Ticker

6/recent/ticker-posts

Abajada

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

Abajada

15. Gun harshe a yo rubutu tilas ne,

 A sanin ƙa’idarsa kana farilla ne,

 Shi ko aro a raya harshe tsari ne,

 Hausa ƙidan baƙinta a, b, c, d, ne,

  Haka nan ta aro shi can gun Turawa.

 

16. Zan fara da sa baƙaƙe a kula su,

 A kiyaye su bi-da-bi kan tsarinsu,

 Akwai ƙi-jima [1]ka ga nan ga tsarinsu,

 Su aka ce wa sauƙaƙa sai ka biya su,

Su duka goma sha bakwai babu daɗawa.

 

17. Sa mini /b/ da /c/ da /d/ ga /f/ ga /g/,

 Lissafin baƙi biyar ke nan har /g/,

 In ka lura tun da /b/ ya zuwa /g/,

 Ƙara kula yanzu bayan sautin /g/,

Ga mu da /h/ da /k/ da /l/ /j/ ka biyowa.

 

18. In ka lura ka gwane kan bitarsu,

 Sauti tara ne ka ƙara duba jimillarsu,

 /M/ na nan da /n/ da /r/, /s/ ke bin su,

 Nan ƙasa ga waɗansu sa su a jerinsu,

/T/, /w/, /y/, da /z/ ga ƙarshen ƙirgawa.

 

19. In ka lisafa su sun kammala daidai,

 Saɓanin hakan ga sai dai in ko dai,

 An yi kure na kama lisafin daidai,

 In ka gane su ka wucce Allah waddai,

Sun zama sha bakwai baƙaƙen Hausawa.[1] Baƙaƙe ƙi-jima su ne baƙaƙen da suka kasance tilo kamar /b/ da /c/ da makamantansu, wato koma bayan masu goyo kamar /kw/ da /gy/ da makamantansu.

Post a Comment

0 Comments