Ticker

6/recent/ticker-posts

Tagwayen Bakake

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

Tagwayen Baƙaƙe

53. Baƙaƙen ƙi-jima ka ji sauƙaƙa ke nan,

 Su ne muka bibiya a babi na ɗayan nan,

 Duk furucinsu guda-guda ne su ɗin nan,

 In aka ce ‘tagwai’ baƙaƙe biyu ke nan,

  Masu zuwa a tare can gun zanawa.

 

54. Za su taho a jere ga wasali ƙarshe,

 Gun furta su nan amonsu ya zo tarshe,

 Ba wasali tsakansu sai dai daga ƙarshe,

 Zanka kula da wanga tsari ko yaushe,

  Dole su zo hakan gabanin furtawa.

 

55. Yanzu biyo ni za ni zano siffarsu,

 In muka ɗauki ‘k’ da ‘w’ mun ka haɗa su,

 ‘Kw’ ke nan kamar a kalmar kware” su,

 Ke nan dai ‘k’ da ‘w’ an manne su,

Sun zame ‘kw’ tagwan baƙi babu musawa.

 

56. Akwai wasulan da ‘kw’ ya zam bai kamawa,

 Ka taɓa jin ‘kwi’ ‘kwe’ ga bakin Hausawa?

 Duba misalan da ke biye don ganewa,

 Ka ga muna da Kwaire, kwasau, kwantawa,

Lura akwai Kwari, Kware ga kwashewa.

 

57. In aka ɗauki ‘g’ da ‘w’ an ka haɗa su,

 To sun komo baƙi guda ne tsarinsu,

 Akwai wasullan da ba sa taɓa bin su,

 Lura da ‘g’ da ‘w’ in ka haɗe su,

  Sai a kira su ‘gw’ ga tsarin furtawa.

 

58. Ga Gwafadi, Gwanda, Gwaiba da Tukwane,[1]

Ga gwanjo, agwada sa gwado duk sutura ne,

 Ga Gwadabawa, Gwandu ga Gwashi birane,

 Gwaggo, gwaggiraɓe suna na mutane ne,

Ga gwauro da gwauruwa sai ganawa.

 

59. ‘S’ na zuwa ga ‘t’ su zam tare tsaye,

 Sai su zamo baƙi guda ka ji tagwaye,

 Gun furucinsu ‘t’ ta zo sai ‘s’ goye,

 Gamuwar ‘t’ da ‘s’ wurin nan a kiyaye,

Su muka ce wa ‘ts’ ga furucin Hausawa.

 

60. ‘Ts’ na ɗaukar dukan wasal in an jero,

 Tsa, tsi, tso da tsu da tse in an tsaro,

 Duba misalai a nan ƙasa an tsattsaro,

 Za ka rubuta tsamiya, tsawa, tsoro,

  Tsufa, tsegumi bala’i yaka sawa.

 

61. Akan ma haɗa ‘s’ da ‘h’ wajen furta su,

 Sai su haɗe su zam baƙi ɗaya duba su,

 Za a haɗe su jumlatan don furta su,

 Harafin ‘s’ da ‘h’ idan an gwama su,

  Sun zama ‘sh’ ga Hausa gun zanawa.

62.  Dukkanin wasal sukan bi masa shirye,

 Sha, shi, sho, shu, da she bi su a shirye,

 Duba misalansu nan ƙasa don ka kiyaye,

 Shanun Sharubutu shuka suka cinye,

  Shashashan shina gani bai korewa.

 

63. Haɗuwar ‘g’ da ‘y’ halas ne ga rubutu,

 Sai mu kira su ‘gy’ ga tsari na karatu,

 Sa wasali gare shi kominsa ya saitu,

 In aka sa wasal garai sai ko ya furtu,

Nan muka samu ‘gy’ tagwai mai dacewa.

 

64.  Ka ga a ‘gy’ ‘a’ kaɗai ake iya ɗorawa,

 Ba a ‘gyu’, da ‘gye’ ga tsarin Hausawa

 Ku duba misalai a yanzu domin ganewa,

 Gyashin gyatuma gyaɗa na tasowa,

  Gyartai shi ka ɗinka ƙorai ɗinkewa.

 

65. Ka ji ajin tagwan baƙi ga bayaninsu,

 Harhaɗa sautuka ake gun furta su,

 Ka ga akwai ‘kw’ da ‘gw’ cikin tsarinsu,

 Sa mana ‘ts’ da ‘sh’ da ‘gy’ ka ji cikonsu,

  Ga jimillarsu su biyar gun ƙirgawa.

 

66. Sai dai su tagwan baƙi gun zanawa,

 Kwai wasulan da ko kaɗan ba a sakawa,

 Ka ga da ‘kw’, da gw rinƙa kulawa,

 Bisa tsarinsu in wasulla aka sawa,

  Wasalin ‘a’ ka barbararsu ga zanawa.

 

67. Sai sauran tagwan idan an duba su,

 ‘Fy’, ky, ƙw da ƙy da ya ne a zubinsu

 Su duka goma ne a duba jimillarsu,

 Harufan ‘ts’ da ‘sh’ idan an duba su,

  Ba wasalin da za su tadan furtawa.



[1] Da “Gwafari” da “Gwanda” da “Gwaiba” da “Tukwane” duka sunayen ƙauyuka ne da ke mabambantan ƙananan hukumomi a jahar Kebbi a Nijeriya. Gwafari tana ƙaramar hukumar Suru-Ɗakingari. Gwanda tana ƙaramar hukumar Maiyama. Gwaiba da Tukwane suna ƙaramar hukumar Koko-Bese.

Post a Comment

0 Comments