Ticker

6/recent/ticker-posts

Haduwar Baki da Wasula

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

Haɗuwar Baƙi da Wasula

25. A karatu na Hausa ai sai da baƙaƙe,

 Yanzu mu je ga yadda ke yi masu sarƙe,

 An yi baƙi, akwai wasal nan ya tuƙaƙe,

 Sa natsuwa a yanzu zan ɗauko baƙaƙe,

  Mu yi wasali gare su domin furtawa.

 

26. A, i, o, u, da e(n) ga dai mun gane su,

 Yanzu baƙi na ‘b’ a ɗauko mu kasa su,

 Ba, bi, bo, da bu, da be, ka ji ajinsu,

 Haka “c” za a sa ta bi su a tsarinsu,

  Ca, ci, co, da cu, da ce, dinga kulawa.

 

27. “D” na nan mu ɗora sautim wasulan nan,

 Da, di, do, da du, da de, daidai ke nan,

 To a riƙe rubuce har furucin wannan,

 Shi kuwa ‘f’ idan ya goyo wasulan nan,

  Fa, fi, fo, da fu, da fe, sai ferewa.

 

28. Kun ga akwai baƙi na ‘g’ in mun waiga,

 In dai munka sa wasullanmu ga shi g(a),

 Ga, gi, go, da gu, da ge, gara hakan ga,

 “H” ke bin baƙi na “g” gun tsarin ga,

  Ha, hi, ho, da hu, da he, iya zanawa.

 

29. Kallamu, kaka, kakalen kolon keke,

 Ka, ki, ko da ku, da ke, ba kekeke,

 Labari ya zo garan yau nan take-

 Labbo da Ladi yanzu sun zo da azakke,

  La, li, lo, da lu, da le, sai lulawa.

 

30. Sa wasula guda biyar kan sautin “j(a)”

 Ja, ji, jo, da ju, da je, ba ja-in-ja,

 Jaji, a can nag ga soja jere da aiki ja,

 Maye mai kwaɗai da idonsa kamar manja

Ma, mi, mo, da mu, da me, ba damewa.

 

31. Kan tsarin ga yanzu in dai kun lura,

An tsara baƙi akwai wasulan kara,

 Na, ni, no, da nu, da ne, Nana a lura,

 “R” na nan gabanta sa wasali tura,

  Ra, ri, ro da ru, da re, sai rerawa.

 

32. Tsarin nan a nau gani mun yo sabo,

 Za mu sako baƙi na ‘s’ mu ga nasa rabo,

 Sa, si, so, da su, da se, sai mai sabo,

 Sautin “t” ya bi su ga daɗin tarbo,

  Ta, ti, to, da tu, da te, sai tarawa.

 

33. Wawa da wawiya ba wayewa,

 Gun wauta da ɗimuwa sai zurmawa.

 Wa, wi, wo, da wu, da we, ba wahalarwa,

 Yaro ya yi yunƙuri don miƙewa,

  Ya, yi, yo da yu, da ye, aka yayowa.

 

34. Zanka kula a ko’ina za ka yi zage,

 In ka ga an sako baƙaƙe, to rege,

 Saitin za ya zo a ƙarshe bari hange.

 Za, zi, zo, da zu, da ze, zabura zage-

Dantse don ka hardace ba wahalarwa.

 

35. Ka ga haɗin baƙi, wasulla ga zubinsu,

 Baƙaƙe Ƙi-jima ne a kai ta misalinsu,

 Sai wasulla da sunka ciccika sautinsu,

 Kalma ba ta zaunuwa sai in ga su,

  Daɗa sai yunƙurin haɗawa, zanawa.

Post a Comment

0 Comments