Yadda Ake Wankan Haila, Janaba, Da Na Jumma'a

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum Malam Dan Allah ina so kayimun bayanin yadda ake wanka haila da wanka janaba da wanka juma'a.?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    وعليكم السلام ورحمة الله. ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،

    Daga Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam Kano.

    Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai Siffatul ijza' (ta wadatar), da kuma wacce ake kira Siffatul kamal (ta kamala).

    Wankan Janaba a siffarsa ta kamala shi ne: Idan kazo zaka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka.

    Farkon abin da zaka fara yi shi ne: zaka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka debo ka wanke gaban ka a dai-dai lokacin da zaka wanke gaban ka a lokacin zaka kulla niyya ta wankan janaba (Ko waninsa) wanda yake wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma'ana kayi tsarki kenan, to daga nan kuma sai kayi alwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah zakayi sai abu ɗaya shi ne wanke kafafu to wannan zaka kyale shi ba zaka yi shiba, to daga nan sai ka tsoma hannunka guda biyu a cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka saboda kowane gashi da ya buɗe a lokacin da maniyyi yake kokarin fita daga jikinka ya koma yanda yake, don gashin ɗan Adam yakan buɗe musammam gashinsa na kai, idan ka zuba ruwa a haka na iya haifar maka da ciwon kai ko wani abu daban, bayan haka sai ka debi ruwa a cikin tafin hannun ka daya sai ka zuba a kanka ka tabbatar ya game ko'ina a kanka, ka sake kanfata na biyu ka tabbatar ya game ko'ina a kanka, haka na uku ka tabbatar ya game ko'ina a kanka.

    To idan kayi wannan sai ka debi ruwa ka game dukkanin jikin ka da shi kana mai farawa da bangaren jikin ka na dama kafin na hagu, sannan na hagu ka tabbatar ruwa ya taɓa ko'ina.

    To idan kayi wannan ne ka kammala, abu na karshe shi ne sai ka wanke kafar ka ta dama sannan kafarka ta hagu shi ne cikon alwalar da ka riga ka faro. Wannan ita ce siffa ta kamala a wankan janaba.

    In wankan janaba ne haka zakayi, in na haila ne haka za'ayi inma wanka ne na biki haka mace zata yi, idan wankan jumu'a ne ma haka za'ayi, wankan idi ma haka zaka yi, banbanci kawai shi ne NIYYA.

    Idan mutum zai yi siffa ta Al-ijza' wadda ta wadatar ba sai kayi alwala acikin ta ba, kana zuwa kayi niyyar yin wanka ɗin kawai sai ka ɗauki ruwan ka watsa a jikin ka ya game ko'ina, inma wani kududdufi ne ko rami ko swimming pool sai kayi tsalle ka faɗa aciki, dama ka kulla niyyar ka kafin ka shiga, daga ka fito abinda zakayi shi ne abubuwa guda biyu, kurkurar baki da kuma shaka ruwa a hanci da fyacewa.

    Shikenan, kuma ya halasta kayi sallah da wannan wankan, Hadisi cikin Sahihu Muslim ya nuna haka.

    Sai dai wanda ya yi wanka na farko ya fika kamala saboda ya bi dukkan sharuddan, ya fika cikar kamala, ya fika lada. Kasancewar ba'ayi alwala ba ciki, wannan ka'idace ta malamai cewa karamin kari (HADATHUL ASGAR) idan sun haɗu da babban kari (HADATHUL AKBAR) to da ka kawar da babban kari, karamin ma ya tafi.

    Amma ba lallai bane idan ka kawar da karamin ace babban ma ya tafi.

    والله أعلم،

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.