shawara,
Ku zaɓi daidai wanda zai
jagora.
9.
Dut mai kwaɗai mai son a
sa shi gare ta,
Ku bas shi wawa bai iya ma gabata.
10.
Ku zaɓi mai ƙi
wanda bai da kwaɗaita.
Da sannu shi ne zai zama da nagarta.
11.
In ko manya suna da ilimi
A ɗauki babban su halifa ilimi.
12.
Gida na malam ba a son a bas shi,
Wurin karatu kawai ɗiyansa su yi
shi.
13.
A zan ka saurarin karatu nasu,
Ban da girman kai fa ko an fi su.
14.
A zan nufin Allah da Manzon Allah,
A sumu yarda nan ta sarki Allah.
15.
Ka bar ganin kai ka hi 'ya'yan malam,
Wurin karatu yanzu kai ma malam.
16. Ba ka buƙatar 'yan ɗiyan malam.
Ganin kakai kai ka ɗara su
fahimta,
17. Ka ɗauki kanka ka ɗara su
fahimta.
Ka zaɓi kanka yanzu kai ka
gabata.
18. Waɗansu manyan ɗalibai na
zaure,
Da babu malam yanzu dut sun ware,
19.
Sun yi ta jayayya karatu nashi,
Sun yi nufin gade gidan nashi.
20.
Ga kau ɗayan nan
nashi sun san fannin
Iri karatu nashi sun kuma gane.
21.
Komi kake yi zan ki kyauta ɗabi'a,
Halin ƙwarai zaƙe
ka zan yin ɗa'a.
22.
Mai wa'azi don kar ka sanya kwaɗanka,
Wurin mutane kodayaushe su ba ka.
23.
Da nuna kai dai ga buƙata taka,
A zan biya ma tun da ga wa'azinka.
24.
Ba ka da koyar wada Manzon Allah,
Da kau waliyyai masu yi don Allah,
25.
Shi wa'azi in ka yi domin Allah,
Shina biyan dut kanin buƙatu Allah,
26.
Shi wa'azi yau an kasa shi ga hanya,
Da kasuwanni don ababan duniya.
27.
A ba ka sadaka ya halatta ka amsa,
Ka daina roƙo koda yaushe
ka amsa.
28.
Kana ta amsa babu kau an bar ka,
An ɗebe kwarjini ga fuska taka.
29.
Ka ɗebe kwarjini
cikin iliminka,
Saboda roƙo koda yaushe
a ba ka.
30.
Sai wanda ya zan nakasa ta kama,
Ba shi da mai ɗaukan lalura
taima.
31.
Shi zan bara nai ban da yin ƙarya ko,
Shina ta yi nai ban da cin zarafi ko.
Waƙar Yabo ga
Liman Aliyu.
1.
Liman Aliyu na ban sha'awa,
Don bai gurub-gurub na siyasa.
2.
Bakinshi ba ka jin wata kalma,
Mugunya da ba so ta siyasa.
3.
Bai nuna wai ka zo ka yi fati,
Da ya zan yana cikin ra'ayinsa.
4.
Limamman ku zo ku zo ku yi kun yi,
Da Liman Aliyu Ɗabi'a tasa.
5.
Kowarriƙa shina nan nashi,
Har wanda bai riƙa bai ƙin
sa.
6.
To ƙaddara hukuncin Allah,
Shi ke izo ma bayi nasa.
7.
Don ɗai ya zan
yana jarabawa,
Domin a gane mai tsoronsa.
8.
Malamai waɗansu sun ƙarnanta,
Karatunsu sun gama da siyasa.
9.
Sai ɗai a ɗauki ayar
Allah,
Ana fassara ta nan ga siyasa.
10.
Tsarin Yahudu wagga siyasa,
Mai hankali ka gane dasisa.
11.
Kana malami bafaden Allah,
To mi ka sa ka zaɓi siyasa?
12.
Wasu kam Yahudu sun halaka su,
Ƙiyayyarsu yau
tana ga siyasa.
13.
Dut wanda ba ya fati nasu,
Kamar kafiri suke hangensa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.