Ticker

6/recent/ticker-posts

Wasula

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

Wasula

20. An karkasa sautuka iri biyu kowanne,

An yi baƙi, akwai wasulla sauti ne,

Masu biyan baƙi ga aiki wasula ne,

 Su wasula a zan kula ‘yan rakiya ne,

  Matuƙar babu su baƙi bai motsawa.

 

21.  Su ka shiga su ba baƙi ‘yancin motsi,

 In ka ga baƙi akwai wasal komai rintsi,

 Baƙaƙe warwatse su suke musu kimtsi,

 Shi wasali ka ba baƙi sautin motsi,

Gun furucinsa nan amonsu ka ƙarewa.

 

22. Duk wasula biyar ga Hausa ga tsarinta,

 /a/, /i/, /o/ da /u/ da /e/ sautukkanta,

 Su suka sauƙaƙa ma kowa ya karanta,

 Zanka kula a ko’ina za a rubuta,

Su ka shiga baƙin da duk aka zanawa.

 

23.  Gyara zama guda biyar zan zana su,

 /A/, /i/, /o/, guda ukun nan ka riƙe su,

 “Ado” da “abinci” duk da /a/ aka fara su,

 Inna da Ojo duba farkon zana su,

  Ga /u/ ƙarasa da /e/ babu daɗawa.

 

24.  Su wasula suna da aiki ga baƙaƙe

 Bai mai motsi ku san baƙi ko an shaƙe,

 Ko an wangale shi ga baki yaƙe,

Su ke jewaɗin jidali da baƙaƙe,

  In aka so a zana zancen furtawa.

Post a Comment

0 Comments