Ticker

6/recent/ticker-posts

Rana ta kan zo wacce za a tare kare,

Rana ta kan zo wacce za a tare kare,

Rana ta kan zo wacce za a tare kare,

Ya yi taimako har martabar sa ta bayyana.


Girman ka ko ƙan-ƙan ka ba ya nu na kai -

Wani ne idan da abin waninka ka dangana,


Ita rayuwa da a ke ta yin cece kuce,

Ba ta yuwa sai an haye wa karan tsana.


Duk wanda yai rainin wurin kwana na ka,

Ka sanar da shi rana ta kan tuna rana.


Bawan da bai da wurin zama ko kyan tufa,

Wataran ya kan zama mai kuɗi yai suna.


Ya zamo cikin wannan da sunkai watsiya,

Da batun shi sarki mai kirarin suna.


Kuma dole ne su ishe shi sui masa magiya,

Ya yi ko bari zaɓinsa ne su yi dangana.


Ko ba su so, ko da da so dolensu ne,

A ƙasan sa za su yi shimfiɗarsu su zauna.


To kunga ƙan-ƙan ya zamo girman da da-

Ba ya da girma ko a ganshi a nuna.


Mu kula da haƙƙin ƴan'uwa na ƙasanmu don-

Wataran ta yu a ƙasan gininsu mu zauna.


✍️⁩Maisugar Ringim (رسول الأدب)
09123098967
ringimmaisugar@gmail.com

Post a Comment

0 Comments