Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Haɗa Wankan Jumma'a Da Na Janaba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Idan Zan Yi Wankan Janaba Da Juma'a Alokaci Guda Ya Ya  Zan Yi Niyyar Kowane? Zan Yi Niyyar Alokaci Guda Ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Idan wankan Janaba da Juma'a suka Haɗu akan mutum, wanka ɗaya ya isar masa, sai ya yi niyyar wankan janaba da na Juma'a baki-daya. Saboda fadar Annabi tsira da amincin Allah suƙara tabbata agareshi:

(إنما الأعمال بالنيات وإنما لكل امرىء ما نوى)

 Bukhari (1) da Muslim (1907)

Ma'ana " Dukkan ayyuka suna tattare da niyyoyi"

Imam Annawawi ya ce acikin Majmuu (1/368) Da'ace mai wanka zai yi niyyar wankansa na Janaba da juma'a baki-daya  wannan ya inganta"

Ibn Ƙudamah Allah ya yi masa rahama yace : "idan yayi wanka ɗaya na Juma'a da Janaba  yayi masu niyya ɗaya, ya isar masa, ba mu san wani saɓanin malamai ba akan haka"

An tambayi Sheikh Ibn Uthaimin Allah ya yi masa rahama: mene ne hukuncin hada wankan Juma'a da na Janaba?

Sai ya amsa da cewa: "Wannan babu laifi, idan mutum ya kasance mai Janaba sai ya yi wanka yayi niyyar dauke Janaba da kuma wankan juma'a babu damuwa cikin wannan, kamar yadda idan mutum ya shiga masallaci yayi nafila raka'a da niyyar raka'o'in da ake yi kafin kowace Sallah ta farilla da kuma raka'a biyun da ake duk lokacin da mutum ya shiga masallaci (TAHIYYATUL MASJIDI) to babu komai akansa.

Wannan mas'ala ba ta wuce wadannan rabe-raben guda uku (3):

1. Yin niyyar wankan Janaba kaɗai.

2. Yin niyyar wankan Janaba da juma'a.

3. Yin niyyar wankan Juma'a kaɗai.

Idan kayi niyyar wankan Janaba ya isar maka akan wankan juma'a idan ya kasance bayan hudowar rana ne, idan kuma ya yi niyyarsu baki-daya Ya isar masa kuma ya samu ladarsu baki ɗaya, idan ya yi niyyar wankan juma'a to ba ya Isar masa ga wankan Janaba, domin wankan juma'a wajibi ne ga maras hadasi, shi kuwa wankan Janaba wajibi ne akan mai hadasi don haka babu Makawa akan yin niyyar ɗauke wannan hadasi.

Wani bangare na malamai sukace: "zai yi wanka sau biyu ne" sai dai wannan zancen ba ya da madogara

Majmu'u Fatawa Ibn Uthaimin(16/137)

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments